Showing 51001 words to 54000 words out of 60293 words
yanayinsa yake cike da farin ciki ya mata dadi.
Kome yake sonyi ita kam zata taya shi. Kaman yanda ya bata kwarin gwiwa ta kira iyayenta.
Dan jiya tai bacci wanda ta jima bata yishi ba. Taji muryar iyayenta. Ta gaisa da kowa.
Sun sa mata albarka. Har kuka sai da tai dan farin ciki. To name ita ba zata taya shi ya samu nashi farin cikin ba.
Tana nan zaune ya fito. Itama ta tashi tayo wanka.
Doguwar riga ta saka loose tai rolling mayafin akanta. Duk da babu kwalliya a fuskarta ta mishi kyau sosai.
Fita zasuyi tazo gabanshi ta tsaya. Hannuwanshi ta riko ta sauke idanuwanta cikin nashi.
So take yaga yanda tai nadamar abinda tai masa. Muryarta na rawa tace
"Har yanzun baka ce ka yafemun ba gentle. Nayi kuskure mai girma nasani amman.......... "
"Na yafe miki husna. Na yafe miki tun kamun ki rokeni"
Batasan lokacin sata rungume shi ba. Dan ji tai kaman ya sauke mata wani katon nauyi.
Hannuwanshi yasa ya rungumeta na wasu dakikai kamun ya sake ta.
*
Sai da suka biya wajen Nas. Dakyar ma yake musu magana saboda magunguna sun fara dibarshi.
Saida yai bacci tukunna suka fito. Su kansu basu san inda zasu je ba.
Hannun ta na cikin nashi. Hanya kawai suka diba.
Duk titin dayai musu su bi. Wani ad husna tagani na poster din wani film.
"O. M. G wallahi ina mugun son actor din can..... "
Ta fadi tana nuna ma prince ishaq. Kallon guy din yai.
"Vijay yayi fa. Kyanshi wani nutsatse ne. Kaga inyai dariya..... "
Mintsininta yai a hannunta da yake rike dashi. Hakan ya katse mata magana ta kwace hannu tana fadin
"Ouchhh gentle mana.... "
Fuskarshi daya murtuke ta kalla.
"Muna tare ne kike kiran wancan tikeken katon nada kyau?"
Kwashe wa tai da dariya.
"You are jealous...... "
Tace tana ci gaba da dariya. Kuma ya wani murtuke fuska zaka rantse bai taba dariya ba.
Da gasken kishi yaji. Ya za ai ma suna tare tace wani nada kyau. Son vijay din ya mata sauki. Nashi ne mai wahala.
Wucewa yai abinshi ta bi bayanshi tana dariya. Wajen ice cream ta gani da sauri tace
"Gentle ice cream"
"Nagan shi ai"
Ya fadi yana ci gaba da tafiya. Ganin zasu wuce yasa tace
"Saimun zakai fa"
Tsayawa yai ya dora hannayen shi a kuqu yace
"Mu koma wajen poster din vijay ki fada masa ya sai miki"
Rau rau tai da ido tace
"Yi hakuri. Kawai yana burge ni fa. Kama fishi kyau"
Murmushi ya kwace masa. Dan yasan sai dai yafi vijay kyawun zuciya da hasken musulunci.
Kama hannunta yai suka tsallaka wajen ice cream din. Guda uku ya sai mata ita kadai.
"Kai baka dauka ba fa"
Ta fadi tana dandana na hannunta. Ta wani lumshe ido dan bata taba shan ice cream mai dadin shi ba.
Ya girgiza mata kai yana kallon yanda take shan ice cream din yana burge shi.
Sha kaji da dadi sosai fa. Kamun yace wani abu ta mika masa. Saboda ya mata tsaho yasa ta mika hannu sosai.
Ta ko dangwala mishi a hanci da kumatu. Da sauri yakai hannu yana gogewa. Baya son sanyi.
Cokalin ya dauka ya dibo ya dangwala mata a fuska. Da sauri ita ma ta goge tana fadin
"Bana so fa. Sai ka samun danqo. Ni ka sha karyai melting"
Kadan ya diba ya sha. Yace mata
"Umm ba laifi"
Ta zaro ido
"Wallahi da dadi sosai. Bakinka bashi da taste"
Gira ya daga mata duka biyun alamar shi dinne bakin shi ba taste.
Jiranta yai ta shanye ice cream din sannan. Tace mishi
"A karo mu tafi dashi"
Ya girgiza mata kai yana fadin
"Ya isa haka. Sai kinyi mura ko?"
Yanayin yanda yai maganar ne kawai yasa tai shiru ba don ta koshi da ice cream din ba.
Fitowa sukai suka sake mikar hanya. Aikam suka shiga wani layi kamar mini market.
Ana saide saiden abubuwa a wajen. Wasu bangles ya hango sun mishi kyau sosai.
Yaja husna wajen. Ya taba yana cema mutumin.
"I want this and that. How much"
Da alama banda wanda prince ishaq ya taba da wanda ya nuna da hannu bai gane me yake nufi ba.
"ve kitane hain?(nawa suke?)"
Husna ta tambaya da yasa prince ishaq ya tsaya kallonta cike da mamaki.
"teen hajaar ma'am" (dubu uku)
Mai saida bangle din ya fada.
"Antim mooly? (gaskiya kenan?)
"Yes ma'am"
Juyawa tai ta kalli prince ishaq tace
"Ka dibo kudi saiya bamu canji tunda ba sanin kan kudinsu mukai ba"
Cike da mamaki ya dauko wallet dinshi ya mika mata. Ta dibo kudin ta bashi
Ya basu guda biyun da prince ishaq ya nuna ya dibo canji.
Sai da ta kamo hannun prince ishaq suka fito daga kasuwar. Kwace hannunshi yai ya tsaya
"Daman kina gane wannan jagwalgwalon hindi din kika barni da mai taxi dazun?"
Dariya tai tace
"Kadan kadan ne fa. Kuma shima dan hindi ne. Mai taxi din dazun urdu yake yi. Ka taho mu tafi"
Ya maqale kafada.
"Kafafuwana sun gaji. Mu sami taxi mu koma hotel dinmu. Ban labarin yanda akai kike ji"
Matsawa tai ta tsaya kusa dashi sannan tace
"Ina ganewa sosai saboda ina yawan kallon film dinsu masu translation. Amman kadan kadan nake rikewa fa"
Kallonta yake tana kara wani burge shi.
Haka suka ci gaba da labari har suka koma hotel dinsu.
Wanka yai ya fito. Itama tayi. Sukai ordering nama da lemo dan sun gwada cin kalar abincinsu rannan basu ji dadin shi ba.
Ita husna ma kadan taci. Dan duk a hanya yaita siya mata tarkacen duk da tagani tace tana so.
💝💝💝💝 💝💝💝💝
Wata Bakwai 7
💝💝💝💝 💝💝💝💝
Written by
Luβπα Sufyαπ
4⃣9⃣
Yauma bayan sun shirya sai da suka fara biyawa suka ce ma Nas zasu je yawo in sun dawo zasu biyo.
Idan doctors din sun yarda wajen shi ma zasu kwana.
"Go do your romantic yawo. Nikam am fine. Bama saikun dawo ba munyi waya"
Nas ya fadi yana musu murmushinsa yana jin dadin ganin yayan na shi cikin nutsuwa da walwala haka.
Saida suka dan kara hira tukunna suka fita.
Mai taxi din da suka hau yana gane turanci dan haka prince ishaq yace yakai su inda ake bada renting din mota.
Aikam shi ya rakasu. Kasancewar ba yan kasa bane yasa da suka biya kudin renting din motar.
Saida ya bada passport dinsu shida husna. Insun dawo da motar a basu abinsu.
Sai da suka shiga ne suka dauki hanya husna tace masa
"Ina zamuje ne wai? Ka wani kama mota kaman kasan gari"
Dariya yai ya daga mata kafadu yace
"Mu dauki hanya kawai muga gari. Duk inda muka gaji mu dawo"
Rigimar shi din nan tana bata mamaki a lokaci daya tana burgeta.
"Kawai ina son yanda nake da damar fita duk inda nake so ba wani fargaba. Ba kallon mudubi ko wasu na biye dani"
Ya fadi cikin sanyin murya da yasa ta jin wani abu ya tsaya mata a wuya. Sam rayuwar su bata mishi adalci wani lokacin.
Daurewa tai tace
"Mu na bin gabas saboda tafi sa.a"
Baisan lokacin da dariya ya kwace masa ba.
Itama dariyar tai. Suka dauki hanya.
Duk inda ya burge shi su fito su gani. Idan wajen siyar da abune su duba su siya wanda yai musu su fito.
Sosai yawo suke abinsu. Wani waje suka tsaya inda suka ga masallaci. Gashi nan maza da mata.
Fita sukai suka shiga. Sukai alwala. Husna ta wuce inda matan ke bi.
Tai sallah. Ta riga shi idarwa ma ta fito wajen motar tana jiranshi.
Saida suka shiga yace
"Wallahi ji nake kaman muyi zaman mu kar mu koma gida fa"
Ta kai hannu ta ja mishi kumatu ya ture yana dariya.
*
Yamma tayi zagayen gari kawai suke. Hadari ya hado. Iska aka fara sosai hakan yasa shi samun wani waje sukai parking.
Zaman su sukai cikin motar shiru. Ya jingina da kujera yana kallon husna da take danne dannenta a waya.
Ruwa ya tsuge ba shiri suka rufe gilasan motar.
"Yau zamu kwana anan kenan"
Cewar husna
A kasalance yace mata
"Inji waye da ruwan nan ya tsagaita zamuyi tafiyar mu abinmu"
Ba ai mintina ashirin ba ruwan ya soma daukewa ya kalle ta yace
"You see... "
Murmushi kawai tai masa suka kama hanya. Ko tafiyar mintina goma basuyi ba motar ta fara wani slow kamun ta dauke.
Suka kalli juna shida husna. Bude motar yai ya fita zaka rantse da Allah yasan abinda ya samu motar.
Yana bude murfin wani hayaqi na fitowa da yasa shi rufewa da sauri yana tari.
Husna ta fita da saurinta. Ta kalle shi yana kore hayakin da hannu yana tari.
"Mechanic gentle. Meye matsalar motar ne?"
Ta tambaya cikin tsokana tana danne dariyarta.
Hannuwanshi ya ajiye. Yana kallonta fuska a hade.
"O. M. G....... "
Husna ta fadi tana wata dariya harda dafa mota. Gaba daya hayaqin ya bule mishi a fuska.
Bakine har goshin shi kaman wanda kurar gawayi ta bata.
Dariya take sosai cike da mamaki yace mata
"Wai meke baki dariya. Mun makale a wajen nan kina dariya ko hussy"
Dakyar ta iya hadiye dariyar tace masa bakomai fa.
Tsaye sukai jikin motar suna jiran wani yazo wucewa ya taimaka musu.
Husna ta kauda kai gefe dan data kalli prince ishaq dariya kara kamata takeyi.
Wani suka samu ya ko tsaya. Babban mutum ne amman yanajin turanci sosai.
Shi ya duba musu motar sukai masa godiya sosai suka shiga suka tafi.
Sam bai kula da bakin dake fuskar shi ba. Duhu harya fara sanda suka maida motar.
Taxi suka hau suka koma hotel dinsu.
*
Husna ta kalle shi yanata shagwabe fuskarshi duk baki baki a jiki ta sake kwashewa da dariya.
Kamota yai tana kokarin kwacewa ya matse ta jikinshi yana fadin.
"saikin gayamun me kike ma dariya"
Jan shi tai wajen mudubi ta nuna masa fuskarshi. Ya zaro idanuwa sannan ya kwashe da dariya shima.
Hannunshi yasa ya shiga goge fuskarshi yana dariya.
"Hussy ke ko...... "
"bakai sarkin gyara ba shisa nai shiru ai....... "
Gani tai bai gama gogewa ba tace
"Akwai fa...... "
Yasa hannu ya ske gogewa. Ta girgiza masa kai alamar baiba tana matsawa gab dashi.
Hannuwanta takai cikin nutsuwa ta na goge masa. Kallonta yake.
Itana tsayawa tai tana kallon shin. Hannunta daya nakan fuskarshi.
Kama hannun dake fuskarshi yai da dayan hannu. Ya riko ta yana dora goshin shi saman nata.
"Husnaa...... "
Ya ja sunanta muryarshi can kasa.
Ta kasa amsa shi saboda gani take tana bude bakinta babu abinda zai fito sai karar bugun da zuciyarta take.
Koma manene take ji a game da prince ishaq babbane. Yanayi ne da bata taba sanin akwai shi ba.
Yanayi ne da babu kalaman da zasuyi adalci wajen bayyana shi.
Hannunta ta kwace daga nashi ta dora shi kan wuyanshi yana sake hade goshinsu tare.
Lumshe idanuwanta tai tana jin kamshin shi na shigarta yana kara saukar mata da abubuwa masu yawa.
A hankali suna goge wasu hotuna na rayuwar ta ta baya ba ma tare data kula da hakan ba.
Basu san iya lokacin da suka dauka ba. Dan prince ishaq sam baya son yanayin nan ya wuce.
Saboda komai na yanayin ya masa. Haka ya hango rayuwar shi babu hayaniyar mulki a cikinta.
Dakyar ya kamata yajata zuwa kan gadon. Kwanciya yai sannan ya rikota jikin shi.
Ko kayan jikinsu basu sake bama balle suyi tunanin yin wani wanka. Kwanciya sukai shiru abinsu.
Sun jima haka sosai kowa da abinda yake ji. Sallar isha.i suka tashi sukai. Babu mai bakin magana.
Wannan karon da suka koma kwanciya. Juya bayanshi yai yana jin wani zazzabin wahalar abinda yake jurewa na saukar mishi.
Ya lumshe idanuwanshi dayaji ta matso jikinshi ta kwantar da kanta a bayanshi.
Dumin numfashinta a kan wuyanshi. Bai juyo ba a haka yai musu addu.a.
Yana jin yanayinta bacci ya dauketa. Ya samu ya janye jikinshi ya shiga toilet ya sakar ma kanshi ruwa mai sanyi shine kawai saukin shi.
Alwala ya dauro dan baccin yaga alamar zai wuyar ya samu wajen shi.
💝💝💝💝 💝💝💝💝
Wata Bakwai 7
💝💝💝💝 💝💝💝💝
Written by
Luβπα Sufyαπ
5⃣0⃣
Rayuwa ba ta da wahala. Yau satin su uku a india. Kullum daga wajen Nas babu inda suke zuwa sai yawo abinsu.
Da wucewar duk wata dakika ta ranakun nan da shigar wata shakuwa ta ban mamaki tsakanin su.
Tare da mulkin dake jiranshi ya hango rikici kwance. Sai dai bai hango shigowar husna rayuwar shi ba.
*
Randa aka sallami Nas sauran kwana biyu kwanakin da suka diba ya cika.
Dan yaji sauki ne sosai. Karfin addu.ar da ake.
Taxi suka dauka su duka ukkun. Tare suka koma hotel din aka kama ma Nas nashi dakin kusa da nasu.
*
Prince ishaq ya dawo daga duba Nas ya shigo yace ma husna ta fito suje waje.
Bata musa mishi ba duk da dare ne. Ta dauki mayafinta suka fita.
*
Kasan hotel din suka shiga wani dan bakery suka siyi coffee suka fito.
Takawa suke suka samu wani lilo babu kowa a wajen. Zama sukayi akai.
Prince ishaq ya soma rocking dinsu. Husna tace
"Gentle karka yaddo mu fa"
Dariya yai.
"Kin cika tsoro"
Saida ta kurbi coffee dinta sannan tace
"Um um fa ba tsoro bane. Da gaskiyata"
Shiru sukai
"Nagode husna"
Ya fadi kaman daga sama.
"Godiyar me kake mun?"
Ta bukata dan ita bataga dalilin yi mata godiyar ba. Itama ya kamata tai masa godiya.
Na fargar da ita dayai daga halaka. Na zama dalilin shiryawarta da iyayenta.
Hannun shi ta riko. Sannan yace
"Nagode sosai husna. For everything"
Shiru tai dan batasan me ma ya kamata tace masa ba. Su. Jima sosai a wajen suna zaune ya a rocking dinsu kan lilon kamun yace mata
"Dare yanayi mu koma ko?"
Mikewa tai.
*
Washe gari su uku suka fita harda Nas din.
Siyayyar tsaraba sukayi. Nas sarkin shiririta. Yaita basu dariya.
*
Da daren ranar suka hada komai nasu washe gari karfe takwas a Airport tai musu.
Karfe tara jirginsu ya tashi zuwa gida nigeria.
***
NIGERIA
Wannan karon harda mumyn Nas akazo tararsu. Da wasu yan mata su biyu da husna bata taba gani ba.
Dayar bakace sosai. Amman tana da kyau. Dayar hasken su zaizo daya da Nas.
Bama su bi takan husna ba. Farar doguwa mai matsakaicin jiki ce ta rike nas din tana wani irin kuka.
"Am okay. Everything is ok billy"
Nas din ke fadi amman kaman ma ba jinshi take ba. Sai da suka sa husna hawaye.
Sakin nas tai takama hannun prince ishaq. Hannu yasa ya goge mata hawayen yana girgiza mata kai.
"He is okay. Komai zai wuce"
Husna dai kallon su kawai take.
Ya saki hannun yarinyar daya kira da billy ya janyo husna yace mata.
"Hussy ga sister na bilkisu. Tana karatu ne a saudi. Ga dayar kuma fauziyya. Su duka suna karatu ne a saudi. Billy ta gama ita fauzy ne da saura"
Murmushi taima husna tace
"Mungode sosai da karamci. Welcome to the family. Muna farin cikin shigowarki"
"Nima nagode bilkisu"
Gaisawa sukai da fauzy fuskarta babu yabo ba fallasa har hakan yasa husna kallon prince ishaq.
"Karki damu haka fauzy take da kowa. Baki ga nima kai kawai ta daga mun ba?"
Murmushi husna tan dan ta fahimci fauzy irinsu daya da prince ishaq miskilanci.
Dukansu gidansu prince ishaq din suka sauka.
*
Nan ma suka kwana. Saboda maganar bikin billy da duka saura sati biyu. Dan tun tana saudi aka sa rana.
💝💝💝💝 💝💝💝💝
Wata Bakwai 7
💝💝💝💝 💝💝💝💝
Written by
Luβπα Sufyαπ
5⃣1⃣
Husna da kanta ta kira gidansu ta fada sa bikin gidansu prince ishaq din.
"Mama ba zaki zo ki ganni ba"
Cewar husna
Tanajin dariyar maman nata ta cikin waya tace
"Husna nikam inzo in miki menene. Idan naji kina kafiya ma ya wadatar"
Husna ta langabar dakai tamkar tana ganinta cikin sanyin murya tace
"Tam shike nan mama. Ki gaishe mun da abba"
"zaiji in shaa Allah. Ki kula banda sakarci husna. Kiyita hakuri zaman yau da gobe sai da hakuri"
Ta amsa da
"In shaa Allah mama zan kula. Sai anjima"
Gaba daya tagaji da kalaluwan abincin da suke ci. Tuwo ma take marmari ita.
Dan haka ta tashi da kanta. Tasa asabe ta rakata store. Shakare yake da kayan abinci.
Ta dauko semo leda daya tasa aka rakata kitchen din da bata taba sanin hanyar da yake ba.
*
Asabe ta tayata. Gyaran cefane tai markada a blender.
Tuwo tayi miyar danyar kubewa da kaji. Ta saka a warmer abinta tasa asabe ta dauko mata zuwa bangarenta.
Saida tabari cewar a bare mata ginger a markada sannan ta wuce.
Sallar Asr tayi. Ta fito ta kima kitchen din ta hada ginger drink ta zubo a jug tasaka kankaru ta fito.
Tana zuwa babban falo prince ishaq na shigowa. Ga hannuwanta duk kaya.
Sallamarshi ta amsa. Ya tako inda take ya na kokarin karbar jug din.
Ta fito masa da idanuwa tace
"Gentle rufamun asiri kar hadimanka sugani ina saka future king aiki"
Dariya kawai yai yace
"Nikam kibani abin nan. Ba aiki zan ba. Ya burge ni ne zan sha"
Da sauri ta wuce tana fadin bafa abinda zan baka ka taho muje ka dan huta sannan.
Ya wani tabare fuska yana binta. Bangarenta suka nufa yasa rikici ai shifa sai ya sha abin nan na cikin jug.
Dole ta zuba mishi yasha yana neman kari
"Gentle zai kulle maka ciki. Please muje kayi wanka tukunna"
Hannun shi ta kama taja shi bedroom dinta. Da kanta ta tayashi ya cire alkyabbar shi ya shiga toilet.
Dakinshi taje ta dauko masa wani yadi marar nauyi fari. Ta feso mishi collections din turarukan