Showing 36001 words to 39000 words out of 57176 words

Chapter 13 - NIDA MALAMATA BOOK COMPLETE BY Fatima Batula.pdf

16 Mar 2025

5534

aka gayawa iyaye na."

Saida ta sauƙe gajerar ajiyar zuciya sanan ta ɗaura da faɗin,"Malam ta,jahili daƙiƙi ɗan kauye iri
na da aura,ko ɗan gaye mai aji mai ilimi da kyau na aura wanda ko wacce macce take son
rayuwa da.?

"Gaya min dan na kasa ganewa,laah ko shi ne wanda malamata ta ke mafarki akan shi?

"Malama ta! ya kike yi shiru ,ki zauna kinji ki natsu,ni Sabreen ba tsararki ba ce,yawwa kuma ki
fita harkar miji na,baki da ikon juyamin shi tunda ba ɗalibin ki ba ne,ina fatan kin gane."

"Ƴar aljanna ke dawa kuma?

Ɗagowa tayi ganin hajia ce yasa ta katse wayar a ranta ta ce," *Ni* *DA* *MALAMA* *TA*.

A fii kuwa dariya tayi ta faɗa kan hajiar tana ihuu tana faɗin,"Oyoo ooyoo hajiata.

"Ba wani bayan kin manta da hajiar aure daɗi ko?

Cikin shagwaɓa ta ce,"Kai hajia ba wani daɗi."

"To ya kike? ina ta kewar ki shiyasa na ce bari na zo na ganki."

"Nima hajia ai nayi kewarki sosai."

Fira suka shiga yi sosai da sosai cikin so da ƙaunar juna.

******

Ɓangaran Haulat kuwa tunda sabreen ta katse wayar ta fasa ihuu,mai rikitar wa.

"Lafiya kike haulat mai ya faru?
A ruɗe momyn ki tambayarta wanda ihunn na ta ne ya fito da ita daga ɗakin ta.

"Waiyo allah na momy na shiga ukku dan allah mu tafi gurin bokan nan."

"Duk da basan abinda ya faru ba,nasan sai irin hakan ta faru,ke ce banza bara wayau ai."

"Sabreen sai na yi ajalinki walahi sai na kashe ki!!

"Mu tafi yanzun nan."

"Matsalar yau baya sauraran mutane sai gobe."

"Ɓakin ciki sai iya kashe ni kafin goben ba zan iya hakuri zuwa gobe ba."

"Tun ranar da nake miki magana kika ƙi saurarata, amma harda shi zamu haɗa."

"No momy bana son a mishi asiri."

"Giyar so ko!,to shi ne wanda ya kamata ayi wa asirin ma ba ita ba."

"Momy baya da matsala ina son shi,soyayyar da yake min ita nake so,bana son a saka shi dole
da bin umrnin."

"Hmm haulat kenan ina fatan zaki gane ki dawo hanya."

~~~~~~~~~~
Bangaran Naufal kuwa tunda ya kwanta ya faɗa duniyar mafarkin da ya saba yi,wanda ya
kasa bin jikin shi,dan kullum abin sabo yake zuwar mishi.

Kamar yadda ya saba tashi a irin lokacin da tare barin shi yau ma hakan ne,farkawa yayi
zuciyar shi na zafi da ƙuna ga zufa ta mamaye shi kanshi a ƙasa.

Sintar muryar ta yayi tana faɗin,
"Miji na ka tashi?

ɗagowa yayi suka haɗa ido,wani iri yaji ,ita kanta kasa tai da kai,"Hajia ta zo tana na jiranka,har
ta wuce baka tashi ba,daman yanzu zan tashe ka dan lokacin sallah yayi."

Lumshe rinannun idanuwan shi yake yi,ya kasa daina barin kallon ta.

Ganin kamar ita yake kallo yasa ta fara kame-kame,"Lokaci yana tafiya fah!

"Ko barcin bai ishe ka ba ne?

Dariya yayi dan sanan ya tashi ya shiga bayin,yana shiga ta ƙara gyran ɗakin tayi tsaba sanan
ta fashe shi da turare.,ɗaukar wayar shi tayi ta kashe sanan ta fita indomi ta haɗa mishi da
kyau sai jus ta kawo har lokacin bai fito ba,zama tayi a bakin gadon.

Yana fitowa yaji ƙamshi me kwantar da zuciyar,idon shi suka sauka akan sabreen wacce ke
zaune akan gadon tana wasa zuben da yake hannunta,ya daɗe yana kallon ta,wani iri yake ji a
ranshi a duk lokacin da yake kallon ta,yadai kasa gane wani irin abu ne.

Ɗago kai tayi suka haɗa ido kai tai da kai da sauri,"Ka ƙara haske yanzu kawai."

Murmushi yayi,"Waya gaya miki wanke ke saka mutum yayi haske?

"Gani nayi."

"Gurin wa?

"Gurin mijina kuma yaya nah!

Dariya yayi mai ɗauke da murmushi ,yana jin daɗin sunan da take kiran shi da shi"mijina"

ƙarasowa yayi har kusa da ita wani towel ɗin zai ɗauka ya goge jiki da shi,kuma yana bayan ta.

kaff da ita ya matsu ya miƙe hannun shi zai ɗauko towel ɗin jikin su ya haɗu da na juna,yarr
dukkan su suka ji ,ruwan girjin shi ya zuba a fuskarta,wani irin sanyi taji har zuciyarta,tsintar kan
shi yayi da son rungumeta, faɗawa yayi kan jikinta ya rungume ta,wani irin baƙon yanayi ya fara
ziyartar zuciyar shi,mutsu-mutsu ta fara tana kokarin janye jikinta,"Ka gyale ni bana so." ta faɗa.
Zuciyar shi ta fara buguwa da ƙarfin gaske,wanan maganar tuno mishi da mafarkin shi tayi,kafin
ya ƙarasa tunanin shi,ta ƙwace jikin ta,barin ɗakin tayi da sauri ta barshi da bugun zuciya....

.
Sir Anas!
[12/23, 1:52 PM] �° � D°�⭕Y: _ �σѕт у �яσυρ � � �уρє �αυѕα
�σνєℓѕ σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/23, 2:16 PM] �° � D°�⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*

*By*
*fatima* *Batula*

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

Page 14
.............................................

*Addu'a Ga Wanda Yayi sabon Aure*

َكَراب ُ
هَّللا ،َكَل َكَراَبَو ،َكْيَلَع َعَمَجَو اَمُكَنْيَب يِف .ٍرْيَخ
Barakal-lahu lak, wabaraka 'alayk, wajama'a baynakuma fee khayr.

Allah Ya sanya albarka a gareka, yayi maka albarka kum aya hada tsakaninku da alheri.

Wanga page na ku ne iyalan bintu Ahmad ,da tana jamcy ina yinki sosai na gode da kulawar
ku,ku sha zaman ku ,ku huta batula tana yinku fiye da tunanin ku.

_____________

Ya daɗe kwance a inda ta barshi,"Ka gyale ni bana so",maganar ke mishi yawa cikin kai ,ba yau
kaɗai aka taɓa gaya mishi ita ba,abinda ya kasa gane meye halaƙar maganar Sabreen da
mafarkin shi,ganin kan shi ya fara ɗaukar zafi yasa watsar da tunanin,ya tashi ya saka kaya
mara su nauyi wayar shi ya ɗauko yana sun kiran Haulat,"Mtseww na rasa gane meye matsalar
haulat a cikin ɗakin take koƙarin taga mun aikata alfasha",ƙara jan tsakii yayi ya jefar da wayar
bai ma kula da wayar a kashe take ba.

Hango kwanan abincin da Sabreen ta kawo mishi yayi,murmushi yayi ya ƙarasa gurin ya buɗe
ci ya fara yi yana murmushi.

Cikin salon magana irin nashi ya ce,"Wai zata iya kwana a ɗaki ɗaya da ni,sai bakin tsiya
yadda take magana kamar wata mai faɗa a gani."

Saida ya gama cin abincin sanan ɗauko system ɗin shi yana chat,murmushi yayi mai ɗauke da
farinciki pics ɗin sabreen ne farrah ta saka a status da kayan makaranta tayi su,nayi kyau sosai
fuskar ta ɗauke da murmushi.

"Mijina!

Tsintar maganar yayi a kunnuwan shi,wani murmushin ya ƙara yi,bai ɗago ba ya ce,"Kin ƙara
dawowa ne?

Saida ta ƙaraso ta zauna a gefen gadon kusa da shi sanan ta ce,"Eh ya bazan dawo ba,ni da

zan kwana a nan."

Sai yanzu ya ɗago ya kalle ta,"Zaki kwana a nan?,ki kwana a ɗakin ki."

"A'a ni tsoron ɗaki na nake ji,to meye idan na kwana a ɗakin miji na."

Kallon ta yayi sosai dan tunda ta fara maganar ya zuba mata ido,har zai yi magana ya fasa,ya
maida hankali gurin abinda yake yi.

Bata damu da hakan ba ta ce,"Me zan dafa ma?

"Kin san haƙƙin miji akan matar shi ? a maimakon ya bata amsar tambayarta sai tambayarta
yayi.

Kai tsaye ta ce,"Na sa ni."

"To gaya min."

Saida tayi jimm sanan ta ce,"Eh ta kula da shi ta mishi biyayya da kula da kayan shi,ta dafa
mishi abinci sai me ma? yawwa sai tarbiyar yaran shi sai...

"Taya ake samun yaran?

"Ciki!

"Taya ake cikin!

"Me?!

"Eh taya ake cikin?

Duk da kasancewar bata san abubuwa sosai ba waɗan da suka shafi ma'arata,amma saida taji
kunya rufe ido tayi da hannuwan ta.

Kallon ta yayi yana murmushi Sabreen tana burge shi komai tayi abin kallo ne,"Hm meye na
rufe ido ko kin san yadda ake yi ne?

kai ta girgiza mishi alamar a'a

"To ba zaki kwana a ɗaki na ba,tunda baki san haƙƙin aure ba." ya faɗa idanuwan shi suna kan
ta yaga yadda zata yi.

"A'a ni anan zan kwana."

Yadda tayi maganar cikin shagwaɓa yasa ta kashe mishi jiki lumshe idanuwa yake yi yana
kallon ta.

"A'a ba zaki kwana ba,wacce tasan haƙƙin mijinta ita ke kwana a ɗakin shi,kinga ke baki sani
ba."

"To ka gayamin sai in sani."

"Saidai na koya miki."

"Ka koyamin."

"Idan baki so shikenan sai ki kwana a ɗakin ki kawai."

"Ina so toh."

Dariya yayi sosai har saida haƙoran shi suka baiyana sautin muryar shi ya baiyana.

"Sabreen kenan idan gaji yadda ta iya kiran mijina sai ka ɗauka tasan meye mijin,kamar wata
wayayya idan ka ganta amma a zahiri bata san komai ba,bata iya komai ba", shi da zuciyar shi
suke wanan maganar har lokacin kallon ta yake yi yana dariya.

Ganin dariyar tayi yawa sa ya ita ma ta fara dariyar,yana jin ta fara dariyar ,ya ƙara fashe wa da
dariya.

dan dariyarta tana bashi dariya,kamar wasu sababbin kamo haka suka dinga dariya ,dan
tsabar dariyar da suke yi bata san lokacin da ta faɗa akan jikin shi ba,kwanciyar da yayi yasa ta
kwanta kan ƙirjin shi.

"Sabreen!

"Na'am mijina."

Dariya ta ƙara bashi amma baiyi dariyar ba yadai murmusa.

Kallon ta yake yi ,a ran shi yana faɗin ,"Ina ma kina so na ina sonki,da munji daɗin rayuwa."

"To mai zai hana ka so ni ɗin."

Zaro ido yayi jin amsar da ta bashi ,badai taji abinda ya faɗa ba.

Dariya tayi,"Naji ai."

Lokaci ɗaya girman kai ya shige shi,"Kinji ai ba da ke nake ba,ni bazan so ki ba,dan ba ra'ayina
ba ce ke."

Ko kaɗan bata ji zafin maganar shi ma,dan ita ma ba son nashi take yi ba,kuma ba ra'ayin shi
ba ce ita,duk abinda take yi dan Malama haulat ne.

A ranta ta ce,"Ban damu da ka so ni ba ni kawai ka manta da waccen banzar wacce bata san
darajar muta ne ba,ni ban ma san abinda ka gani a tattare da ita da kike son ta ba."

Shiru suka yi ba abinda kunnuwan su ke ji banda bugun zuciyoyin su,musamman ita da ke
saman ƙirjin shi,hannun ta takai saitin gurin zuciyar shi,bata ke komai ba tana dai jin yadda take
bugawa ne.

Yana jin ta taɓa ya rufe ido dan ƙaruwa bugun zuciyar ta ƙara yi.

Lumfashin ta kan fuskar shi yake sauka,ɗaga ta yayi yaga tayi barci murmushi yayi,"Savreen
kenan mai abin mamaki." zame jikin shi yayi sanan ya ƙara gyara mata kwanciya.

~~~~~~~~~~~~~

"Aunty Haulat dan allah karki biye momy abinda ta ke so kuyi bashi da kyau,kuma ba daidai ba
ne,ga tarin zunubai ga ɗaukar haƙƙi gashi kuma baku san abinda zai biyo baya ba,dan allh....

Cikin daka tsawa ta ce,"Keee Sakina zaki gaya mana allah ,ke idan baki fita daga ido na ba,wllh
zan ɓata miki rai,ni tsarar ki ce ma,ke a dole malamar addini ko,zaki dinga wani wa'azi an gaya
miki ban san allah ba ne,ko ke kaɗai kika taɓa zuwa islamiya da za.....

"Sakina ko." faɗar momy wacce ta shigo ɗakin,kallon Sakinar tayi wacce ke tsugunne a ƙasa.

"Sakina anya kuwa ni na haife ki?da a asibiti na haife ki wllh sai na ce canja min aka yi."

Hawaye ya wanke fuskarta gaba ɗaya ,kuka mai tsuma zuciya take yi,halin uwarta yana ɓata
mata rai ga tsanar da take nuna mata da banbanci,cikin muryar kuka ta ce,"Kiyi hakuri."

"Dalla ɓace ki bani guri bazan shasha wawayi wacce ta ɗibo ɗabiyar dangin mahaifinta na."

Jan jiki tayi tabar ɗakin tana kuka mai tsuma zuciya tausayin kanta ya kamata.

Kallon Haulat Momyn tayi ta ce,"Gobe da sassafe zamu tafi ki shirya da wuri dan a katsina ne."

"Momy ban yi tunanin zan yi barci ba,ko tsakiyar dare ne a shirye na ke."

"Yawwa Ƴar albarka."

~~~~~~~
"Sabreen ki tashi an kira sallar maqrib."

Sautin muryar shi ya doki dodon kunnan ta,a hankali ta fara buɗe ido,kan fuskar shi idanuwan
ta suka sauka,kallon juna suka fara yi,ganin baya da niyyar barin kallon na ta yasa tai ƙasa da
kai haɗe da tashi zaune.

"Kai ya aka yi nayi barci?

"Hm ko dan kin kwanta akan ƙirjin mijin ki ne?

Dariya yayi,yana kallon fuskarta.

"Eh haka ne."

Murmushi yayi a ranshi yana faɗin,"Hmm komai aka faɗa miki yarda zaki yi da shi wawiya
kawai."

Tashi tayi ta shiga bayin shi,tai alwala tana fitowa taga baya ɗakin,ita ma ta fita ɗakinta ta nufa
saida tayi sallah sanan ta fito kicin ta shiga ta haɗa musu abinci sanan ta koma ɗakinta tayi
wanka,doguwar riga ta saka ɓaka ba kwalliya a jikin rigar amma yadin rigar zai tabbatar ma da
rigar bata yara ba ce,ta kama jikin ta komai ya fito kamar yarda allah yayi shi,hula ta saka bata
ɗaura ɗan kwalin rigar ba.

Turaren miski shi ne turaran Savreen dan haka shi ta shafa a jikin ta sai da haɗa da wani turare
wanda hajia ta kawo mata,ba abinda ta sha ko mai bata shafa ba,amma kasancewar yanayin
fatar jikin ta mai kyau ce baka ce bata shafa mai ba.

Cikin tafiyar ta irin ta kasaita ta ƙaraso falon,yana zaune yadda ya zauna zaka tabbatar da
hanlakin shi ba'a jikin shi yake ba,saida ta ƙaraso daff da shi ta ce,"Miji na tunanin me kake yi
ne?

ɗagowa yayi ya kalle ta,fuska ba yabo va fallasa,kamar bazai yi mata na ba,sai kuma ya ce,"Ina
tunanin mosoyiya ta ne," ya kuma ɓata rai ya kau da ganin shi daga gare ta.

Haushin gaske taji cikin raunanniyar murya ta ce,"Ai mata gare ka."

"Matar da bata san haƙƙin miji ba."

"Zan koya kaji," da shagwaɓa tayi maganar.

Murmushi yayi har sai da haƙuran shi su ka baiyana,ya rasa dalilin da yasa yake son yi mata
magana akan aure.

"Zaka koyamin?"

wanan karan dariya yayi sosai,"Sabreen ƴar hajia."

"Eh ba zaka koya min ba."

"Baki iya ba kike ce kina son aure,saboda fiti na irin ta ki."

"Ba fiti ba ne."

Bai ce mata komai ba dan bashi da lokacin yin magana da ita,baya cikin yanayin jin daɗi ko
kaɗan abubuwa sun mishi yawa,gashi yana bugatar macce ga wacce yake so ba aure take so
ba,gashi baya jin zai iya kula matar shi.

Ɗakin shi ya tafi,yana zuwa ya faɗa kan gadon.

Ko kaɗan Sabreen bata ji haushi ba dan taɗau alwashin duk abinda zai mata ba gudu ba ja da
baya zata shanye har sai lokacin da ta tabbata ya manta da haulat sanan zata rabu da shi.

Ɗakin ta bishi ,da salama a vakin ta,ta isa ɗakin hannuwan ta ɗauke da tiren abinci,kusa da shi
ta ajiye abincin,"Ka ɗaure ka tashi ka ci abinci."

Tabbaa yana da buƙatar amici,shiyasa bai yi mata musu ba,ya tashi ta zuba mishi ya fara.

Kallon yadda yake tauna abincin take yi,yana tsaka da ci aka kira sallar Isha'i kasancewar
akwai masallaci a nan unguwar ta su.

Yana gama ci ya tashi ya fita,duk da bai gaya mata inda za shi ba tasan masallaci zai je.

Yana fita ta kwaahe kayan da maida su ma'ajiyar su kicin,sanan ta dawo ɗakin ta gyara,ta koma
ɗakin ta,tayi sallah,bayan da idar ta koma ɗakin shi baya nan ,falo ta zo ta ganshi zaune yana
kallon tivi ita ma zama tayi indian film ne,daga satar kallon shi ta gefen ido,shi kuwa gaba ɗaya
hankalin shi ya tattara akan film ɗin kasancewar yana jin yaran,gajiya tayi gashi yaƙi mata mgn
gashi bata gane komai a film ɗin.

"Mijina Barci ne ke ji,sai ka tawo," tana gama faɗa ta wuce ɗakin shi kai tsaye,tana zuwa tayi
alwala sanan tayi addu'o'in da suka zama jikin ta sanan ta kwanta.

Karfe goma sha ɗaya da rabi ya tashi,saida ya kashe komai sanan ya hawo sama dakin shi ya
nufa,bai yi tunanin zai ganta ba,mamaki ya tsaya yana,taya zai iya kwanciya tare da ita,ya daɗe

yana tunani sanan ya je nesa da ita ya kwanta,wani iri ya dunga ji zuciyar shi tana bijiro mishi
da su,ƙin sauraran zuciyar yayi,a haka har barci barawo ya ɗauke shi.

~~~~~~~~~~~~~

Tun asubar fari Haulat ta tashi a gaggauce tayi sallah,ta shirya wayar momyn na ta kira saida
tayi kira biyu sanan ta ɗauka.

"Momy baki tashi ba ne?

"na tashi jira ni a falo gani nan zuwa."

Ko sallah bata yiba tsabar sauri,a falon suka haɗe lokacin ƙarfe biyar,motor momyn suka hau,
kamar waɗan da zasu birnin sin,dan tsabar sauri ko da takwas tayi suna kaduna.


Ƙarfe ɗaya da wani abu suka isa garin katsina,saida suka wuce birnin ta suka fara ratsa
dajujjuka sanan momy ta tsayar da motor a wani ƙungumin daji mai yawan
duwatsu,kasancewar haulat bata taɓa zuwa ba hakan ba karamin tsoro da ji, Amma tsabar
ƙiyayya da guguwar ɗaukan fansa da ke tashi a zuciyarta ya hana ta baiyana tsoron ta.
Tunda suka fito momy ke rike da hannuwan ta,basu yi magana ba ko kaɗan,sunyi tafi mai tsawo
akan duwatsu,kafin suka iso wata ƴar bukka wani irin hayaki na tashi daga cikin,da ido momy
tayi mata alama da zu juya ma'ana da baya da baya zasu isa har cikin bukkar.

"Ya murmurken kulumruke,ɓaaɓun ɓuturen ƙaranjauuu,Da baya -da baya fitinan jan jaburan
ƙaranjauuu na kan dutsen wuta yana muku barka da zuwa.

Sun daɗe a tsaye fuskar su tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login