Showing 48001 words to 51000 words out of 57176 words

Chapter 17 - NIDA MALAMATA BOOK COMPLETE BY Fatima Batula.pdf

16 Mar 2025

5538

amma bai ɗauka
ba,number ya zubawa ido number 9j ne bawai yasan mai number ba ne,yadda gaban shi ke
mugun faɗuwa ne yasa ya kasa ɗauka,wani kiran ya ƙara shigowa,yai jan hali ya ɗau wayar da
kalmar "Hello" a bakin shi..

.

love u guys irin over ɗin nan fah.
Sir Dboy
[12/23, 2:26 PM] �° � D°�⭕Y: _ �σѕт у �яσυρ � � �уρє �αυѕα
�σνєℓѕ σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/23, 2:27 PM] �° � D°�⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*

*By*
*fatima* *Batula*

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

Page 19
..................................................................

_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{MUTANE SUNA DA HALIN MUTUM BIYU NE; NA KIRKI
TSARE DOKA MAI 'KIMA A WAJEN ALLAAH, KO BANZA MARA RABO DA 'KIMA A
WAJENSA.}*_

```[Sahihul Jaami'i;7867]```
~~
_Wannan hadisin yana nuna mana cewa shi dan Adam a halinsa dayan abu biyu ne; ko dai ya
zama na kirki mai tsoron Allaah ko kuma ya zama na banza mara qima da rabo a wajen Allaah.
Allaah Ya sanya mu daga cikin masu halin kirki. Allaahu a'alam._

```Allah ta'ala yasa mudace```

________________________

A tare su ka ce, "Me ya faru da ita?

Farrah ta ruɗe sama kawai ta ke nuna musu,cikin inda-inda ta ce,"Sabreen bata da lafiy...

Tun kafin ta rufe baki sun bar gurin saman su ka hau da sauri,suna zuwa su kai kanta lokacin
zazzaɓin ya tsanan ta.

"Ƴar aljanna!
Gaba ɗaya hajia ta ruɗe,momy ce tai ƙarfin hali ta ɗauke ta,da gudu su ka fita da ita dukkan
su,su na zuwa su ka shiga motor direba ya ja su.

Su na isa asibitin doc zain ya tarbe su,alluran barci yai mata,duk suna tsaye a gurin bayan ya
gama ƴan abubuwan shi,sanan ya juyo ya kalle su.

"Momy Hajia akwai damuwa a tare da ita,ban son shiga lamarin da ba nawa ba,ba ita ba ce
matar Naufal? kuma kamar ita yai ma laifi?amma ta hakura ta yafe mishi ba lallai sai ya zauna
da ita ba idan ba ku san haka,amma yana buƙatar ku yafe mishi yana cikin wani hali ƙiris
zuciyar shi ke jira ta fashe,ɗazun bayan fitar ku ya kalle Farrah,ya farka saida yayi zuma sama
da ashirin da aman jini da ƙyar mu ka samu yayi barci."

Tunda ya fara magana jikin su yayi sanyi,hatta hajia saida tayi kwalla farrah kuwa kuka me ƙarfi
ne ya kama ta,Allah sarki momy kukan zuci kawai ta ke yi.

Shi kuwa doc ta zain ganin kalaman shi sun shiga jikin sui yasa ya fita daga ɗakin.

~~~~~~~~~~~~~

Haulat kuwa a ƙasa ta taka har unguwar su,kamar wata mahaukaciya tana tafiya tana surutu ga
hawaye,tana isa gidan su ta fara jin ihuuu yana tashi,gigicewa tayi jin muryar me ihuun da gudu
ta faɗa cikin gidan.

"Haulat nasara a jini na ta ke,ko yanzu na ci nasara,kin gani kin gani,ina ita yarinyar?

Momy ke wanan maganar tana rawa duk ta raba jikin ta da kaya,alamun hauka ƙarara.

Sakina ita da Salma sai kuka su ke yi,sun kasa riƙe ta gashi sai ɓarna ta ke duk ta fasa glass ta
yanke hannuwan ta.

Kamar gunki haka Haulat ta koma hawayen da na sani sun wanke fuskarta,"Momy mun cuci
kan mu,ba muyi nasara ba ,momy"

Ita kuwa momy sai hauka ta ke yi tana rawa tana ihuu sun yi nasara,da ƙyar salma da sakina su
riƙe ta ,a ɗaki su ku kulle ta.

Sakina ta fashe da kuka,"Sanda na ke gaya mu ku,baku saurare ni ba,tun yanzun kenan a
duniya,ga haƙƙin mutanan da ke kanku wanda allah ba zai iya yafe mu ku shi ba,yanzu su waye
da nasara? kun mata duk nisan jifa ƙasa zai dawo ai...

Luuu Haulat ta faɗi kasa zumamma wanda zuman ne ya katse sakina maganar da ta ke yi,a
ruɗe su ka je gurin ta su na ihuuu.

~~~~~~~~~~~~~

A hankali ta fara buɗe nauyayan idanuwan ta,sama-sama ta fara ganin mutanan da ke ɗakin.

"Dady Yaya"dan Allah dan annabi hajia."

"Ya isa kwanta kin ji ki kwantar da hankalin ki."

Zaune ta tashi tana hawaye,"A'a Dady dan allah yaya zai mutu ba wllh bashi da laifi dan ..

"Shikenan!

Dukkan su sunji daɗi da har su ka kasa ɓoyewa,ko wanne su fuska ɗauke da annuri hatta hajia.

Sabreen kuwa rungume Dady tayi tana kukan jin daɗi,"Na gode dady muje mu gan shi."

Daman a lokacin doc zain yana nan yai musu jagora har ɗakin,hatta dady sai da ya tausaya
mishi ganin halin da ya ke ciki,Dady da momy ne kawai ba su yi kuka ba,momy na zuciya tayi.

Kusa da shi Sabreen ta matsa tana kuka mai ratsa zuciya,kan shi ta taɓa a hankali ta ce,"Yaya!

Kamar daga zama ya fara jin muryar ta,lokaci ɗaya yaji zuciyar shi wani haske da daɗi yana kai
mata ziyara,koƙari ya fara yi ya buɗe idanuwan shi,dan ya kan ta.

Sama-Sama ya fara ganin dushi-dushi,ganin hakan yasa Sabreen ta yin wani yalwataccen
murmushi.

a kan fuskarta idanuwan shi su ka zauka,kallon-kallon su kai wa juna,wani irin abu ke ziyarar
zuciyar shi,duk sai yaji ya manta da komai.

Wasu hawayen ne su ka fito mata,"Ya jikin?

Hannu ya miƙa mata ta riƙe alamar ta zauna kusa da shi yai mata,zaman tayi kusa da shi,da ido
yai mata alama da ta goge hawayen ta.

Su kuwa tsayawa kallon ikon allah su ka yi,abin ya basu mamaki ganin wata ɓoyayyar soyayya
a idanuwan su,momy kuwa ita da farrah sun fi kowa jin daɗi ,Dady kuwa mamaki ne ya kama
shi,"To daman yana mata irin wanan son kuma zai aikata abinda yayi.",abinda zuciyar shi ke
gaya mishi kenan.
Su kuwa sun manta da akwai wasu muta ne a ɗakin kallon juna kawai su ke,su na fira da ido.

Farrah ce ta ƙarasa gurin basu san da zuwan ta ba,murmushi tayi ta ce,"Yaya ya jikin?

Kallon ta yayi ya ɗaga mata kai,daidai da haɗuwar idon shi da momy,da sauri yai ƙasa da
kai,zuma ya fara yi,a ruɗe su ka ƙaraso gurin shi harda Dady duk sun ruɗe,ita kuwa sabreen
kuka ta fara yi.

Aman jini ya fara yi nan da nan numfashin shi ya fara koƙarin fita,Ihuu su ka yi gaba ɗayan su
banda Dady,jin ihuun yasa doc zain ya shigo a ruɗe ya kore su,da ƙyar dady ya ja Sabreen dan
ƙin fita tayi.

nan da nan doc zain ya fara koƙarin taimakon rayuwar shi.

su kuwa su na waje Sabreen sai rusa kuka ta ke yi an kasa samun wanda zai bata hakuri,dan

kuwa kukan ya ke yi.

Hankalin momy ya tashi ainun,tasan ganin ta ɗin ta yayi ne,"Taya anya kuwa idan har da gani
da zuciyar shi zata buga kenan abinda ya aikata ne wanda na ganshi ya tuno." sai hawaye,"Hm
koma mene ba da san ran ka ba ne Naufal mutumin da baibi mata a india ba sai a nan."duk a
zuciyarta taita maganganu tana hawaye.
Hajia kuwa faɗi ta ke,"Allah sarki Naufal mun yafe ma,kadɗara ce."

Shi kan shi Dady jikin shi duk ya mutu.

ko doc zain ya fito bayan ya dau lokaci mai tsawa, yana fitowa su ki kan shi.

"Na shaida mu kar ya farka da wani tunani wanda zai fada mishi rai ko ya ga wani avu, a
gaskiya yanzun idan ya farka da irin haka to gaskiya va zamu iya komai va, yanzu kawai ku tafi
gida dan va zaku samu damar ganin shi ba."

Gaba dayan su jikin su ya mutu sun tausaya mishi ainun, savreen kuwa sai rusa kuka ta ke yi,
Dady ne yai karfin halin jan su,haka su ka koma gida ko wanne jiki a mace hatta dadyn ma.

Ba wanda ya saurari wani kowa da kan shi yayi, da kyar sabreen ta samu tayi sallar isha'i ta
kwanta bayan ta kama kwaranyo mishi addu'a, ba ta yi wani barci va ,tana jin kiran sallah ta
tashi tayi...

Abubuwa sun dan min yawa kuyi hakuri da wanan

.
[12/23, 2:27 PM] �° � D°�⭕Y: _ �σѕт у �яσυρ � � �уρє �αυѕα
�σνєℓѕ σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/23, 2:29 PM] �° � D°�⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*

*By*
*Fatima* *Batulah*

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

Page 20

.......................................
Addu'a ga Wanda Ya ce Maka: Allah Ya yi Maka Albarka:
َكيِفَو َكَراَب .ُهللا
wa fika barakallah.

Kai ma Allah ya yi maka albarka.

.......................................
Zaune ta ke akan sallaya tana kuka tana cewa,"Allah na tuba! ka yafe min duk laifi na ne da ban
shiga rayuwar shi ba ,da hakan bata faru ba,nayi kuskure."

"Ba wani kuskuren da kika yi Sabreen ,ke ce alkairi a rayuwar shi,Yaya Naufal yana son ki
Sabreen."

Kallon Farrah tayi da jajayen idanuwanta ta ce,"A'a Farrah baya so na malama Haulat ya ke so
ba ni ba..

Tass ta kwashe dukkan labarin abinda ya faru tsanin ta da malama haulat har dalillin da yasa ta
ce zata aure shi bayan bata son shi baya son ta.

Saida Farrah ta sauke raguwar ajiyar zuciya sanan ta ce,"Sai yanzu na fahimce wani abu,amma
kuma zargi ne kuma ba komai,amma zan yi bincike akai sosai."

"Me kike zargi?

"Ba komai zan gaya miki komai idan na tabbatar da bincike na,Sabreen abinda kike yi daidai
ne,kuma yaya na son ki."

"Baya so na Farrah."

"Hm yana son ki,ke ma kina son shi."

zare ido tayi,"Me? rufamin asiri yaya ba zai so ni ba,nima bana son shi."

Ganin ba zata iya fahimtar da ita ba yasa ta ce,"Yanzu ki tashi mu je gurin shi."

"Ni ai tun dazun na shirya ,ke na ke jira."

Murmushi kawai Farrah tayi,tana mamakin sabreen da bata gane abubuwa sosai.

Tun da safe momy ta tashi daman ba wani barcin kirki tayi ba,tunanin ɗan ta ya hana ta yin
barci,ba ita kaɗai ba hatta Dady saida yayi tunani.

Tun da safe momy ta,tashi ta haɗa musu abinci har wanda zasu kai asibiti,saida ta gama haɗa
komai ta shirya,tana cikin shirya abinvi hajia ta shigo kicin ɗin a tare su ka gama.

Suna zaune a falon su sabreen su ka zauko kasa,cikin girmamawa su ka gaida su.

Momy ta kalle Sabreen so da kaunar ta yana ƙara shiga ran ta,murmushi tayi mata alama da
ta zo gurin ta tai mata,tashi tayi daga kusa da farrah ta dawo inda momyn ta ke.

"Sabreen ya jikin?

"Da sauƙi momy."

"Masha allah ki kwantar da hankalin ki sabreen karki sawa kan ki damuwa kin ji,yau idan mun je
asibitin ke kadai zaki shiga,dan na ga alama ganin mu ke ɗaga mishi hankali."

Kai ta ɗaga ta ce,"To momy."

"Yawwa allah yai miki albarka."

"Amin."

"Momy ni fa ce,"cewar farrah haɗe da turo baki.

Murmushi momy tayi ta ce,"Allah yai mu ku albarka baki ɗayan ku."

A tare su ka amsa da ,"Amin."

Saida Dady ya fito sanan suka ci abinci bayan sun gaisa,Sabreen na jikin shi yana bata a baki
kamar wata yarinya,saida ya tabbatar da ci sosai sanan ya gyale ta.

Suna gama ci su ka tashi,motor biyu su ka yi,Dady da su Sabreen da farrah a motor shi,Momy
ita da Hajia.

Suna isa asibitin su ka naimi doc zain,bayan sun gaisa ya kalle Dady ya ce mishi,"Tun jiya bai
farka ba,ina jin tsoron ya farka ne da wani ɓacen rai a zuciyar shi gaskiya zaku iya..

Katse shi Dady yayi da faɗin,"Dan Allah doc kai mishi allurar da zata tashi shi ,matar shi kaɗai
zai gani kuma nasan ganin ta zai kwantar mishi da hankali kamar yadda ita ma ganin shi zai
samar mata natsuwa."

"Okk ba matsala,amma plss karki mishi maganar da zata ɗaga mishi hankali,"ya kare maganar
yana kallon Sabreen.

Ɗaga mishi kai kawai tayi alamar eh zata yi yadda ya faɗa.

A tare su ka fita daga office ɗin na shi,har sun kusa ƙarasawa ya juyo ya kalle su ya ce,"Ku
tsaya daga nan plss."

Ba abinda su ka ce mishi illa bin umarnin shi da su ka yi kawai,ita kuwa binshi tayi da sauri yana
buɗe kofar ta shiga ita ma.

Saida yai mishi wata allura,kamar a jikin ta za'a yi taji,yana kama allurar ya fita ya barta ita
kaɗai.

Akan gadon ta zauna har jikin su ya na taɓa juna,hannuwan ta ɗaura a saman kan
shi,kwantaccen baƙin gashin shi mai laushi ta fara shafawa,cikin wata irin murya ta ce,"Miji na!

Kai tsaye muryarta ta kai zuciyar shi,wanda hakan ya harfar mishi da jin daɗi wanda saƙon
zuciyar ya isa fuskar shi.

Murmushi tayi ganin murmushi a fuskar shi,ta ƙara faɗin,"Mijina! ka buɗe idon ka,Sabreen ce
matar ka!

Murmushin fuskar shi ya ƙara faɗaɗa idanuwan shi su ka fara koƙarin buɗewa bakin shi ya fara
motsi.

Dushi-dushi ya fara buɗe nauyayan idanuwan shi wanda har yanzun bakin shi yana motsi.

"Sabreen! ya faɗa tare da sauke idanuwan shi a kan ta,ba wai taji sautin muryar ba ne,ta ga
yadda bakin shi ya nuna alamar ita ya kira.

Kallon juna su ka fara yi wani irin baƙon yanayi yana ziyarta ko wannen su ,sun daɗe a haka
kafin ta yanke shirun da faɗin,"Ka ji sauki dan allah mu koma gida ga ji,gidan ba daɗi kasan na
xaba da kai,ko kana son nayi ta kuka ne?

Murmushi yayi mai ƙyayatarwa muryar ta na mishi daɗi musaman yadda idam tana magana
cikin sauri bata tsayawa sauke numfashi.

Lumshe ido kawai yake yi yana kallon ta tana magana lips ɗin ya zubawa ido yana ganin yadda
ta ke sarrafa su,yakan rasa dalilin da yasa idan yana tare da ita yakan manta komai da kowa.

"Ka ji Sauƙi ko! mu tafi gida,ba zan ɗinga damun ka ba."

Murmushi kawai yake yi.

Turo baki tayi ta ce,"Ba xaka yi magana ba ne,zan tafi fah."

Da sauri ya riƙo hannun ta,saida wani abu ya tsikari zuciyarshi a hankali dan baiyi tunanin zata
ji ba ya ce,"Pls stay with me,mai xan ce?

Dariya ta fashe da ita,a ranta tana faɗin,"Ba xaka canza ba halitta ce wanan iyayin na ka.

mutum ba lafiya ji yadda ya ke magana."

Ganin ta fara dariya yasa shi ma ya fara duk da sautin nashi baya fitowa sosai ita kaɗai ta ke ji.

Kallon kallo su Dady ke wa juna dan jin dariyar Sabreen ƙarara mamakin su ya baiyana,momy
kuwa da hajia da farrah sai washe baki su ke yi,shi kuwa dady mamaki ne ke ƙara kamashi
matuƙa.

Doc zain ne ya zo inda su ke ,shi ma fuskar shi ɗauke da annuri ya ce musu,"Kun ji ko? suna
matuƙar son juna,wanan shi ne maganin shi,am srry to say,ba zaku gan shi ba har sai ciwon
yayi sauƙi ,amma ita dole a barta anan,yanzu zaku iya tafiya,zan shigar da abincin a
bashi,amma zuwa anjima zaku iya dawowa ku ɗauke ta idan ya kwanta."
Ba wanda yaji ba daɗi a ranshi sai ma jin daɗin da su ka yi,dan samun sauƙin shi na tattare da
sabreen ɗin.

Kallon shi Dady yayi fuskar ɗauke da annuri ya ce,"Ba komai doc mun gode sosai kuma mun ji
daɗi allah ya ƙara mishi lafiya."

A tare su ka amsa da ,"Amin ya Allah!,su juyo abin su .

Murmushi yayi doc zain yayi ya ɗau kular abincin ya shiga da ita ɗakin,da sallama ya shiga
dariyar da su ke bai bari sun ji sallamar ba.

" Hmm irin wanan love!

A tare su kalle shi suna ƙoƙarin tsagaita dariyar su,shi ma murmushin yayi ya ce,"To ga abinci
ya shi sai ya sha magani yadda za ku tafi gida da sauri."

Murmushi Sabreen tayi ta ce,"To doc nima na ƙagara mu tafi shi ne dai ya ke son zaman."

Bai ce komai ba,ya fita abin shi yana murmushi.

Kular abincin da buɗe farfeson dan kalin turawa ne da hanta,sai tashin ƙamshi su ke yi, zubu
mishi tayi.

"Au sai ka ɗan tashi zaune kaɗan,"Tana faɗa ta kai hannuwan ta kafaɗar shi da zummar
taimakon shi ya ɗan zauna kaɗan.

Tsigar jikin shi ta tashi yarr,lumshe ido kawai yayi,wani abu ya mishi yawo a zuciya.

Ɗauko abincin tayi "Ka fuɗe baki da ido,ka ci abinci."

Buɗe idanuwan yayi,amma ya ƙi buɗe bakin,marairai ce fuska tayi alamar shagwaɓa.

Murmushi yayi komai Sabreen tayi burge shi yake yi,ba wai abincin ba ne ba zai iya ci ba,yana
son ya wanke baki ne.

"Ba ka son muje gida ko?

"Ina so ko dan.. sai yai shiru.

Bata naimi ƙarin bayani akan abinda ya kasa faɗa ba,ta ce,"To ka ci dan allah,"cikin shagwaɓa
ta ƙarasa maganar.

"Baki na ba'a wanke ba."

"Hm kai ana ta kai kana ta kaya.",a ran ta ta faɗa a fili kuwa cewa tayi,"Toh bari na kawo ma
roba da ruwa ko."

Tana faɗa ta ajiye abincin ta nufi bayin,maclean da brush,sai ta ɗibu ruwa a wani cup sai ta
tawo da ɗan ƙaramin ruba kamar bahu me faɗi.

Da ɗayan hannun ya ɗan wanke bakin,taɓe baki kawai ta ke yi ganin haƙuran basu yi datti
ba,ya gama ta maida da su bayin,ta zubar da ruwan.

Har ta shiga bayin ta fito idanuwan shi su na kanta.

"To bismillah! faɗa haɗe ta ɗan murmushi,shi ma murmushin yayi ya buɗe bakin ta fara bashi,a
hankali yake ci,ka ɗauka haɗiyewa kawai ya ke yi,ba taunawa ba.

Yaci sosai shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login