Showing 21001 words to 24000 words out of 60293 words

Chapter 8 - WATA BAKWAI BOOK COMPLETE by Lubna Sufyan.txt

19 Feb 2025

11488

duba kayayyakin. Wasu dogayen riguna data gani sun bala.in burgeta.


Gaba daya kayan sunyi kyau. Harda takalma. Flats din kawai ta dauka aka mayar da hill dan ba damunta sukai ba.


Gani tai kayan da yawa. Dole ta kira akazo aka daukar mata zuwa bedroom.


Wannan karin ba zatai ma kanta karya ba. Kayan sun bala.in burgeta. Harda hijabai aka kawo mata.


Taso ta yaba zurfin tunani irin na shi ta fasa. Beside shisshigi yai mata.


*


Kwanci tashi babu wuya wajen Allah. Haka rayuwar take tafiyar musu.


Abin har mamaki yake ba husna. Wai wata na hudu kenan da wannan kadararren auren nata.


Zamansun nan yana mata dadi. Balle a satikan nan da zatai kwanaki ko giftawar natacce bata gani ba.


Saidai ko in ta fito falo zataji nataccen kamshin shi din nan dayake tsaya mata.


Komai na amfani tana dashi. Dan haka bataga amfanin me ganinshi zai mata ba.


Sai biyu yazo dakinta. Duk lokuttan yana gaya matane zai je kano. Ta kuma rasa dalilin shi na fada mata hakan.


Matsalarta dayace. Ammar ya soma gajiya. Ya soma damunta kan maganar kashe auren nan.


Batasan ta ina zata fara ba. Kukantane kawai yake saka shi yai shiru.


Banda maheer bata waya da kowa a gidansu. Tayi kewarsu sosai.


*


Lokutta da dama mantawa yake da natacciyar nan dan abubuwa sun masa yawa.


Hidimomin da ya kawoshi garin abuja ya shiga yi. Hakan ya bala.in rage masa tunani har yammaci.


A hanyarshi ta dawowa gida yana bayan motar yana tunanin komawarsa.
Baisan ko rashin huddy bane yake saka zuciyarsa numfasawa natacciyar yarinyar nan. Yasata yi masa katsalandan cikin tunani.


Baya son tuna yanayin dayaji game da ita lokacin da jikinsa ya hadu da nata. Qamshinta. Idanuwanta da suke kallonsa da yanayin tsanarsa da tai.
Idanuwanta masu bayyana kome zuciyarta take ji.


Har yanzun idan ya tuna sai yaji wani iri. Ya girgiza bai taba ganin tsana da rauni hadi da tsoro irin wanda yagani a idanuwan natacciya ba.


Dafe kai yai. Ya Allah! Meke damuna ne haka? Yake tambayar kansa dan yaga daga jiya da daddare zuwa yau gabaki daya zuciyarsa ko ta kawo mishi tunanin huddy zata tattara ta danganto shi da natacciya.


Ya rasa wannan naci. Yau yakai kwana hudu bai sata a idon shi ba. Akan me zata dinga cuso masa kai cikin tunani.


Wayarshi tahau ringing ya dauka


"sweet Qani"


yagani a rubuce. Mamaki ya bayyana a fuskarshi.
Saboda number din naseer ce ta nigeria.


Dauka yai yakara a kunnensa hadi dayin sallama kaman yanda tsarinsa yake.


"Yaya ina qofar gidanka!"


Naseer ya fadi cike da doki.
Murmushi yai. Yakan jima yanzun bai hakan ba har manta kalarsa akan fuskarshi yake.


"Qanina babu sanarwa koh?"


Dariya yai


"Ai nace maka ka shirya zan baka mamaki ko ka manta?"


"Hakane harka shiga cikine?"


Ya buqata.


"Um um yanzun zan shiga wajen antyn nan tawa inga wannan data qoqarta wajen daukemin hankalin yaya."


Nas ya fadi cikin siga ta tsokana.


"Kai dai bakajin magana zanzo in sameka ne ai."


Dariya yake sosai ya furta


"Allah ya huci zuciyar sarki ishaq."


Baisan lokacin da dariya ta subuce masa ba. Kashe wayarshi yai sai yake jin kaman sabon abu.


Ta wani bangaren kuma ya na tunanin kalar tarbar da natacciya zatai ma kaninsa.


Kaninsa dayafi so duk cikin gidansu.


Dafe kai yai yana sauke wani numfashi.


Bayason damuwa sam.




💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


2⃣2⃣


*Kar ka dauka addu.ar da kake bata kaiwa. Karka dauka kai kadai kake cikin kunci a rayuwa. Idan ka samu kaci me kyau ka sha me kyau, me kake nema da rayuwa? Ko kasan akwai wanda idan ya samu yaci sau daya sai kuma washe gari? Ka zamana mai godema Allah. Ka zamana mai wadatar zuci. Alhamdulillah. Allah ka yayema masu damuwa damuwarsu!!!(Amin thumma amin)*


Tun dazun da safe da tazo fitowa ta hango natacce da sauri ta koma dan bata son su hadu.


Ya bala.in yin kyau cikin fararen kayan daya saka. Komai farine a jikin shi.


Bata sake fitowa ba saida tai sallar azahar. Falon saman tai zamanta tana kallo. Pillow din kujerar ta dauka ta gyara ta kwantar da kanta.


Kamshin natacce ya cika mata hanci. Da sauri ta zame filon ta cillar kan kujerar dake can nesa da ita.


Wani yanayi takeji data kasa fassara shi. Koya maganan natacce ya fado mata sai zuciyarta tayi wata irin dokawa.


Kawai kamshin shi dan naci ya tuna yanayin duminsa da maganar shi da komai nashi.


Ammar! Ammar kawai! Ammar shi kadai. Haka take ta nanatawa zuciyarta ko zata daina kaita inda bata da buqata ba kuma a buqatarta.


Wayarta ta dauka ta duba lokaci.Tai mamakin jan lokaci haka Kusan la.asar sai ta tsinci kanta dayin murmushi ammar ya kusan dawowa aiki.


Tana wata irin kewarsa yau.
Sallama taji da karfi ana kiran


"Anty! Anty!!
Gidan ba kowane???


Cike da mamaki ta mike tana sauka benen zuwa falon kasa.


Saurayine matashi mai kimanin shekaru sha takwas zuwa sha tara. Duka bazai wuce shekarunta ba ko zata girme shi bazai shige watanni ba.


Kallo daya tai masa taga yanayin kama da suke da natacce sosai. Saidai wannan ko hannun rigarsa bai kama ba a kyau.


Kyau! Ta nanata, zuciyarta bata ma ammar adalci dahar tama tsaya kula natacce na da kyau.


Murmushi yake mata


"lallai banga laifin yaya ba"


Dariya tai haka kawai taji ya shiga ranta tana son mishi kirki.


"Um kaji zolaya. Zuwa babu sanarwa haka?"


Ta fadi.


Dariya yai shima


"Anty afuwa naso in muku bazata ne. Shisa ko yaya ban fadama ba."


"Bai jima da fita ba shima ta ce tana qarawa da fatan baka kwaso yunwa ba dan bamu da abincinka gaskia"


Zaro idanuwa yai ya dafe qirji da


"fadin anty! Ke kin fara sakin na hannuna fa!"


Dariya sukai gabaki daya.
Sai taji ta duk wani iri duk da dawowar ammar farin cikinta ragagge ne. Amman yaron nan yasataji daban.


Da yanayin fara.arsa da wasanninsa.


"Bara na kira a shigo maka da kayanka ko"


Husna ta bukata.


Girgiza kai yai yace.


"Suna bangare na ai an shigo dasu"


Nas ya fadi yana dorawa da.


"Gosh am damn tired. Anty barin watsa ruwa"


Kamun husna tace wani abu harya wuce da gudu. Gidan ba baqonsa bane kuma yana da bangarensa a ciki.


*


Mamaki ya cika husna. Banda falo bama ta taba kula da komai a kasan nan ba.


Kodan yaushe ma take zaman kasan. Kullum tana can sama a zaune abunta.


Bata son natacce. Amman kaninshi ya mata. Yanayin shiriritarsu iri daya data maheer kaninta.


Murmushi tai ya debe mata kewar ganin maheer kadan.


*


Wanka Nas yai. Ya sake kiran mumyn shi yace mata yana gidan yaya ishaq.


Saiya huta sosai zai shigo kano.


Mumyn shi bata ma wani damu ba. Tasan tsakanin Nas din da yayanshi sai Allah. Yana iya kwana biyu bai kirata ba ya kira yayanshi.


Blue jeans ne a jikinshi matsatse. Sai riga fara kal data kama shi.


Fitowa yai ya samu husna zaune a falo tana kallo.


Kujerar da take opposite ta husna ya zauna.


Ba yanda batayi dashi ba akan yaci wani abu yace mata shi bayajin yunwa.


Sunata hira yana bata labarin yan school dinsu. Kalar pranks din da ake playing wa malamai da haukan yan makaranta dai. Zaka rantse sunyi shekara da sanin juna.


Kamun daga bisani wani comedy a new world cinema ya dauke musu hankali.


Dariya suke tayi ta sha su a gaddama wanda yafi wani shirme cikin yan film din.


Sam basuji sallamar prince ishaq ba.


Tsayawa yai yana kallonsu. Karo na biyu daya taba ganinta tana dariya haka.
Murmushi ya qwace masa dabaisan dalili ba.


Qarasawa yai ciki sai lokacin suka ganshi.


Kaman qaramin yaro naseer ya ruga da gudu ya ruqunqume yayan nashi.


Dariya yake da fadin


"Naseeru zaka karyani ne bakasan nagaji ba koh?"


Sakin shi nas yai kaman zai kuka yace.


"Yaya naseeru fa?"


Dariya prince ishaq yai sosai. Yasan ya tsani ace masa naseeru.


Kallonsu husna take ya qara kyau dayai dariya. Kaman bashi ba.


Sai ta tsincin kanta da son boye halin da suke ciki ita da natacce ko dan yaron nan da taji sunansa a yanzun.
Already iya zamansu da bai shige awa daya ba taji kaman ta saba dashi.


Duk da hakan bazai hanata kashe auren su da natacce ba.


"Sannu da zuwa"


Ta furta a hankali.


Kallonta kawai yake cike da mamaki saiya tuna nas na wajen dan haka yace


"sannunki da gida"


Wannan shine magana ta farko da suka fara cikin natsuwa da junansu. Sai takejin daban.


Tashi tayi ta basu waje su gana da junansu.


Sai da prince ishaq ya haura sama yai wanka ya dauro alwala sannan ya sakko kasa.
Dan yaga magrib ta kusa.


Hira suke shida Nas ya kalle shi a nutse yace


"Yaya matarka na da kirki i know babu mai maye gurbin huddy,sai dai zaka samu wadda zaka so kala daban"


Ajiyar zuciya ya sauke nas bazai gane ba yayi yarinta da yawa wajen da huddy ta bari babbane.


Babu macen da yake zaton zata so shi kaman ita. Ba kuma ya zaton zai sake samun so irin nata.


Komai na huddynsa dabanne. Shi din take so. Tasan shi fiye da kowa.


Badon kudi ko matsayin shi ba. Sone na tsakani da Allah.


Rayuwa kenan. Ba komai da kake mafarki bane zai zamo maka gaskia.


Bakomai daka tsara bane zai faru. Kana ta tsara rayuwarka kana hango abubuwa da dama. Allah ya gama tsara komai. Tsarin shine Mafi cancanta.


Murmushi kawai yai ma nas.


Hira suka ci gaba dayi cike da shaquwa.


*
Tana shiga dakinta kiran ammar na shigowa.


Dan haka tai kwanciyarta suka soma shan hira abinsu yana bata labarin wani film da ya kalla a office.


Sai da aka kira magrib sannan suka katse wayar da cewan zai sake kiranta can anjima.


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


2⃣3⃣


*Rayuwa ba abakin komai take ba. Shekara biyu cikakkiya zai wuce in wuce. Magana bata taba hadamu ba. Naji wani iri, naso ko da sau daya mun taba gaisawa. Allah ya gafarta maka Dan ladi. Allah ya ya saukaka maka kwanan farko nayau a kabarinka. R.I.J DAN LADI*


Ta jima a zaune tana addu.o.i. bayan ta idar da sallar magrib.


Dan tana mikewa ana kira. Isha.i dan haka ta sauke nauyi.


Jingina kanta tai da gado. Tana sauke ajiyar zuciya. Batasan ta yanda zasu soma magana da natacce ba.


Basa magana da ganin juna kullum ma ya ta kare da bugun zuciyarta duk idan sun hadu.


Ita da take neman makasar auren nan.


Kwankwasawa taji anyi a hankali ta furta.


"Shigo"


Kaman ko da yaushe kamshin shi ya cika mata hanci. Wannan karin sai taji gajiya ta saukar mata.


Batai kokarin fada da yanayin da take ji ba. Kyale kamshin tai ya ratsa ko ina na jikinta.


Da sallamar sa ya karasa inda take. A kasalance husna ta amsa.


"Nas yace in fada maki saida safe. Ya gaji sosai ya kwanta"


Ya fadi idanuwansa na yawo a fuskarta.


Cikin sanyin murya tace.


"Allah ya kaimu lafiya"


Ya amsa da.


"Amin"


Yana dorawa da


"Thank you"


Jin tayi shiru ya sashi mikewa.


"Good night"


Ya fadi bai jira amsarta ba ya fice abin shi.


Wani numfashi husna ta sauke da batasan tana rike dashi ba.


Wani iri take ji. Wannan kirkin nashi yasata jin daban.


Wayar ammar ta katse mata tunanin da take.


Dagawa tai tace.


"Nawan barin zo. Wanka zan sai mu sha hira"


Ya amsa da.


"Karki dade"


Wanka tai ta rigar bacci marar nauyi. Ta dauki wayarta ta kira ammar.


Bai dauka ba ya kashe ya kirata.


Sunata hira yace.


"Tawan ina jin tsoro fa. Jikina yana bani zan iya rasaki har abada"


"Hmm nawan. Dan Allah ka daina karyamun zuciya haka. Believe in us mana"


Shiru yai na wani lokaci sannan yace.


"Bakomai"


Hira sukai tayi har bacci ya soma daukar husna. Hakan yasa suka hakura.


Tai addu.a.


Bacci ya dauke ta.


*


Prince ishaq harya kwanta yana mamakin karamcin da natacciya taima kanin shi.


Shi mutum ne da baya manta alkhairi ko ya yake. Sannan indai kai masa mutunci komin kankantarsa yakan ji dadi.


Yana son Nas sosai. Duk wanda ya nuna ma Nas kauna dole ne ya samu karammawa a wajen shi.


Zai kokarin ganin ya mata mutunci gwargwadon wanda taima kaninsa yau.


A karo na farko a watannin nan da bacci yazo masa cikin sauki da nutsuwar zuciya.


*


Sai bayan tayi sallar asuba. Tai wanka tana zaune tana shafa mai, mafarkin da tai jiya ya fado mata a rai.


Wani irin dokawa zuciyarta ta shiga yi. Komai ya dawo mata.


Mafarki tai ammar da natacce na tsaye kowanne a gefenta.


Tana kallon ammar ta nufi natacce ta rike hannun shi gam. Suka tafi abinsu ko juya batai ba duk yanda ammar yake ihun kiran sunanta.


Harta gama shiryawa jikinta kyarma yake. Tana ta karyata mafarkin da tai.


Ko da ta kwanta. Kasa komawa bacci tai. Tunani ya mata yawa kanta harya soma ciwo.


Ko da sukai waya da ammar saida ya tambaya ko lafiya kuwa.


Tace masa kawai kanta ne yake ciwo. Zasuyi magana anjima.


Fitowa tai daga dakinta zuwa falon kasa. Ganin nas yasa murmushi ya qwace mata.


"Um me ake taci haka ba.a neman mutane?"


Ta buqata cikin siga ta tsokana.


Bakinsa cike yace


"Ina kwana anty"


"lafiya Nas ya gajiyarka"


Tai maganar tana zama kan kujera.


Shikam yana zaune kan kafet tsakiyar falon da plate din stuffed cabbage sai mug da coffee a ciki.


Saida ya hadiye abinda yake bakin shi sannan yace


"haba anty fushi muke fa. Jiya kikai tafiyarki.Inkin manta da yaya ni ai bai kamata a mantani ba. Ko ya kace yaya?"


Husna ta mayar da kallonta inda nas yakai nashi sai lokacin ta kula da natacce da haryanzun da tasan sunansa bata shirya daina kiransa da nata ba.


Sanye yake cikin wando jeans blue da riga mai dogon hannu baqa.


Karo na farko data fara ganinshi da shigar kana nan kaya.


Saurin dauke idonta tai daga kanshi kamin mayyar zuciyarta tace yayi kyau.


Ga yanda zuciyarta take dokawa fiye da ko yaushe saboda mafarkin da tai ya dameta.


Cikin muryarshi dakakkiya yace


"Ji bakinka a wajen wato inta mantani kai ba zata mantaka ba. You are nuts"


Muryarshi din nan kanta karin matsala ne. Tun dacan ko wani yai magana da muryarsa babba haka saita dago ta kalle shi.


Saidai ammar dinta muryarshi sanyi gareta ba kaman ta natacce ba da inyai magana take jin wani abu na miqewa a bayan wuyanta.


Sai yanzun zuciyarta ke tattara bangarori da dama da batasan ta kula dasu ba waje daya akan natacce.


Hatta yanda yake zama tattare yake da nuna isa da iko irin na jinin sarauta.


Dariyar nas ta katse mata tunaninta.


"Anty kinji yaya koh?"


Ya fadi a tabare da sai da ya sata dariya.


"Zo ga waje ki zauna"


Prince ishaq ya umarta.


'ki' din da yai amfani da ita yasata fahimtar da ita yake kasancewar babu wata mace a wajen.


Sororo tai tana kallonshi da wani yanayi data kasa fahimta.


Idanuwansa ya kafa mata yako yi sa.ar sauke su cikin nata, sai taji tamkar tana shirin nitsewa cikin wani irin qaton kogi hakan yasata kauda idanuwanta daga cikin
nasa.


Hannunsa ya miqa mata alamar ta taho ta kalli nas daya zuba musu ido.


Saita miqa masa hannunta yana riqeta taji tamkar wayar wuta ta jata zuwa yanayi na daban.


Rikon dayai mata sak da wanda yai mata a mafarki.


Ga zuciyarta da take zaton natacce dake zaune yana jin harbawar da take yi.


"Oh God this is so gross!


Nas ya fadi yana dafe kai. Ya dora da


"Inta zauna a jikinka dakina zan tafi"


Dariya sukai gabaki daya hakan yaba husna damar qwace hannunta daya riqe ta nemi gefensa ta zauna tana murza inda ya taba ko zata cire duminsa da yanayinsa daga jiki.


*


Komai yake yi saboda nas ne. Baya son da minti daya qaninsa ya fahimci auren nan bai dame shi ba.


Koh dan farin cikin da yaga ya samu na ganin kamar komai ya soma dai daita a rayuwarshi.


Ya gaji da qaryata zuciyarsa kan cewa yanajin wani yanayi game da yarinyar nan da baisan meye ba.


Sai dai daya kalleta zuciyarsa kan doka da tsanarsa da yagani cikin idanuwanta.


Zai iya cewa yana ganin tsana data fi tata a idanuwan mutane akansa. Kan mulkin da sam baya gabanshi. Shisa ma ko tunaninsa bayayi. Asalima da akwai abinda zaiyi ya gujema matsayinsa da tuni yayi.


Ya kula taji abinda yaji da jikinsa ya hadu da nata.Hakan ya mishi dadi saboda shine fa.


Prince ishaq komin tsanar da zata mishi dole taji wani abu game dashi.


Yanzun ma ya tabata ne dan yana son ta fara sanin zai iya duk abinda yaso. Kuma saboda nasir. Saida taba tan ya bude masa shafi a zuciyarsa da ya jima da rufewa.


Ajiyar zuciya ya sauke.




💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


2⃣4⃣


*Godiya mai yawa da fatan alkhairi ga duk masoyan WATA BAKWAI*


Ta rugasu tashi dan haka bata jira komai ba tai breakfast dinta. Ta samu waje ta zauna.


Text ta tura ma ammar taji ko lafiya dan bai kirata ba da safen nan.


Kaman ko da yaushe hancinta ya fara jin shi. Bata juya ba.


Karasowa yai inda take ya zauna gefenta.


Saita tsinci kanta da ce masa


"Ina kwana"


Cikin babbar muryarshi yace mata.


"Kin tashi lafiya?"


"Alhamdulillah"


Ta fada tai shiru.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login