Showing 45001 words to 48000 words out of 57176 words

Chapter 16 - NIDA MALAMATA BOOK COMPLETE BY Fatima Batula.pdf

16 Mar 2025

5544

irin sabulon su zaka sai min nayi fari irin na su."

Dariya ya ɗan yi,"Ai ke zama abin kallo ce a gurin su."

Saida ta ɗan zare ido,"Wai saboda muni ko.?

Wanan karan saida sautin muryar shi ya fito,ita kuwa ya mutsa fuska tayi tana kallon shi.

‍♀‍♀Ina zan iya muku dan firar ku bata ƙarewa.

~~~~~~~~~~~~~

Banka gudu Momy ke yi,har suka isa garin katsina ba wanda ya ce da wani komai,wanan ƙaran
tsoron Haulat ya ragu.

Kamar yadda suka yi farkon zuwa yanzu hakan suka yi,saidai shi yanayin shi ya ƙara canzawa
ya ƙara muna,kuma bai yi dariya ba kamar wancen zuwan sai uban ihun ta yake yi.

Ya daɗe yana amvaton shi yana ihiuu yana yarfe-yarfe dukan su sun tsorata ainun ganin sun
daɗe bai ce musu uffam ba gashi sun daɗe da zuwa.

Cikin mummana kuma kaussar muryar ya ce,"Hatsabibiyar yarinya ce,da ƙyar ƙaranjuug yasha
ya kasa kusantar inda ta ke,ba nazara ba nazaraaa,ba zai iya zuwa inda take bahhh."

Wata razanannar ihuu yayi wacce dan tsoro har hantar cikin su saida ta juya,hatta kasar gurin
da bukkar zai da ta girgisa.

Bayan wasu ƴan mintina sanan komai ya lafa shi ma ya tsagaita.

Cikin rawar murya momy ta ce,"Yaanzuu shiii yaaron f."

Ai kamar ta ƙara tunzura shi ya ƙara buga wani sabon ihhu na tsawon sakonni sanan ya
murtuke fuska,ƴan karance karancen shi da kalle-kallen shi yayi sanan ya bushe da muguwar
dariya saida yayi mai isar shi sanan ya ce,"Akwai nazarraa Nazara,me kuke da bukatar ai
mishi?
Har momy ta buɗe baki zata yi magana haulat ta katse ta,"Ya so ni kamar ya mutu sanan sai
abinda na ce zai yi magana ta kaɗai zai ji sai yadda nayi da shi."

Dariya ya bushe da ita ,sanan kuma ya murtuke fuskar,"Wanan ƙaramin aiki ne amma akwai
sharaɗi bai tsauri...

Kallon Momy Haulat tayi a tsorace sai zare ido take yi.

"Hhhhh maganar tsoro babu ita tunda kuka kawo kan ku ƙaranjuuug ya amshi saƙon ku dole ku
yarda da sharaɗin."

Tsuull! fitsari ya zubowa Haulat tsabar tsoro da farga ba,kallon momyn take yi wacce ba alamar
tsoro da fargaba ko kaɗan a idon ta.

Kallon shi momy tayi ta ce,"Kasan ni indai akwai nazara to ina amincewa da ko wani irin
sharaɗi."

Dariya ya ƙara fashe wa da ita,wanan karan saida na tsorata da gudu na fito ina haki ina
naiman taimako duk na ruɗe na kasa gane hanyar da zan bi,kawai sai ga Aunty beelat janyo
hannu na tayi muka fara gudu,kwatsam sai ga ommu deedat da motorta tayi fakin a gaban
mu,ai tsorum muka taɗa,ina shiga ng bloody a ciki janyo ni jikinta tayi ta fara jijjiga ni tana ban
baki nayi shiru cikin raɗa ta ce min,"Bloody na ki kwantar da hankalin ki kinji ga shadowwn ki
tana jiran ki tun dazun."

Cikin hanzari na ɗago na kalle ta‍♀‍♀‍♀‍♀‍♀kunga dole na kama ɗariqa shadow tayi
kira.

.

Ina mugun -mugun son ku har raina,ba abinda zan ce saidai allah ya barni da ƙaunar ku a
raina❤.
[12/23, 2:24 PM] �° � D°�⭕Y: _ �σѕт у �яσυρ � � �уρє �αυѕα
�σνєℓѕ σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/23, 2:25 PM] �° � D°�⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*

*By*
*fatima* *Batula*
*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*
Page 18
.......................................

_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{BABU WANI AIKI DA AKE 'DORAWA AKAN MIZANI YA
SANYA MIZANI YAYI NAUYI KAMAR KYAWAWAN HALAYE DA 'DABI'U, KUMA LALLAI MAI
KYAWUN HALI YANA SAMUN MATSAYIN MAI RAYA DARE DA IBADA, DA RANA YA RAYA
DA AZUMI.}*_
```[Sahihut Tirmizy;2003,Sahihul Jaami'i;1620]```

_Shi kyawun hali yana dauke da dumbin alkhairi wanda mai yi zai amfana da shi Duniya da
Lahira. Allaahu a'alam._

```Allah ta'ala yasa mudace```

ﻚﻧﺎﺤﺒﺳ*_ ﻢﻬﻠﻟﺍ ,ﻙﺪﻤﺤﺑﻭ ﺪﻬﺷﺃ ﻥﺃ ﻻ ﻪﻟﺇ ﻻﺇ ،ﺖﻧﺃ ﻙﺮﻔﻐﺘﺳﺃ ﺏﻮﺗﺃﻭ _*​​.ﻚﻴﻟﺇ


_______________________________

Wata mahaukaciyar dariya yayi mai haɗe da ihuu sanan ya murtuke fuska ya kalle Momy ya
ce,"Kin yi nisa! asiri zai kama shi amma kuma duk sanda ya ƙarye kan ki zai dawo zaki haukace
ne."

Ya kara bushewa da dariya sanan ya ɗaura da faɗin,"Kuma asirin ba mai nisan zango ba
ne,duk sanda ya tambaye kan shi akan naiman dalilin da yasa yake bin umarnin ki kamar
raƙomi da akala to ranar zai ƙarye."

Haulat dan tsabar tsoron jin abinda ya faɗa saida fitsarin da yake zulluwa ya fito gaba
ɗaya,zuciyarta ta shiga buguwa da karfin gaske zufa duk ta wanke ilahirin jikin ta,kallon Momy
tayi wacce ita kan ta tana cikin tsoro da tashin hankali.

Murya na rawa Momy ta ce,"Mun amince!!

Ya kwarara uban ihuuu yana kallon ta yana tasar baki,"Duk sanda yaji muryarki asirin zai fara
aiki."

Ita kuwa Haulat kamar gunki haka ta koma,saida ya ƙara kwanciya da su sanan suka tafi.

~~~~~~~~~~~~~

Bayan sun kama firar suka shiya gidan su hajia suka nufa a can suka tadda dukkan su momy
da dady da farrah,fira suka yi sosai dan Naufal ma ya manta da wata haulat ni kuwa na ce
daman ba son nata yake yi ba.

Har bayan maqrib sunan nan zaune a falo Dady wacce Sabreen ke zaune akan cinyar shi ya
zaunar da ita kasa gaban shi,kiran Naufal yayi ya zo kusa da ita ya zauna.

Cikin dattijowar murya ya ce,"Naufal!

Naufal wanda ke zaune a kasa gaban Dadyn kusa da matar shi ɗukar da kan shi yayi ya
ce,"Na'am Dady."

"Naufal ba zan iya misalta maka irin farincikin da na ke ciki ba,duk da nasan ka ji magana ta
kuma ka bi umarni na ka amshe matarka da hannu biyyiyu,amma hakan ba zai hana na ƙara
tunatar da kai akan amanar da ka ɗauka ba,Naufal Sabreen amana ce na danƙama, ka sani
Naufal ko wani irin yanayi zaka tsinci kan ka a rayuwar nan idan har ka cutar da sabreen ban
yafe ma ba ko bayan ba raina bani ba ka."

Zuciyar Naufal ta fara bugawa da mugun ƙarfin wanda faruwar hakan yai sillar haifar mishi da
mutuwar jiki,bai yi tunanin zai iya magana va yai karan banin buɗe bakin shi,"Dady na ma
alkawari ba zan cutar da ita ba komai rintse komai wuya zan rayuwa da ita zan kyautata mata."

"Yawwa Naufal Allah yai maka albarka."

Jin amsar da Dadyn ya bashi ne ya tabbatar mishi da ya faɗi abinda ke ran shi kenan.

"Naufal ka ga Sabreen ba sabawa da zuwa irin ƙasacen nan tayi ba ,dan haka sai ka kula da ita
sosai,Sabreen matar ka ce nasan ka fi ni sanan yadda zaka kula da ita,tsananin son da na ke
mata ne yake sawa naga kamar ba wanda zai iya kula da ita,Naufal karka cutar da sabreen dan
ni zaka cutar ,idan ka kyautata mata ka kyautata min,ina son sabreen fiye da tunanin ka jinin jiki
na ce,ka kula da ita k....

"Ya isa haka kamar yadda kake son ta shi ma yana son ta matar shi ce,"
Cewar hajia ,kallon Naufal ɗin tayi fuskar ta ɗauke da murmushi wanda shi har lokacin kan shi
yana ƙasa,"Naufal ba abinda zan ce ma sai abu ɗaya ni ma na baka amanar Sabreen shi ne
kawai abinda zan faɗa ma,matarka ce ka fi mu sanin yadda zaka kula da ita,allah ya kaiku
lafiya ya dawo da ku lafiya."
Dukkan su suka amsa da amin,sanan momy ta kalle shi ta ce," nima abu ɗayan zan faɗa ma ka
riƙe amanar Sabreen Naufal allah ya kaiku lafiya."

Nan mu suka amsa da amin,sanan suka ɗan taɓa firar duk akan tafiyar su ɗin labarin garin su

ke yi,da gidan ya zasu sauka.

Duk abinda ake yi jikin Naufal a mace,zuciyar shi ta cunkushe wanda hakan ya hana shi yin
tunanin komai.

Sai ƙarfe takwas suka tashi zasu koma gidan su,Sabreen tayi kuka kamar ranar auran ta tunda
goben tun biyar zasu bar gida ba haɗuwa zasu kuma yi ba,da ƙyar aka janye jikin ta gurin hajia.

"Kiyi hakuri ki daina kukan nan plss."

Kallon shi tayi cikin kukan ta ce,"Ji na ke kamar na tafi kenan bazan dawo ba."

Saida gaban shi ya faɗi taka burkin motor yayi da sauri ya juyo
ya kalle ta,janyo ta jikin shi yayi ,"Hava ƴar aljanna yaushe kika zama haka ne ban san ki da
rauni ba fah,taya zaki ce haka zamu dawo cikin ƙushin lafiya."

"Ba zamu daɗe ba ne."

"Eh ai sai yadda kika ce,idan kina so a fasa zuwan ma za'a fasa."

"A'a ina son zuwa."

"Kina son cin amarci kenan."

Murmushi tayi ta ɗaga mishi kai alamar eh.

"To ai baki iya komai ba."

"To ba ka ce zaka koyamin ba."

Ɗago kanta yayi kasancewar akwai haske a motor yasa ya ga fuskarta da kyau lipa ɗin ta ya
fara kallo,haɗa bakin shi da nata yayi sun ɗau lokaci suna abu ɗaya kafin ya fara fita haiyacin
shi,ganin abin yafi ƙarfin ta yasa ta fara koƙarin zame jikin ta,amma ta kasa.

"Ya Naufal!

Yaya yayi nisa nishi ya fara yi,janye jikin ta tayi da ƙarfi ita ma haƙin ta fara yi.

Sun daɗe a haka suna nishi wanda kowa ke jin na kowa,can ya ja motor cikin ƙanƙanin lokaci
ya isa gidan.

Tunda yayi fakin ɗin ya tsaya yaƙi saukowa,ganin hakan yasa ta ce,"ka zauko."

Tana gama faɗa ta sauko gaba tayi bata tsaya jiran shi ba.

"ke ce kaddara ta Sabreen dole na karɓe ki ba yadda na iya,nasan wata rana zan son ki."

Ya daɗe yana tunanin ya amincewa zuciyar shi yin rayuwa da ita cikin kulawa ga alƙawarin
iyayen shi baya son ya saɓa musu,kuma ko da ba alƙawari Sabreen abin tausayi ce marainiya
ta uwa da uba dole a tausaya mata,ya yaken wa zuciyar zai koyan son ta idan sun je turkey .

Ita kuwa kai tsaye ɗakin shi ta nufa saida yi ɗan gyare-gyare sanan ta shiga bayi tayi wanka ta
tauro alwala,shafa'i da wutiri ta yi.

Tana cikin yi ya shigo murmushi yayi dan san tayi sallar isha'i zama yayi bakin gadon yana
kallon yadda take sallar komai daidai cikin natsuwa,bayan ta gama ta fara addu'o'i duk yana
jinta saida ta yi komai sanan ta tashi da nufi ɗauke sallayar ganin shi yasa tayi murmushi.

"Ka shigo? na haɗa ma coffee?

"Eh lipton ki matsa lemon tsami."

"To wai kana jin daɗin shi ne."

"Eh!

"Nima zan haɗa na sha."

Vata tsaya jin avin da zai ce mata va ta bar ɗakin,saida ta shiga ɗakin ta sanan ta sauko kicin
ɗin ,cup biyu ta haɗa duk ta saka lemon tsamin sanan ta nufi ɗakin.

Da sallama a bakinta,ta isa ɗakin,can ƙasa ya amsa mata gaban shi ta je ta ajiye mishi sanan ta
ɗau na ta.

"Kin saka ma naki lemon tsamin ne?

"Eh baka ce akwai daɗi va."

"Magani ne fah kuma bai kama ta ki sha ba."

"maganin me? ko ma na meye tunda kai kasha nima zan iya sha,oh yanzu gobe iwar haka
muna can garin ƴan gayu."

Kallon ta kawai ya ke yi yadda ta ke jero zance wani kan wani,murmushi kawai yake yi,kuma
taƙi dainawa zai yi ta ke yi.

Can ta gaji lokacin ta sanye lipton miƙa tayi da sauri yai ƙasa da kai dan baya son yaji wani abu.

Cikin muryar jin barci ta ce,"Ni barci na ke ji kar na makara gobe."

Tashi tayi ta hau akan gadon yana kallon ta,ta rufe da bargo,murmushi kawai yake yi yana jin
wani irin baƙon yanayi yana kai wa zuciyar shi ziyara.

Bai tsaya wani tunani ba ya kwanta nan da nan barci yai awan gaba da shi.

>>>><<<<

Kamar dai kullum yau ma hakan ita ta fara tashi da jin kiran sallar farko na asuba,bata
tsaya tashin shi ba ta fita ɗakinta,ta nufa na zuwa ta fara haɗa ƴan abubuwan da zata naima
Dady ya ce gidan akwai kayan sakawa amma saboda tsoro zu ɗau abinda zasu bukata,haka ta
haɗa abubuwan ta a cikin akwati duk abinda tasan zata buƙata,tana gamawa ta shiga bayi tai
alwala,da ta fito saida tayi nafila sanan ta wuce ɗakin shi tashin shi tayi dan lokacin an kira
sallah,yana tashi ya shiga yai wanka ya ɗauro alwala,ko kafin ya fito ta fara gyara ɗakin,yana
fitowa ya tafi masallaci ,ita kuwa ta gyara ɗakin tsab.

Yana dawowa Dady ya iso dan shi zai kai su tashar jirgin,tara da hajia su ka zo dan ta ƙara yi
musu sallama basu wani ɓata lokaci ba suka ɗau hanyar ,saura minti hudu jirgin ya tashi,hajia
da Sabreen kuwa sun sha kuka.
��Wai sai ƙasar turkey.

~~~~~~~~~~~~~

"Ke dan allah ki kwantar da hankalin ki wahalar da muka yi ba zata tafi a vanza ba,kawai dai
yanzu kiyi ta kokari ki samu wayar shi yana jin muryar ki aiki zai fara,idan ya so zai ki bishi ƙasar
ma."

Ita kuwa Haulat ɗin wacce ta zuba uban tagumi a gaban Momyn tana hawaye da wayar a
hannun ta.

Dafa ta momy tayi,"Ki kwantar da hankalin ki idan sun sauka ki ƙara kira ,karki manta ba duk
abinda kika faɗa shikenan to meye da damuwa."

"Kina ganin zai ɗau wayar kuwa."

"Dolen shi ba,ai ki fara shirin zuwa ƙasar turkey private zaki hau ya kai ki yau ɗinnan komai
dare."

"Taya Momy."

"Wai yaushe kika zama banza ban sa ni ba,kuna yin waya ya turo miki kuɗi ki bishi."

"Je ki fara shiri ma,kuma idan jin je karki rama ma ƴar iskar matar ta shi,ku ƙuntata mata dan
uban ta duk ita ce ta bamu matsala."

Wani irin farin ciki ya mamaye Haulat da rawar jiki ta tashi ta fara shiriii.

~~~~~~~~~~~~~

Ƙasar turkey kyakyyawar kasa ce mai abubuwan birgewa,yanayin tsarin garin da yadda al-adar
mutanan garin ya ke shi yafi komai birgewa.

Tunda suka zauko Sabreen ta fara zare ido tana kallo riƙe shi tayi gamm kamar wani zai ƙwace
shi.

Wata tsadaddiyar motor da wani ɗan afirka a cikin ta yazo tarbar su,cikin harshen turanci ya
gaida su cikin girmamawa,suna shiga motor ta lafe a jikin shi.

"Lafiya ko garin bai miki ba ne?

gaɗa kai tayi alamar a'a,taɓa jikin ta yayi,dan ya lura yanayinta ya canza da zuwan su.

Cikin nuna kulawa ya ce,"Baki da lafiya ne?

"A'a lafiya lau,yaya karka barni plss."

Saida gaban shi yai mummunan faɗuwa,"Sabreen ba zan barki ba ki kwantar da hankalin ki
,amana ce a guri na,taya zan bar ki na je ina? kin san ban isa na ce gida babu ke ba,ke fa ƴar
uwata ce ,zan kasance da ke har abada." cikin sigar lallashi ta tausasawa yayi magnar.

Ɗago da kanta tayi wanda ta kwantar da shi akan ka faɗar shi,ta kalle shi yaƙe tayi.

A zahirin gaskiya tunda suka zauko dga jirgin faɗuwar gaba ya kamata jikin ta ya mutu,wani irin
yanayi mara daɗi ya shiga zuciyarta.

Sun daɗe zuna tafiya a motor bata ɗago ba balle ta kalla yanayin garin shi ma haka,wani irin
abu mara daɗi ya ke ji a ranshi.

Wani hamshaƙin gida dan madaidaici direban ya nufa yana isa mai gadin wanda shi ma ɗan
africa ne ya buɗe musu hamshaƙin get ɗin,karamin gida ne amm huɗuwar ta yi yawa,wanda
idan kwatantawa zai ya ɗauke mu fiye da shafi biyar.

Yana tsayar da motorn ya fito da sauri ya buɗe musu,hannunwan ta ya riƙo su ka fito cikin su ba

wanda ya tsaya kallon gidan sun bi bayan mutumin da ya kawo ne ,sun ɗanyi tafiya kafin suka
isa cikin lafiyayyan falon suna isa ya tsaya,cikin harshen yar musu barka da zuwa ya juya.

Zaunar da ita yayi a kan kujerar da ke fallon kallon falon ya tsaya yi ,ya mishi kyau ainun,ita ma
kallon falon tayi tai gutun murmushi ta ce,"Gidan yayi kyau sosai."

Kallon ta yayi ya sakar mata murmushi,"Nima yamin kyau,tashi mu je ɗaki muyi wanka muyi
sallah sai mu fito mu kewa ya mu ƙara ganin gidan ko."

"Eh!

Hannunta ya riƙo suka nufi wata hanya wacce su ke tunanin ita zata sada su da ɗakin
kwana,hakan kuwa ɗaku na ukku ne a jere,fuɗe wanda su ke kusa yayi suka shiga,ai nan suka
yada ido dan haɗuwar ɗakin har yafi falon kyau gashi babba harda tavi da kujeru a ɗakin sai
gadon ne ɗan ƙarami.
Basu wani tsaya ɓata lokaci ba,gurin ajiyar kaya ya nufa yana duvawa ya gane ɗakin ta ne,dan
kayan mata ne.

"Ki shiga bayi kiyi wanka." ya faɗa haɗe da nuna mata bayin ,ba musu ta shiga,tana shiga ya
fita ɗayan ɗakin ya shiga yana dubawa kowa yaga ɗakin shi ne,bayi ya shiga shi ba wani
tsayawa kallon haɗuwar bayin yayi ba,dan ba yau ba ne farkon ganin gida irin shi ba.

ita kuwa ta zuba ƙauyanci kamar wacce ta fito a zaria ba abuja ba.

Da ta fito baya ɗakin sakin jikin ta tayi ta saka kaya duguwar riga cikin wacce ta tawo da
ita,sallah ta fara yi.

Shi ma hakan sallah ya fara yi,tun yana sallah yake jin ringin ɗin wayar shi har ya idar ana
kira,kafin ya idar anyi jira goma sha bakwai,yana idarwa ya nufi gurin wayar sabowar number ya
gani,gaban shi yai mummunan faɗuwa yana gurin har aka ƙara kira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login