Showing 54001 words to 57000 words out of 77288 words

Chapter 19 - ABARI YA HUCE Complete 1,2,3,4 Book by Sumayya Abdulkadir Takori .txt

Advertisement

da musulmi sai yaudara da soyayyar manufa).
Jikinsu ne watakila ya ba su ana kallonsu, su duka suka juyo a razane, amma abinka da nasara da babu digon kunya ko tsoron Allah a tare da shi, sai suma suka zuba mishi idanun.
Ya yi saurin dauke idonsa ya fito falon ya barsu a nan. Ya zauna cikin kujera yana fidda wani irin wahalallen numfashi yana fesarwa da kyar, yana shaka da kyar.
Idan wani ya fada mishi Harrit zata yi mishi haka ba zai taba yarda ba, ya godewa Allah da bai taba kusantar Harrit ba tare da ya yi amfani da kwaroron-roba ba. A take ya fiddo takarda ya dora biro ya rubuta mata sakin aure kamar yadda addininshi ya tanada.
Ya leka waje ya kira Raymond da Franklyn ya ce, ya ba su minti goma su fitar da duk wani abu da ke cikin gidan su loda mata shi a waje.
Ya leka dakin ya cilla mata takardar sannan ya kara fadi mata da bakinsa cewa ya sake ta saki uku. Ko babu sakin dama auren ya riga ya gurbata a nashi addinin. Ya kuma sanar da su minti goma suka kara yi mishi cikin gida 'yan sanda ne za su raba shi da su.
Harrit sai kuka ta ke tana ba shi hakuri, ta kama kafafunshi ta rike tamau! Jan gashinta (blonde) ya baje a bayanta da fuskarta kamar na mahaukaciya. Tuni kwarton nata ya gudu, ta gaban Amiru ya rarrafa ya wuce da rigarsa a hannu, da ya ga ya iso kofa lafiya sai ya taka da gudu iya karfinsa ko motarshi bai dauka ba. Su Raymond ne ke cika umarnin ubangidansu. Masu fushi da fushin wani. Fatali kawai suke da komai dake cikin gidan. Ya fizge kafarshi cike da kyama yana ja da baya tamkar ta dana masa garwashin wuta, a baya in Habibu ya ce kyamar Harrit yake mugun haushinsa yake ji, amma a yau ji yake har zuciyarshi na tashi da kallonta, ya fice babu waiwaye yana mai kara jaddada mata cewa, kada ta sake ya dawo ya ganta ko wani tsinkenta a cikin gidanshi.


Bai kara bi ta kan Harrit ba, don ya lura idan ya ce bakin cikinta zai sa a ranshi shi ne zai cutu a banza. Amma alal hakika Harrit ta sanya kasar America ta fice mishi a rai. Dan burbushin kewar kasar da ya rage a baya ya kara zagwanyewa
Ya samu kanshi da rashin yarda da kowa, hadi da shi kansa kuwa. Mairo ce kadai yake tunawa ya ji sanyi a zuciyarshi. Itan kam ya yarda da ita da wata irin yarda da bai taba yiwa kowa ba bayan Habibu in ka cire iyayensa, bayan budurcinta data kawo masa cikin girma da daraja, yana da wata irin yarda akanta, yana samun wata irin nutsuwa a duk lokacin da yake tareda ita. Amma ita kanta Mairon a yau sai yaji bazai iya magana da ita ba. Don haka ya kashe dukkan wayoyinshi.


Cikin sati daya rak! Duk abin da ya kai shi ya gama shi, hankalinshi ya yo gida kwarai, amma dole ya biya wajen Habibu maganar karatun Mairo.
Don haka daga Washington kai tsaye Michigan gidan Habibu ya nufo a Detroit. Habibun ya je da kanshi filin jirgi ya taho da shi.
Hakika idan ka dube shi zaka lura cewa, a razane yake, a firgice da al'amarin mata. Ita ma Mairon sai yake ganin kamar kafin ya koma zata yi mishi haka! Don haka ya kulle kanshi a hotel din (RAMADA INN) tare da kulle wayoyinshi don ya samu daidaituwar kwakwalwarshi da tunaninshi. Ba abin da ke tashinshi daga shimfidarshi sai sallah da cin abinci, shi kansa Habibu bai san inda ya shiga ba.
Tsayin sati guda sannan ya samu ya yi 'regaining consciousness'. Sannan ya nufo gidan Habibu. Habibun ya ganshi kamar daga sama, koda wasa bai yi gigin fada mishi abin da ya faru ba, don yasan dariya zai yi mishi, dariya har da ta keta, tunda babu yadda bai yi ba ya nuna mishi illar da ke tattare da auren mushrikiya, amma Amirun bai gane hakan ba, sabida giyar soyayya na dibanshi a wancan lokacin, don haka idan yana da kunya ai ba zai neme shi ba. Da ya tambaye shi Harrit sai ya ce da shi, sun rabu ta koma Philppines, bayan idan za a kashe shi bai san inda ta nufa ba.


Dina na kicin tana hada musu abincin dare, a yayin da su kuma suke baje a falon suna aikin takardunsu cikin systems.
Kallo daya Habibu ya yi mishi ya tabbatar yana cikin wani bacin rai mai zurfi, ya yi tambayar duniyar nan amma zurfin ciki irin na Amiru ya hana shi fadar abin da ke damunsa.
Shi kuma Habibun ya takura sai ya ji, daga karshe ya yanke shawarar fada mishi ko da kuwa zai yi mishi dariyar ne, akalla ya samu rangwamen radadin da zuciyarshi ke yi da nauyin da ya danne ta.
Habibu ya yi shiru, can kuma ya ce
"Ban yi mamaki ba. Shi arne wannan (adultery) a wajenshi ai ba wani abu ba ne extraordinary. Sai a yi hattara, Allah Ya kara tserar da mu daga kutungwila da kaidin ZUCIYA.
Amma ni a ganina wannan ba wani abu ba ne da zaka sanya shi a ranka har ya haifar maka da hawan jini, tunda ka san abin da ka aura ai ka aura din. Sannan sabawa mahaifa ai ba abin da ba zai janyo mana ba mu 'yan Adam, don haka sai mu yi fatan Allah Ya kiyaye gaba, Ya sa mu gama da duniya lafiya".
Ya ce.
"Ina son farantawa Mairo Habibu, kamar yadda ta ke haifar min da nau'o'in farin ciki a kullum. Don haka nake ganin zata dawo nan ta karasa karatunta kamar yadda ta faro shi cikin nasara.
Ba zan bari ya kasance ni din na yi silar rabata da burin rayuwarta ba, da tubalin da ka jima kafin ka assasa. Don ko a yanzu na fita na dawo kullum sai na ganta tana bitar littafanta, duk da cewa bata taba yi min korafi akan hakan ba. Ni da na yi mata na ga farin cikinta fiye da kullum, tayi min abinda bata taba yi ba, idan na samu sarari zan dinga lekowa akai-akai insha Allahu".
Habibu ya ji dadin wannan karamci da Amiru ya yi mishi, don shi ma abin yana damunshi, don bai san tsarin sa bane shi yasa tun farko bai neme shi da zancen ba. Don haka a washegari suka nufi Michigan State University tare don gyara mata registration dinta.
Ya rage saura kwana uku Amiru ya dawo, Hajiya ta yi kiran Mairo, ta hadata da wasu jarkokin magani da zuma roba guda da Mairo ba ta san ko na mene ne ba. Ta ce, ta je ta yi ta kwankwada, ta kawo mata jarkokin kafin kwana uku.
Ta bi umarnin Hajiyar don tasan ba zata ba ta abin da zai cuce ta ba, bare wannan magani mai shegen dadi da zaki.
A'ah! Ai tun a washegari ta ji yanayin jikinta na sauyawa, ba abin da ta ke bukata sai dawowar Ameeeru, da yake saukar karfe shidda na yamma za su yi, don haka tun safe tana kicin dinta tana hada abincin tarbar angon nata.
Da taimakon daya daga cikin masu aikin Hajiya da Hajiyar ta bata don su Sabah duk sun koma makaranta, komai ya hadu.
Babu yadda Hajiya ba ta yi ba ta je airport ta tarbo shi ba, amma kunya ta hanata. Wannan na daga cikin halayen yarinyar da suke kara mata kaunarta.
Ta lura bayan kunya, tasan mutumcin kanta, kuma ta iya zama da kowa da wata mu'amala ko ya ya ta hadata da shi.
Tana sassan Hajiya suna sauraron labaran MBC a lokacin da ya iso, daga bakin kofa ya tsaya, ya tokare kofar da hannunshi na dama yayin da na hagun ke dauke da falmarar din ‘Italian suit’ ruwan toka, wato 'grey' da ke jikinshi.
Ya rausayar da kai yana kallonta, da kyawawan idanunshi, ba tare da ita din ta sani ba. Sassanyan kamshin 'miyaki' da ya bakunci hancinta shi ya ankarar da ita tsayuwarshi a bakin kofar n wasu mintuna.
Ji ta yi kamar an yi mata gafara sabida farin cikin dawowarsa cikin koshin lafiya. Ta lumshe ido ba tare da tasan lokacin da ta yi hakan ba. Hajiya tana ta magana, amma ba ta ji Mairo ta bata amsa, sun yi nisa a kallon junansu kamar yau suka fara ganin juna.
Ta juyo don ta dubi Mairo, a sannan ne ta ankara da inda Mairon ta kafa wa ido. Ta ce "Au, ashe mijinki kika gani kika manta da ni nake ta sambatu ni kadai?".
Ya yi dariya ya idasa shigowa dakin. Ita kuwa don kunya sai ta zame ta gudu gidanta ba ta kara lekowa sassan Hajiya ba.
Tana shafa a gaban mudubi, ga dukkan alamu daga wanka ta fito. Daure da tawul iya cinyoyinta. Ya bude kofar ya shigo cikin bakaken pyjamas, tana hango shi ta cikin mudubin a lokacin da ya iso gare ta. Ya dora kai a hankali kan kafadunta ta baya, kyawawan fuskokinsu suka bayyana cikin mudubin a jere, a hankali ya sanyata cikin jikinshi ya lullube da hannayenshi, yana shakan sassanyan 'bathrobb' dinta na ‘rasasi’ yana lumshe ido. Ya ce
"Tell me how much you misses me, ko ba ki yi kewata ba ne Mairo? Don na ga ke har wata kiba kika kara abunki, ni kuwa ina can tunaninki ya hana ni sukuni".
Murmushi kawai ta yi har 'beauty point' din mai kara mata kyau ya lotsa ciki sosai. Ya sumbuci wajen with a very warm kiss, kana a hankali ya soma warware mata tawul din suka soma aikin lada.


***


Wata guda da dawowarshi, suka yi shiri suka nufo Kano don yi wa Baffa sallama, kasancewar a cikin satin ne zata koma Michigan. Su Habiba an shiga makarantar ta nutsu don yanzu Mairon da suke wulakantawa ta zame musu uwargijiya da bazarsu suke rawa.
(To ina ruwan Allah!)
Tuni aka sa Lawan ya gyare musu dakin baki, ya kunna 'burner'. Abinci kam sai wanda suka zaba. Baffa ya ji dadin ganin yanayin da Mairon shi ke ciki, ta cika ta yi bul, ta zama babbar mace, kamar kajin Agric jawur da ita.
Ya tarasu duka ita da Amirun ya yi musu kyawawan nasihohi akan rayuwa, da kuma yadda za a yi a ci ribarta. Ya kare da yi masu nasiha akan muhimmancin riko da sallah akan lokacinta.
“Ita ce idan ta yi kyau dukkan ayyuka za su kyautata”. Amiru na son Baffan Mairo, sabida sauran mazan jiya ne ba na yau ba, irin wadanda kyale-kyalen duniya ba sa gabansu. Ya cika su da alheri duk gidan, a washegari suka nufo Michigan.


Dina ce ta zo ta tarbe su, domin Habibu ya yi balaguro zuwa New-Jersey. Mairo ta rungume 'ya'yanta kamar ta tsaga kirjinta ta sanya su. Suna fada mata,
"Mun yi missing dinki Anti Mairo, da gaske ne da Daddy ya ce anyi miki aure da Uncle Amiru???" Inji Bedi.
Murmushi ta yi, cikin matsanancin nishadi tana shafa kan yaron, amma ba ta amsa musu tambayar ba. Amirun ne ya ji, ya juyo daga maganar da suke yi da Dina ya bashi amsa cikin daga gira.
“yes Muhammad da gaske ne, Daddy is absolutely right! Har ma ta kusa ta kawo wa little Mairo kanwa, nan da wasu watanni kadan”. Da sauri Mairo ta bace a wurin.


A ranar Amiru ya juya Washigton don karasa wasu hidimominsa tare da jaddawa Dina amanar rayuwarsa, wato Mairon da ta dusar da hasken sauran matan duniya baki daya daga idanunshi.
Sun kulle a daki ita da Dina ana labarin bayan rabo. Dina ta kura mata ido ta ce
"Anya Mairo? Jikin nan naki babu bayani? Irin wannan fari da kyau haka sai ka ce mai shafe-shafe? Ko dai kwanan nan za fara goyo ne? Naji Amiru na fadawa yara dazu na dauka wasa yake"
Mairo ta rufe fuska da tafukan hannunta, ta ce "Kai Anti Dina, wallahi ba ni da komi. Karewa ma yanzu haka period nakeyi. Ni fa tunda na je gidan dakina daban nashi daban. Kuma ba sai ana kwana daki daya ne ake yin cikin ba?". Dina ta kyalkyale da dariya ta ce.
"Amirun? To abar kazar cikin gashinta tunda ba kya son a fige ta kada in zama babbar banza".
Ta jawo lokarta ta soma fiddo mata magungunan mata masu kyau da tsada 'yan Indonesia data ke saya tana yi mata bayanin tsarin shan su.
Mairo ta ce
"Maganin mene ne?"
Dina ta murmusa, ta ce, "Maganin basir ne, ke dai ki dinga sha don da alama akwai basir a jikinki tunda ga shi nan duk kin yi fari".
Mairo ta yi dariya. Ta rasa dalilin da yasa kullum Dina ke treating dinta yarinya kamar Little Mairo.
Idan dai wadannan magangunan ne ai tunda ta zo gidan ta ke ganin Dinan na shansu, sai dai ba ta taba tambayarta ko na mene ne ba. Amma yanzu ai ta yi girma da hankalin da zata san amfaninsu.
Daga baya ko me Dinan ta tuna? Ta zaro ido ta ce "Ke! Bani magungunan nan bai kamata ki fara amfani da su ba, sai mun je asibiti anyi checking dinki don ban yarda da ke ba. Mai juna biyu ba ta amfani da irinsu".
Mairo ta bata fuska kamar ta yi kuka, don gani ta ke kamar Dinan na kallon abin da ta ke yi a goshinta. Ta tashi gudu tayi dakinta.
Dina sai ta yi dariya, kuruciyar Mairo da halayenta na alkunya suna burge ta matuka.


Satin Amiru daya da tafiya sai ga shi kamar an jefo shi. Tana kicin tana hadin salad don haka Dina ce kadai a falo, ita ma ba ta jima da dawowa aiki ba, ta sanya Mairon ta hada mata salad zata ci.
Kararrawar kofar shigowa ta yi kara, ta umarci Lynder ta bude. Amiru ya bayyana a falon cikin bakaken suit-spanish. Ta daga kai tana kallonshi tare da amsa mishi sallama, ganinshi wani 'as a smart pace' (afujajan) ya bala'in ba ta dariya.
A gajiye ya zauna cikin kujera idanunshi a kwance ya ce "Dariyar me kike yi min?"
Ta ce "Ganinka na yi kamar an jefoka, lafiya dai ko?"
Ya ce "Da babu lafiyar ai ba za ki ganni ba, sai dai sako. Ina kanwar takin nan ne? Yanzu haka kina nan kina hadata da wadannan girke-girken naki na tsiya".
Ta ce "Au na tsiya ne, amma idan an baka kake ci?"
Bai amsa mata ba ya nufi kicin inda ya jiyo motsin tangaraye.
Ta juya baya ta takarkare tana bude gwangwanin 'heinz-beans' ya mika dogayen hannuwanshi ya rungume ta. Ya soma sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Kwanaki bakwan nan da ya yi ba tare da ita ba, jinsu ya yi kamar shekaru bakwai. Ka zalika ita ma Mairon, don dai ta kasance mai zurfin ciki da kawaici ne. Amma ta yi missing din mijinta yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba.
Sun yi nisa cikin duniyar faranta ran junansu, kafin Mairo ta ankara da inda suke, ta yi kokarin kwatar kanta. Ya dago habarta da hannun damanshi yana son kallon kwayar idanunta, amma bai yi nasarar hakan ba sabida matsananciyar kunyarshi da ta lullube ta. Ta yi azamar hankade shi sabida warin 'aspen' da ta tsinkaya cikin bakinshi.
Ya sake kamota ta fuzge, ya ce, "Haba Mairo? Mairon Dina, Mairon Yaya Habibu?"
Zata fice ya sha gabanta a galabaice, ya ce, "Kina so Mala'ikun rahma su soma tsine miki ko, bayan da kina ta kwasar lada?"
Inda abin da Mairo ta tsana to wannan furucin ne, kamar ta yi kuka ta ce,
"Ni na ce ka sha taba?
Tun a gida ka ce min ka daina sha, amma ai ga shi nan na ji-ta a bakinka".
Ya rufe mata baki, ya ce, "Wallahi bazan kuma ba. Wannan din ma a jirgi aka ba ni. Ba kudina na sanya na siya ba. Ce miki nayi “bazan kuma sayen taba ba”, ba “bazan kuma shan taba ba..” Sun ba ni 'wine' ne, ni kuma na ga da na shata ai gara na sha tabar".
Ta zumbura baki, tana toshe hanci ta ce.
"Ni don Allah ka ba ni hanya na wuce..."
Amma fa banda kaduwa ba abinda jikinta ke yi, Amiru ya bala'in sanin 'weakness' dinta. Karfin halinta da jarumtakarta suna ba shi mamaki. Kiri-kiri ga shi tana cikin kewar mijinta, a idanunta da gangar jikinta, amma a fatar baki ta nuna ba haka ba ne.
“Ko in baki (hanky) ki toshe hancin da kyau??”
Kanshi ya tura cikin gashin kanta ta baya, bayan ya cillar da 'bound' din da ta daure gashin da shi. Yana shakar kamshin kumfar 'pert-plus' da ta ke amfani da shi ba tare da ta sa wa gashinta 'relaxer' ba. Amma sai ka rantse kullum 'relaxer' ta ke shafa mishi.
Can cikin kunnenta yake rada mata. "Rakiya za ki yi min Mairo".
Da sauri ta ce
"Zuwa wajen budurwarka?"
Ya yi dariya, ya ce.
"Ga budurwata nan ina tare da ita, shopping zan yi".
Ta ce "Ni ba zan bika ba kullum kana yawo da wadannan gardawan masu shegen kallon tsiya kamar wasu 'body-guard' dinka". (Raymond da Franklyn).
Yayi dariya. Ya ce
"To zan sallame su. Mu biyu zamu yi tafiyarmu, sannan ba shan Aspen a hanya, in kin ganni zan saya ki kwace credit card din, hakan ya yi miki?"
Ta gyada kai cikin gamsuwa.
"Amma kai zaka fadawa Anti Dina".
"Idan don wannan ne, ta kwana gidan sauki, uuwata ce ita ko kanwar ubana? Daga kawo ajiya?”
Abin ya bata dariya amma ta gimtse.
"To bari na karasa hada mata salad din, yunwa take ji".
Har zuwa lokacin bai sake ta ba, ya bi ya kankane ko'ina na jikinta. Sai faman sunsunarta yake yi kamar zai hadiyeta. Sai da ta hada da magiya sannan ya sassauta rikon da ya yi mata.
Tare suka fito ta isa ga Dina ta mika mata farantin, ta nufi dakinsu don ta kimtsa.
Wanka ta sake ta zuba riga da siket na wani material yellow mai santsi, ta nada dan bakin mayafi a kanta, ta matse da fil ta kara feshe jikinta da turaren (fahrenheit). Tana kokarin saka takalmi ta jiyo Dina na kwala mata kira, don haka ta dauki jakarta 'polo' mahadin takalmin da ke kafarta ta fito.
Ba ta san me ya fadawa Dina ba, ta ce
"Amiru ya ce za ki raka shi shopping ko? To sai kun dawo".
Suka hada ido ya daga mata gira, ya kashe ta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login