Showing 1 words to 3000 words out of 57176 words

Chapter 1 - NIDA MALAMATA BOOK COMPLETE BY Fatima Batula.pdf

16 Mar 2025

5536

[12/6, 9:38 AM] �° � D°�⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*


*By*
*fatima* *Batula*

*Dedicated*
*to* *my* *shadow*

wattpad@fatimaumarmoddibo

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

...............................................................

*~We are bearer's of so golden pen~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen,savour our words, for it will cause you no pain.~*

..................................................................

Page 1
.

.....Cikin yanga da ƙasaita take saukowa daga matakalar benan gidan, idan ta ɗaga kafa daya
kafin ta ƙara ɗaga ɗayar ta sai ta ɗau saƙonni,duk wanan abun cikin kayan makaranta take
yi,sikit ne ɗan ƙarami iya gwuwarta nevy blue sai rigarta fara mai ratsi-ratsin blue ba hijjab a jikin
ta sai hular da ke kanta.
Wata kyakykyawar dattijowar matar da ke zaune a cikin tanƙameman falon ta hango yadda take
saukowa daga benan murmushi tayi sanan ta ce "ƴar aljanna!! ke kullum sai kinyi latti,kinsan
ƙarfe nawa ne yanzu kuwa?
cikin tausasawa take mata maganar.

It kuwa wacce aka kira da ƴar aljanna ko a jikinta banda ma ƙara rage saurin da tayi.

Wanan dattijowar bata ƙara ce mata komai ba, binta da kallo da tayi ko kaɗan bata nuna
alamun ɓacin rai ko wani abu makamancin haka a fuskarta ba banda ma wani lafiffayan
murmushi da take yi .

Ƙamar ta ƙarye dan tsabar yanga,ta iso falon,kan jikin dattijowar ta faɗa ,kanta matar ta
taɓa,cikin so na nuna damuwa ta ce "Ƴar aljanna ko ba zaki makarantar ba ne? idan ba zaki ba
muje ki cire kayan sai ki gayamin inda kike son zuwa mu je"

Kamar mai tsoron magana ta buɗe bakinta cikin shagaɓa ta ce "Zani *Hajiya* bana son wahala
ne gashi wanan ƴar iskar malamar ce maiyar turanci zata fara shiga ajin ,ta kai ƙarshen
maganar haɗe da ramutse fuska tana kallon Hajiyar.

"Kam to kina jina,duk abinda aka miki ki kira ni,zasu ga wanda ya tsaya miki,ni da su ne shege
ka fasa ɗan halar sai yanka"

Washe ƙaramin bakinta tayi ,tana jin daɗi da alfahari,rungume hajjiyar tayi "Ina sonki hajiyata"

Tana faɗa ta tashi tabar falon cikin jin daɗi.

"Nima ina sonki ƴar aljanna sai kin dawo"

Tun kafin hajiya ta gama maganar ta bar falon.

Ɗaidai waata ƙatowar makaranta wacce kallo daya zaka mata ka fahimce makarantar bata
ƴaƴen yara ba ce,ta tsaro da navy blue da farin fanti,yanayin makarantar idan ka gani ka ce ba'a
j9 ba ne dan yadda suka tsarata,ƙatowar motar ta tsaya.

horn ɗaya direban yayi aka buɗe ya kunna kai,saida ya isa inda ake faking ɗin motoci sannan
ya tsaya,bata wani tsaya ɓata lokaci ba ta fito.

J S S 3
Aka rubuta a saman ajin,kai tsaye ta kutsa kai ba tsoro ba tantamar komai,kanta a ƙasa.

"Hy how dare u enter me class without any excuse"

Saida nayi da ƙyar sanan naji abinda take faɗi,dan yadda take turanci kamar ba ƴar 9j ba,ko
wacce tai karatu a kasar turai.

Ko ƙadan bata ji tsoro ba ta ɗago kai ido biyu suka yi,da wacce tai maganar

Tsaye take a gaban Allon,kyakykyawa ce ajin farko kallo daya zaka mata ka fahimce yadda
tsarin halitar jikinta yake,ƴar gajerace ba cancan ba,sirirya ce ga dogon hanci kyakykyawa,bata
da wani girman jiki amma kana kallon fuskarta zata san cewa wanan ba yarinya ba ce,dan ta
kwana biyu.
Tun a kallo na farko na gane ƴar iyaye ce,dan yadda take yamutsa fuska kamar tana kallon

ɗanyen kashi.

Ido cikin ido suke kallon juna,bata ɗauke idanta ba ta fara tafiya.

"Keee wacce irin dabbace mara hankali da wayau kuma jahila"
Cikin ɓacin rai da kausassaiyar murya ta faɗa.

Wani irin mugun kallo ta bita da shi mai cike da tsana ,amma sai naga ta sake wani ɗan karamin
murmushin keta ta ce "Au sari kinsan bana jin turanci balle irin naki me kama da yaren chaina"

Tana rufe baƙi yan class ɗin suka fashe da dariya wanda daman tunda ta shigo hankalin su ya
dawo gareta dan sun san sai anyi drama...

Fita tayi daga cikin ajin ranta a ɓace,ita kuwa ko a jikin ta daman hakan take so ,tana jin zafin
maganganun da Aunty ke gaya mata,shiyasa ta ke son ganin ɓacin ranta.

" *Sabreen* *Muhammad* *mai* *taƙama*"
Da ƙarfi ya kira sunan cikin faɗa.

"Kina ina?yana maganar yana kallon ƴan class ɗin.

Gaba daya ajin yayi shiru kamar ba halitta a ciki dan ko numfashi a hankali suke yi dan tsabar
tsoron wanda ya shigo ajin.

Cikin nuna ko a jiki na ta tashi daga gurin da take zaune ,hankali kwance ta nufi inda
suke,kallon Aunty ta fara yi wacce tare suka shigo class ɗin da shi.

Saida ta matsu kusa da shi sosai sannan ta tsaya ,ta kuma zuba mishi manyan idanuwanta
wanda ba alamar tsoro a tare da su.

"Me kika cewa Malama *Haulat* *Hashim* *Kabir* ?eyeeh ba dake nake ba,kin kafe ni da ido"

Saida ta kalle malama Haulat ɗin sanan ta dawo da kallonta gare shi "Ce mata na yi ni bana jin
turancin ƴan chaina,tamin na ƴan nigeria"

Shi kanshi bai san lokacin da dariya ta suɓuce mishi ba,dan duk makarantar kowa yasan
iyayenta gurin turanci amma ba wanda ya taɓa mata magana sai Sabreen.

Ganin shi ma ya fara dariya abin ya ɓata mata matuƙa ga yan ajin suna dariya,a fusace tabar
class ɗin,tsanar sabreen kuma da niyyar ɗaukar fansa.

Ganin ta fita yasa shi ma yai sauri yabar ajin.

wani annuri ya baiya na a fuskar sabreen dan jin daɗin yadda ta ga ranta a ɓace,komawa tayi ta
zauna amma duk ji take yi bata rama hulaƙancin da malama haulat ɗin ke mata.

Zaune take ita kaɗai a staff room tana tunanin wani irin abu zata ma Sabreen ta
huce,murmushi naga tayi wanda ya ƙara baiyana kyawun ramammiyar fuskarta,wato abinda
zata ma Sabreen tayi shi yasa ta yin murmushi.

Ƙarfe ukku daidai aka buga ƙararrawar tashi,koya hankalin shi ya koma gidan, gaba ɗaya
malamai da ɗalibai sun fito kuwa ya nufi hanyar gurin ajiyar motoci.

Har aka gama zuwa ɗaukan dalibai Sabreen tana zaune ita kadai ,ranta ya ɓace sai huci take
yi,tana turo baki,tashi tayi zata fita bakin get.

Da mugun gudu motar malama Haulat ta zo wuce wa,ta gabanta kamar zata ɗauke ta,da sauri
a ruɗe sabreen ta matsa har saida ta faɗi kasa,wani irin ƙululon takaici ya kamata,da zafin
nama ta tashi ta nufu motar.

Tana ganin ta nufota ,ta fito daga motar tana wani yamutsa fuska kamar wacce tai arba da
kashi

" U are very no what u are,okkk i forget u are illiterate ,baki da gwagwalwa ne ko a garin
mahaukata aka daukoki da kina ganin mota ba zaki iya kaushewa ba"

Tunda ta fara magana Sabreen ki binta da idanuwa wadanda sukai jajiir dan tsabar takaici.

Ita kuwa malama Haulat ganin ta cinma burinta yasa ta wuce ta barta anan tsaye, ta kuma ja
motar da karfi har saida ta watsa mata kura.

Wani lafiyayyan hawaye ya fara bin fuskar Sabreen wanda ita kanta bata san da zuwan su ba,
sai jin su tayi a fili ta ce tana huce kamar wacce tai faɗa da zaki "Hmm baki san waye Sabreen
Muhammad mai taƙama ƴar Aljanna ba ne,bana yafiya kuma bana biyar bashi zan rama
ramuwar gaiyya"
Tana faɗa ta sa hannuwanta ta fara goge hawaye tana faɗin "Hm kika sa ƴar aljanna hawaye
zai kin biyasu"

"To yah zanyi idan na gayawa hajiya ,A'a ba zan gayawa hajiya ba,ni da kai na zan ji da ita "

Ita fitowa bakin get ɗin direban ta ya zo ,bata ce mishi komai ba ta buɗe motar ta shiga.

"ƴar aljanna kiyi hakuri wallahi faci tayar motar tayi,jikin shi har rawa yake yi dan tsoron karta
gayawa Hajiya"

Banza tayi da kamar bata san da wani a cikin motar ba.

Sai magiya yake mata akan karta gayawa hajiya.

"To naji amma zai kamin abu ɗaya ta faɗa tana kallon shi

"to zanyi ƴar aljanna koma meye zanyi"

Murmushin mugunta tayi da jin daɗi ,harda sauke ajiyar zuci.

Daidai wani katafaren gidan direban yayi horn aka buɗe mishi,giɗan ya haɗu iya haɗuwa abin
sai wanda ya gani,dan tsayawa kwatanta muku sai ya ɗauke ni lokaci mai tsawo.

Tana jin ƙarar motar su,ta fito da sauri har bakin motar ta fito tana wace baki ,ita da buɗe mata
kofar hade da faɗin "Ƴar aljanna kin dawo tun ɗazun naji shiru ina ta jira hankali na ya tashi ina
fatan dai kina lafiya"

Murmushi tayi sannan ta rungumeta "Kina lafiya hajiyata yau bamu fito da wuri ba ne,wanan ƴar
iskar malamar ce ta tsayar da mu"

"Cikin nuna damuwa ta janye jikin ta tace"Wai ko sai na tura anje gurinta ne aja mata kunne,ko
na fitar da ke daga makarantar gaba ɗaya ma"

"A'a Hajiya ki barta kinji "

"to ni bansan duk wani mahalukin da zai ɓata miki rai,zan iya yin komai akan farincikin ki"

Daidai da isar su cikin katon falon wanda shi ma ya ƙyyatu har tsoro yaban dan tsabar kyaun
shi,ga wani asirtaccen kamshi wanda ya haɗe da AC ɗakin.

Murmushi tayi cikin shagwaba ta ce "Nima na sani hajiyata,amma tunda na ce ki barta kawai ki
barta zanyi maganin ta ,zan gwada mata ni ɗin ƴar gata ce"

"Hajiya bari na hau zama nayi wanka sai nayi sallah na huta"

"Yawwa ƴar aljjanna na manta ban gaya miki ba,ɗan india ya dawo an jima sai ki je ku gaisa"

Yamutsa fuska tayi yin sunan wanda ya dawo din"Wanan dan iyayin wanda aka je ɗauko mu
tare"

"Eh shi fa"

"Tabbb gaskiya ni ba zani ba saida shi ya zo "ta faɗa tana hada rai

"to shikenan ba zai kin ɓata rai ba,zan sa ya zo da kanshi,kinji hankalinki ya kwanta"

ta washe baki "eh hajiyata,ta haye sama ,a ranta tana faɗin yadda zata ganshi dan tun sanin
farkon da ta mishi kafin yaje india dan iyayi da kinibibi ne,to bari yanzu da yaje india....

Kasa kwanciyar tayi, tunanin abinda zata yi ma malama Haulat ta shiga yi, wani guntun
murmushi tayi dan ta gano abinda zata mata , gajiya da zama ita kaɗai tayi ta sauƙo falo.

Ba Kowa a falon ,har zata ɗakin Hajiya sai kuma ta fasa ta dawo ta zauna.

"Banza dabba daƙiƙiya mara hankali"
Runtse idanuwanta tayi tuno zafafan maganganun da malama haulat ke gaya mata.

Bata san lokacin da hawaye suka ƙankaro mata ba,sai jin su tayi ,ƙasa share su tayi dan
takaici a fili ta ce "Wallahi sai kin biya,baki san waye ƴar aljanna ba,bana yafiya kuma ba zan
yafe miki.

Wani irin hamshakin ƙamshi hancin ta ya ji,wanda saida ta lumshe ido tai wata irin ajiyar
zuciya ,ɗago da manyan idanuwanta tayi dan ganin wanda ƙamshin ke tashi a jikin shi.

Waw masha allah ,allah yayi halitta wanda duk wanda yai arba da ita saiya ɗan tsorata dan
tsabar kyau,kyakykyawa ne first class ga kwarji ni irin na jaruman maza ga izza,abin kamar a
novel,fari ne sul mai yalwar gashin kai da na ido da na gira,ga dugon hanci kamar na
indiyawa,duk da fuskarshi a murtuke take amma saida kyawun shi ya fito
Tsaye yake a kofar falon hannuwan shi gaba ɗayan su ya rungume su a ƙirjin shi,fuskar nan a
murtike sai yatsinata yake yi ,kamar wanda ya shigo bola.

Tun kallon farko da Sabreen ta mishi ta gane shi,ganin yadda yake yatsina fuska yasa ta kau da
kai ,ta ƙara gyara zaman ta rimot ta ɗauka ta chanja tasha ta kuma ƙara bulum,ta gafen ido take
kallon shi yakai saƙonni a tsaye a gurin kafin ya fara tawo wa,wani ƙululon takaici ya
kamata,Sabreen ta tsana mutum mai iyayi da kilibibi.
Dan guntun tsaki ta ja,ta cigaba da kallon tivi abinta.
Har tsakiyar falon ya iso,kallon ta yayi yana mamaki hali irin ta,wanda zai kira da rashin
tarbiyya,bai ce mata komai ba ya samu guri ya zauna yana wani yatsina fuska haɗe da hura
ɗan karamin hancin ta,yana kuma taɓe ƙaramin bakin shi,ni dai kuwa kallon shi kawai nake yi
ina murmushi dan abin ya mishi kyau.
Ganin bata da niyyar mishi magana gashi yana sauri yasa ya kalle ta a hankali cikin wata irin
murya wacce zamu kira da ƴan kilibibi ya ce "Sabreen plss go call hajiya for me"

Da sauri ya juyo tana kallon shi bata san lokacin da wata irin muguwar dariya ta kubuce mata
ba,"Bala'i yau ga wanda yafi malam haulat bala'i to ikon allah "
A zuciyarta tayi maganar ta kuma ƙasa daina dariyar.

Wani irin kallo ya bita da shi yana yamutsa fuska haɗe da taɓe baki,cikin wani irin ƙaƙale ya
ƙara ce mata "What Rong with you"

Haba ai sai ta ƙara fashewa da wata muguwar dariya harda hawaye dariya dariya kamar ba
zata daina ba,idan zata daina sai ta ƙara tunowa ta ƙara kwacewa da dariya.

"Ƴar aljanna dariyar me kike yi haka ,lafiya?

Hajiya ta faɗa lokacin da ta shigo falon gurinta ta ƙarasa,ɗagowan da tayi ta ganshi ,ta washe
baki ta ce "Ƴan india ne a gidan yaushe ka shigo"

Saida ya yamutsa fuska kamar wanda ke jin wari ko wanda yake kallon kashi ya ce "Ɗazun
ne"

Haba ai wata irin dariya ta ƙara fashewa da ita har saida ta faɗo daga kan kujerar dan tsabar
dariya.

"Waiyo ni Sabreen hausar ma ba za'a barta ba"

A zuciyar ta faɗa,ita kuwa Hajia ruɗewa tayi dan ganin irin dariyar da Sabreen ke yi.

"Waiyo Allah na bani ƴar aljnna"

*Naufal* hajia ta kira shi, ka taimaka ka kira likita"

"u mean doctor"

Ba Sabreen ba ni kaina saida na dara dan yadda ya ƙira doctor ɗin,mugun ɗan ƙaƙale ne,dan
abin dashi ya wuce iyawa ya koma kaƙale,kamar yadda ake fitar da harafin larabci haka yake
fitar da kowanne harafi harda ƙari ma.

Kuka hajia ta fara "Waiyo na shiga ukku ni yau"

Ganin hajia na ƙara ruɗewa yasa ta fara kukarin tsaida dariyar amma ta kasa,saida ƙyar da
sassauta dariyar ta kalli hajia ta ce "Waiyo hajia ta ba komai lafiya ta lau dariya ne Kawai"

Shi kuwa Naufal yana gefe yana kallon su dan bai gane shi take yiwa dariya ba,dan shi a nashi
ganin baiyi abin dariya ba,kallon mahaukaciya yake mata.

"Jajia bari na tafi ana jira na"

yadda ya ke kiran sunan hajiyar ma abin a dara ne,dan mugun ɗan ƙakale ne na ƙarshe.

Kasa ɗaurewa Sabreen tayi haba ai sai ta cigaba da dariyar.

"To mutun india ka gaida hajiyar ku ,zamu shigo da daddare mu amshi tsarabar mu"

"Okkk hajia sai kun zo"

Kamar wanda ba bahaushe ba haka yake hausar.

Yana gama faɗa yabar falon yana tafiya cikin ƙasaita da izza tafiyar ma abin kallo ce,da ana
karatun iya tafiya da sai na ce ,yayi digiri gurin iyawa.

Da ƙyar sabreen ta iya tsaida dariyar ta"Hajia ta wai ke ba ki ji abinda da nake yiwa dariya ba"

"Yo ina zan ji ni tsoro ma kika ban"

"Wancam ɗan indian ne yaban dariya ji yadda yake magana kamar shi ya kawo magana duniya
u mean doctor"

ta maimaita abinda ya faɗa ta irin yadda yayi maganar.

Dariya ita ma hajiyar tayi ta ce "kin san daga india yake shiyasa"

"Su ƴan indian haka su ke,ƙilibibi ne na bala'i,kai bari n Je nayi wanka dan jikina duk ya mutu .

"Ba dole ba irin wanan mahaukaciyar dariya ai dole jiki ya mutu"

hajiar na gama maganar ta haye sama tana dariya da mamaki dan bata taɓa tunanin za'a samu
wanda yafi malama haulat iyayi da ƙilibibi ba...

~~~~~~~~~~~~~

Zaune take a tankameman falon wanda yasha fentin pink da fari haka zalika komai na cikin
falon kujeru da flowers da sauran kayan alatun rayuwa.

Fuskar nan tata dauke take da annuri wanda nake ganin kamar haka halitta yake wato smile
face akan 2 sitter take zaune,ita ma karya kyakykyawace ga murmushi, babba mace ce mai
halin girma.

A gafe guda kuwa Wata kyakykyawar yarinyace ko na ce budurwa wacce shekarun ta ba sufi

goma sha takwas ba, tun kallo na farko na gane suna da alaka da matar nan dan irin Yadda
suke gama.

Cikin siririyar murya ta kalli matar ta ce "Momy nifa na ƙagara naga tsarabar da yaya Naufal ya
kawo min,wai ina ma yaje ne daga zuwan shi"

Murmushi tayi wanda ya ƙara baiyana zatin fuskarta ta ce "ke kuwa *farrah* kina da gajin hakuri
kuma kin san halin Naufal baya son damuwa idan kika nuna mishi kin zaƙu ya hanaki,ya je
gurin Hajia ya gaida ta"

Taɓa fuska tayi ,bata ƙara cewa komai ba,da juya ta fuskanci tivi.

"Assalamu alaikum ya faɗa a hankali ita kanta sallamar kamar da turanci yayi na ce da Sabreen
nan hhh da tasha dariya.

A tare suka amsa mishi kowanne su fuska ɗauke da Annuri ,Farrah ce ta fara magana "Yaya ka
dawo"

cikin yatsine ya ɗaga mata kai bai ce komai ba.

Ita kanta farrah bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login