Showing 24001 words to 27000 words out of 60293 words
Can tace masa.
"Nas fa?"
Murmushi ya kwace masa jin sunan kanin nashi kawai. Ya kuma ji dadi har zuciyarsa data tambaya.
Yana kuma yaba karamcinta na kokarin boye ma Nas halin da suke ciki.
A nutse yace.
"In yazo adjusting banbancin lokacinmu yana masa wuya. Bacci yake"
Su duka zaune suke shiru. Idanuwansu duka kan T.V din yake amman babu wanda hankalin shi yake akai.
Kaman yanda komai na jikin husna yake sane da zaman natacce kusa da ita hakan yake a nashi bangaren.
Zata iya rantsewa duk da karar t.v bai hanata jin fita da shigar lumfashin shi ba da yake kara ma zuciyarta sauri wajen dokawa.
Ba karamun dadin fitowar Nas taji ba dan saiya dauke mata yanayin da take ji.
Saida ya karya sannan ya dawo falon.
Hira suke su dukansu wayar nas tai ringing.
"Ina zuwa pls"
ya fadi yana miqewa.
Prince ishaq ya maida natsuwarsa kan husna.
Cikin muryarsa ya soma magana.
"Nakan jima ban ma wani godiya ba. Hakama nema alfarma abune mai nauyi a wajena.
Nagode da karamcin da kikai ma kanina. Nagode da boye masa zamanmu.
Ina son mu zama friends a iya zaman da nas zaiyi damu. Kome zamu ci gaba bayan nan bai dameni ba."
Miyan dake cikin bakinta taji ya qafe. Harshenta ya mata nauyi. Saboda bata ma san me zatace masa ba. Kai kawai ta daga masa alamar ta amince.
Hannu ya miqa mata hadi da fadin
"friends?"
Tayi jim kamin ta karbi hannun nasa
"friends"
Ta amsa. Cikin wata murya da ta kasa gane ko tata ce.
Murmushi tai masa cike da yanayi da yawa.
Shima murmushin yai mata data fahimta tamkar yana son gaya mata a can wani bangare na zuciyarsa yaso ace sun hadu a wani lokaci ba irin wannan ba.
"Ishaq"
Ya fadi yana zuba mata idanuwansa.
Daurewa tai ta rike kallon da yake mata cikin nata idanuwan sannan tace.
"Husna"
Agogon shi ya duba ya kalli husna yace.
"Zan fita bazan jima ba. Ki kula da kanki alright? "
Dakyar ta hadiye abinda ya tsaya mata a wuya tace masa.
"Allah ya dawo dakai lafiya"
Amin ya fadi yana mata murmushin da saida dimple dinshi ya fito sosai.
Bata taba kula dashi ba. Ko da yake bata kula da abubuwa da yawa akan shi.
Sai take jin kaman taci amanar ammar a yanzun nana.
Zuciyarta na gaya mata bata kyauta ba. Wani bangare kuma mafarkin datai ya mata tsaye.
Haka Nas ya fito ya sameta. Ya tambayeta ina prince ishaq yace ya fita amman bazai jima ba.
Nas yace mata zai koma daki zasuyi video chat da friends dinshi ta imo.
*
Dakinta ta koma tana kwanciya text din ammar ya shigo yana fada mata charge ne baida shi tahau whatsapp suyi hira.
"Tawan inajin nisanki da kusancinki a lokaci daya a zuciyata na kasa tantance yanayin kowanne."
Ammar ya rubuto.
Murmushi tai ta rubuta masa amsa.
"naka yanayin mai sauqine tunda har kana iya dorashi akan kalamai nawan. Ni kadai nasan me nakeji."
"Bazan iya rabuwa dake ba husna kin zamo ni gabaki daya. Ki tausayawa rayuwarmu ki dawo gareni."
Wani daci taji dan a yanzun komai ya kwance mata. Ta rasa mafita. Gaba daya kanta ya kulle.
"Hmm ka tayani addu.a ina ta tunani ne nawan."
Alama tagani cewan yana recording voice message. Hakan yasata mika hannu ta dauko earphones dinta kan gado tasa jikin wayar.
Voice note din farko ta bude.
"In aka yarda daso aka amsa shakuwa bataki shiga ba. Tunda nai miki kin mini naji sai mu killace sirrin juna.
Abinda zai fita kan harshe da zuciya ya fita. Ki dan matsar da mayafinki ki ganni daina rufa. Idan naganki cikin shauki sai na daina kwafa. Farin cikinki adona ne fushinki shi na tsana"
Wani abu taji zuciyarta nayi. Shi ba ciwo ba. Shi ba tsayawa ba.
Tasan ammar. Tasan ammar sosai ta kuma san cewar ko hira suke in har ya soma yi mata waka. To abinda yake ji ya girmama.
Muryar prince ishaq ta soma sata manta yanda take bala.in son muryar ammar. Musamman in yana mata waka.
Mamaki take akan yaushe ya juye mata zuwa prince ishaq a zuciyarta.
Wani voice note din taga ya shigo kamun ta gama budewa wani ya sake shigowa.
Kuka ya kwace mata. Kuka take sosai da sosai tana jin zuciyarta kaman zata fado.
Yanayin muryarshi a wakar karshe tasan ko ba kula yake ba yana jin ciwo fiye da wanda ita take ji.
Sam bataji sallamar prince ishaq ba. Dan wayar ma tana gefe ta cire earphone din ta hada kanta da gwiwa tana kuka.
*
Ya dawo baiga kowa a falon kasa ba. Gidan yayi wani shiru. Zuciyar shi ta bashi shawara yaje ya duba husna.
Ko ba komai sun zama abokai. Koda kuwa na iya zaman Nas ne. Ya fison yai komai yanda ya kamata.
Ya kwankwasa yaji shiru ya tura hadi da sallama. Ganinta yai kan gado ta dunkule jikinta.
Daga inda yake tsaye yana jin saukar ajiyar zuciyarta. Karasawa yai kan gadon ya dafa mata kafada. Cikin taushin murya yace.
"Husna"
*
Sam bataji shigowar shi ba. Ko kamshin shi bata ji ba yau sai dai dumin hannun shi kan kafadarta.
Da yanayin yanda yaja sunanta da halin da take ciki bai hanata jin wani iri ba.
Dagowa tai ta kalle shi fuskarta cike da hawaye. Idanuwanta sun canza launi saboda kukan datai.
Wata irin kewar huddy ta doki zuciyarsa. Ya danne abinda yakeji ba yanzun banne lokaci.
Batare da tunanin komai ba yasa hannuwanshi ya tallabi fuskarta yana fadin.
"Menene? Are you ok?"
Hannun shi tai kokarin turewa ta a sake fashewa da wani irin kuka.
Ta rasa yanda akai ganin shi ya kara karyar mata da zuciya.
Gyara zama yai sosai kan gado ya riketa a jikin shi yana fadin.
"Shhh husna. Komai zaiyi dai dai. Koma menene it will be alright"
Baison kukan mace. Yanayin kukan ta ya dagula mishi lissafi.
Husna kam duk wani abu da take ji ne yale fita ta hawayenta. Jitai gaba daya ta wani gaji. Ta zame daga kirjin shi.
Gaba daya fuskarta kamshin shi take yi.
Kallonta yake.
Hannu tasa ta goge fuskarta. Ta kalli kirjinshi gaba daya ta jika masa riga da hawaye ne da wanne tsiya.
Duk powder dinta ta goge tas a jiki harda jagirar ma. Kasancewar kayan farare.
Ta zaro idanuwa. Muryarta a dishe sosai saboda kukan datai tace.
"Dan Allah kayi hakuri. Duk na bata maka kaya"
Kallon kirjin shi yai. Ya wani bata fuska da taga ya kara masa kyau yace.
"Eww. Gross"
Kaman zata sake fashewa da kuka tace.
"I am sorry please"
Da sauri yace.
"Wasa nake fa. Enough, do you want to talk about it? I mean nasan ba hurumina bane. A matsayin aboki"
Kai ta girgiza masa alamar aa. Ya sauke wani numfashi. Kukanta kadai ya sa mishi ciwon kai.
Ganin shirun yai yawa. Yasa shi fadin.
"Kinci abinci?"
Ta girgiza masa kai. Ya soma gajiya da amsa masa magana da kai da take yi. Baya so sam.
Ya share ne yau dan yanayin da take ciki.
Mikewa yai sannan yace.
"Tam barin watsa ruwa. Ki tashi kema. Kiyi wanka and no more kuka zan dawo ok?"
Yanda yai mata maganar cikin umarni zaka rantse da yarinyar da bata fi shekara uku zuwa hudu yake.
Karasawa yai daf da ita sannan yadan tsugunno dan ya dai-dai ta fuskar shi da tata.
Cikin idanuwa ya kalle ta yace.
"Da gaske nake fa. Banda wani sabon kuka zakiyi ciwon kai"
Dakyar tace.
"Bazan yi ba"
Ya furta
"Good"
Ya fita yana ja mata kofar.
Gaba daya ya kara saukar mata da gajiya. Hatta zuciyarta tagaji da aikin tunani.
Dakyar ta sauko daga kan gadon ta nufi toilet.
💝💝💝💝 💝💝💝💝
Wata Bakwai 7
💝💝💝💝 💝💝💝💝
Written by
Luβπα Sufyαπ
2⃣5⃣
*Babu abinda yakai ciwon rashin wanda ka shaku dashi. Babu abinda yafi tashin hankali sai ya fado maka a rai muryarshi da take cikin tunaninka ta soma dishewa. Saika nemi yanda sautin dariyarshi yake ka manta saboda ya maka nisa. Ya tafi inda zakaje wata rana. Da duk yawan hawayen da zaka zubda da karin tabbacin cewa bazai taba dawowa ba. Sadaukarwa ga duk wanda ya taba rasa wani mai kusanci a tare dashi!!!*
Tsaye yake kawai ya sakarma kanshi shower.Yanajin yanda ruwan ke bi masa jiki.
Idanuwan shi a rufe. Baisan dalilin kukanta ba amman ya tsaya masa a rai sosai. Da ganin yanayin kukan yasan ko menene ba karami bane.
Har ranshi dai yana fatan bashi bane sanadin kukan ta. Mutum ne shi da baya son ya takura ko a takura shi.
Dan haka tun randa aka kawota sai dole suke magana. Balle daya sake kula da cewar ko magana kan dole take masa ya kara fita harkarta.
Yau kukanta ya dawo masa da abubuwa da yawa. Wankan ya fito ya shirya. Fararen kayan dai ya kara sakawa ya nufi dakin husna.
*
A daddafe tai wankan ta fito. Doguwar riga tasa milk color. Ta daura mayafin rigar a kanta. Hijab taje dauka kaman yanda ta saba zama da ita.
Taji kwankwasa kofar prince ishaq. Cikin sanyin murya tace
"Shigo"
Ya turo ya shigo hadi dayin sallama.
Gefen gadon ya zauna kanshi tsaye yana kallonta.
Tayi kyau saidai fuskarta ta kumbura da idanuwanta saboda kukan datai.
Hijab din ta zura baice mata komai ba. Abokantakar tasu mai rauni ce sosai. Saitai kwari zai hanata saka wannan hijab din tunda ba kalar matan dabai gani ba.
"Muje"
Ta ce masa.
Tashi yai ya karasa daf da ita. Fuskarta yake kallo sosai kaman me neman wani abu. Muryarshi a dake yace.
"Kuka kika kara yi ko?"
Da sauri ta girgiza masa kai alamar Aa saboda yanda yake sa gabanta ya fadi.
Yanda take jin wani shakkar shi na cika mata zuciya. Kallon ta yaci gaba dayi na yan mintina baice komai ba ya wuce gaba.
Kafafuwanta ba kwari tabishi har dining room din. Ta zauna.
Zagayawa yai ya zauna kujerar dake fuskantar husna.
Plate ya dauka ya zuba mata white rice da miyar nikakken nama. Ya zuba plantain a sama ya tura mata. Kanta a kasa taja plate din.
Ta soma ci a hankali dan bayau ta fara cin abinci a gaban shi ba. Kawai dai yaune na farko da shi ne ya zuba mata.
Tayi mamaki saboda tana masa daukar mutum maijin kanshi da izza amman ya zuba mata abinci. Kamun taci ko rabi ya zuba fruits yankakku a plate ya sake turo mata da fork a ciki. Dagowa tai ta kalle shi.
Shima fruit dinne cike yanata ci. Ba yunwa take ji ba ma. Kawai dai tana cine. Ture plate din abincin datai ne yasa shi dagowa ya kalleta.
"Me kike nufi?"
Ya tambaya.
"Nako shi"
tace idanuwanta a kasa. Muryarshi a dake yace.
"Tam ki zabi daya. Ko ki cinye abincin nan ko ki shanye fruits din."
Yau bata da karfin gaddama ko neman rigima. Cikin raunin murya tace masa.
"Nako shine fa"
"Just shut up and eat husna. Bana son gaddama, ki zabi wanda zai miki saukin cinyewa."
Yana karasa maganar ya maida hankalinshi kan fruits din dayake sha.
Da yawan lokuttan da suke daidai ton zama cin abinci waje daya kulewa yake da yanayin cin abincinta.
Dan baya son mata magana ne. Ya tsani wasa da abinci duk da shima bawani cin kirkin yake ba.
Kallon shi take ya wani hade rai yana tauna fruit din a yangan ce.
Dan fa sun zama abokai na wucin gadi bazai sa ya dinga mata wannan shisshigin ba. Fruit din ta dauka ta soma ci.
Ta kusan rabi ta ture ta kwantar da kanta a table din. Kallonta yake.
With time zata koyi yin duk wani abu da ya umarta. Kyaleta yai bai takurata ba. Yasan limit dinshi.
*
Satin Nas daya yau a gidansu kasancewar ya kira mumyn shi tace masa yai zamanshi abuja yafi mata kwanciyar hankali.
Dan tasan in yana kano bamai kwabarsa. Bamai hana shi fita yawo yaje a samu matsala.
Abuja kam tana da tabbacin prince ishaq zai kula da Nas fiye da yanda zai kula da kanshi.
Husna ji take kaman sun shekara tare.
Yaron ya wani shiga ranta tana jinsa tamkar maheer qaninta sai dai wannan ya girmi maheer.
Zasuyi hira. Suyi game. Zuwanshi yasa ta daina wuni da qunci. Da dare zasu sha waya da ammar dinta in kuma yanayin aiki bai riqe shi ba sukanyi chatting.
Prince ishaq kaman yanda ta soma kiransa dan a ganinta lokaci yayi da zai zama hakan. Saboda dalilai da dama. Sukan gaisa. Sukanyi hira su uku amman indai su biyune a waje sai su rasa me zasu cewa juna.
Duk wani iri kowa saiya daburce. Dan haka suka dinga qoqarin in nas na nan kawai. In baya wajen kowa yai harkarsa.
*
"Yaya menene idan na fita ni kadai nan ai ba kano bane. Beside babu wanda ma yasan waye ni."
Nas ya fadi kaman zaiyi kuka.
"In zaka fita wani waje da yake da yawa mutane haka kaman cinema nas you must go with securities.Banson hauka"
prince ishaq ya ke maganar cikin qosawa.
"I want some normal yaya ka fahimce ni mana. Shisa baso bane banayi inzo inda kuke hakanne yake damuna am 18 fa koda ka manta"
"And?"
Prince ishaq ya fadi da alamun ranshi ya soma baci.
Cikin fuska nas ya kalle shi
"hakan yana nufin zanyi yanda nake so da rayuwata. Ba zai yiwu duk inda zani da masu gadina ba kaman wanda za.a kashe"
Ya bude baki zai bashi amsa husna tazo wajen.. Kallonsu tai su duka. Tasa akwai abinda yake faruwa.
Nas yace mata
"anty kice yaya yabarni na fita."
Kallon shi tai duk da yana mata kwarjini naban mamaki. Cikin dakiya tace
"Kabarshi mana tunda yazo sau daya ya fita"
Harararsu yai su duka.
"Kibar abinda ba zaki taba fahimta ba. Yaron nan bazai fita gate din farko bama babu masu gadi. Chapter closed"
Yanda yai maganar yasa sukai shiru su duka. Yabar wajen kawai.
Nas kaman zai kuka yace
"I fucking hate this life!"
"Calm down kagane kabishi a hankali."
Husna ta fadi cikin sigar ban magana.
A hasale nas yace
"bazai bari ba anty. Wani lokaci rayuwa bata da adalci. Amman wallahi saina fita"
Kamin ta samu bakin magana yabar wajen. Zama tayi abin ya daure mata kai. Meke damunsu su duka biyun.
Tasan bata damu da prince ishaq ba amman nas kam dan uwa takejin shi a zuci da jikinta gabaki daya.
Wajen minti talatin tsakani taji text ya shigo wayarta. Ta duba taga nas ne.
"@silver bird cinema"
Kawai yace.
"Please take care!"
Ta bashi amsa.
Bai mata reply ba dai.
Tana zaune a wajen prince ishaq ya zo.
Kallo daya taima yanayinsa taji gabanta ya fadi. Bata taba ganinsa haka ba. Fuskarsa a hade take idanuwansa sun wani canza launi.
A dake yace.
"Ina Nasir?"
Cikin rawar murya tace
yana silver bird cinema"
"Dammit!!!"
Ya furta yana dukan kujeran wajen saida husna ta tsorata.
Kallon ta yai da wani yanayi yace.
"Saboda me zaki barshi ya fita? Akan me ba zaki zo ki fadamun ba?"
Ta bude baki zata amsa shi dan bata ga fa yanda zata fara hana Nas fita ba ya katse ta da fadin.
"Forget it"
Ya dauko wayarshi kenan. Nata wayar ta soma ringing ta dauka nas ne.
"Hello qani yadai?"
"Wasu ne suka biyoshi sun ji masa ciwo yanzun haka muna bayan silver bird qarqashin wata mota wannan ne number din qarshe takan kiransa dana gani shisa na kira"
Kallonshi kawai tai da bayanannen tsoro cikin idanuwanta fuskarta da alamun tashin hankali ya karbi wayar.
Magana sukai da kowaye yake riqe da wayar nas din.
Prince ishaq ya miqa mata yana tafiya ta tsayar dashi da
"Kana tunanin zaka tafi kabarni anan?
Cikin damuwa yace
"ki zauna saboda yanayi na tsaro"
"Wlh saina biyoka aiba qaninka bane kai kadai"
Babu yanda zaiyi kuma baya son yawan surutu a wannan yanayin.
Dan haka yabarta taje ta dauko alkyabba ta dora kan kayan da suke jikinta.
Gabanta faduwa kawai yake. Jami.an tsaro ne tako ina suke zagaye dasu banda wanda yai waya su isa wajen.
Husna bata san kuka take ba saida taji abu nabin kuncinta. Jini ne kaman an yanka qaramar dabba a gurin.
Da gudu su duka suka karasa wajen Nas din.
Girgiza kai prince ishaq yake cikin tashin hankali ya riko Nas jikinshi da bayama numfashi a rikice yake fadin.
"Nas banda kai. Please ka bude idanuwanka"
Husna na tsugunne gefe
"Nasirr"
ta kirashi cikin muryar kuka.
Baima san tanayi ba.
"Ya mutu koh?"
Take tambayar prince ishaq.
Shiru yai ya kyale yarinyar nan. Dan shima zuciyarsa zafi kawai take masa ba zata iya daukar wani rashin ba.Na huddy kawai ya ishe su.
Wai me mutanen nan suke nema dasu ne? Duk akan mulki.
Mulkin da in an tona zuciyoyinsu ba qaunarshi suke ba.
Ya Allah! Yake fada a zuciyarsa ya dora da Allah ka tausaya mana.
Nas yake jijjigawa. Kasa ya ajiye shi kamun ambulance din da aka kira ta karaso.
Hannun shi ya dora kan zuciyar shi yana dannawa. Lokaci daya abinda ya faru da huddynshi yake masa yawo akai.
Iska ya soma ba Nas ta baki yana jijjiga shi amman a banza. Baiga amfanin karatun shi ba. Ya kasa saving hudeesa yanzun ma ga Nas.
Tare suka shiga motar asibitin su dukansu tare da nas. Kuka husna keyi kaman zata shide ganin qoqarin da likitoci suke tun daga cikin motar na ganin ya farfado amman abin yana neman gagara.
Prince ishaq ya kalleta sai yaji zuciyarsa tayi wani irin yanayi. Hannunta ya riqo bata hanashi ba dan bama a hayyacinta take ba.
Matso da ita yai jikinsa tako ruqunqume shi dam. Duk da halin da suke ciki bai hanashi jin wani abu na daban ba.
Kuka take har lokacin amman wannan karon a qirjinsa take yanajin yanda jikinta ke jijjigasu gabaki daya.
Saiya tuna masa lokaci mai nisa. Hannunsa yakai kaman zai riqota amman yana tunanin hakan. Wata zuciyar tace kayi ko babu komai tanajin halin da qaninka yake ciki.
Hannuwansa duk biyun yasa ya riqe husna yana lallashinta.
A haka har suka isa asibitin. Hana su shiga akai dole suka tsaya suna kallo ta window.
Ganin yarinyar mutane na shirin sume masa yasa shi janyeta daga wajen window din suka zauna.Tana maqale jikinsa har bacci ya dauketa.
Anfi awa biyu wani