Showing 9001 words to 12000 words out of 60293 words

Chapter 4 - WATA BAKWAI BOOK COMPLETE by Lubna Sufyan.txt

19 Feb 2025

9156

gidan tukunna zuciyarta da take dokawa tadan dai-dai tu.


Tana saka shade in dai zata fita amman ba kowanne lokaci ba.


Yauma ta saka ne saboda ya boye idanuwanta dan kallo daya zakai mata ka fahimci ta sha kuka harta godewa Allah.


Date din data gani ne ya sake tunzurata ta fita bada izinin mijin da aka daura mata ta fin qarfi ba....duk da sanin hakan ba dai-dai bane bai dameta ba.


Tunda ba tada mota a gidan ta yanke shawarar daukar drop zuwa diamond bank ta ciri kudi sannan kuma ta zo stop and shop ta siyi abinda take buqata.


Mamakin girman gidan take yi harda titi a ciki kaman na estate dinsu ta dan soma gajiya da tafiya dan ba sabawa tayi ba.


Gate tagani a garqame kuma babu kowa a wajen taji wani takaici ya rufeta takai mintina goma a tsaye a wajen wai ko zataga wani ya bullo tasa ya bude mata amman babu kowa.


Juyawa tai idanuwanta cike da hawaye tanata qoqarin tarbesu karsu zubo kenan fita ma in zatayi komin buqatarta saita sauke ajinta ta tambayi natacce kenan.


Bata kaunar abinda zai hada su magana da juna.


Tana son fitar nan kam ko dan gyaran jikinta ma dole ta fita....tafiya take ga nauyi da zuciyarta tai mata.


Ko a wanne hali ammar yake? Allah kadai ya sani tana dai da tabbacin tsakanin jiya da yau ya tsaneta!


Tasan abinda ya kamata tayi....duk da kashe di da mahaifinta yai mata.


Ta tabbata inda shi ya tsinci kansa a halin data tsinta zai fahimci yanda takeji.


Da wani sabon qarfin gwiwar data jima bataji shiba ta juya ta shiga gidan.


*


Prince ishaq kam keys din shi ya dauka ya shiga dakinshi ya dakko system ya dawo babban falo.


Yana zaune a falon hankalinsa akan system dinsa husna ta shigo.


Ta tsane shi wata irin tsana dabata san kalarta ba ko ganinsa bata sanyi.


Ganinsa kuma datai sai yake kokarin ruguza mata dan kwarin gwiwar da take ji.


Abin takaicin ma sai da taji gabanta na faduwa. Ga wani kwarjini da taga ya mata.


Tsaki taja cikin zuciyarta. Batason wannan abin da yake mata ko kadan.


Cikin muryar dabata gane tata bace tace masa


"kazo kasa a budemin gate zan fita."


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


1⃣0⃣


In dedication to the reader. May Allah's blessing be with you all. Thank you!!!


Yaji shigowarta sarai ya ci gaba da game dinsa.


Ya kuma ki abinda tace. Dame take ji da ba zata dauke shi da muhimmanci ba.


Dan shi bata gabansa bashi zai bata damar jin hakan game dasji ba. Ba ai macen da zata nuna masa iyakarsa ba. Ko da huddy ce kuwa.


Dole ta bashi girma ko bata so.


In tana son magana dashi ta zagayo ta kalli fuskarsa.


Husna kamar zata saka ihu don takaici.


"Magana fa nake maka kazo kasa a budemin gate."


Ta sake fadi cikin alamar qulewa.


System dinsa ya rufe ya miqe yana shirin nufar dakinsa.....tasha gabansa shade din idonta ta cire ta kalle shi cikin fuska sosai.


Tunda yake bai taba ganin kiyayya irin wadda yagani a cikin idanuwanta ba.


"Don na tambayeka abu zaka nemi wulaqantani?"


Da mamaki sosai yake kallonta. A. Lokaci daya kuma yana tambayar kanshi akan me zata aure shi.
Ta tsane shi!!!


Yagani cikin idanuwanta bata son shi. Ko da zaka auri mutum dan kudin shi da kalar tsanar datai masa kam zata hakura.


Sai dai duk wannan bai bata damar yi masa magana yanda take so ba.


Kamar wanda magana ke ma wahala yace.


"Not that i care. Ki rubuta ko me kike so aje a siyo miki"


Hawayen ta take iya bakin kokarinta wajen tarbewa. Da tana da bindiga harbe wannan nataccen zatai.


Me yasa baya ganewa ne. Me yasa yake son kara mata kunci har haka.


Muryarta na rawa tace.


"Kabarni da abinda yake damuna. Just kasa a bude mun gate"


Kallon nutsuwar nan ya tsaya yake mata.


Kallon da zaka rantse bashida wani muhimmin abun dazai daya wuce ya zuba mata idanuwan shi yana kallonta kamar yana hango har abinda yake bayan fatar jikinta.


Tun da ta kalli idon shi tai magana dazun ta sauke kanta kasa.


Tana jin yanda idanuwansa ke mata yawo. Saboda duk damuwar da take ciki bai hana kamshin shi damunta ba.


Bai kuma hana bangaren zuciyarta dake dokawa duk idan taganshi ci gaba da aikin shi ba.


Ganin suna shirin daukar mintina biyar bai ce komai ba. Yasa ta fadin.


"Bana son duk wata alfarma da zata fito daga wajenka zan je da kaina kuma zan shiga motar haya"


"Motar haya" ya nanata a zuciyar shi. Bawai bai san akwai bayin Allah da suke hawa motar haya bane.


Sai dai har ga Allah ya manta da wani abu waishi motar haya.


Saida yazo daf da ita wannan karon ma kanta a qasa hannu yasa ya dago mata da fuska ranshi ya baci.


Bakuma ya son ana bata mishi rai saboda bako yaushe yake iya controlling abinda yake aikatawa ba cikin bacin rai.


"Ba.a fadamin duk abinda ake so....idan kika qure haqurina ba zai maki kyauba. Daga randa kika tako kafafuwanki cikin gidan nan kike cin alfarmar da duk wanda yake karka shin sa yake ci."


Ganin yanda jikinta ke kyarma a hankali ta kuma kasa kallon idanuwanshi. Duk da idanuwanta akan fuskar shi suke.


Ya jinjina kai kamun yace.


"Ko hadiman gidan nan suke bukatar wani abu fita ake a siyo musu."


Ko ina na jikinta kyarma yake. Karo na biyu kenan daya kai hannun shi a habarta.


Kuma dumin hannun yana shigar mata wajaje da yawa a jikinta.


Hannunta tasa ta ture nashi hannun. Karfin gwiwar da take ji ya gama narkewa. Kawai so take ta samu abinda take bukata.


Karo na biyu da yai misalin matsayin yan aiki da nata.


Ta rasa abinda yasa hakan ya sosa mata rai.


Yana kallonta ta bude jakar hannunta ta dauko dan karamun diary da biro.


Ta rubuta always da recharge card. Ta rubuta pin din ATM dinta daga kasa taja masa layi.


Sannan ta rubuta 10k da take so a ciro mata.


Ta dauko ATM din 3k. Always ta 1k. Katin MTN na 2k.


Batare data kalle fuskar shi ba ta mika mishi takardar da kudin da ATM din.


Wani irin kallo yai mata sannan ya karbi takardar kawai yabar kudin da ATM din suka fadi kasa.


Bai jira amsarta ba ya wuce abinsa ya tsani wannan yarinyar da take ji da kanta.


Duk a yanzun ya tabbatar ba kwadayine yasa ta aure shi ba tunda yaga tsanarsa a idanuwanta.


Sai dai ya rasa dalilin dazaisa ta aure shi idan tana masa wannan tsanar.


Waya yai akawo always din guda goma da katin MTN na 5k.


Bai koma dakin shi ba saida ya bar umarnin in an kawo kayan akai ma natacciya bangarenta.


Yana shiga dakin shi ya sake duba list din yaga ta saka a ciro mata kudi.


Yaja tsaki. Baya son harkar karanta ko kadan da zubda mutunci.


Drawer din gadon shi ya janyo ya dauko rappers na kudi yan naira dubu dubu.


Na 50k ya dauka dan babu ma kudin sosai. Sai ya kira an ciro mishi.


Baya jin zai iya sake fita babban falo. Saboda yanda ranshi yake a bace.


Waya yai ma Kamala da yake kula da komai na gidan. Yasa a turo masa wata bangare shi.


Falon shi ya fito ya tsaya. Sai da tazo ya bayar da kudin a akaima natacciyar yarinyar can.


Kan kujerar falon ya zauna. Ya lumshe idanuwan shi yana karanto addu.o.in dazai samu nutsuwa a bisa koyarwar musulunci.


Sallama yaji. Ya bude idon shi. A ladabce hadimar da take tsugunne tace.


"Allah ya ja da ran yarima"


"Lafiya?" ya bukata muryarshi a dake.


A tsorace hadimar tace.


"Rankai dade. Uwargida tace a dawo maka da sakon nan"


"Kije da shi kawai"


ya fada yana kirga 1-10 cikin kanshi.


So yake ya nutsu ko yaya ne kamun ya fitar da kafarshi daga falon nan.


Cikin rawar murya hadimar tace.


"Rankai dade ban fahimta ba"


Cikin tsawa yace.


"ki dauki kudin nace yaren hausa ne bakya ganewa!!!"


Da sauri ta mike tana fadin.


"Allah ya huci zuciyar yarima"


Tana fita ya saka takalmanshi ya nufi sashin husna da tun ranar da aka kawo ta rabon da ko hanyar ya kalla.




💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


1⃣1⃣





This is for you "Maman Nu.aym. Allah ya raya mana Nu.aym ya albarkaci aurenki.


Thank you for being a big fan of wata bakwai 7.


Husna kam tana zaune gefen gadonta ta rafka tagumi da tunani kala kala a zuciyarta.


Sanda aka zo aka kawo mata kudi wai inji yarima. Wani abu taji tun daga dan yatsan kafarta har zuwa zuciyarta.


Waye shi dahar zaiyi zaton tana bukatar kudin shi?


Tana kallon mamakin da yake fuskar hadimar data ce ta mayar masa da kudin shi.


Kasa jurewa tai. Batasan lokacin da hawaye suka zubo mata ba tasa hannu ta goge su.


Kirjinta na mata wani irin zafi.


Turo kofar akai da wani irin karfi da saida karar tasa husna zabura.


Da yanayin yanda ya turo kofar haka ya mayar da ita y kulle. Tana kallo yasa mukullin jiki ya na shirin kullewa.


Gabanta ya shiga dukan uku uku.


Murya na rawa tace.


"What are you doing? Ka fitarmun daga daki. Bana........ "


Ganin ya cillar da mukullin gefe ya nufo gadon. Yanayin fuskar shi ya sa ta hadiye sauran maganarta.


Da sauri ta dinga jan jiki tana matsawa har takai karshen gadon. Ta takure jikinta.


Gefen gadon yazauna ya fuskanci idan take.


Cikin muryarshi da ta kara budewa saboda bacin rai ya kalleta sosai yace.


"Zo nan"


Yana bubbuga kan katifar kusa dashi.


Girgiza kai ta shiga yi tana kara matsawa jikin gadon kaman zata shige cikinsa.


"Bazai miki kyau ba inhar na karaso na jawoki da kaina"


Ya fadi a gajiye. Muryarshi da yanayin shi sun tsorata husna. Wasu hawaye suka gangaro mata.


Kallonta kawai yakeyi. Gani tai bata da wani zabi. Batason me yake nufi da ita ba.


Ko menene bata son yazo inda take ya janyota. Bataso hannun shi ya sake kaiwa jikinta. Bataso sam.


A yanayin daya fadi maganar tasan zai aikata. Saboda bata ga wasa a fuskarshi ba.


Gata Allah ya zuba mata tsoron tsiya.


A hankali taja jikinta ta matsa tsakiyar gadon tana hawaye.


Kallonta yake yi. Yanda duk ta firgice ga hawaye wani nabin wani.


"I really don't want to repeat myself"


Ya fada yana kallonta. A yanda yake jin shi komai zai iya faruwa.


Matsowa tai inda ya nuna mata. Jikinta ko ina kyarma yake.


Yaja wani uban tsaki a zuciyar shi. Daga shi har ita auren nan da akai musu an shiga rayuwarsu ya kula.


Kalli yanda jikinta yake kyarma kamar wanda ta ga wani mugun abu.


Ranshi ya kara baci. Bason tabata yake ba. Bata jin magana ya kula.


Ya kuma rasa dalilin dayasa take da karfin bata mishi rai har haka.


Bayason raini. Inhar yan son rage matsalar zaman su dole ya koya mata guje ma bacin ranshi.


Duk tsanar datai masa kuwa. Dan haka ya kamo hannuwanta da baisan mai taje ta tababa sukai sanyi karara haka.


Hannu daya ya saki. Yakai shi fuskarta ta janye.


"Stay still"


Ya fadi da wata irin murya da tasa ta tsayawa. Wasu hawayen suka kara zubo mata.


Hannu yasa ya goge su yana fadin.


"Bana son ganin hawayen nan. Magana nakeso muyi. Kina jina?"


Husna kam a tsorace take. Kai ta daga mishi. Tana kokarin tarbe hawayen ta kasa.


Hannu yakai ya dago mata fuska. Ya tsani yanda duk da hawayen fuskarta tayi kyau.


Cikin idanu yake kallonta dan yana son ya tabbatar da sakon shi ya kai mata.


"Yau ya zama ranar farko da zan aiko miki abu kisa a mayarmun. Matsalolin da nake ciki sun mun yawa bakuma nason kara su da gulmace gulmace tsakanin hadimai na, cewar matata ta raina ni"


Yanayin abinda tagani a idon shi sai taji sam abinda tai masa din bata kyauta ba.


Sai dai shima yanayin da ya saka ta shiga da wanda ta tabbatar yanzun haka ammar yana cikin fin nata bai musu adalci ba.


Bata son yanda jikinta yake bin umarninsa. Hannun shi dayake taba mata fuska take son turewa.


Saidai bata son bijirema umarninsa. Bata son mai zai iyayi ba. Ga dakin ya kulle hakanma shi yafi daga mata hankali.


Kai ta daga masa alamar.


"Eh"


A dake yace.


"Talk to me da bakinki bana son magana da kai"


Sai da ta hadiye wani miyau sannan can kasan makoshi tace.


"Eh naji"


"Good girl"


Ya fadi yana cire duka hannuwanshi daga jikinta.


"I am waiting"


Ya fadi a kagauce. Saida ta sa hannu ta goge fuskarta sannan tace.


"Me zanyi kuma?"


"Kinmun laifi and bakisan me ya kamata kiyi ba kenan?"


Da wata sabuwar tsanar shi tace.


"Kayi hakuri"


Jinjina kai yai ya mike daga kan gadon. Inda ya cilla mukullan dakin ya dauko.


Yana budewa wata hadima zata kwankwasa. Da sauri ta tsugunna kasa tana fadin.


"Allah ya kara maka lafiya"


Ko kallonta bai ba ya wuce.


Tashi tai ta karasa cikin dakin da sallama. Ta tsugunna ta mikama husna ledar hannunta.


Karba tai ta ce mata zata iya tafiya. Dan ta kula inba tace su tafi ba haka zasuyita tsugunno.


Zuciyarta yanzun bata natacce take ba. Ture shi da abinda yai mata tayi gefe daya sai zuwa anjima.


Ta bude ledar ta zazzago kayan ciki. Katin wayar ta dauka ta kankare su duka.


Ta lalubo wayarta tai loading hannunta ma rawa yake. Kaman yanda zuciyarta ke rawa.


Numbar ammar da take kamar tambari a zuciyarta saboda zaman datai ta saka ta danna kira.


Da duk ringing din da zatai da yawan hawayen da suke zubo mata. Sai da ta yanke bai dauka ba.


Ta sake kira bai dauka ba. Saida ta jera kira biyar bai dauka ba. Tanajin zuciyarta kamar zata fashe sabo da fargaba.


A karo na shidda ya daga muryarshi can kasa yace.


"Hello"




💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


1⃣2⃣





In dedication to my mentor Arc Haidar.


Ko a mafarki ko a ido biyu ko a cikin dandazon taron jama.a zata iya gane muryar ammar dinta.


Sai yanzun dataji muryarsa tasan kewar sa da zuciyarta tayi.


Numfashinta har wani barazanar daukewa yake.


Cikin murya mai matuqar rauni tace


"Nawan nice."


"Husna ta"


ya fada tasan shi sosai hakan yasata fahimtar yanayin muryarsa da alamar rashin yarda da cewar ita dince ta kirashi.


Shirun da yaji tayi ne yasa shi cewa


"husna da gaske kece? Tawan kimin magana dan Allah."


Muryarta na rawa tace


"nice ammar."


"Ya Allah"


ya fadi yai shiru.


Tasan kuka yake daga yanayin muryarshi.


Can kasan makoshi cikin kuka yace.


"Husna dan Allah kice mun mafarki nake. Kice abinda suke fadamun ba gaskiya bane."


Itama kuma kukan na neman cin qarfinta tasan idan ta kuskura ta fara batasan ranar barinta ba.


Dole ta zama mai qwarin gwiwa tai masa magana.


"Ka saurareni....wallahi bana son auran nan bana son wanda aka auramin ban taba son kowa ba sai kai ammar ka yarda dani."


Tun da take bata taba jin namiji saurayi babba kaman ammar na gunjin kuka haka ba.


Kukan shine ya karasa karyar mata da zuciya. Bata san sanda kukan ya kwace mata ba.


Sun fi mintina goma sun kasa magana kamun ya samu yace.


"me yasa zakimin haka? Ke baki san irin son da nake miki bane? Haba babyna komai da nake nema a rayuwa don na aureki ne."


"Nasani nasan haka wlh ta fada"


zuciyarta na wani tafasa. Lokaci daya zazzabi ya rufeta ruf.


Wani irin kuka take daga zuciyarta yake fitowa dan hawayen ma sun daina zuba.


Cikin kuka ammar yace.


"To ki kashe auren nan indai kina sona da gaske ba qarya kikemin ba husna"


Bata san ya akai ma bata taba kawo ma ranta wannan shawarar ba a tsahon sati biyu datai a wannan qaddararren gidan.


Wani sanyi taji a zuciyarta ta wanni fannin.


Hannunta tasa ta dafe kirjinta saboda zafin da yake mata.


"Ammar zan kashe auren nan na maka alqawari zamuyi rayuwarmu tare."


Tanajin yanda ya sauke ajiyar zuciya. Muryarshi harta shige saboda kuka.


"Husna ina sonki da yawa nasan ba zaki taba barina ba wallahi tun jiya dana dawo aka fadamin na dauka zuciyata zata fashe ne tunda nazo daki na kwanta jiran mutuwata nake...husna kece numfashina."


Murmushi tai duk da halin da suke ciki bai hanata jin son shi har ranta ba wanda ta jima bataji irinsa ba.


"Nima kasan ina sonka aiko?"


"Da auren wani akanki husna zai wahala zuciyata ta yarda da hakan"


Ya fadi a raunane.


Da sauri tace.


"Zan kashe auren nan. I promise you nawa"


Hira sukai tayi abinsu yace mata bara ya tashi yai sallah yai wanka.


Bata bari ya tafi ba saida tasa yai mata alkawari zaici abinci tukunna.


Duk da taji muryar ammar da alqawurransa masu sakata natsuwa.


Itama ta masa alqawarin da bata san yanda za.ai ta cika shiba.


Wani farin ciki take ji ammar bai tsaneta ba yana sonta har yanzun.


Wani bangare na zuciyarta yana son nuna mata kuskuren abunda suka aikata.


Ita kam koma menene bai dameta ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login