Showing 27001 words to 30000 words out of 60293 words

Chapter 10 - WATA BAKWAI BOOK COMPLETE by Lubna Sufyan.txt

19 Feb 2025

11636

likita ya fito daga dakin da Nas yake. Tashin dayai ne yasa husna bude idanuwanta dan yama manta tana jikin shi.


Girgiza masa kai likitan yai. Wani jiri yaji ya dibe shi.........!




💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


2⃣6⃣


TO THE READERS!!!


Bango ya dafa dan ya kusan faduwa. Husna ce tai karfin hali cikin rawar murya ta ce ma likitan.


"Ya dai?"


Ya bude baki zai magana wata Nurse ta fito da gudu ta kirashi.Ai bai saurare su ba ya koma ciki.


Prince ishaq gani yai bazai iyaba. Husna yabari tsaye ta jingina da bango ya tura kofar ya shiga. Ihu zasu fara masa ya fita, ya zaro I.D card dinshi ya nuna ma daya daga cikin likitocin.


Safar hannu kawai suka mika masa. Baima damu da saka abu ya toshe hancin shi ba. Na.urar dake gefe ya kalla.


Addu.o.i yake karantawa dan gaba daya yagama karaya. Bugun zuciyar Nas cikin dari yana kan sha biyar. Yana tsoron taba shi. Saidai yasan bazai taba yafewa kanshi ba inhar bai kokarta da wani abu ba.


Rayuwa da mutuwa duk yana hannun Allah.


Wani irin ciwo ne gefen kanshi da har kashin wajen kana hangowa.


Aikin shi ya ci gaba dayi tare da sauran likitocin na dinke dinken ciwukan dake cikin shi. Yankan wukane.


*


Husna kam da taji su shiru. Karasawa tai wajen glass din tana kallon su. Kanta wani irin ciwo yake yi.


Ga hawayen daketa zubo mata. Bata taba ganin tashin hankali kwatankwacin nayau ba. Prince ishaq take kallo yanata kai da kawowa. Batasan iya awannin da suka dauka ba. Sannan suka fito.


Da sauri ta karasa inda prince ishaq yake. Idanuwanshi sun wani canza launi. Sai taga harya rame saboda tashin hankali.


Da idanuwanta take rokon shi yace mata Nas lafiyar shi kalau. Yace mata bai mutu ba.


Jikin bangon ya jingina a hankali ya zame zuwa kasa ya hade kanshi da gwiwa. Husna ta tsugunna gabanshi. Hannunta na rawa ta dafa kafadarshi.


Dagowa yai ya kalleta kyawawan idanuwanshi cike taf da hawaye.


Mayar da kanshi yai ya hade da gwiwar shi.


Yanda numfashin shi ke fita ne tasan kuka yake. Jitai zuciyarta ta sake karyewa itama zama tai kusa dashi.


Batasan me zatai masa ba saboda batasan me yake jiba. Idan har ita dabata hada komai da Nas ba tana jin wannan dacin a ranta. Shi kuma me yake ji.


Hannuwanta ta saka kan kafadun shi. Prince ishaq kam wani abune ya tsaya mishi a wuya.


Wani irin ciwo zuciyarshi take masa. Kirjin shi ya masa nauyi. Saboda har yanzun zuciyar Nas bata da karfi. Huhunshi bashida karfin taimaka masa wajen numfashi sai da na.ura. A minti daya komai zai iya tsayawa. Yanajin duk abinda yake samun kowa laifin shine. Shi ake turo ma kashe di.


Yakamata ace ya janye daga karbar mulkin nan dayai. Tun akan huddy baiji kashe din ba. Gara ya rasa komai. Abar masa kaninsa. So yake wani ya rike shi ya lallashe shi.


Har cikin zuciyarsa so yake wani ya girgiza shi yace masa komai zai zama lafiya kalau. Nas zai ji sauki. Za a daina kokarin kashe su saboda za.a kama koma wanene su samu shaida a hannun su.


Jin hannuwan Husna kan kafadarshi yasa shi dagowa. Ganin hawayen dake bin fuskar shi ba karamin girgiza husna yai ba.


Tasan maza manya na kuka in abun yakai inda yakai. Amman yanayin prince ishaq yakan nuna zai iya daukar komai duniya ta jefe shi dashi.


Zai iya jure duk wani kallo da kaddara zatai masa. Batasan lokacin datasa hannu tana goge masa fuska ba. Hannuwanta ya ture alamar ta kyale shi baya so.


Kai kawai take girgiza masa tana maida hannunta tana ci gaba da goge masa fuska. Zamanshi ya gyara.


Wani irin karyewa yaji zuciyarshi tayi. Hannuwanta ya ture ya dora kanshi kan kafafuwanta.


Tsayawa tai tana kallon shi na yan mintina kamun ta dora kanta akan bayanshi.


Su dukansu kuka suke. A wannan lokacin ba tare da saninsu ba abinda suke ji ya kulla alaka.


Kaman yanda aurensu ya kullu a bisa kaddara haka kaddarar data fada ma Nas ta kulla alaka a tsakanin su.


Sun shafe wajen awa daya a hakan kamun husna ta tashi daga bayan shi.


Ta daukama bacci yake taga ya motsa. Bayanshi tadan bubbuga muryarta a dishe tace. Ka tashi.


Bai mata musu ba ya dago daga jikinta ya sauke mata idanuwanshi da suka kumbura. Abinka da farar fata. Fuskar tai ja. Kayanshi duk jini ne.


"Muje gida kai wanka ka sake kaya"


Ta fadi muryarta na rawa. Dan bata so hankalin shi ya dawo jikinshi yaga jinin dan uwansa.


Girgiza mata kai yai alamar a.a.Dan gani yake yana tafiya daga asibitin Nas mutuwa zaiyi.


"Ina wayarka"


Ta bukata. Hannunshi yasa a aljihunshi ya dauko wayar ya mika mata.


"Wazan kira ya dauko maka wasu kayan?"Ta tambaya.


Karbar wayar yai ya lalubo lambar kamala. Muryarshi dakyar take fita yagaya masa ya kawo masa kaya. Yasa a shiga dakin husna ma a dauko mata a hado musu da kafet din sallah.


Mintina wajen Ashirin tsakani kamala ya shigo dan saida aka kira prince ishaq sannan suka barshi ya wuto. Yana kawo musu.


*


Wani kofa ya bude kusa da dakin da Nas yake ciki. Kujeru ne da wani gadon a ciki. Sai kofa ta glass datai connecting zuwa dakin da Nas yake ciki.


Nan yabar husna zaune tana kallon yanda gaba daya jikin Nas yake jone da wasu na.urori.


Addu.a ta shiga karantowa tana masa fatan samun sauki.


Kayan jikinshi kawai ya cire ya ajiye su nan kasa cikin toilet din ya sakar ma kanshi shower.


Jin shi yake wani sama sama. Haka ya saka kayan da aka kawo masa ya fito.


Kallon shi husna tai. Yana tsaye gefe duk da a hargitse yake yayi kyau cikin black jeans da riga fara.


Gashin a harmitse ga suma yana da ita baka duk tai coil. Tashi husna tai ta karasa inda yake.


Saman goshin shi da gefen fuskar shi jini ne. Ruwa ya jika shi ya zama kaman lokacin ya goga.


"Me kai hakan?"


Ta tambaye shi. Idanuwan nan ya zuba mata kaman bazai amsa ba sannan yace.


"Wanka"


Hannu takai zata goge masa jinin dake fuskar shi ya kauce fuskar shi.


"Bana son gaddama"


Ta fadi cikin yanayin muryar dayakan mata amfani dashi wasu lokuttan.


Ita kanta mamakin yanda take son kula dashi take yi. Dan yau ya zame mata kaman wani yaro karami da yake matukar bukatar kulawa.


Kallonta kawai yake dan a yanayin da yake ji kwakwalwar shi bata da lokacin tunani.


Hannun shi husna ta kama taja shi zuwa toilet din. Bai mata musu ba ya bita.


Towel din dake ajiye sabo fil cikin leda ta bude. Ta jika da ruwa ta soma goge masa fuska dashi.


Rufe idanuwanshi kawai yai yana jinta. A gefe daya kuma yana fata da addu.ar samun sauki wa Nas.


Hannuwanta sun soma gajiya saboda ya mata tsaho da yawa. Sanda ta gama goge masa fuskar tsaf har wani nishin wahala take.


Jin ta kama hannunshi yasa shi bude idanuwanshi. Janshi tai takai wajen kujerar.


"Zauna to in fito"


Ta bukata.


Wani kasalallen kallo yai mata yace.


"I am not a kid husna....."


Wani guntun murmushi tai masa ta juya zuwa toilet din.


Alkyabbar dake jikinta ta cire ta rataye. Kayan daya ajiye ta saka cikin wani bucket dake gefe ta cika shi da ruwa.


Sabulun data gani ta fasa ta soma wanke su. Saidai sun rigada sunyi stain. Haka ta wanke iya yinta ta dauraye ta rataye su.


Alkyabbar ta mayar ta fito ta zauna gefen shi.


Kanshi ya kwantar a kafadar husna. Muryar shi can nesa yace mata.


"Ina jin tsoro sosai"


Cikin sanyin murya tace masa


"komai zaiyi dai dai in shaa Allah.Babu abinda zai same shi."


Muryarsa can qasa yace


"inajin tsoro sosai husna sunyi sanadin rabani da huddy. Bansan me zancewa su umma ba"


Sai lokacin ta kalli fuskarsa. Abinda tagani ta tabbatar ba zata taba mantashi ba har qarshen rayuwarta. Saita samu kanta da sa hannu ta taba fuskarsa.


Tana son da duk wani abu da take dashi ta nuna masa komai zaiyi dai dai.


Idanuwansa dauke da nisantacciyar damuwa.
Tun ba yanzun ba husna ta kasance mai tausayi ko ga dabbobi ballantana kuma en adam.


Hankalin prince ishaq ya koma can wani waje wani lokaci.


*


Riqe yake da hannun huddy suna jiran ambulance tazo ga mutane da suka dabaibaye su.


Duk ciwukan da suke jikinshi basu dame shi ba. Huddyn sa yake ji ita kadaice damuwarsa.


Duk wani kokari da zai iya ta fannin aikin shi a banza yake saboda baida kayan aiki.


Ciwon dake gefen wuyanta yanata zubar jini. Rigar dake jikinshi ya cire dagashi sai singlet.


Ya danne mata wajen a rikice yake fadin.


"Stay with me huddy. Eyes open. Karki kulle su"


"Yaya"


ta fadi cikin murya mai dauke da ciwon da takeji.


"Huddy dan Allah kiyi shiru karkice komai sannu yanzun taimako zaizo"


Yake fada yana tarbe hawayen dake son zubo masa.


Bata saurare shi ba tace


"yaya karka barsu su sake dauke mana komai. Karku bar musu mulkin da basu cancanta dashi ba........"


Tari ya sarqeta wanda tun tanayi harta soma na jini. Hankalinsa ya qara tashi ya tallabota jikinsa


"huddy don't give up on me please ki taimaka"


Murmushi tai masa


"I love you yaya"


"Na sani huddy nima ina sonki da yawa dan Allah karki barni."


Baiga amfanin karatun shi ba a yanzun. Saboda bashida abinda zai taimaka mata dashi.


"Damn....."


Ya rasa inda zaisa ranshi yaji dadi.


Hannunta ta dago wanda da alamun fuskarta ba matuqar dauriya taiba don azabar da take ciki.
Ta taba kuncinsa a hankali tace


"karka mantani. Ka zama cikin farin ciki yaya kamin alqawari"


Yanzun kam hawaye ne suke zuba a idanuwansa rabon shi da hakan harya manta.


"Na miki huddy na maki alqawari.


Murmushi tai


"La ilaha Ilallah........."


Ta karasa muryarta na sarkewa.Lumshe idanuwanta tayi sannan komai ya tsaya cik!


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


2⃣7⃣



*Ina godiya mai yawa ga masoyan da suke mun addua ako da yaushe. Allah ya biya muku bukatunku na alkhairi. Amin*




Ganin yanayin fuskar shi yasa husna girgiza shi ta dawo dashi daga dogon tunanin da yake yi.


Dafe kanshi yai cikin hannuwanshi yana maida numfashi da sauri da sauri.


Wayar shi ya dauko. Baisan me zaice ma su mumyn Nas ba.


Husna ya kalla idanuwanshi bayyane da duk tsoron da yake ji muryarshi na rawa yace mata.


"I don't know what to tell them, mumyn nas ta dauka zan kula dashi........"


Kasa karasawa yai ya dafe kanshi kawai yana jin kaman ace kasa ta bude ya shige ya huta da wannan nauyin da yake kanshi.


Husna bata san me zatace masa ba ko kuma taya zata rage masa abinda yake ji.


Wayarshi ta soma ringing. Ya duba umman shice. Kai ya shiga girgizawa kaman tana ganin shi.


Hakan yasa husna duba wayar ta ga wayake kira. Dagawa tai ta mika masa.


"Kai mata magana kawai. You can do this"


Jikinshi babu wani kwari ya kara wayar a kunnen shi yai shiru.


"Babana kana lafiya?"


Umman ta fada da rauni a muryarta. Sai yaji ya samu wani dan karfi kadan jin muryarta.


Cikin karfin hali yace.


"Mungode ma Allah umma...... Mumy fa?"


Yanajin ajiyar zuciyar data sauke sannan tace.


"Tun dazun kamala ya fada mana abinda ya faru. Mai martaba yace adan dagata tukunna muzo saboda yanayin tsaro. Ita tace tunda kana tare da Nas tabar ma Allah komai"


Lumshe idanuwanshi yai yanajin kaman mumyn Nas a gabanshi tai maganar. Yana kuma jin nauyin girman da ta dora masa.


"Allah yasa umma. Kuyita addu.a shi kadai Nas yake bukata a yanzun...... "


Yanda yai maganar ne yasa tace masa.


"Ya Naseer din?"


Yasan ma.anar tambayarta saboda yajita a muryarta. Bataso kai tsaye ta tambaye shi idan su saka rai da tashin Nas ko kuma su soma shiryama zuciyarsu hakuri dashi.


"Umma zan kiraki in an sami wani ci gaba"


Ya fadi yanajin yanda ta furta.


"Ya Allah.... "


Kamun ya kashe wayar. Dan yana tsoron tambayar datai masa.


Tun da suka shigo asibitin nan yake kokawa da zuciyarshi kan wannan tambayar.


Jiyai cikinshi ya wani kulle ya gyara zaman shi ya dora kanshi a cinyar husna yai shiru kawai.


Kyale shi tai. Tunda batada hanyar da zata rage masa abinda yake ji. Wacece ita da zata hana shi yin abinda yaji zai iya ya samu saukin zuciyar shi.


*


A asibitin sukai sallar isha.i. Duk yanda likitoci suka bashi magana kan cewa yanayin Nas a yanzun stable ne.


Suna kuma addu.a da fatan ya tsaya haka a kuma samu ci gaba kin yarda yai.


Da kanshi ya dudduba Nas din dabai masan duniyar dayake ba. Har lokacin bugun zuciyarshi ba wani karfi.


Saidai yana dan karuwa da uku zuwa hudu kan dazun sai kuma ya sauka. Amman yaki yarda daya tafi yabar Nas din.


Kallo daya zakai masa kasan cewar shi kanshi yana bukatar hutun amman yaki yarda ya tafi gida.


Husna ya kalla yace mata.


"Idan kamala ya zo kawo blankets ki bishi ya mayar dake gida"


Girgiza masa kai kawai tayi. Dan batajin zata matsa kafa daya ma batare dashi ba.


Bawai dan bata taba kwana ita kadai sai yan aiki a wannan katon gidan ba.


Saidan wani sabon tsoro daya shigeta da kuma son ta zauna kusa da prince ishaq din.


Ga tausayin shi daya addabeta.


Bazai iya wani surutu mai yawa ba. Dan haka ya kyale husnar. Shima yafi son ta zauna.


Yana bukatar wanda zai kula dashi. Tunda ummar shi tayi masa nisa babu wadda zai juya ya kalla yadanji karfi karfi sai husnar.


Dakin su suka bari suka shiga inda Nas din yake kasancewar dakin tankameme.


Can gefe husna ta shimfida musu bargunan manya masu matukar laushi suka zauna shiru.


*


Nan inda husna take zaune bacci ya dauketa. Shi ya kamata ya kwantar da ita ya lillibe ta. Addu.o.in tsari ya tofa mata sannan ya koma ya zauna.


A haka ya kwana kanshi hade da gwiwarshi. Da duk shigowar da wani likita zaiyi duba Nas tare zasu duba shi.


Da asuba saida yai wanka yayo alwala yazo da niyyar tashin husna ya samu ta tashi.


Toilet ta nufa itama wankan tai ta saka kayan da aka kawo mata jiya batai amfani dasu ba.


Sanda ta fito prince ishaq harya idar da sallah hana zaune yana addu.o.i.


Sallar tai itama. Taima Nas addu.ar samun sauki ta koma kan bargunan tai zamanta.


Shima nan ya koma kusa da ita ya zauna. Saida taji cikinta na ihu ne ta tuna rabonsu da abinci tun na jiya da rana.


Dayan dakin husna ta tashi ta shiga. Prince ishaq kam da ido yake binta. Kayayyakin ciye ciye da kamala ya kawo musu kiya ya zuba a fridge din wajen ta dibo.


Fresh milk da snacks ta dibo masa fruits dan a yan kwanakin nan ta kula yana son su.


Kome take da ido yake binta. Yana kallo ta miko masa fresh milk da burge.


Kai ya girgiza mata dan tun jiya yake jinshi wani iri. Kallon wannan tarkacen ma jiyai amai yake ji.


Kyale shi tai tadan samu taci burge guda daya da fresh milk.


A hankali tace.


"Kaci wani abu please. Ko fruit dinne"


Kanshima ciwo yake masa. Bayason magana at all. Dan haka ya karbi apple din data bashi.


Gutsura daya dakyar ya hadiye yana wani yatsine fuska. Kula tayi kaman jikinshi nadan kakkarwa.


Kallon shi tai sosai. Idanuwanshi sun shige ciki sunyi wani kanana.


"Are you okay?"


Ta tambaya. Daya daga mata kai alamar eh, sai kuma ya gigiza mata kai alamar a.a dan jinshi yake wani irin sama sama.


Apple din dake hannunshi taje karba. Taji wani zafi fiye da yanda takanji jikinshi.


Da sauri takai hannu ta taba fuskarshi. Wani irin zazzabine rufe dashi.


Ido ta zaro tace.


"Baka da lafiya. You are burning up"


"Lafiyata kalau"


Ya fadi yana kauda kai gefe.


"Baka da lafiya bara wanj doc ya shigo"


Husna tace tana kallon shi. Batare daya kalli inda take ba yace.


"Bana wani bukatar doc saboda lafiyata kalau"


"Ka cika gardama"


Ta bashi amsa. Kallonta yai cikin fuskata yace.


"Kin cika son jan magana"


"Bafa kada lafiya"


Ta maimaita tana kallonshi cikin idanuwa wannan karin.


Yatsina fuska yai a dake yace.


"Bana son jan magana and bana bukatan doc"


Shiru tai kawai. Ta kula ba wai saurararta zai ba.


Dakyar ya iya mikewa saboda jirin dke kwasar shi dan ba karamar dauriya yake ba.


"Ina zaka?"


Ta tambaya.


Baice mata komai ba ya wuce ya fita. Numfashi ta sauke. Batabi bayanshi ba. Yanda baison takura ta saka mishi ido kawai.


*


Allurar zazzabi akai masa data sake taimakawa wajen kara mishi jirin dayake yi.


Da doc din yaga prince ishaq yaki saurarshi kan cewar kodai ya yarda ya kwanta asibiti ko kuma ya koma gida ya huta dan stress ya mishi yawa yasa shi biyo shi har dakin da Nas yake.


Husna yaima magana yace prince ishaq din na bukatar hutu.


"Ka kira azo a dauke mu kaje gida ka huta please"


Ta bukata muryarta a tausashe.


Girgiza mata kai yai hadi da fadin.


"Ba inda zani"


Dafe kai husna tai. Taurin kanshi ya soma gajiyar da ita. A nutse tace.


"Nas bazai so kai masa haka ba. Zaiso ka zamana mai kwarin gwiwa yanda zaka kula dashi sosai. Ba ka yarda Allah bane mai bada lafiya?"


Shiru yai kanshi a kasa yana saurarenta. Ganin hakan yasa husna cewa.


"Duk zaman nan da muke bashi Nas yake bukata ba. Addu.a yake bukata. Please muje gida ka huta.... "


A gajiye ta karasa maganar. Yana tsaye inda yake. Kyale shi tai kawai.


Ga mamakinta waya taga ya zaro daga aljihunshi. Ya kira kamala.


*


Saida suka shiga mota prince ishaq ya kalleta na wasu yan mintina.


Hannunta ya riko dayasata juyowa ta kalle shi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login