Showing 54001 words to 57000 words out of 60293 words
shi ta dawo.
Harya fito ta bashi kayan ta sake fita. Ko minti biyar baiba ya fito falonta ya zauna yace mata
"Yunwa nake ji fa"
Ya fadi dan duk ranar sunata hidimar auren billy. Bai samu zama ba.
"Me zakaci? Sai inje in dibo maka"
Ta bukata dan bata tunanin zaici tuwo.
"Duk abinda zakici"
Ya fadi. Ta ce
"um um fa. Ni nagaji da kalaluwan abincin nan. Na shiga kitchen nayi tuwo miyar kubewa"
Ai gani tai ya gyara zama yace
"amman kin taimaka husna. Kisan rabon da inci tuwo anyi shekaru? Da umma tana mana tun kamun in tafi karatu"
Kallon shi take da mamaki tace
"Wai da gaske zakaci tuwon?"
Daga mata kai yake yace
"Nikam ki zubo mun hanjina yana kullewa"
Xuba musu tai. Suka sauka kasa kan kafet. Tai mamaki sunci tuwon sosai.
Suka shanye lemonsu. Prince ishaq nata mata santi.
"Husna gobe ma ki dafa mana wani abu. Na gargajiya"
Da dariya a muryarta tace
"Zakaci dambun shinkafa"
Ya jinjina kai yace
"Ban tabaci ba. Amman komai kikai nasan zaiyi dadi"
Hira suka shigayi sosai kan abinci. Itama sai taji dadin yanda taga yaci
Ta godema Allah taima mahaifiyarta addua data tsaya taga ta koyi girki.
Ta dauka niyya a ranta daga ranar kome take zata shiga kitchen tunda ga yan tayi ta dafa ma mijinta duk abinda yake so.
Da dare haka yace mata lemon dazun ya masa dadi sosai.
Batace komai ba ta tashi taje kitchen ta kara hado mishi wani.
Kissing dinta yai a goshi da kumatu.
Nan dakinta ya kwanta yace bazai iya zuwa dakinshi ba yagaji sosai.
***
Kwanci tashi babu wahala wajen Allah. Ga bikin billy yau saura kwana biyu.
*
Zaune ya sameta a parlour d'in kasa ta kurawa wayarta ido tana chat da khausar sai uban murmushi takeyi harma batasan yashigo ba.
Kamshinsa ne daman take gane shigowarshi dashi. To yanzun kamun ya fita ya gama dakunata itama kamshin nasa take.
Ko da taji shi ya cika mata hanci ma ta dauka na jikinta ne daya rungumeta sanda zai fita.
Tabayanta ya zago ya warce wayar juyowa tayi gaba daya ta kalleshi.
Murmushi tai tace
"Gentle yaushe ka shigo?"
Dariya ya saka ya wuce abinshi yana fadin
"Kinata danna waya ina zakiga shigowata"
Mikewa tai ta bishi tana fadin.
"Gentle ka tsaya mana. Kaifa nake jira daman"
Side dinshinsuka wuce. Ya ajiye wayar kan gado. Yana wani dakuna fuska shi a dole fushi yake.
"Waya fad'a maka banji shigowar kaba,naji fa bayan kamanta fushi nake dakai kafita bansaniba"
Juyowa yayi ya kalleta kawai ya wuce dakin sake kaya. Ya fito
"Ki shirya, umma tamun waya komai naki yana can wai kije tun yau"
Wani murmushi ya kwace mata
"Inje in dauko hijab dina?"
Janyo ta jikinshi yai ya furta
"Kina murna zaki barni har kwana wajen hudu. Ko kewana ba zakiji ba ko?"
"Waya gaya maka ni baruwana duk inda zakaje zan bikane"
Murmushi yamata yace
"hargun mai martaba saikin bini?"
Waro idonta tayi suka kwashe da dariya dukkansu....
*
Biki ya kankama yau ake kamun Amrya Billy da Angonta saeed.
Amarya da ango sunsha kyau a taheer guest palace ake bikin kamun.
Hussy tashirya tayi kyau iya kyau domin kuwa takanas ta kira belleza, tazo tamata makeup kuma ba laifi tamasifan yi kyau, blue and yellow tayi bawani mayafi ta yafaba.
Ashoeke ne blue nakai da na yafawa a kafad'a tayi kyau matuka kai kace itace Amaryar.
Prince ishaq ta kira a waya dan yace inta gama shiryawa shine zai kaita. Ga yan gidansu duk za.a tafi gaba daya amman yakiya.
Kallonta ya tsaya yanayi domin kuwa ta masifar masa kyau.
Murmushin dake karawa fuskarta kyau ta sakar masa tace
"Gentle I'm set"
janyota yayi jikinshi yashaqi kamshinta mai dad'i ya furta
"Hussy anya kuwa zan barki ki fita ahaka kinga yanda kikayi kyau kuwa? Wurin fa da maza"
Langwabe kai tayi ta furta
"Gentle ba dakai zamuba aiba wanda ma zai kalleni ansan ni matar prince Ishaq ce da anganni"
baice komaiba ya sake ta dan yaga mutane nakai kawo. Mota suka shiga.
*
Wurin ya matukar kayatuwa domin kuwa komi yaji sam barka.
kallo ne ya koma sama sanda prince ishaq ya shigo shida hussy domin kuwa sunsha kyau shikuwa sai shan kamshi yake ala dole ana Kallar masa hussyn shi.
Ahaka taro ya watse ....
*
Washe gari dinner akayi a guest house na mai martaba.
Nanma sunsha kyau matuka amma antaru sosai wurin ba kama hannun yaro.
Zaune prince Ishaq yake shida hussy,shifa duk inda take yananan manne da ita.
Wani friend d'inshi zahar yamai waya kancewar yana waje yazo yashigo dashi.
Ya nata duba wanda zaisa yaje ya shigo da zahar din bai samu ba. Dan haka yace ma hussy.
"Yanzun zan dawo. Karkije ko ina fa"
*
A hanya taro mutane yayi yawa shikuwa yau mulkin yakeji ahankali yake rabe mutane yana wuceww harya kusan isa gate din da zai sadashi da waje.
Ji kawai yayi an cakamai wuka hannu kara yasaka ya dafe wurin dagowar dazaiyi yaga ko waye.
yaga ankuma daga wukar zuwa kirjinshi da sauri ya kai hannu dan ya kare.
Ya same shina wuya. Ya rike shi dam ya soma ihun kiran mutane.
Hankalin mutanen kuwa ya soma yo kansu. Jirin dake dibar shine yasa mutumin ya kubce masa.
Amman ina an nasarar damke shi.
Prince ishaq kam kasa ya tafi luuu. Ya sume saboda jinin dake zuba jikinshi.
*
Hussy ta taso domin ta dubashi kasancewar taga wayanshi dayabari kan table nata tsala ihu,da alama wanda yafita ne yashigo dashi basu haduba.
Wayar hannunta taga tana ringing. Ganin Nas ne ta dauka tun dazun take mitar bata ganshi ba.
"Hello kanina"
"Anti fito waje please yanzun nan"
Yanayin muryarshi ya tsoratata. Da gudu ta fita waje. Taga komai ya hargitse ga yan sanda sunzo.
Nas ta hango ta kara Sa wajen shi. Baice mata komai ba ya kama hanya tabishi.
Mota suka shiga gidan baya su dukansu.
Sai lokacin take ce masa
"Me ya faru. Ina gentle?"
Shiru yai kawai. Gani tai yasa hannu yana goge fuskarshi.
Ai nan take kuka ya kwace mata.
"Dan Allah naseer ka fadamun kome ya same shi"
Dakyar ya sauta muryarshi yace
"Wani ne ya ji masa ciwo. Amman komai ya kusa karewa. An kama mutum daya yau"
Ai tun daga kalmar "ciwo...... "
Ta daina fahimtar komai. Kuka kawai take suna hanyar asibiti.
So take taganshi ta tabbatar da lafiyarshi kalau. Babu abinda zai samar mata miji.
ππππ ππππ
Wata Bakwai 7
ππππ ππππ
Written by
LuΞ²ΟΞ± SufyΞ±Ο
5β£2β£
A hargitse suka shiga asibitin. Tana ganin umman prince ishaq ta ruga wajenta tana kuka.
Sunfi awa biyu zaune likitoci babu wanda ya fito yace musu wani abu.
Hankalin kowa a tashe yake. Ko da likita ya fito kusan su duka suka isa wajenshi kaman zasu cinye shi da tambaya.
Dakyar ya samu suka nutsu yace musu.
"Yana hutawa ne. Ciwukan nashi anyi sa.a ba wani zurfi sukai ba. Ya zubda jini ne shi ya galabaitar dashi"
Sai lokacin hankalin kowa ya kwanta.
Umma tace azo a tattara kowa ya koma gida dare yayi. Su tafi da husna ma. Abar Nas kawai.
Kuka husna ta saka ga shi ta kasa cewa komai. Ganin hakan yasa umma tace abar husna hankalinta zaifi kwanciya.
Su duka suka zauna dakin da prince ishaq din yake.
Dinkine a hannunshi da wuyanshi. Banda nan babu wani ciwo a jikinshi.
Husna taja kujera ta zauna kanta ta dora gefen dagon tana riko hannun shi.
Tayi kuka har fuskarta ta kumbura. Bacci kam barawo ne ya saceta.
****
Hannun prince ishaq taji saman kanta. Da sauri ta dago ta sauke jajayen idanunta da suka sha kuka cikin nashi.
Murmushin shi yai mata kawai. Dan bazai iya magana ba. Makoshin shi ciwo yake masa sosai.
Hawaye zatai da idanuwa ya nuna mata alamar baya so. Tako tarbe su. Nas dake kwance gefe ta taso.
Yaje ya kira likita. Akazo aka duba shi.
Sai bayan ta idar da sallah sannan ta kira gidansu ta fada musu da asibitin da Nas din take.
Sukace da gari ya kara wayewa zasu zo.
***
Tun da sassafen suke shan baki. Husna kam ba yanda ba ai da itaba ta koma gida ta yo wanka ta sake kaya taqi.
Saida umman prince Ishaq tazo sannan tasa Nas ya mayar da ita gida.
***
Duk saurin da take yi sanda suka koma mamanta har sunzo sun duba shi sun tafi.
Taji kaman zata saka kuka. Waya ta dauka ta kira
"Mama ko ki jira in dawo mu gaisa"
"Husna zamu dawo gobe in Allah ya kaimu. Kuma su yayanki ma zasu zo da yamma"
Ba yanda ta iya. Dole ta hakura. Addu.a tai ma prince ishaq din sosai tukunna sukai sallama.
***
Yau kwanan su uku a asibiti. Prince ishaq tunda ya fara samun sauki yake mita shi fa sai a tafi gida.
Dole ranar da yamma aka sallame su da warning cewan kar yai stressing kanshi.
Ya zauna ya huta sosai. Saima juya idanuwan shi wa doc din dayai hadi da fadin
"Zan iya kula da kaina. I know the rules"
*
Tunda suka dawo gida falonshi ya zauna yanata waya.
Husna tana kitchen ta hada masa ginger drink din da yake bala.in so.
Farfe sun kifi tai mishi ta zubo ta dawo falo.
A plate ta zuba mishi ta zauna ta gyara ta cire kayoyin sannan ta tashi taje ta wanko hannunta ta dawo.
Kallonta yai yace
"Sannu da aiki hussy"
"Kaine da sannu. Ya jikin?"
Ya langabar dakai gefe kawai maimakon ya amsata sai yace
"Nas ne ya kirani wai an fara zaman court ne kan shari.armu. Gobe sai naje"
Plate din ta dauka takai kusa dashi tana fadin
"Allah ya kaimu. Allah ne ya kawo karshen mugayen mutanen nan."
Ya amsa da amin. Saida ma taita matsa mishi ya dan kara ci.
Tun a asibiti yake cewa kifi yake son ci. Amman kaga yanzun an dafa ya kasa ci.
"Menene mama ta kawomun dazun da safe?"
Kallon shi tai sosai
"Dambun nama ne. An kuma hanaka tauna abu for long"
Ya tabare fuska
"Ni kam zanci fa"
Ta sauke numfashi tace
"Gentle ka hakura yana nan na ajiye maka. Idan ka kara samun sauki sai kaci"
Ya girgiza kai shi bai yarda ba.
"Ki tauna saiki dinga bani"
Zaro idanuwa tai. Dakyar ta lallabashi. Shifa a dole sai ta tauna ta bashi.
Da dare tare suka shiga toilet. Ita ta kama mishi ya cire riga saboda hannun shi.
Ya cire har single. Dagashi sai boxers. Wata kunyarshi ta saukar mata.
Ta kasa hada idanuwanta da nashi. A hankali tasa towel da ruwan dumi ta goge mishi jikin shi tas.
Yai brush sannan ya fito. Wani boxers din ta dauko mishi da singlet ya shiga dakin sake kaya ya canza.
Ya fito yasa singlet din zuwa wuyansh kawai. Ta taimaka masa ya karasa sakawa.
Magunguna ta ballo da cup din ruwa. Ta mika mishi ya wani girgiza kai yana yamutsa fuska.
"Bana sha"
Zama tai ta kalle shi sosai.
"Bangane baka sha ba. Nika karba ka shanye in tashi in wanke singlet din can daka cire"
Gani tai da gaske yake baya shan maganin.
"Saina narka a ruwa na dura maka ko?"
Dariya ta bashi. Ya tsareta da ido yana fada mata zai so ta gwada dura mishi maganin.
"Allah in baka sha ba zan kira umma in fada mata"
Da sauri ya karbi cup din da maganin ya shanye. Dan yasan umma sarai. Asibiti zai koma ya zauna sai yagama shan maganin.
Dariya tai. Ta wuce ta wanke mishi boxers din. Tai wanka sannan ta fito.
Sanda ta dawo har yai bacci. Ta zauna gefen shi. Kallon shi take.
Bata tabbatar da abinda take ji game dashi so bane. Koma tace ya girmi so. Sai da nas yace mata anjima sa ciwo.
Saida taganta asibiti likitocin sun ki fitowa su bata bayanin. Yanda taji numfashin ta na barazar daukewa.
Yanda taji tana son taganshi ta tabbatar da lafiyarshi. Indai wannan ba so bane. Bata san menene ba.
Saita tsinci kanta da tofa masa addu.o.i tana fatan Allah ya ci gaba da tsare mata shi.
***
Yau ake gama zaman kotu shari.ar su prince ishaq. Da ikon Allah dayai alkawarin biwa duk wani wanda aka zalunta hakkinsa.
An nasarar kama masu laifi dumu dumu. An kuma yanke musu hukunci dai-dai da laifukan da suka aikata.
Tunda suka fito daga court din jikinshi a bala.in sanyaye yake.
Nas ya dafa mishi kafada yana fadin
"Yaya komai ya wuce...... "
Numfashi ya sauke yace
"Nasani nas kawai raina ne bayamun dadi. Duk jimawar nan. Duk abubuwan nan mun riga mun san daga bangaren su Nawaz yake. Amman kamala......... "
Yama kasa karasa maganar. Tunda aka kama harda kamala a laifukan nan jikin shi ya gama sanyi.
Ko motar su da tai hadari kamala ne ya kwance musu brake.
Duk wani motsin dazaiyi kamala da ya yarda dashi shine babban munafukin shi.
Kamala shi yai sanadin mutuwar huddy. Shikuma ya so yai sanadin ta Nas.
Well Allah kenan. Ga asirinsu duk ya tonu. Ko ba komai daurin rai da rai ne. Shine sassaucin da alkali yai musu.
*
Gadonta tagama sakema bedsheet. Tana saka pillow case din.
Sam bataji turo kofarshi ba. Sai dai taji ya rungumeta ta baya. Kanshi a kafadarta.
"It is over hussy. Komai ya kare. We are safe"
Hamdala tai wa Mai Ikon Rayuwa da mutuwa sannan ta zame jikinta ta juyo ta kalle shi.
"Sarki......... "
Gira ya daga mata alamar ta karasa amman sam ta kasa. Sunan shi wani bala.in nauyi yake mata a baki.
Janta yai sosai jikinshi. Sumba ya manna mata a wuya. Cikin kunnenta yace
"Ina son jin sunana kan lips dinki husna"
Kanta ta sake boyewa a kirjinshi tai shiru abinta.
Dole ya hakura ya kyaleta.
Sakinta yai yana fadin
"Jeki dauko hijab dinki zamu fita unguwa"
Harta wuce ta juyo tace
"Abinci fa?"
Ya girgiza mata kai
"Na biyo ta gida. Naci nama wajen umma. Kinci wani abu dai ko?"
Ta amsa da
"Eh naci nima"
Hijab dinta ta dauko ta saka. Shi yake tukasu. Saida suka biya ta sahad.
Yace mata ta dibi duk wasu kaya na ciye ciye da biscuits. Duk da har yanzun baice mata ga inda zasu ba.
Abinda yasa tayi haka ta diba. Basket guda suka cika da kayan ciye ciye.
Ya biya kudin suka koma mota. Ga mamakin husna hanyar estate dinsu taga ya nufa.
Murmushin datai mishi har ranshi ya jishi. Tama kasa magana dan murna.
*
Ba karamun dadi su mama sukaji ba. Babban falonsu suka zauna.
Bakowa gidan sai mama. Duk suna islamiyya. Abbansu kuma yana kasuwa.
Duk abubuwan da aka kawo masa. Dambum nama kadai yaci. Shima dan yaji dadin na kwanaki da maman ta kawo masa.
"Mama dan Allah aisha tazo in anyi hutu mana"
Cewar husna
Mama ta amsa ta da
"Wai husna islamiyyar kuma fa. Kinsan suna hadda"
"Mama sai a dinga kawota kullum ai"
Prince ishaq ya fadi yana ma mama murmushin dayakasan siye mutane dashi.
Kwarjinin shi yasa mama ta yarda cewar zata fadama abbansu idan ya dawo.
Suna shirin tafiya su aisha suka dawo.
Maheer ne ya fara shigowa da sallama.
"Anty husna"
Ya fadi muryarshi da mamaki da kuma farin cikin ganinta. Ai aisha najin haka da sauri ta ture shi ta karasa ciki.
Da gudunta ta fada jikin husna tana ihun murna.
Mama tace
"Oh ni aisha ki nutsu dan Allah. Baki iya gaida mutane bane"
A ladabce suka gaishe da prince ishaq din ita da maheer.
"Su maheer ko adan leqo ni"
Husna ke mishi mita. Sosa kai yai a kunyace yace
"Zanzo in shaa Allah."
Hira suka dan taba kadan. Mama tace ya isa haka. Sun tsaida su ga yamma tanayi.
Prince ishaq yace ma maheer ya biyo shi mota ya dauko musu abu.
Kamun su dawo mama ta shiga kitchen ta ciko musu wata rubber da dambun nama. Sai turarukan wuta taba ma husna.
Ganin lodin ledojin da maheer ya shigo dasune yasa mama salati. Cewar hidimar tayi yawa.
"Mama ai kune da hidima"
Inji prince ishaq.
Addu.a tai musu sosai. Har mota su aisha suka rakasu sannan suka koma gida.
Husna wani dadi ne da farin ciki fal zuciyarta. Suna shiga mota tace
"Nagode sosai gentle. Nagode da karamci"
Kallonta yadanyi ya maida hankalin shi kan tukin. Murmushi ya kwace mata.
Kawai ya wani kHualleta ya basar. Prince ishaq akwai jin kai. Da zata ce masa yana jin kai. Ko ta kwaikwayi abinda yai yanzun.
Zakaga fuskar nan tai ja. Wai shi yaji kunya.
ππππ ππππ
Wata Bakwai 7
ππππ ππππ
Written by
LuΞ²ΟΞ± SufyΞ±Ο
5β£3β£
*2nd to the last page*
Da gudunta ta ruga ta sameshi a dakinshi yana kwance yasaka laptop a gaba yana aiki bayanshi ta dare ta zauna abinta ta sakalo hannayenta ta wuyanshi ta kwanta ta furta
"Gentle kausar ta haihu ansa mu baby boy"
Laptop din ya janye gefe daya. Ya kamo hannunta ta sakko daga bayanshi. Ta zauna gefen shi.
Wani yanayi yakeji. Daman ace babyn nan nasu ne. Da ba karamun dadi zaiji ba yau.
Da murmushi a fuskarshi ya ce.
"Ma shaa Allah. Allah ya raya babyn da mumynshi"
Ta amsa da amin kamun yace
"Yaushe ne suna?"
"Yau aka haihu kaga Friday suna ze kama" bata fuska yayi yace
"To yaushe zaki tafi saboda nasan Wanan satin me zuwa ayyukane kaina barkatai bazan samu damar binki abj ba"
"Thursday zantafi indawo Sunday"
Zaro ido yayi yace
"Hussy kwana uku kenan fa ko?"
Rau-rau tai da idanuwanta.
"Please gentle. Kausar ce fa"
"bazan hanaki tafiyaba kinsani, amma hussy kwana uku fa. Ko dan ke ba zakiyi kewata ba?"
Murmushi tamasa tana dora kanta a kafadarshi. Ita kanta tasan a daddafe zatai kwanakin nan.
Ko bikin gidansu da akai. Dadewa take batai bacci ba. Ta saba duk juyin da zatai ya gyara mata kwanciya a jikinshi.
"Gentle kayi hakuri zan dawo saturday.Wallahi nima zan kewarka sosai."
Matseta yayi tamkar wani zai kwace masa ita. Yai shiru kawai. Kwanakin daya rage musu yake kirgawa.
Yanajin da husna ta soshi da bata soshi ba.