Showing 42001 words to 45000 words out of 57176 words

Chapter 15 - NIDA MALAMATA BOOK COMPLETE BY Fatima Batula.pdf

16 Mar 2025

5541

riƙe hannuwan shi,ta ce a ɗan ruɗe,"Yaya ka manta ne zaka wuce gidan hajia ko ba
ka so na je ne?

Taka birkin motor yayi da sauri,kallon ta yayi ido cikin ido sanan ya ce,"Yanzu idan na ce bana
so ki je ba zaki je ba?

"Eh Momy da hajia duk sun gaya min duk abinda miji na ya ce baya so kar nayi kuma idan ya
hanani yin abu kar nayi,idan ka ce baka son zuwa ba zan je ba."

Lumshe ido yake yi yana kallon lips ɗin ta yadda ta ke maganar,idanuwan shi har sun canza
kala bugun zuciyar shi ya ƙaro,cikin izza da zafin nama ya janyo ta jikin shi ya haɗa bakin shi da
tana ya fara kissing ɗin ta,abin mamaki yau bata yi koƙin ƙwatar kan ta ba,cikk ta tsaya yana
juya harshen shi cikin bakin ta,shi kuma jin ta natsu ya saka ya ƙara zaƙewa,lalubarta ya fara yi
,jin ya fara taɓa jikin ta yasa ta ja jikin ta da sauri tana sauke ajiyar zuciya.

shi kuwa gogan kife kan shi yayi akan sitiyarin motor yana sauke nannauyar ajiyar
zuciya,zuciyar shi kamar ta fasa ƙirjin shi ta fito dan bugawan da ta ke yi.

Bata ce mishi komai ba,har tsawon lokaci ba wanda ya iya yin magana a cikin su.

Ganin bashi da niyar magana gashi yamma na yi,ya saka ta mishi magana,"Yamma tana yi mu
tafi."

Bai yi tsammanin jin wanan maganar daga bakin ta ba,yayi tunanin ɗan iska zata ce
mishi,ɗagowa yayi yana so su haɗa ido taƙi bari.

"Sabreen! da ƙyar maganar ta fito dan ma ta saba da jin maganar shi da ,da ne ba zata ji abinda
ya faɗa ba.

Kan ta a ƙasa ta ce,"Na'am."

Har lokacin idon shi yana kan fuskarta,yana son fahimtar yanayin ta,ganin yana ƙara shiga wani
hali dan kallon ta yasa ya ja motor da gudu baya ya juya ,ya kai ta gidan hajiyar.

Sun isa harabar gidan yayi farkin ,yana yin farkin ɗin ta fito da gudu tai cikin gidan.

Kallon yadda tayi gudun yayi,yasan irin yadda ta ke son hajia a fili ya ce,"Ke nan Savreen zata
iya zama da ni a matsayin mijin ta,hakan yana nufin ta aminta da ni,an ya kuwa ,koma me nene
zan gano."

Shi kaɗai ya ɗinga saƙa yana warwara.

Ita kuwa tana isa falon ta dunga kwala ma hajia kira.

"Hajia ta! Hajiata!

Hajiyar tana ɗakin ta da sauri ta fiton falon jin muryar Sabreen Rungume juna suka yi suna ihun
jin daɗin ganin juna.

Saida suka gaji da tsayuwar sanan suka zauna sanan suka gaisa cikin farin ciki da jin daɗi.

Bayan sun gama gaisawa d daɗewa sanan ya shigo da sallama a bakin shi.

Hajia tana amsawa ta ce tun kafin yakai ga zama,"Da ba zaka shigo ba ne,ko baka so ta zo ba
ne."

Saida ya zauna sanan ya kalle ta yana murmushi ya,"Na isa na hana ta zuwa gurin bugun
zuciyarta muradin ranta."

Dariya suka yi su dukkan su kuwannan su yana cikin yanayin jin daɗi,bayan sun gaisa da shi

suka fara fira.

Kallon Naufal hajia tayi fuska ɗauke da annuri ta ce,"Naufal na gode,na gode lallai ka haifu,duk
da Sabreen jikin ka ce dole akwai so a tsanin ku amma dole mu jin ji na ma dan abinda kayi ba
ko wanne ɗa ba."

"Haba hajia ni kashe min jiki kuke idan kuna min godiyar ne."

Amma can ƙarƙashin zuciyar shi tunanin abinda ta ce yake yi,"Akwai so a tsananin ku" yana son
ya gane wani irin so ne wanan.

Kallon ta yake yi yana son su haɗa ido amma taƙi yarda da hakan ta faru.

A zuciyarta ta ce,"Ba wani so wanan ne zai so ni, tabb kin saɓa number hajia."

Suna gidan aka kira sallar maqrib ya fita yayi su ma,su ka tashi zuka yi,bayan ya dawo saida
suka ci abinci sanan suka tafi.

Saida hajia ta bata garin magarya da sabon magarya sanan suka tafi.

Har suka isa gida ba wanda yai ma wani magana,ɗakin shi ya tafi ita ma ɗakinta ta wuce dan ta
chanza kaya.

Dan samon tayi wanka ta saka riga dugowa mara nauyi ba kwalliya a jikin rigar sai da ta fashe
jikin ta da tararen da ta saba amfani na shi sanan ta fara gyara ɗakin ta duk da kafin su tafi ta
gyara.

Yana isa ɗakin shi ya faɗa kan gadon kan shi na kallon saman ɗakin,sauraran bugun zuciyar shi
ya tsaya yi,ya daɗe a haka sanan ya tashi yai toilet.

~~~~~~~~~~~~~

Kuka sosai haulat ke yi,"kin gani momy har yanzu ba wani labari tun muna kan hanya kika sa a
fara saka ido amma ba wani labari sai ganin su ma da aka ce anyi suna jin daɗi har da kiss fah
aka ce ya mata."

Dafa ta momy tayi,"Ki kwantar da hankalin ki,na gaya miki aikin shi a ranar ya ke yi,kuma yanzu
baki ga gobe tayi ba ance bata hauka ce ba,yau komai dare sai aikin mu yayi ki kwantar da
hankalin ki."

"Hankali na ba zai iya kwanciya ba momy."

"Na gaya miki ki kwantar da hankalin ki idan wani abu bai faru ba sai mu koma goven."

Duk wanan abun da suke yi sakina tana jin ,idanuwan ta sunji ja kwalla dam a idon ta.

Cikin raguwar murya ta ce,"Momy ba kyau kuyi tsoran allah,dan.....

"keeeeee dan uban ki ,ki ɓace daga nan kafin na buɗe ido na."

Gaba ɗaya jikin sakina rawa ya fara yi,da ƙyar ta iya jan ƙafar ta,ta bar gurin.

Ita kuwa momy taita vamvami kamar karamar mahaukaciya sai kwace ma sakina albarka ta ke
yi.

~~~~~~~~~~~~~

Da sallama ya shiga ɗakin yana tashin ƙamshi,ganin kamar hankalin shi baya jikin shi yasa,ta
lallaɓa ta vayan shi ta rufe mishi ido da hannuwan ta.

Mai da idanuwan yayi ya rufe su,dan yasan ita ce,a hankali zuciyar shi ta fara bugawa
hannayen shi ya ɗauka kan na ta,sai da yaji wani irin jin lallasar fatar mai.

Cikin wata irin siga wacce shi kan shi ba zai iya bambance yanayin ba ya ce,Sabreen!

"Maimaita."

"Sabreen!

"Waw na baka kyautar Abuja harda kaduna ba,kasan me? ta sake shi ta dawo inda ya ke zaune
taff da shi ta zauna,har suna gogan jikin juna.

Kallon ta yayi ya sake mata wani irin kyakyyawan murmushi sanan ya ce," taya zan sani."

"Ka bala'in iya kiran sunan da indiyanci kike kira gaji daɗi ku....

Dariya ta fashe da ita sosai ya dara ita kuwa bin shi da kallo kawai ta ke yi dan bata ji abin
dariyar da ta faɗa ba.

Saida yayi me isar shi sanan ya tsaya bai ɗaure fuska ba ce kalle ta ya ce,"Wai da indiyanci,kai
sabreen kina da abin dariya."

"Toh ai gaskiya na faɗa wa gaji yana kira na irin yadda kake kira na?

"Hajia da Dady."

"A'a su da hausa su ke kira."

Murmushi yayi mai ɗauke da annuri,"Hm kina da abin dariya,na tambaye ki."

"Uhum!

"Wai lokacin nan da na zo gurin hajia a lokacin ban daɗe da dawo wa ba,har na same ki a falo
kina kallo kika banza da,naga kina da dariya a lokacin me ya sa ki dariyar?

Yana kai ayaa ta fashe da dariya,kallon ta ya ke yi tana dariya kamar irin wancen lokacin,taya
da yayi.

Saida suka yi me isar su sanan su ka tsaya,suna kallon juna,wani irin abu ke ta so mishi a rai.

Cikin yanayin jin barci ta ce,"Barci na ke,bari na kwanta."

Bata jira cewar shi ba ta,tashi saida ta shiga bayi nayi al-awla sanan da tayi nafila tayi addu'o'i
iri iri sannan kwanta,duk yana kallon ta,tana kuma ƙara birge shi,addu'o'in da yaji tana yi yayi
magana dan wasu mai iya ba,wasu ya manta su.

"Na hakura nayi rayuwata da ita,bata da matsala ko kuma hakan zai saka iyaye na su ji daɗi
sosai."

Nannauyan numfashi yayi sanan ya ƙara faɗin,"kai abin is not easy taya? to daman ai matsalar
tawa ce," dafa kan shi yayi wanda ya ɗau zafi,wata zuciyar tana tausar shi akan ta zaduda
kawai wata kuma na bijiro mishi da abubuwa marasa amfani.

Safa da marwa ya kw yi a tsakiyar ɗakin yana kuma kallon ta ,ta duƙunƙune guri daya tana
varcin.

Tausayin kanshi ya kama shi tabbas yana da buƙatar macce,kuma yasan idan har mai samu
yadda yake so ba,har wani ɗan lokaci zai iya samun matsala.

Kamar wanda aka ba umarnin ya zauna can kuma ya tashi tsaye,hura hanci ya fara, a fili ya
ce,"Ba zan iya cutar da kai ba,bayan allah ya ƙubutar da ni."

Murmushi yayi me ƙyayatarwa har da lumshe ido da hura hanci,"Ban san ta yadda zaki ji
al'amarin ba amma dole zanyi Sabreen, ba yadda..

.
[12/23, 2:22 PM] �° � D°�⭕Y: _ �σѕт у �яσυρ � � �уρє �αυѕα
�σνєℓѕ σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/23, 2:24 PM] �° � D°�⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*

*By*
*fatima* *Batula*

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

Page 17
......................................................

Kwanciya yayi ɗan nesa da ita kaɗan,ya daɗe yana saƙa da warwara, yana jin tana barcin ta
hankali kwance,shi kuwa sai juye yake yi sai ƙarfe ɗaya saura sanan barci ya ɗauke shi.

Kamar dai kullum kiran sallar farko ke tada ita yau ma hakan ne,tana tashi da kunna hasken
ɗakin kallon inda yake tayi saida tayi murmushi ganin yadda yake barcin hannayen shi gaba
ɗaya a ƙirjin shi.

Saida tayi alwala sanan ta matso kan shi ta taɓa sanan ta ce,"Miji na ka tashi lokacin sallah."

Shiru barci yayi nisa ganin hakan yasa ta matso kusa da hunnan shi ta hura mishi iska,motsi
yayi amma bai buɗe ido ba,hancin shi ta fara ja nan ma shiruu na koma gurin idon shi ta fara
shafa batar idon nan ma shiruu,ganin hakan yasa takai hannunwan ta kan lips ɗin shi ruwan
alwalan da bai bushe ba na hannunta shiyasa lips ɗin suka jiƙe,shafasu ta ke yi,ta shafa da
ƙasa ta shafa na sama nan da nan ya fara juya su kamar me kokarin cin wani abu,ganin hakan
yasa ta fashe da dariya,wacce tai nasara isa ga dodon kunnan shi.

Firgittt! ya tashi kallon ta ya ke yi cike da mamakin abinda ta ke ma dariya.

Cikin dariya ta ce,"Wai Halan yunwa kake ji."

Cikin rashin fahimta ya ce,"Me?

"zan tashe ka ne ka ƙi tashi shi ne ta hura ma kunne na jajja hancin ka ƙi tashi shi ne da na taɓa
ma baki ka fara motsawa kamar zaka ji wani abun."

Murmushi yayi labarin sabreen yana bashi dariya ya kuma bashi mamaki.

"To meye na dariya."

Har ta buɗe baki zata yi magana akai kiran sallah,"Kai ka tashi."

Tana faɗa ita ma ta tashi ta shimfiɗa sallaya sanan ta fara sallar nafila kamar yadda ta saba.

Ganin hakan yasa shi ma ya tashi ya faɗa toile bai ɗau lokaci ba ya fito gurin saka kaya ba bai
ɗau lokaci ba ya fita.

Bayan ta idar da sallah ta fara aikin gyara ɗakin saida ta ƙimsa komai sanan ta wuce ɗakin
ta,tana zuwa ta gyara shi sanan ta nufi kicin.

Yau bai zauna dan barci bai ishe shi ba,yana shigowa falon yaji ƙamshin abinci yana
tashi,kallon hanyar kicin ɗin yayi kamar ya shiga sai ya fasa ya wuce ɗakin shi bai yi mamaki
ganin shi tsab ba dan yasan halin ta ne,ya kula da ita sosai tana da tsabta har ta kusa fin
shi,kwanciya ya koma yayi.
Bayan ta gama haɗa komai ta koma ɗakin ta,tai wanka ta shirya cikin riga da siket na
atamfa,Karuwan jiki sabreen gare ta,irin jikin da ko wani irin shiga yana amsar shi,irin shi ne ka
kan kasa gane al-adar mutum idan ya kasance mai yawan shiga iri-iri.

Bayan ta gama shirin ta tsab,kai tsaye ɗakin shi ta nufa,a hankali ta buɗe kofar,ganin shi
kwance yasa ta ƙarasa hawa tayi kan gadon,naniƙe shi tayi,shi kuwa bai sani ba yayi nisa yakai
ziyara golden pen

Ita barcin ne ya ɗauke ta.‍♀nidai nayi nan asha barci lafiya.

~~~~~~~~~~~~~

"Baki san waye mutumin nan ba,bashi da mutunci kar mu koma mu bani mu lalace dan mugu
ne."

Cikin kukan mai sauti Haulat ta kalli momyn nata ta ce,"Haba momy gaskiya mu koma kina gani
momy ya daina so ba,na shiga ukku momy ya zanyi."

"Ai tun farko shi ya kamata ayiwa asirin ba ita ba,da shi aka mawa ya isa ya daina sonki bai
isa,amma me kika buɗe baki kika ce min,ke baki son a mishi asiri kin fi son irin son da yake mi
ki,to ai gashi kin ga ni irin son da yake miki dai ko yanzu kin ganshi."

"Har da it..

"Harda ita ko,ke banza ce har yau baki gane avubuwa da dama an gaya miki namiji irin macce
ce."

A sanyaye ta ce,"Momy yana so na ni ce nai bishi abinda yaji haushi."

"Koma meye da anyi asirin bazai ji haushin ki ba duk abinda kika mishi saida ya baki hakuri."

"Momy to muje dan allah mu je yanzun nan."

"Tashi to mu tafi."

Cikin gaggawa suka tashi ko shiri basu yiba mayafi kawai suka ɗauka,a harabar gidan suka
haɗu da sakina ta dawo daga makaranta ko kallon banza ba su yi mata ba.

Ita kuwa tana kallon yanayin su tasan ba hanyar allah zasu bi ba,aran tai musu addu'ar gafara
da shiriya ta wuce avin ta.

~~~~~~~~~~~~~

Sama-sama ya fara fuɗe idon ƙamshi ya fara ziyarta hancin shi,na hanzari ya buɗe su dan
tabbatar da abin da yaji,a hankali zuciyarshi ta fara bugawa da ɗan ƙarfi,lumshe idanuwa yake
yi,kallon hannuwanta yayi waɗan da gaba ɗayan su suna rungume a jikin shi,kafafuwan ta duk
suna kan cinyar shi,fuskarta kuwa tana ƙirjin shi kasan cewar yafi ta tsawo.
A hankali yasa zame hannun shi da ga jikin ta ya tallafo fuskarta idanuwa ya zuba
mata,numfashin ta yana dokan fuskar shi,a ran ya ce,"kamar mu kasance a haka,"

Ko kaɗan baya gajiya da kallon ta,wani irin yanayi ya shiga wanda bai san irin shi,bai kuma taɓa
shiga ba,saida ya ƙarewa halitta fuskarta gaba ɗaya kallon,ɗan ƙaramin bakin ta shi yafi ɗaukar
hankalin shi,gai gashin idanuwanta,tsarin fuskar ya mishi kyau,hannu ya kai kan lips ɗin,da
sauri ta buɗe ido,sai cikin nashi kallon ƙuda suka fara yiwa juna,cikin muryar da batai yi tunanin
zai ji abinda zata faɗa ba ta ce,"Kai ma zaka rama ne."

Bai ji sautin muryarta ba amma motsin bakin ta ya gani,murmusawa kai yayi.

"Yaushe ka tashi?

"Ɗazun."

Shiru tayi sanan ta ce,"Kai baku ƙarya ba."

Janye jikin ta tayi ,wani irin abu ya zake shi a heart ɗin shi,ko kaɗan bai ji daɗin janye jikin ta ɗin
da tayi ba,lumshe ido yayi yana jin wani iri a ran shi.

Hannuwan shi ta yanyo,"Ka tashi rana tayi."

Wani irin yaji kallon hannu yayi sanan ya kalle ta shagwaɓe fuska tayi haɗe da rausaya kai
alamar ya tashi.

Kai tsaye zuciyarshi ta amsa umarnin ta,tashi yayi ya banɗaki ya nufa,ita kuma ta fita.

Ƙarfe goma sha ɗaya da rabi agogon bangon dake manne a jikin bangon fallon ya nuna.

Gurin abincin ta nufa ya ɗan rage zafi amma bai yi sanyi ba zasu ci a haka.

Bayan ya fito daga bayin saida ya zuba kasaita gurin shiri,cikin ƙananan kaya ya shirya sun
mishi kyau ainun navy blue rigar sai baƙin wando,saida ya gyara fuskar shi da gashin shi sanan
ya fashe jikin shi da turare,sanan ya fito.

Tun daga saman benan ya hangota tsintar kan shi da yin murmushi yayi wanda bai san dalilin
yin shi ba,kamar ance ɗago kai ta ɗago suka haɗa ido murmushi suka sakar wa juna,wanda ya
fito ne daga ƙasan zuciya.

Zama yayi,ta fara zuba mishi waina ta fara zuba mishi sai lipton da kwai,ita ma shi ta zuba,ba
wanda yace ba wani ƙalla saida idan sun haɗa ido su sakar wa juna murmushi.

Dukkan su suka tsince zuciyoyin su cikin natsuwa da jin daɗi da farin ciki da walwala,ita ta fara
gaba ci yana jin ta tsaya shi ma ya tsaya kallon shi tayi wai murmushi,"Nima na ƙoshi."

"Ka ci dai ka ga ni ko ban ci ba,ina da qiba ta,amma kai kuwa idan baka ci ba sai yadda...

"Kin fi ni qiba ne?

"Kam wa zai haɗa ma."

Kauda zancen yayi ya kawo wani ta hanyar faɗin,"Gobe ne fa!

"Wai zuwa honeymoon ɗin mu."

"Kin shirya ne?

"ƙwari kuwa ,kai baka shirya ba ne?

"Hmm na shirya zaida ke nake tunanin anya kuwa."

"Na shirya ma komai da komai ka daina shakka."

"Komai da komai fa kika ce."

"Eh komai da komai."

"To amma kin koya kuwa."

"Me?

"Haƙƙin miji!

"Ka fasa koya min ne?

Murmushi yayi mai ƙunshe da abubuwa da yawan gaske.

Bai kai ga bata amsa ba ta ce,"Dady ya ce,wai da wuri zamu tafi goben yau sai muje muyi musu
sallama,amma fa ina ɗan jin tsoro kar wani abu ya faru mara kyau a can,ko da yake tsoran me
zan ji ina tare da mijina ɗan uwa na,nasan ba zaka bar wani abu ya cutar da ni ba."

Ta ƙare maganar tana kallon shi,yanayin shi kuma ya ɗan canza wanda zai iya alaƙanta wa da
maganar da ta mishi.

"Wai zanga fararan muta ne,ai nima kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login