Showing 60001 words to 60293 words out of 60293 words
husna take ya dora hannuwanshi akan kafadarta.
Sumbatarta yai a hankali yana shanye duk wani fushi da take da yanayin kaunar shi.
Ture shi tai tana maida numfashi.
"Seriously gentle in baka gida ni kake bari da wahala. Daga ita har yasir. Garama Nur"
Dariya yai yace
"Kibarmun yara na. Idan na sake ajiye wani a cikinki zan dinga mishi hausa"
Zaro idanuwa tai tace
"Gentle ka rufamun asiri. Duka watan yassar nawa? And beside yara ne saika gaji dasu"
Murmushin sa yai. Yasan kishi ne yake cinta. Dan a cewarta ya taba ganin sarki da mata daya?
Hanci ya ja mata yace
"Hussy please mana. Banfa zama sarkin ba. Idan na riga mai martaba mutuwa fa?"
Bakinshi ta rufe da hannunta tana girgiza masa kai.
"Kar in kara ji"
Rungumeta yai a jikinshi yana fadin
"Tam kema karna sake jin hangomun rayuwa da wata matar bayan ke. Kin yarda?"
Kai ta daga mishi.
"You are my now and forever hussy"
Ya fada yana hada bakinshi da nata sukaji an buga kofar
"Mami. Yassar na kuka"
Cewar Nur(dayake hakan suke kiranshi. Shi yaci sunan mai martaba)
Da sauri prince ishaq ya saketa. Hannu ta saka ta goge mishi jan bakinta daya bata mishi lips tana fadin.
"Gentle ka shiga toilet din su yusra ka wanke fuskarka duk jan baki"
Mudubi ya kalla yaga ba komai fuskarshi ta riga da ta goge.
Juyowa yai ya nufota yana fadin
"Hussy zo nan?"
Da gudu ta fita daga dakin ya bita..........!!!
ALHAMDULILLAH.
Godiya ta musamman ga
-ummijay novels
-dimples novels
-taskar lubiee mai tafsir
-exquisite online writers
-strictly divorced diaries
-Yar baraya novels group
-Hausa novels da sauran da ba zasu lissafu ba.
Shout out to Architect Ishaq aka bifham. Thank you for being my inspiration throughout WATA BAKWAI.
Nagode da kauna da addu.o.in da nake sha daga dubban mutane masoya WATA BAKWAI 7.
Allah ya biya muku dukkannin bukatunku!!!
Th£ £xceptioπαl.
Karshe!!!