Showing 18001 words to 21000 words out of 60293 words

Chapter 7 - WATA BAKWAI BOOK COMPLETE by Lubna Sufyan.txt

19 Feb 2025

9155

mayar damu."


Ganin tayi shiru tana wani kumbura fuska yasa kausar ci gaba da fadin


"da aurenki kike waya da gardi???"


Cikin bacin rai husna tace


"karki sake kiranshi da gardi. Bana qaunar mutumin nan ko na qaramin lokaci. Idan na zauna dashi son ammar kasheni zaiyi. Na tsane shi kausar dole ne na rabu dashi na auri wanda zuciyata take muradi."


Husna ta karasa tana goge hawayen da suka taru a idanuwanta.


Girgiza kai kausar take cikin tashin hankali:


"kin samu tabin kwakwalwa. Kuma kina gab da saka ammar da duk masu sonshi cikin tashin hankali da rudu. Husna kinsan wa kike aure?"


Ta qarasa maganar cikin rawar murya.


A zuciya husna tace wai natacce din nan waye shine?


Fine a yanzun tasan yanada alaka da sarauta ko dan cikin gidansu data gani. Saidai bai dameta ba.


Tunaninta bai taba je mata wajem bama.


A fili kuwa girgiza mata kai tayi alamar a.a.


"Prince ishaq"


kausar ta fadi tana ci gaba,


"dan sarki kabeer. Wanda yake jiran gadon mulkin garin kano.Husna zaki jefa rayuwar ammar cikin garari inhar ya gane abinda kike. Meyasa ba zaki haqura da ammar bane ki zauna gidan aurenki? Ba kowacce qaddara ake sauyawa ba."


Wata irin dokawa zuciyarta take. Idanuwanta cike taf da hawaye tace


"kausar ki taimakamin wlh bazan iya haqura da ammar ba. Nayi qoqarin hakan na kasa."


Hannunta ta riqe tana fadin


"husna babu yanda zamuyi da Hukuncin Ubangiji, ammar ba mijinki bane."


Fisge hannunta tai a zuci tana fadin babu wanda ya isa ya rabani da ammar ko sarkin ne ma da kanshi ballantana dansa.Saina kashe auren nan ko ta yaya.


A fili kuwa ta goge fuskarta tace Allah yai mana jagora mubar maganar nan kausar sai wani lokacin.


Tashi muje ko breakfast banyi ba.


"Hmm mudai je nikam a qoshe nake."


*


Kausar ta wuni gidan. Da zata tafi ma ta sake ma husna kashe di.


"Kinga ki rufa mana asiri husna. Har yanzun su abba basu gama hucewa dake ba. Karki jawo wata sabuwar matsalar"


Fuska babu walwala husna tace.


"Nafa jiki da kyau. Yanzun yaushe zaki kara dawowa? Ko nice zanzo?"


Fito da idanuwa kausar tai tace.


"Rufamun asiri. Ni yar ubana. Duka satinki nawa da aure daza ki soma yawo. Zan dawo in shaa Allah"


Dariya husna tai tace.


"Yasan da hakan ya jajibo ni har abuja"


Girgiza kai kawai kausar tai ta wuce tana fadin.


"Sai munyi waya"


*


Falon kasa tai zamanta tana ta kallo.


Kamun daga bisani ammar yazo online su sha hirarsu.


**


Satinsu uku kenan abuja. Husna zata iya cewa tun ranar da sukai karo da natacce.


Magana bata sake hadasu ba.


Zasu hadu ko a falon sama. Ko na kasa tana zaune. Ko wajen cin abinci.


Tun satun da sukazo sau uku a haduwar da sukai zai taba fuskarta da goshinta yaji ko da zazzabi.


Badai magana yake mata ba. Wasu lokuttan idan yazo ya ganta a zaune babban falo shima zai zauna.


Sai dai taji idanuwansa na mata yawo alamar yana kallonta.


*


Prince ishaq kam hidimomin shi kawai yake.


Yanajin dadin yanda natacciyar can bata damun shi.


Bata zame masa kaya ba kaman yanda yake zato.


Asalima ya sake kula haduwarsu sai dole. Kawai dai bashida lokacin batawa ne akanta a yanzun.


Amman daya dan samu time dole in yana waje ta dinga kallon shi indai tana son zaman lafiya.


Badon ya damu da ita bane. Aa kawai ya damu da ta girmama shine bai kuma son dalili ba.


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


1⃣9⃣


This is for you Namesake(iLubiee). Thank you for the support and encouragement. May Allah bless you.


Tunani yake in ya tafi har kano bai fada ma natacciya ba sam bai kyauta ba.


Yasan ba magana take hadasu ba sam. Amman duk da hakan baya son rashin adalci.


Beside zai fada matane kawai ko da wani abu ya faru. Tashi yai daga kwanciyar da yake ya fito.


Ya koyi sa.a ta rage masa wahalar zuwa bedroom dinta dan tana zaune falon su na sama tana kallo.


Gidan ba kaman na kano ba. Da kowa yake da part din shi. Duk da nan dinma dai part dinsu daban amman falo ya hadasu.


Sallama yai mata. Yana neman waje kusa da ita ya zauna.


*


Kamshin shi kawai husna taji tasan ya nufota.


Ta lumshe idanuwanta ta budesu a hankali. Batason fitina da yammacin nan.


Cikin sanyin murya ta amsa sallamar shi hankalinta na kan t.v.


Remote ya dauka da yake kan Centre table din wajen ya kashe kallon da take.


Hakan yasa ta fuskantarshi. Idanuwanta a kasa.


Shisa bayason mata magana sai dole. Bayason yanda take yin kaman bata son ganin shi. Kaman wata kazanta ce a jikin shi.


A nutse yace.


"Zanje kano gobe in Allah ya kaimu. But ba dadewa zan ba. Kwana uku zuwa hudu"


Shiru tai ta kyale shi dan bataga dalilin da zaisa ya fada mata ba. Asalima taga zuwan shi kano ba damuwarta bane.


Ba magana suke ba. Saitai kwana biyunma bata saka shi a idonta. To wacce gulmar zata kwaso kafafunsa yanzun?


Kilanma da yai shiru har yaje ya dawo ba kula zatai ba. Bama ta damu ba.


*


Abu na farko da ya tsana shine yai magana ai shiru. Dafe kanshi yai na yan dakikai.


Ranshi ya soma baci. Bayason yanda take bata masa rai sam.


Muryarshi a dake yace.


"Magana nake miki"


Kaman wadda akaima dole tace.


"Naji ka"


Mikewa yai kawai ya nufi bangaren sa. Dan inya biye ta natacciyar nan zai yi abinda zaizo daga baya yana dana sani.


Saboda tagama kure hakurin shi.


*


Wani karamun tsaki taja ta dauki remote ta kunna kallonta.


Share bangaren zuciyarta tayi dake mata fadan cewar ko yankar naman juna suke da natacce dayazo yace mata zai tafiya tai masa addu.a


"Allah ya tsare hanya" ta fada a hankali dan tasan ba zata zauna lafiya da zuciyarta ba inhar bata fada ba.


Zatai tajin wani irine tunda ba sabawa tai ba.


*


Tun da yai asuba baima koma bacci ba. Dan jirgin karfe 9 na safe zaibi zuwa kano.


Bayason ya kwanta baccin bai gama isarshi ba yai ciwon kai.


Tun takwas yagama shiri. Babu wasu kaya dazai dauka. Dagashi sai I.D card sai wayoyi.


Driver ya dauke shi daga gidan zuwa Airport.


Headphones ne a kunnuwanshi yana sauraren karatun Qur.an.


Jiyai kaman driver din na magana kasancewar bai kure maganar ba.


Ya saka pause ya zare daga kunnuwanshi yace.


"Magana kake?"


A tsorace yace.


"Rankai dade kamar ana binmu ne. Tunda muka fito gida wannan motocin ukku suke biye damu"


Tunda driver din ya soma magana zuciyar prince ishaq ke dokawa.


Yasan ba karamar wauta yai ba fitowa babu security. A nashi zaton duk wannan zai kara janyo hankalinsu ne.


Bai zata sun biyo shi abuja ba. Addu.o.in tsari ya shiga karantowa dan yadan samu nutsuwa.


"Kaci gaba da tuki. Karkai gudu"


Ya fada a hankali. Wayarshi ya dauka ya kira kamala.


"Muna hanyan airport akwai motoci uku suna binmu. Do what you can and make it snappy"


Kamala baima amsa shi ba ya kashe wayar.


Ko mintina biyar ba aiba tsakani suka soma jin jiniyar motar yan sanda.


Cikin rawar murya driver din yace.


"Rankai dade sun sha U-turn"


Wata ajiyar zuciya ya sauke. Mutanen nan so suke suga bayansa.


Har airport yan sandan suka rakasu. Tukunna.


Text ya turama umman shi saboda ya tabbata abinda ya faru a abuja dan kadanne da abinda zai iya faruwa a kano.


*


Wayar ammar ta tasheta daga bacci.


Muryarta can kasa tace.


"Hello"


Dariya ya kama yi mata.


"Tawan koma baccinki"


Kamun ta amsa ya kashe wayar. Kwanciya tai shiru dan inta tashi bacci takan dade batai magana ba.


Sai da ta wartsake sannan ta tashi. Brush kawai ta sake yi dan tai wanka tun da asuba.


Kawai sai take jin mugun kewar yan gidansu. Duk da babu wanda ya kirata har yanzun. Ta kuma son fushin suke basu huce ba.


Bayan ita akaima rashin kyautawa aka liqa mata nataccen can da bata so.


Wayarta ta dauka ta kira maheer kaninta. Wayarshi a kashe. Ta tuna safiya ce kuma ranar laraba. Yana makaranta.


Dining ta nufa ta ci dankali da kwai ta koshi abinta ta koma falo ta zauna.


Batasan gulmar datai zuciyarta tunanin ko natacce ya sauka lafiya ba.


Kallo ta kunna dan bata son yanda yai mata katsalandan cikin tunani.




💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


2⃣0⃣



To a young girl i have never known and will never get to know. May your gentle soul rest in peace. May Allah grant you endless peace.(XeeXee)


Allah ka yafe mana ka jikanmu da Rahmarka(Amin thumma amin)


Kwanan shi biyu kano yagama abinda zaiyi. Jirgin yamma yabi zuwa abuja.


A falo ya zauna. Sai lokacin duk gajiyar daya kwaso take tambayarshi.


Ya sake gyara zama cikin kujerar yana lumshe idanuwansa. Magrib kawai yake jira tayi yai sallah yadan kwanta.


*


Husna kam tana son fita sosai. Danma ta kira kausar ta kawo mata kayan sawa.


Akwatin data dauko shirmene kawai cikinsa. English wears ne da bata tunanin zata iya saka su tsautsayi ya gifta natacce yaganta cikinsu.


Sai fama take da alkyabba kullum. Data sakasu saita dora dan ta rufe mata jiki indai zata fito falo.


Sai hijab dinta ta sallah.


Tasan da wahalar gaske abarta ta fita. Bama tason zubda aji shisa sam bata gwada ba.


Zata jira sai ta hadu da natacce inya dawo kenan. Ta sauke ajinta a gefe tai masa magana ko dogayen riguna ne ta fita ta siyo tunda da yan kudinta a hannu taba kausar ATM ta ciro mata.


Falo ta fito. Kamshin shi ta fara ji kamun taganshi. Zuciyarta ta wani doka.


Hannu tasa kan kirjinta tana so ko bugun da zuciyarta yake zai dan dai-dai ta amman a banza.


Kafarta har wani rawa take abin takaici. Karasawa tai inda yake da sallama.


Idanuwan shi ya bude ya sauke su akanta da doguwar hijab sanye jikinta har kasa.


Amsa mata sallamar yai a kasalance. Sai taji muryarshi ta kara budewa.


Bata son yana mata magana saboda tayar mata da tsikar jiki yake.


Tana son taji muryar namiji babba haka. Saidai ammar dinta muryarshi yar karama ce.


Da sauri kamun kwarjinin dayai mata yasata kasa tambaya tace.


"Ina son fita zan siyayyar kaya"


Idanuwan shi kawai ya zuba mata. Babu yanda za.ai ta fita saboda yanayin tsaro.


Banda kamala babu wanda ya aminta dashi cikin gida. Kudi zai iya siyan kowa yaci amanarsu.


Baya son karin matsala. Ko dan darajar auren da aka liqa masa na natacciya. Tana karkashin kulawar shi.


Bazai bari komai ya samu yar mutane ba.


*


Husna kam harta kawo iya wuya. Dole ce tasa ta tambaye shi ya zuba mata idanuwansa yana kallonta.


A dakile tace.


"Magana fa nake maka"


Idanuwan dai su ya zuba mata. Ya gaji sosai. Idan yagaji baya son surutu. Wannan yarinyar bata ganewa ne. Ta kyale shi baya son naci.


Yana kallo ta tashi tabar wajen. Ya maida kanshi ya kwantar jikin kujera ya lumshe idanuwanshi.


Yana zaune a wajen har aka kira sallar magrib ya tashi yaje yai sallah. A masallacin cikin gidan yai zaman shi. Sai da yai sallar isha.i tukunna ya koma cikin gida.


Apple ya diba a dining din dake cikin falon ya wuce dakin shi ya ajiye su kan gado. Jikin shi duk ciwo yakr mishi.


Wanka yai sannan ya kwanta. Yana gama addu.a bacci ya dauke shi ko apple dinma bai ci ba.


*


Wasu hawaye masu dumi ta goge. Dan taje wajen shi ta tambayi alfarma ne zaisa ya wulakantata.


Zata hakura tai amfani da kayan da take dasu. Inyaso ta kira kausar taji yaushe zata sake shigowa sai ta sissiyo mata.


Wayar da sukai da ammar ne ma ya rage mata bacin ran da take ciki.


*


Washe gari da safe tun da ta gama baccinta ta tashi wajen goma. Sai da tai wanka sannan tasa aka kawo mata brkfst har daki.


Batason fita taga nataccen nan ya sake wulakantata kaman jiya.


*


Duk da wankan dayai gajiyar jiya bata gama sakin sa ba.


Shadda ce a jikin shi dinkin kaftan. Ruwan toka da hula mai cizawa kalar aikin jikin shaddar takalminsa ma haka.


Bai manta da abinda natacciya ta tambaya ba jiya. Maganar ce baiga damar yi mata ba saboda yagaji.


Bangarenta ya karasa. Ya kwankwasa kofar tace ya shigo.


*


Abinda take ci taji ya tsaya mata a wuya. Bata zata shi bane. Ca take ma daya daga cikin hadiman gidan ne.


Hijab din da take gefe tai saurin dauka ta saka.


Kallonta yake yi. Taso tabashi dariya ma. Kome take boye mishi oho.


Gefen gadon ya zauna ya mika mata dan notebook karami da biro.


Bai jira ta karba bama ya ajiye akan gadon kusa da ita. Kanta a kasa dan bata son idanuwanshi cikin nata.


"Ki rubuta abinda kike so. Da sizes za.a kawo maki. You can't go out a yanzun"


Yai maganar a nutse.


Yama raina mata hankali. Wato sai yanzun yaga dama. Muryarta can kasan makoshi tace.


"Kabarshi kawai na fasa"


Hannu yasa ya dago mata da haba. Bayason yanda bata iya kallon shi tai masa magana.


Ture hannun shi tai kanta na kasa. Tanajin hawayen da suka cika mata ido. Bata son yanda zuciyarta ke saurin karaya a gabanshi.


Sake dago mata da haba yai. Wannan karon data kawo hannu ya ture nashi yasa dayan hannunshi ya rike nata gam.


"Bana son gaddama. Ki kalle ni kimun magana. And ba tambayarki nai ko zakiyi siyayyar ba. Canai ki rubuta. Akwai bambanci tsakanin biyun"


Bata yi kokarin kwace hannunta ba saboda rikon dayai mata bana wasa bane.


Muryarta na rawa tace.


"Ka sakeni in rubuta"


Sakinta yai. Wannan yanayin irin na rannan dabai san fassarar shi ba yake ji.


Tafin hannuwan shi ya murza tare yana son ya goge yanayin da yake ji a jikinsu.


Bayason tabata. Saidai gaddamarta ce take ja masa wannan wahalar.


Yana kallon yanda hannunta ke rawa wajen rubutun. Hakan ya mishi saboda bata da girma da ajin da zata dinga raina shi.


Miko masa tai kanta a kasa. Ya tsaya ya zuba mata idanuwa.


*


Tanajin yanda idanuwansa ke mata yawo ta kuma san abinda yake jira.


Dakyar ta dago da kanta ta sauke idanuwanta kan fuskarshi.


Ta mika masa littafin da biro din.


"Good girl"


Ya furta a hankali sannan ya karba ya mike ya fice. Yana ja mata kofar ta diro daga kan gadon.


Mukullin tasama kofar jikinta ba inda baya rawa. Ta cire hijab din da kayan jikinta tai toilet.


Kwamin wanka ta shiga ta sakarma kanta ruwa. Soso da sabulu ta saka ta dinga gurzar hannunta inda take jin shatin dumin hannun nataccen nan a jiki.


Amman a banza tanajin shi har lokacin. Kuka tai mai isarta tana tunanin yanda zata soma bi ta kashe auren nan.




💝💝💝💝 💝💝💝💝


Wata Bakwai 7


💝💝💝💝 💝💝💝💝


Written by


Luβπα Sufyαπ


2⃣1⃣


*Rayuwa tana hadaka da mutane da dama. Saidai ko a mafarki ban taba zaton rubutu zai hadani da mutane masu karamci har haka ba.Mutanen da zasu karrama ni. Idan in tsaya lissafo su bansan ta ina zan fara ba.Ummijay da duk yan group dinta. Musamman ita kanta ummin, safiyya galadanchi da anty billy.Dimples da mutanenta. Godiya mai yawa.Anty lubabatu mai tafsir da nata.Musamman ita antin da kanta.Allah ya saka muku da alkhairi.UMMU SABREENA nagode da karamcinki. Wannan page din naki ne*


Dakin shi ya koma ya zauna. Saboda yana son duk abinda yake ji yadan tsagaita tukunna.


Yakamata ace ya daina taba yarinyar nan. Saidai ita take ja. Hakan ne kawai yake sakata ganin girmanshi.


List din ya duba. Riguna ne kawai ta rubuta. Kamala ya kira ya ce masa ya samu wata designer ya tambaye ta tai list na abubuwan da mata suke bukata a turo mishi.


Ba afi mintuna goma ba text ya shigo wayarshi. Wani dogon list yagani da karanta shi ma ciwon kaine.


Don rabin abubuwa bai san suba. Wasu kuma ana bukatar sizes. Shi bazai iya komawa bangaren yarinyar can ba.


Don haka yaima kamala text cewan ya dibi ko nawa yake bukata. A sissiyo kayan su taho da matar ta zabi wanda yai mata a koma da sauran.


*


Da zundumemiyar hijab dinta ta fita falo ta dibo fruits taji sallama bata mutum daya ba.


Haka yasata fitowa daga dining din babu shiri tana amsawa.


Hadimaine sunkai shidda da kaya niqi-niqi. Sai wata mata mai matsakaicin shekaru. A ladabce ta gaishe da husna.


Ta amsa fuskarta babu yabo ba fallasa. Hadiman suka ajiye kayan husna tace musu zasu iya tafiya.


"Ki zauna mana"


Husna ta bukata.


Da fara.a a fuskar matar tace.


"Bama sai na zauna ba. Ki duba kayan nan ki dauki size dinki. Zankoma da sauran"


Ta karasa maganar tana ware wasu ledoji.


Da mamaki husna ta dauka ta duba. Bra's ne da panties. Ta juya idanuwanta tadan dafe goshi.


Har ta bude baki tace bata bukata a mayar ta tuna jan kunnen da natacce yai mata.


Ta kuma san tabbas bada wasa yake ba. Dan haka ta duba ta dauki size dinta.


"Nagode fa"


Tace da matar.


"Babu komai. Nabarki lafiya"


Ta fadi tana tattara kayan da zata koma dasu ta nufi hanyar benen dan ta sauka.


A wajen husna ta tsugunna ta dinga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login