Showing 12001 words to 15000 words out of 60293 words

Chapter 5 - WATA BAKWAI BOOK COMPLETE by Lubna Sufyan.txt

19 Feb 2025

9158

a yanzun da wutar soyayyar ammar take tsarga mata.


Kwanciya tai kan katon gadon maganganun su na mata yawo.


Sanyi taji tanaji dakyar ta iya sakkowa daga kan gadon ta kashe AC din dakin ta koma ta kwanta.


Ta lullube amman jikinta kyarmar sanyi yake saboda zazzabin da ya lullubeta.


A haka asabe ta shigo ta sameta. Da gudu ta sauka kasa ta je ta fada a kira kamala a gaya mishi ya kira prince ishaq uwargida ba lafiya.


*


Prince ishaq kam tunda ya fita daga dakin husna. Ya sa aka kaishi lambu yai zamansa.


Dan sam zaman gidan duk da bangaren su daban dana natacce ya fita daga ranshi.


Baya son yanda take bata masa rai tana saka shi yana abu dan dole.


Yana kishingide kan daya daga cikin kujerun dake lambun ya lumshe idanuwanshi yana tunanin kalar zaman da zasuyi da natacciyar nan a abuja.


Wayarshi ta kama ruri. Yanaji ya share sai da tai har sau uku. A na hudunne ya dauko batare daya duba ba ya amsa ya kara a kunne.


Cikin ladabi kamala ya gaishe dashi kamun ya fada mishi cewar husna bata da lafiya.


Ya bude idanuwan shi a hankali yanajin tamkar duka nauyin duniya aka dora mishi akai.


Ina amfanin wannan auren da babu komai a cikin shi sai matsala da takura.


Yayi niyyar ya kira doc din kawai yaje gida ya dubata sai dai baya son karanta.


Wannan kuma zai nuna cewar bai damu da matarshi ba wanda gaskiyane.


Yadai damu da kare mutunci da martabar gidansu.


Dan haka ya kira cikin hadiman wajen yace ai ma driver dinshi magana yazo au tafi.


*


Yana shiga gida bangaren husna ya nufa.


Ya sallami hadiman da suke zagaye da ita. Gefen gadon ya zauna.


Yanda yaganta sai ta bashi tausayi. Hannu yakai ya taba goshinta yaji shi kamar wuta.


Cikin rawar murya tace.


"Karka sake tabani.... Bana so"


Bai san sanda murmushi ya kwace masa ba.


Cikin taushin murya yace.


"Save it saikin warke. I am stuck with you like you are stuck with me. Badon ina so hannuna ke kaiwa jikinki ba"


Baya son jin kanta. Saboda shi ya kamata ya daga mata kai. Ba wai ita ba.


Duk da yasan abinda ya kamata yai mata. Saidai bazai karya alkawarin daya daukar ma kanshi ba.


Doc dinsu ya kira.


Tashi yai ya shiga toilet dinta.


Ya wani yamutsa fuska ganin pants dinta da bra data wanke.


Karamun towel ya dauka ya jiko shi ya matse ya fito.


Bargon da take lillibe dashi ya janye.


"Banaso" ta fadi dakyar.


Ko bi takanta baiyi ba. A goshi ya fara dora mata towel din.


Ta zabura saboda sanyin da ta kara ji.


Hannuwanta duk biyun tasa tana rike nashi.


Dayan hannun shi yasa ya rike nata duka biyun gam. A dake yace.


"Bana son gaddama. Ba yanda za.ai muyi tafiya bakida lafiya. I am not rescheduling saboda ke"


Bata da karfin yin fadan. Ba kuma tason yana tabata. Musamman yau dataji muryar ammar.


Sai ta sake tsanar shi. Wasu hawaye suka gangaro fuskarta.


Bata manta abinda yai mata ba dazun. Da kuma wanda yake mata yanzun.


"Ka sakeni please. Dan Allah ka sakeni"


Ta fada tana kallon fuskarshi.


Hannuwanta ya saki yaci gaba da dora mata towel din a goshi.


Ta bude baki zata sake magana dan taga bai gane me take nufi ba aka kwankwasa kofar.


"Come in"


Ya fadi dan yasan yace in doc din yazo ya ce a rakoshi bangaren husna din.


Da sallama ta turo kofar. Ta gaishe da prince ishaq da ya amsa cikin mamaki.


"Kayi hakuri. Doc amir ya samu flat tire a hanya saiya kirani coz ina kusa daku fiye dashi"


Jinjina mata kai yai kawai. Ya nuna mata husna da take kwance.


Duddubata tai sosai da aune-aune.


Tace ma prince ishaq. Damuwace tai mata yawa.


Tana bukatar hutu sosai. Ta bada list na prescription din data rubuta.


Kira yai akazo aka karba. Doc din ta zauna saboda za.ayi allurai guda uku dan zazzabin ya sauka.


Ba.afi mintina sha biyar ba aka kawo.


Ai husna na kyalla ido taga allura ta mike zaune. Idanuwa cike taf da hawaye tace.


"Wallahi na warke. Dan Allah karka bari taimun allura"


Doc din ta kalli prince ishaq. Matsawa yai kusa da husna ya kamo hannuwanta.


A tsorace ta rike shi sosai tana magiya.


Tun tana karama harta girma sai an riketa ake mata allura. Bata sonta ko kadan.


Ko wani za.ayiwa hankalinta tashi yake balle kuma ace ita.


Hannuwan shi ya zame daga na husna ya tallabi fuskarta. Ya saba mu.amala da patients irinta da yawan lokutta a baya.


Musamman yara kanana. Cikin idanuwa ya kalleta yace.


"Pull yourself together. Babu zafi fa"


A rikice husna ke girgiza masa kai tana fadin.


"wallahi zan bika abuja karka bari tamun allura"


Girgiza kai yai a ranshi yana fadin saikace zuwan shi abuja da ita zabi ne.


Kamo ta yai. Ya dagota sosai ya rike rungumeta a jikinshi. Kiciniyar da take ta kwacewa ma taso ta bashi dariya.


Sake matseta yai sosai a jikinshi hakan yasa ta yin luf. Alama yaima doc din cewar tazo tai mata allurar.


Ganin tana kokarin zame skirt din dake jikin husna ya sakashi lumshe idanuwanshi.


Yanajin yanda husna ta sake rukunkume shi da shigar allurar.


Haka kawai yaji zuciyarshi wani iri.


Yanda take rike shi yana saka shi jin wani yanayi da baisani ba kuma bama yason ya fahimta.


.
"Na gama"


Doc din ta fada.


Kai kawai prince ishaq ya daga mata. Ya nuna mata kofa.


Ta tattara kayanta ta fita.


Yana rike da husna har yaji yanayin numfashinta ya canza alamar bacci ya dauketa.


A hankalo ya ajiyeta yana bambareta daga jikinshi.


Da wani irin yanayi a jikinshi mai wahalar fassarawa ya fita daga dakin yana ja mata kofa.
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Wata Bakwai 7


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Written by


Luβπα SufyΞ±Ο€


1⃣3⃣





Precious writer's forum (PWF) we are not the best but we are surely unique for we love what we do!!!


Da tunani barkatai a zuciyarshi harya tashi da safe.


Tun wajen karfe bakwai daya koma bacci bai tashi ba sai yanzun nan. Yana duba agogo har sha daya tayi.


Dakyar ya rabu da katifar yaje yai wanka. Ya shirya cikin wani kaya na karan miski brown.


Yayi kyau matuka. Har ya wuce zaiyi dining room din ya tuna da yar mutane da take karkashin kulawar sa bata da lafiya fa.


Yaja wani gajeran tsaki sam sam baya son matsala a rayuwar shi.


Bangaren husna ya wuce yaga ko taji sauki. Dan bai niyyar daga tafiyar shi ba saboda ita. Yanda aka lika masa aurenta haka aka lika masa tafiya abuja da ita.


*


Husna kam dayake ba sallah take ba. Tunda ta tashi tai wanka ta shirya cikin wata doguwar riga simple.


Suka sha wayarsu da ammar harya shirya zuwa aiki. Dan ya ce mata ya samu aiki a wani gidan mai.


Suna gama wayar ta kwanta shiru abinda ya faru tsakaninta da prince ishaq yana mata yawo.


Sai taji kaman tanajin kam shi har yanzun kan gadonta. Taja tsaki.


Bakin natacce ta fada a ranta. Tanata tunani har bacci ya dauketa.


*


Kwan kwasawa yai yaji shiru haka yasa shi turawa a hankali yaganta kwance tana bacci.


Babu karya tana da kyau. Shi kyan ta baya gabanshi.


Gefen gadon ya karasa ya zauna. Ya duba magungunan daya ajiye gefe suna nan yanda suke bata sha ko daya ba.


"Yarinyar nan ta rainani" ya fadi a hankali. Sai daya saka aka kawo plantain da fried eggs sannan.


Ba inda zai kwashi kaya ya tafi dashi yake fada ma kansa.


Hannu yasa ya shafi gefen fuskarta. Da sauri ta bude ido ta sauke shi a fuskarsa.


Ganin shi yasa ta saurin tashi zaune tana matsawa. Har haushin yanda take shakkar shi ta ba kanta.


Ga jarababben kamshin shi har ya gauraye dakin.


Hannu yakai zai sake tabata ta kara matsawa. Bai kobi takanta ba.


Ya matsa kusa sosai yaka UK hannu ya taba fuskarta ta rufe idanuwa. Ya taba wuyanta na minti daya yaji akwai sauran zazzabi.


Plantain din ya ajiye mata kan cinya da cokali a ciki yace mata.


"eat ki sha maganinki"


Ya wani hade rai yana kallonta kawai.


Husna ta kule. Bata son yana mata shisshigi. Inba naci ba me zai kawo shi dakinta.


Girgiza masa kai tayi alamar bata ci.


"Ki ci ki sha magani ko kuma ki zauna a dawo ai maki allura. I can't take you ko ina da wannan zazzabin"


Ya ce a gajiye. Kaman maganar kawai ta cinye duk karfin jikin shi.


A hankali ta dauki plate din. Turawa kawai take badan bakinta nada wani appetite.


Dan gara komai da allura. Banda auren natacce babu abinda ta tsana sama da allura.


Jitai inta kara amai zatai. Ta ture plate din. Matsawa tai ta dauko magungunan. Ta duba yanda zata sha su. Ta ballo saidai ba ruwa kusa.


Ga mamakinta prince ishaq ya tashi yaje inda fridge din dakin yake ya dauko mata swan da cup dayake a jiye kan fridge din.


Ya zuba ya mika mata. Saita tsinci kanta da danjin nauyin shi.


Ta karba cikin sanyin murya tace.


"Nagode"


Kai kawai yadan daga mata yanda yakanyi ma wasu cikin hadiman gidan in sun gaishe dashi.


Saida yaga ta shanye magungunan. Tana ta yatsina fuska yace mata.


"Kina jin ciwon kai?"


Ta girgiza kanta.


"Dizziness fa? Ko amai?"


Ta sake girgiza kai dan ya soma isarta. Shi ba likita ba ya tsare da tambayoyi.


Mikewa yai ya karasa daf da ita. Hannu yakai ya sake tabawa yaji yanayin zazzabin. Ta janye fuskarta.


Wani abu ya tsaya mishi a wuya. Ya rasa dame yarinyar nan take ji. Baya son ta zame masa kayane dan suna setting kafarsu abuja bashi da lokacin wannan shirmen.


Share ta yai ya matsa ya taba kumatunta. Ganin yanda bata so ne yasa shi dora hannun kan wuyanta.


Yabarshi akai fiye da yanda yake bukata dan kawai ya takurata. Tadai ki kallon shi harya dauke ya fita.


Zanin gado husna ta janyo ta goge kumatunta inda ya taba ta kuma goge wuyanta.


Amman da yake kaman yanda Allah ya zuba masa naci haka ma duk abinda yabar mata ajiki yake da naci.


Yaki fita sam. Ta ki daina jin dumin hannunshi da yanda tsikar jikinta ke tashi.


A fusace ta sakko daga kan gadon ta je wajen dressing mirror dinta. Duk wani collection na turare da take dashi saida ta feshe dakin dashi.


Jin turarukanta sunki korar kamshin nataccen nan yasata bude akwati nan da kayan kwalliya ne kawai a ciki da turaruka lefenta datai ma kanta alkawarin ba zata taba ba.


Tunda bata son mai kayan ba kuma tason abin hannun shi.


Kala uku ta bude daka gansu kasan masu bala.in tsada ne. Ta feshe dakin. Sannan taji yamata kamshi na daban.


Tana komawa kan gado ta kwanta ammar na kiranta.


"Assalamu alaikum tawan"


Ya fada tanajin fara.arshi cikin muryarshi.


Ta amsa da murmushi a fuskar ta.


Yanda yaji muryarta ya sashi tambayarta lafiya kuwa.


Tace.


"Nawan zazzabi nake danyi fa"


A rikice ya shiga jero mata tambayoyi.


"Ya Rabb. Yanzun ya jikin? Kinsha magani? Ko sai kinje asibiti? Husna ko....... "


Dariya tai ta katse shi da fadin.


"Ya kira likita an dubani har gida. Yanzun ma yazo yaban magani ya fita"


Lokaci daya muryar ammar ta sauya.


Can kasan makoshi yace.


"Husna karki soma son shi. Karya tabamun ke, husna in baki kashe auren nan ba wallahi zan iya mutuwa. Ki tausayamun"


Muryarta a tausashe tace.


"Relax nawan. Ka yarda dani mana. Ni bansan meyasa ya aureni bama. Wallahi bai damu dani ba. Bai taba yunkurin tabani ba."


Wani dumi taji inda ya tabata dazun tamkar waje na neman karyata zancenta. Ta kuma tuno yanda ya riketa da za.ai mata allura. Duk da dumin zazzabin da take ji bai hanata tuno nashi dumin ba.


Haka ta samu ta kwantarma da ammar hankali da sake jaddada masa alkawurran da bata san yanda za.ai ta cika shi ba.


*


Kan kujerar falon shi ya zauna yai shiru.


Kanshi ma ciwo yake. Yana so ya hada kayan tafiyar shi gobe duk da yanada kaya acan.


Amman akwai yan abubuwan dazai hada saboda yanayin tsaro. Ko da kwana hotel zai kamasu ba komai na can din yake son amfani dashi ba dul da cewar sababbi ne.


Wani lokaci yakan godewa halayya irin ta ummarshi da duk matsayinsu tai kokarin koya musu yin abubuwa da dama dakansu.


Takance kar matsayin da Allah yai musu ya saka su girman kai ko wulakanta na kasa dasu.


Su dauka cewa matsayinsu wani abune mai nauyin gaske da Allah zai musu tambaya akan yanda suka rike shi.


Duk da haka kamala ya kira dan ya yarda dashi sosai. Shi yasa ya hada mishi duk abinda yake bukata.


Ya kuma ce shine zai kaisu Abuja goben in shaa Allah. Dan haka kawai yake son canji.


A mota zasuyi tafiyar. Rabon shi dayai tafiyar fin awa daya a mota harya manta.


Ya sanar da kamal baya son security saboda hakanma na janyo hankalin mutane akan su.


Normal yake bukata ko da ta rana dayace. Yana son yayi abu kaman yanda kowa yake yi.


Yana son ajiye prince ishaq a gefe yai abu a ishaq dinshi zallah.






πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Wata Bakwai 7


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Written by


Luβπα SufyΞ±Ο€


1⃣4⃣





In dedication to billy galadanchi, safiyya, ummie, dimples, jidderh and all the members of ummie jay novels.


Tun wajen karfe tara ya gama shiryawa Sai dai baisan ko ita ta shiryaba ko bata shirya ba.
Fitowa yai babban falo ya sami hadima daya dabai san sunanta ba don ba damuwa yai da hakan ba.


Har qasa ta tsugunna kanta a sunkuye tace


"fatan yarima ya tashi cikin qoshin lafiya?"


Lafiya ya amsa a taqaice mulkin na motsa masa.


Yana son ya tura a ce mata ta fito sai dai yana gudun zata iya fadar magana a gaban hadimansa.


Baya qaunar yarfi da harkar yada girma duk da bawai son matsayin nasa na yanzun da na gaba yake ba.


Da kansa ya taka zuwa bangaren ta ya nufi dakinta. A hankali ya qwanqwasa.


*


Husna kam tunda ta tashi taji jikinta babu zazzabi sam. Tadai yi wanka ne tasa aka kawo mata soyayyen dankali tadan ci.


Tasha magungunanta dan bata da bukatar natacce yazo ya maimaita abinda yai jiya.


Dan ta kula namiji ne shi da yake yin abinda yaso babu kuma wanda ya isa ya hana shi inya tashi.


Chatting suke da ammar a whatsapp dan jiya da dare ya sata tai downloading sabo.


Taji an kwankwasa kofar. A zatonta asabe ce ta dawo kwashe kayan data kawo dan haka tace


"Shigo"


Tura qofar yai tana kwance da wayarta a hannu ta dago.
Saurin sadda kanta qasa tayi tana ci gaba da danna wayarta.


Wannan nataccen nema sai dai ya gaji da tsayuwarsa a wajen ya shigo ko ya koma.
Chatting din da take da ammar ya fiye mata komai na gidan nan.


Shi kullum yaita fama da kaya kaman wani dan sarki. Duk da tsanarsa da tai baya hana mayyar zuciyarta ganin yayi kyau.


"Ki fito mu tafi."


Ya fada cikin wannan muryar tasa ta yanga. Sai lokacin ta tuna yaune yace mata zasu tafi abuja.


A kasalance tace


"ba zani ba aina fada maka"


Wani abu yaji ya tsaya masa a wuya.


Inda ba.ai masa umarnin ya tafi da itaba sai dai kawai taga bata ganinsa.


Zuciyarsa ta dibe shi ta watsa wani lokaci can baya.


**** ****


"Yayana ni fa saina bika......yai dariyarsa


"huddy kiyi haquri ba dadewa zanyi ba kwana uku kawai Kuma zamuyi waya"


Ta sake goge hawayen dake bin fuskarta


"bana so kanamin nisa."


Sauke numfashi yai


"huddy ke kinmin nisa ai"


ya fadi a zuciyar tasa.


A fili kuma yace


"banson jan magana ko bacin rai. Umarni ne na cewar na tafi dake.Ki shirya nan da 15 minutes. I don't want to drag you myself, don't tempt me "


Ganin bata da niyyar cewa komai yasa shi ficewa.


Ita yanzun kam me zai bata mata rai bayan tana manne da ammar a whatsapp....wuni suke hira ko yana office ma haka da dare suna manne yana rikitata da voice notes dinsa.


Da batai niyyar shiryawa ba sai wata zuciyar tace yanzun in ma baki tashi ba dawowa zaiyi.


Kuma ta tabbata tsaf zai aikata abinda ya fada.


Maganar ma da take yi dashi lokacinta take bashi.


Tashi tayi ta sake kayan jikinta. Wani karamun akwati ta dauka badan tasan menene a cikin shi ba.


Gara ma ta bishi abuja din dan ya sake tabbatar da baya gabanta.


Mayafi kawai ta dora kan kayan jikinta taja akwatinta zuwa falo...inda wata daga cikin masu aikin tai saurin zuwa ta karbar mata. Fita akai dashi.


Natacce ne ya fito daga side dinsa sanye da alkyabba ruwan hanta mai cizawa da wata irin hula akansa. Bata so ta tsaya zuciarta ta misalta mata kyawunsa.


"Ungo"


ya fadi.....hannunsa ta kalla daya miqo mata batare data yarda ta kalli fuskarsa ba.


Alkyabba ce mai kalar tasa sai dai wannan akwai ado na mata a jikinta.


"Ki saka saboda zamu fara biyawa ta gida sannan mu wuce."


Karba kawai tayi. Bata son magana mai tsaho na hadasu inba dole ba.


Tanajin idanuwansa na binta har ta saka ba tare data kalle shi ba tace


"muje"


Gaba daya kamshinsa ne cike da alkyabbar jikinta. Ta kuma tsani yanda hancinta ke jin dadin kamshin.


Gaba ya shiga ta bishi a baya har zuwa wajen motar (Range Rover) wata fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login