Showing 15001 words to 18000 words out of 60293 words

Chapter 6 - WATA BAKWAI BOOK COMPLETE by Lubna Sufyan.txt

19 Feb 2025

9168

mai kyau.


Bude musu akai ta shiga shima ya shiga baya.
Har suka isa gidan babu wanda yacewa kowa komai.


Ita tana ta chatting da ammar abinta. Dan haka bata kula da komai ba sai tsayuwar motar data ji.


Aka zo aka bude musu qofa suka fito. Ya zo kusa da ita ya tsaya.


"Na iya lokacin da zamuyi a cikin gidan nan kiyi pretending komai normal ne a tsakaninmu."


Ya fada cikin muryar da takanji yaima yan aiki.


Cike da mamaki ta kalle shi.


Bata dai bashi amsa ba duk inda yai nan take binsa suna tafiya.


Tana kallon yanda mutanen cikin gida suke tsugunnawa tun kamin ya qaraso inda suke suna gaishe dashi amman ko kallon arziqi balle taji ya amsa.


"Ana gaishe dakai ko baka ji?" Ta buqata.


Bai bata amsa ba.. Taji haushin kanta ma datai masa magana.


Wani irin daki suka shiga da saita wuni a tsaye a wajen bata gama qarema kyawunsa kallo ba.


Ya zauna kan daya daga cikin manyan kujerun dakin.


"Ki zauna"


ya furta a hankali yana nuna mata waje a kusa dashi. Bata musa ba ta zauna.


Wata kyakkyawar mata ce magidanciya ta shigo dakin cikin shiga ta alfarma.
Sai taga matar ta mata wani irin kwarjini.


Kasa taga ya sakko ya tsugunna itama bata san lokacin databi yanda yai ba.
Saida matar ta zauna tukunna ya gaishe da ita cike da girmamawa...itama gaishe tan tayi....da fara.a ta amsa musu sannan taga ya koma kan kujerar ya zauna...itama tayi hakan.


"Babana an shirya kenan?"


Ta buqata. Cikin tausasawar murya yace


"yanzun zamu wuce nace saimun biyo ta nan mun gaishe dake."


"Aikam ka kyauta sosai ba zaka je da ita taci wani abu ba kuma kudan zagaya ciki?"


"Uhm uhm umma sai dai ko inmun dawo muna sauri ne kinsan ba jirgi zamu bi ba"


ya fada yana miqewa..
Saita tsinci kanta da sake tsugunnawa tace mata mun tafi.


Addu.a tai musu sosai. Kamun su kama hanya su fita.


Motar suka koma. Daga su sai driver din.


Tun dazun take mamakin yanda cikin motar yake.


Ba ta inda driver din zaiga me sukeyi saboda akwai barrier a tsakaninsu.


Hannu prince ishaq yakai ya taba goshinta. Ya sake taba kumatunta sanna ya koma cikin kujerar ya zauna sosai.


Husna kam batai mamaki ba. Kadan da aikin wannan bakin nataccen.




💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


1⃣5⃣





*I am sorry for the delay. Thank you for reading. May Allah's blessing be with you all. Amin Ya Rabb*





IPhone din shin ya dauko ya saka headphones yana sauraran wakokin larabci na Rashid Al Majeed.


Ita kam husna suna hira ne da ammar sai dai idan network ya dauke ta tsaya saiya dawo.


Can yace


"Tawan me kike yine haka??


"Muna hanyar abuja"


Ta bashi amsa.


"Abuja???"


Ya rubuto da alamar tambaya.


Tasan mugun kishi irin na ammar koda yaushe saiya tambaya ko natacce yana da kyau tace masa mummuna ne shisa ta kara tsanarsa.


Shirun dayaga tayine batai reply ba yasa yace


"ke dawa zaku je abuja? Kuma me zaku yi?"


"Nima ban saniba ammar haka yace mu tafi ta bashi amsa."


Yafi mintina goma bai bata amsa ba sannan yace


"husna dan Allah karki bari ya tabamin ke kar ki so shi....ki taimakamin ki kashe auren nan."


Wasu hawaye taji zasu xubo na tausaya musu.


Hannunta na rawa ta rubuta masa


"yanda bana sonshi shima haka bazaimin komai ba...kayi haquri saina kashe auren nan munyi rayuwarmu."


"Zanso kina kusa dani yanzun zanyi shirune ina kallon kyawun idanunki masu nutsar dani cikin wani yanayi."


Ya rubuto.


Ta sauke ajiyar zuciya,yama zata fara zaman aure da wani ba ammar dinta ba mai nuna mata soyayyarsa.


Battery dinsa ne ya dauke. Don haka ta sauka akan whatsapp din tana nazarin yanayi na hanyar abuja dan bata taba zuwa ba.


Jingina tai da kujerar. A hankali ta juya kanta ta kalli natacce. Ya lumshe idanuwan shi da alama bacci yake.


Taja dan karamin tsaki a zuciyarta tana fadin bacci da headphones.


Batasan me yasa take jin inta bar masa bata kyauta ba. Hannu tasa ta dauki wayar da take ajiye kan cinyarshi.


Yana jinta saboda ba bacci yake yi ba. Ta dauki wayar tana swiping dayake ba password ta bude.


Pause ta sakama wakar da yake ji ta ajiye masa wayar inda taganta.


Bude idanuwansa yai ya juyo inda take, a kasalance yace.


"Saboda me zaki tsayarmun da waka?"


Shegen shisshigina mana ta fada a zuciyarta. A fili kuma shiru tai ta kyale shi. Dan bata da abinda zatace masa.


Kunnawa yai ya sake komawa yanda yake. Itama shirun tai batama san sanda bacci ya dauke ta ba.


Jiyai ta kwanto masa kan kafada. Ya bude idanuwanshi, daman yasan wannan natacciyar kaya zata bala.in zame masa.


Kamata yai a hankali ya kwanto da ita kan cinyarshi dan yanayin yanda take yana ganin jikinta zai iya ciwo in ta jima a hakan.


Kallonta yake da wani yanayiba zuciyar shi da baigane ba.


Kawai kuma ya basar. Gajiya yai shima yaso ya zame kujerar yadan kwanta sai dai bayason motsa wannan natacciyar.


Yanda bayason a tashe shi in yana bacci haka bayason ya tashi wani.


Saman kafadarta ya dora hannayensa ya dora kanshi. Shima baccin ya dauke shi.


*


Husna tana bude idanuwanta kamshin shi ya cika kata hanci. Abu taji a kafadarta. Takuma ji dumi sosai inda take kwance.


Sai lokacin ta kula da yanayin da suke. Kawai sai taji kasala ta saukar mata. Motsin datai ne ya sashi bude idanuwansa.


Muryarshi da take a bude ta sake zama wata babba saboda baccin daya tashi.


"Dagani to, tunda kin tashi"


Ya fada.


Lallai ma husna ta fada a ranta. Shima fa a jikinta yake kwance dan rainin hankali zaice ta wani daga shi.


Ita bama tasan me take kan cinyarshi ba bayan alkawarin datai ma ammar dinta.


A kufule tace.


"Ka dagani tukunna"


Murmushi ya kwace masa. Tashi yai daga kafadarta.


Ya zuba mata idanuwansa da bata so saboda yanda suke saka ta ji.


Gefe ta matsa ta wani daure fuska har taso ta bashi dariya ma.


Kujerar ya saukar ya kishingida sosai ya koma baccin shi.


Husna ma rakubewa tai can gefe ta koma bacci.


Bata tashi ba sai da suka karasa cikin garin abuja.


Ta glass din motar take kallo tana yaba kyawun garin.




💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


1⃣6⃣


Yanayin tsari na garin abuja ya burgeta matuqa.


Zataso ace da ammar dintane sukazo dataji dadin zuwan.


Bude musu mota akai. Tana fitowa takalli yanayin ginin gidan batasan


"wow"


ta subuce mata ba.


Zagayawa tai dan zatonta zaa bude bayan motar ne su dauki kayansu.


Ganin ta tsaya yasa shi fadin


"Muje mana"


"Zan dauki kayana ne" ta bukata tana masa kallon da yake fassara wannan wacce irin tambaya ce?


Kallonta yai sosai kamun yace.


"Muje za.a shigo maki dashi"


Ganin ya wuce abinsa yasa tabi bayanshi


Tsakiyar wani qayataccen falo suka isa.


"Za.a nuna miki bangarenki. Inkina buqatar wani abu hadiman gidan zasuyi miki"


Ya fada mata.


Bai jira amsarta ba ya wuce.
Wata ce tazo ta rakata har bangarenta. Wajen ya hadu dan duk tsanar mammalakin gidan datai bai sa yaqi burgeta ba.


Wanka tayi dan tagaji sosai tunda bata samu tsarki ba balle tace zatai sallah.


Ta duba wayarta ammar bai dawo online ba har lokacin.
Ta soma kewarshi.


Tunawa tai ashe fa kausar na abuja.


Wani murmushi ya qwace mata.
Wayarta ta dauka ta kirata.


Bayan sun gama gaisawa tace


"Ke er uwa ina abuja fa"


"Wooo bani address zan shigo gobe in shaa Allahu"


kausar ta fadi cike da farin ciki.


"Ta dora da meye sirrin? Rabon da inji muryarki haka harna manta husna."


Dariya tai tace


"kausar kin cika zolaya akwai labari saikin shigo ke dai"


"Ba damuwa kimin text din address din fa karki manta."


"Zan miki yanzun in shaa Allah."


Husna ta fadi.


"Tam ina jira"


kausar ta ce sukai sallama.
Ajiyar zuciya ta sauke.


Yunwa takeji dan haka ta yanke shawarar sauka qasa ta tambayi address din gidan nan ta tura ma kausar.


Daya daga cikin hadiman gidan ta tambaya suka fada mata.
Zuwa tai inda aka shirya musu abinci taci wanda yai mata.


Bataga natacce ba baya gabanta kuma. Ba.a shigo mata da akwatinta ba tun dazun dan kayan jikinta ta mayar. Ta tsani yanda kamshin nataccen nan yake manne dasu.


Sama ta koma tai kwanciyarta dan ammar ya dawo online.


Hira sukai tayi bata sake fitowa ba har qarfe goma na dare.


Tasan Ammar ya tafi kallon ball yace mata suna da wasa.


Ko ya dawo ma ita dai bai kirata ba kuma bata neme shi ba.


Duk da gajiyar dake jikinta baisa bacci yazo mata ba.


Fitowa tai daga dakin baccin zuwa qayataccen falon dake saman nasu.


T.V ta kunna. Channel din yana kan star movies.
Bata canza ba dan tasan suna saka films masu kyau sosai.


Wani horror ne mai tashin hankali.


A tsorace take kallon amman ta kasa tashi ta sauya tashar ko ta kashe.


Lokacin da suka gama sha biyu saura.


Sai yanzun take dana sanin kashe qwayayen wajen da tayi dan ta dauka ba zata ma fito ba.


Ga gidan yayi wani shiru musamman data kashe t.v din.
Sanyin AC bai hanata jin zufa ba.


A hankali take tafiya zuwa dakinta.


Wani abu taji taci karo dashi ta saki wata irin giggitacciyar qara.


*


Sai juyi yake kan tanqamemen gadonsa ya kasa bacci. Dan yanzun wahala yake masa tunani baya barinsa bacci.


Nas ya kira yaji lafiyarsa sukaita hira.


Yana fada masa ya shirya fa dan suprised din da zai masa ya kusa.


Dariya yai duk da sautinta ne kawai yakan fita ya manta yanda launinta yake a xuci.


Sukai sallama.


Fridge din dakinsa ya bude duk apple din daya samu ciki ya cinye shi dan yau babu komai cikinsa sai shi.


Fitowa yai ya dibi wasu dan dare yayi balle ya sa akawo masa.


Mamaki ya cika shi ganin duk an kashe wutacen lungun.


Yama manta natacciya tana rayuwarsa ma gabaki daya balle kuma a gidan.


Tafiya yake dan ya lalubo switch din ya kunna.
Yaji wani abu ya kawo masa karo kuma an saki qara.


Tamkar wanda aka dauka aka watsa duniyar tunani zuciyarsa ta budo masa wani yanayi:


**** ****


Ta baya ya lallabo ganin bataji tafiyarsa ba. A hankali yasa hannu yaja jelar kitsonta guda daya data sauka har gadon bayanta.


Wata qara ta saki a razane hadi da juyowa.


Shi kansa ta bashi tsoron riqeta yai dam a faffadan qirjinsa yana shafa bayanta.


"Huddyna kin cika tsoro daga tsokana."
Cikin tabararta tace


"Yayana kaban tsoro sosai."


*


Iya tsoro kam husna ta tsorata numfashinta har barazanar daukewa yake yi.


Rungumeta taji anyi cikin wani faffadan qirji.
Qamshinsa taji tasan shine. Natacce ne ya tsoratata haka.


Kanta yake shafawa


"huddyna kin cika tsoro daga tsokana."


Ya fada batare daya sani ba.


"Huddy?"


Ta nanata a zuciyarta.


"Ammar"


zuciyarta ta sake furta mata.
Idanuwansa a rufe suke yanajin duminta dan singlet ce kawai a jikinsa da boxers.


Sai dai akwai wani abu daya banbanta.


Wannan ba kalar turaren huddy bane.


Jin an ture shi yasa zuciyarsa ta sake shi daga duniyar tunanin data watsa shi.


"Ya salam"


ya furta dai-dai lokacin data kunna hasken wajen.


Idanunta ta sauke cikin nashi.
Da gudy tabar wajen.


Dafe kai yai? Why? Meyasa zuciyarsa take masa haka ne?


Saboda me zata dinga kaishi irin wannan wajajen dai-dai lokuttan da qaddara zata jeho masa natacciyar yarinyar nan.


Jikinsa ya hada da nata duk da yana qaryata cewar yaji wani abu.
Amman abinda ya qona masa rai ba damuwa dayai da natacciya ba son ganinsa da batayi.


Sai kace wani dodo ko wanda yake da abin qi a jikinsa.
Jibi yanzun tana kunna hasken wajen suka hada ido sai tayi tamkar wadda tai kuskuren kallonshi tabar wajen.


Fasa daukar apple din yai ya koma daki ya kwata kawai.




💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


1⃣7⃣


Husna kam dakinta ta koma.


Kuka take sosai.


Ya zatai ma ammar haka? Wannan cin amana ne.


Tunda tasan natacce ne. Kamshin shi kawai taji tasan shine.


Bata manta yanayin qamshinsa ba tabari ya rungumeta a qirjinsa.


Yanayin rungumar dayai mata batasan ya zata fassara shi ba. Tanajin sawun hannuwanshi akan bayanta har yanzun.


Tana jin dumin jikinsa gauraye da nata.


Da sauri ta miqe ta shiga toilet. Bathtub ta shiga bayan ta cika shi da ruwa.


Soso da sabulu tasa ta durje ko ina na jikinta har ya soma radadi ko zata wanke abinda take ji.


Sai dai ga mamakinta yanayine daya samu waje daram cikin zuciyarta bawai iya jikinta bane.


Da ace zuciyar nan zata ciru. Data fito da ita ta wanke ta tas. Ta goge ko menene ya dasa mata a ciki. Saboda bata son shi sam.


Tai kuka harta gaji.


Tunawa tai wayarta a silent take da sauri ta janyota.
Missed calls na ammar har 26.


Text messages guda 10.


Maganar dayai mata a whatsapp 53.


Tana cikin dubawane kiransa ya sake shigowa.


Da sauri ta dauka


"Nawan"


Wani nannauyan numfashi ya sauke da har taji ta cikin wayar.


"Ina kika shiga haka?"


Ta tsani kanta ta tsani qaryar da bakinta yake shirin furta masa.


"Bacci ne ya daukeni nawan wayar na silent yanzun na farka naga kana kira."


Ta karasa maganar cikin sanyin murya.


"Wlh naji tsoro sosai babyna babu tunanin da baizomin ba. Gashi kincemin kin bishi abuja. Husna mutuwa zanyi idan na rasa ki. In ya tabamin ke zuciyata fashewa zatayi wlh kishi kasheni zai husna"


Ya qarasa muryarsa na rawa.
Hawayen dake bin fuskarta ta goge cike da tausaya mishi. Dayasan abinda ta bari ya faru yanzun........


Da sauri tace


"kana karyamin zuciya in kana tunanin zan hada shimfida da mutumin dana tsana. Ni taka ce nawan. Kai kadai bazan taba hada maka jiki da wani ba gara an dauki gawata da hakan ya faru."


"Hmm husna ba zaki gane me zuciyata takeji ba inba kashe auren nan kikayi ba naga kin zama tawa tunani kawai zai iya kassarani."


Sun jima suna waya kamin suyi sallama.


Washe gari tana yin sallar asuba ta koma bacci danko wanka batai ba. Baccin ne a idanuwanta sosai.


Wayar kausar ta tasheta wajen goma da yan mintina.
Ta fada mata tana hanya.
Wanka tayi ta shirya kanta cikin doguwar riga simple ta sakko qasa ta zauna.


Hadiman gidan ta fadama tana da baquwa su shirya mata wajen cin abinci na falon sama.
Kausar na sallama ta tashi da gudu taje ta ruqunqumeta tana tsalle tsalle.


Dariya take sosai


"yau mun banu husna kaman wata yarinya."


Dai-dai lokacin da prince ishaq ya sakko daga benen.


Kausar ta ganshi ita kam husna tsalle tsallenta take yi.


*


Tunda ya fara sakkowa yake jin dariya da tsalle tsallen husna.


Kallonsu yake da mamaki a tsahon ganin da yake mata ko murmushinta bai taba gani ba.


Kullum fuskarta kaman zata saka mishi kuka. Sai kuma hawayen tan nan da baya so.


Inta fara zubo dasu har wani ciwon kai yake shirin kamashi saboda dagula masa lissafi take.


Sai yau tana ta dariya. Baisan murmushi ya qwace masa ba ma.


Sai yaga ta qara kyau.


Ohh ya fada a zuciyarsa yarinyar da ta tsane shi ya zauna yana ganin ta qara kyau kenan ma ya lura tana dashi.


Kauda kansa yai.


Muryar kausar qasa qasa tace


"dan ubanki ki nutsu."


"Wai me kike kallo husna ta fadi tana juya."


Lokaci daya fara.ar da take fuskarta ta dauke.


Tsikar jikinta ta wani tashi duk da ta janye idanuwanta daga fuskarsa zuwa qirjinsa.
Yanayin dumin qirjin ya fado mata a zuciya ta girgiza kai tamkar tana so ta batar da abin ta hakan.


Hannun kausar ta damqa da niyyar janta suhau sama ganin natacce ya nufo inda suke.


Amman taqi.


Cikin qasaita ya iso inda suke.


Murmushi ya dora a fuskarsa.


Cike da girmamawa kausar tace masa


"barka da warhaka."


"Barkanki"


ya amsa yana dorawa da.


"Mungode da ziyara"


Murmushi kausar tayi tace.


"Bakomai Allah ya kara girma"


Kai kawai ya daga mata ya wuce abin shi.


Husna ta jata suka wuce suma.


Kan hanya taketa faman masifa


"meye na wani gaishe dashi harda girmamawa. Ai wlh kin bani haushi ba kadan ba.A hakan ma sai uban yangar tsiya"


Shiru kausar tai mata saida suka sami waje suka zauna sannan tace


"husna kinsan ko waye shi din?
Naga alama baki sani ba koh?"


"Kinga nifa baya gabana asalima ke nake jira kizo kiban shawarar yanda zan kashe auren nan. Ammar ya dawo."


Sakin baki kausar tai tana kallonta.


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


1⃣8⃣





To dimples group.


"Ba canai ki tsaya kina min wannan kallon kaman na samu haukaba nace miki ammar ya dawo yanzun haka ko yau da safe munyi waya dashi."


Husna ta fada tana kallon kausar cikin fuska.


Girgizata kausar tai tace


"Husna kina da hankali a jikinki kuwa? Kin manta kalar tashin hankali da muka shigane? Tabbas kin manta da har kike son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login