Showing 3001 words to 6000 words out of 57176 words
Chapter 2 - NIDA MALAMATA BOOK COMPLETE BY Fatima Batula.pdf
son hali irin na shi ga rashin kula mutum ga sharewa ga yatsine.
"Naufal ya hajiar"
"Tana lafiya tana gaida ke wai anjima zata shigo"
Yana faɗa ya tashi cikin yauƙi yabar falon.
"Allah momy yaya ya ƙara Chanjawa daa da ɗan sauki ,amma yanzu tunda ya dawo abin ya
ƙaru"
Murmushi momyn tayi dan nasan gaskiya farrah ta gaya mata.
~~~~~~~~~~~~~
Cikin shigar doguwar jira ƙirar dubai ta ke baƙa ce rigar ta matuƙar amsar jikin ta kamar dan ita
aka yi rigar,rolling tayi da ɗan ƙaramin gyalen waw,masha allah *Sabreen* kyakykyawa ba wani
haske gare ta ba,amma akwai kyau kamar me,ɗan karamin bakin ta wanda yake kamar an zana
shi,shi ke ƙara fidda kyawun ta,hancinta dogo ne amma ba siriri ba ne tana da cikar fuska ga
fararen haƙora da ido gata da yalwar gashin gira da na ido ,ga iya murmushi hmmm abin dai
sai wanda ya gani dan kamar a novel lolx to meye wanan..
♀♀yehh yanzu zan fara.
ga me bukatar shiga grp ɗin 08155184562
comment
shire
✅ote me on wattpad@fatimaumarmoddibo
~Bhartoolerty~
[12/6, 9:38 AM] ° D°⭕Y: _ σѕт у яσυρ уρє αυѕα σνєℓѕ
σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/9, 1:05 PM] ° D°⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*
*By*
*fatima* *Batula*
*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*
Page 2
.......................................
Cikin yanga ta ƙara su falon tana murmushi ta ƙagara gobe tayi,dan taje makaranta ta rama
abunda Malama Haulat tayi mata.
"Kai masha Allah ƴar Aljanna kinga yadda kike da kyau kuwa "
Hajiya ta faɗa tana kallon Sabreen ɗin.
Washe baki tayi ta ce"Hajiya ta ai ke na biyo shiyasa nayi kyau"
Ƙarasawa gurin Hajiyar tayi fuskan nan tata ɗauke da annuri, kan jikinta Hajiyar ta kwanta.
"To tashi muje tunda kin shirya"
Murmushi tayi tuno Gidan su Naufal zasu je,wanda ba wani tazara a tsakanin su dan a layi
ɗaya suke.
"To muje ta faɗa haɗe da tashi ta fita gurin direba ta nufa ,yana ganinta ya taso a ruɗe.
"Kai kaji dai abinda na gaya maka,wallah inda aka samu matsala kasan abinda zan ma ba zai
na gayama ba,da zaran ka ga kira na goben sai ka shirya,kasan yadda zaka yi da mai gadin
makarantar ka kul....
"Ya dai lafiya ko wani abun ya miki ne" faɗar Hajia.
"A'a ba abinda ya min ,muje ko"
Buɗe musu motar yayi suka shiga,ba wani lokaci suka ɗauka ba dan daman duk a layi ɗaya ne.
Baban Gida ne mai ɗan karan kyau amma bai kai na su.
Hajiyar Gidan da farrah suna zaune a falo suka isa cikin falon.
Ba wanda Sabreen take jin kunya a rayuwarta sama da iyayen Naufal musamman hajiyar shi.
Har kasa da duƙa a gaban ta ce "Ina wuni momy ya gida"
Fuska ɗauke da annuri ta kalle ta ce mata" Lafiya lau Sabreen ya makarantar baki son zuwa
gidan nan bansan abinda aka miki ba"
Ita murmushin tay ta ce "Ba komai momy zan dunga zuwa"
"Yawwa ko kefa ƴar gatan hajia"
Dukkan su suka yi murmushi,momy ta gaida hajia cikin martabawa da mutuntawa.
Inda farrah take nan Sabreen da zauna suna shiri da ita sosai ɗan farrah bata da iyayi da nuna
iyawa da alfahari da gadara shiyasa suke shiru sosai da ita.
Hajia ta kalli Momy ta ce "Wai ina mutan india ne,ya zo ya bamu tsarabar mu "
"Sun fita tare da Alhaji amma yanzu zasu dawo tunda yasan da zuwan ku"
"To allah ya kawo su "
"allah yasa kar nayi dariya" sabreen ke faɗi a zuciyar ta.
Basu wani jimaba sai ga sunan ,Alhaji babban mutum ne kallo ɗaya zaka mishi ka fahimce
hakan ga Annurin fuskar ko da yaushe kamar yana murmushi haka fuskarshi take irin ta hajia.
Da sallam suka iso falon,Shi Naufal ba wanda yaji tashi sallamar dan bala'i irin nashi.
Kan kujerar da Hajia ke zaune a nan Alhaji ya Zauna fuskan nan tashi ɗauke da murmushi
"Sabreen zo nan Alhajin ya kirata.
Cikin jin kunya ta taso kasa da tsugunna,yasa hannu ta ɗago ta ya zaunar da ita kan cinyar shi.
Wani gululun takaici ya kama Naufal "Duk kun lalata yarinya da gata sai abinda ta ke so ake yi
ba dole ta lalace da dinga yiwa mutane fitsara ba,kamar wanan katowar yarinyar zaka zaunar
da ita kan jikin ka "
Duk a zuciyar shi yake wanan bambamin yana wani yatsina fuska kamar wanda ke kallon
ɗanyan kashi.
"Sabreen ya gida ya makaranta?
"Lafiya lau dady"
"Masha allah Sabreen ki dage kinji,yanzu tunda ga yayan ku ya dawo kafin ya fara Aiki zai
ɗinga zuwa har gida yana miki lesson"
Dumm Dumm gaban shi yai mugun faduwa,"shi xai ɗinga yiwa ƴar rainin wayun nan lesson
kuma sanan shi zai bita har gida bama ita zata zo ba" a zuciya yake wanan tunanin dan baya
gardama da dadyn shi.
"Aiki ja wanan ba zai iya da ni ba,nima kuma ba zan iya da bala'in kiliibin shi ba,yanzu ya zanyi"
"Naufal kullum zaka ɗinga zuwa indan ta dawo daga makaranta ka ji"
Maganar da dadyn yayi shi ya katse musu tunanin da kowannan su ke yi a zuci.
A sanyaye ya ce "Toh dady ,yana gama faɗa ya tashi zai wuce rai ɓace,dady yai saurin kiran shi
"Naufal ka fito musu da tsarabar su,indan ka shiga ɗaki"
"To dady ya faɗa fuskar nan duk ta jagwalgwale da ɓacin rai.
Ya dade bai fito ba,har saida suka je daining table suka fara cin abinci sanan ya fito hannun shi
dauke da kaya.
Yana zuwa ita ya fara miƙa mawa ,wani abu ne a baƙar jaka,ita ma kamar yadda ya ɓata rai
haka tayi ta ce"Na godeee"
Ko nuna almar yaji bai yiba balle ya bata amsa.
"Ke baka ji ta ce ta gode ba" Dadyn ya faɗa.
Bai kalla inda take ba ya ce "u are wllcm"
Cikin salon kilibibi.
Dariya ce da zuwa Sabreen duk yadda taso ta shanye kasawa tayi saida tayi ciki-ciki bata so a
gane sai da hau yin murmushi me kama da dariya
Iri ɗaya da abinda yaba ma Sabreen yaba farrah sai momy da hajia kowanne nashi a rufe,har
ya juya sai tafi dady ya kira shi "Ina zaka ba zaka tsaya muci abinci tare ba yaushe rabonka da
zama cikin ƴan uwa ,wai me yasa baka son mutane ne ,kuma har ƴan uwanka"
Bai ce mishi komai ba yaso ya zauna akan kujerar dake fuskantar Sabreen.
Kallon shi take yi tana son yin dariya ganin yake kallon abinci kamar kashi,yana fara cin abincin
Sabreen tai kasa da kanta dan tasan zata iya yin dariya.
Bayan sun kammala cin abincin suka dawo falo.
*ASALIN* *SU*
Maryam sunan hajia na ainihi ƴar asalin kauyen bauchi ne,cikin rashin gata da taso gurin
iyayenta,har suka mata aure,Muh'ad mai taƙama shine babban ɗan ta kuma shi ne mahaifin
Sabreen,sai rabi'u (Alhaji)mahaifin su Naufal.
Muh'ad mahaifin sabreen yana zuciyar naima kuma ya taso yana son karatu duk da tasarar
shekara ɗaya da rabi ne a tsanin shi da Rabi'u amma haka ya hakura da karatun shi dan kanin
nashi yayi,tun yana shekara goma mahaifin su ya rasu,shi ya ɗau dukkan nauyin su ci da sha
sutura da makarantar rabi'u,wanan ne dalilin dayasa Hajia ke mugun son shi.
Bayan rabi'u ya kammala secondry ,yayi iya kuƙarin shi har samu gurbi a ABU zaria ya tafi
,bayan tafiyar muh'd ya cigaba da naiman kuɗi yana kula da kansu kuma yana turawa Rabi'u.
Bayan rabi'u ya kammala karutun digirin shi ya dawo gida,aka fara fafatukar naiman aiki,Cikin
sa'a allah yasa ya samu a garin abuja.
Saboda riƙon alkawari da amana da biyayya irin na Rabi'u yasa ogan shi ya aure mishi ƴar shi
Zainab ƴar ɗaya takk ƴar gata ga mahaifinta masu kuɗin gaske ne.
Bayan Auren Rabi'u ya ƙasa gaya ma ƴan uwan shi yayi aure gashi har matar da samu
ciki,bayan shekara biyar ya lokacin zainab ta haifi Naufal yana d shekara huɗu,Rabi'u ya zo
gida da sha tara na arxiƙi,kuma ya ƙasa gaya musu yayi aure,kwana biyu yayi ya koma abujan.
Bayan tafiyar shi hajia(maryam)ta matsa mishi yayi tunda abubuwa sun daidata gashi yana ta
manyan ta.
Bayan shekara hudu da tafiyar Rabi'u aka kira shi yayan shi zaiyi aure,a lokacin ya yanke
shawarar zuwa da iyalan shi.
Hakan kuwa ta faru ,basu nuna ɓacin ransu ba ko ƙaɗan sai ma farincikin da suka yi ga Naufal
ya girma a lokacin yana da shekara takwas.
Bayan bikin muh'ad Da shekara ɗaya aka haifi Naufal,lokacin Haihuwar Naufal allah yayi wa
mahaifiyarta rasuwa.
Sabreen ta taso a hanun hajia cikin jin dadi,har ta girma,ta fara zuwa makarantar firamari har ta
kai aji shidda.
Rana ɗaya aka wayi gari Muh'd ya rasu ,hajia tayi kuka tayi kuka kamar ranta zai fita dan tana
matuƙar son shi,A lokacin da Rabi'u yaji yayi kuka kamar me dan duk duniya yafi son yayan shi
sama da komai ,a lokacin Sabreen bata da wayau sosai.
Wanan ne dalilin dayasa suke matuƙar son Sabreen musamman Hajia dan son ɗanta ne ya
koma kan sabreen ɗin gashi tana jin tausayin ta.
Bayan rasuwar shi da sati ɗaya Alhaji rabi'u yaso ya ɗauke hajia suka dawo Abuja.
Lokacin basu daɗe ba Naufal ya tafi india karatu.
Da aka kai Sabreen makaranta aka ce primary 3 za'a maidata,taƙi yarda da gyar da zauna a aji
biyar.
Sabreen bata iya turanci ba,tana ji dai,ta tsana kilibaban mutum da mai nuna shi wani ne da son
na iya ta gadara da taƙama.
wanan kenan nan to muje zuwa,kashh shadow tayi kira bari na tafi ma haɗe anjima⛹♀⛹♀.
.
Sir Dboy
[12/9, 1:05 PM] ° D°⭕Y: _ σѕт у яσυρ уρє αυѕα σνєℓѕ
σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/9, 1:07 PM] ° D°⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*
*By*
*fatima* *Batula*
*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*
Page 3
___________________
Ta kai tsawon minti biyar a gurin da Malama Haulat ta barta , tsabar takaici da baƙin ciki, yasa
ta ƙasa komawa cikin motor ,sai da direban ya fito ya mata magana sanan ta koma cikin motor.
Karfe hudu da rabi suka isa Gida,cikin ɓacin rai ta isa falon ,ko sallama bata yiba.
"Kee! ya buga mata tsawa.
Tsayawa chikk tayi bata kuma juyo ba,ganin bata da alamar juyowa yasa ya ƙara faɗin "Wai ke
wacce irin yarinya ce kina ganin mutane ba zaki iya gaida su ba,kuma dan rashin tarbiyya ko
sallama baki yi ba"
Yadda taji maganar yasa ta tabbatar da Naufal ne dan iyayin da taji yana yi,ɓacin ran da take
ciki ya hana da yin dariya.
Juyowa tayi Zaune ya ke akan one siter ta ganshi yasha baƙin glass fuskar nan a dagule kamar
wande ke zaune a cikin bola.
Kamar zata ce mishi wani abu ta fasa,tai wucewar ta zama da sauri.
"Ɗuk ɗady ne zai ja min raini kamar ni za'a ce na zo har gurinta"
Cikin ɓarin rai yayi maganar wanda ɓacin rai har ya samu gurin zama a fuskarshi shiyasa ɓacin
rai ke mishi kyau,tashi yayi yabar gidan gaba ɗaya.
Tana isa ɗakinta ta shige toilet ta daɗe tana watsa ma jikinta ruwan sanyi.
"Ba abinda na ya taɓa min rai ban rama ba,karki yi tunanin zan gyale ki dan kin kai ne ƙarshe
zan miki abinda sai kin zubur da ƙwalla da idanuwan ki,kuma sai kin ce na haifu ni sabreen
muh'd mai taƙama,bana ɗaukar bashi" wasu zafafan hawaye suka biyo kyakykyawar fuskarta.
Tana cikin yin Sallah hajia ta shigo ɗakin ,zama tayi har ta idar.
"Ƴar aljanna lafiya ki kuwa ,ki faɗamin abinda ke damunki zan miki maganin shi komeye shi"
Sabreen bata iya ɓoye ɓacin ranta ba shiyasa hajia ke ganewa.
Kan jikin hajiar ta dawo ta kwantar da kanta,ta ƙaƙalo murmushi ta ce "ba komai hajia ta kin san
ina gaya miki abunda ke damu na,karki damu ba komai"
"Taya ba zan damu ba,dumwarki damuwa take sa ni "
"hajia zan sha ice-cream muje ki sai min"
"Ice cream to yar aljanna muje direba ya kai mu ko"
Tai saurin katsi ta" a'a Yaya Naufal nake son ya kai mu"
Hmm baka san waye Sabreen ba da zaka min tsawa ni nace ka zo gidan mu ko da zaka sauke
fushin ka a kai na ,a zuciyarta ta ke wanan tunanin haɗe da yin murmushin mugunta.
Cikin sigar rarrashi hajiar ta ce "Naufal to shi zai kai mu,karki damu je ki shirya,wai ba alhaji ya
ce yazo yau ya miki karatu ba"
taɓe baki tayi "hm ai dan raini ne ba zuwa zai yiba"
"Bari zan haɗa shi da dady "
Murmushi tayi na jin daɗi ta ce " to ki kira shi bari na chanja kaya" tana faɗa ta tashi ta nufa
gurin kayanta ,ita kuma hajia ta fita falo.
Cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga ta shirya ,rigar ta matuƙar yi mata kyau kuma ta kama
jikinta wanda yasa dukkan shape ɗin ta ya baiya na,pich colour ne rigar da ratsin baki,bata
ɗaura ɗangwalin ba ɗan karamin gyalen kayan ta yashi a kanta,kana iya hango baƙin gashinta
mai santsi,duk da tana da ɗan tsawonta amma tana son dugon takalmi,shi kuwa ta sa ɓaki mai
ɗan karen kyau,bata yi wata kwalliya mai yawa ba,huta sai kwalli da pink ɗin jan baki wanda yai
ma ƙaramin bakin ta kyau.
Cikin yanga da ƙasaita take saukowa daga matattakalar.
Hango shi tayi a zaune cikin ɓarin rai duk da ɓarin ya saba zama a fuskarshi ,amma yanzu kam
kana ganin shi kasan ɓacin ran mai tsanani ne,yai hura hanci yake yi yana wani yamutsa fuska.
Cikin fara'a ta isa fallon ,kallon shi tayi tana murmushin mugunta ta ce "Ya Naufal ina wuni ya
gida ya aiki?
Ko kallon inda take bai yiba,ya miƙe tsaye "Zamu iya tafi?ya faɗa cikin salo da ƙaƙale.
Kasa ɗaurewa tayi saida dariya a zuciyar ta tana faɗin"Bala'i Wai hausa ma sai an mata ƙaƙele
wannan da kai ka kawo yare da ni kuwa bani ba koyan magana"
Hajia ta kalle shi rai a ɓace ta ce"Kai kana jin tana gaida kai wai meyasa kake wa yarinyar nan
haka ne"
Taƙaici kamar yayi kuka,gashi yanzu da yayi wani abu zata gayawa dady shi kuma baya son
ɓacin ran dadyn shi ko kaɗan.
Wani mummunar kallo ya mata ya ce "Me kika ce Sabreen maimaita ban ji ba"
Saida da lumshe idon daya kira sunanta ji tayi kamar ba wanda ya taɓa kiran sunan da
daɗi,sabo sunan ya dawo mata,ydda ya kira har zuciyarta saida ta ji shi,amma saboda hali irin
da Sabreen cewa tayi haɗe da taɓe fuska"Salo sunan ma da turanci za'a faɗa kai dai abunka
yayi yawa"
A zuciyarta tayi wanan mgnr amma a fili cewa tayi" Cewa nayi ina son ganin gari,zaka kai ni duk
inda ka sani"
Bai san lokacin da wani tsadaddan murmushi ya fito ba saida jin haƙurin shi a waje iskar falon
ta duke su.
Ba komai ne ya haifar mishi da wanan tunann ba sai jin mamakin sabreen da ƙarfin hali,ita gani
take ita me wayau ce.
"Laaah ashe ya iya murmushi to ko me yasa yayi ? ohhhon mishi .
Ta tambayi kanta sanan ta ba kanta amsa.
Har ya bar falon ,binshi a baya suka yi ,yayi tunanin a gaba zata zauna sai ya ga kuma ta zauna
a baya.
Sai zubawa hajia shagwaɓa take yi da biyu ganin yana ɗan gutun tsaki yasa ta ƙara yinta da
salo ma.
"Kun lalata yarinya,kun koya mata fitsara" a zuciyarshi yake wanan maganar.
ostrich bakery wanda ke unguwar sarki ya fara kai su,kaya mai yawan gaske ta zaba duk da
biyu tayi hakan dan hajia ta saka Naufal ya ɗauka.
"Washh hajiata ba zan iya kai kayan na n gurin motor ba"
"To daman ai ba ke zaki ɗauka ba Naufal zai ɗauka"
Juyowa yayi ya kalle hajiar.
"Ko ba zaka ɗauka ba ne"
kasa magana yayi dan ɓacin rai bai iya cewa komai ba ya ɗau kayan,har yayi dan nisa Sabreen
ta kira shi "Ƴaya tsaya na duba wani abu"
Tsayawa yayi yana mata wani irin mugun kallo ,wani murmushi yayi na mugunta dan ya ga
yadda zai mata ,ruwan da ke hannun shi ya kalla,a hankali da dubara ya buɗe ruwan yayi
kamar zai sha ya zubar a ƙasan gurin.
Allah sarki Sabreen bata sani ba,kuma dai ita ma bata san ba ko wacce fansa ake ɗauka ba.
Cikin yanga ta tawo habba sai jinta tayi dimmm ta zame ta faɗi har saida ƙafarta tayi ƙara.
"Waiyooo Allah na hajia ta ,ta sake ihuu da karfi.
Da gudu a ruɗe hajiar ta ƙaraso gurinta "Na shigo ukku ƴar aljanna me ya same ki ,gaba