Showing 27001 words to 30000 words out of 57176 words
Chapter 10 - NIDA MALAMATA BOOK COMPLETE BY Fatima Batula.pdf
ma zai iya yin kukan da yayi ,dan shi ne abin kuka ba su ba.
Ganin basu da niyyar daina kukan Dady ya ce"Ya isa haka kuyi hakuri dole daman sai wanan
ranar ta zo."
Kallon Naufal yayi ya ce"Naufal tashi ku tafi"
Gaban shi ya faɗi"Na tashi mu tafi"ya maimaita abinda Dadyn ya faɗa a hankali,shi kanshi zaida
yaji wani iri wai yau zai bar gidan su ya kwana a wani gida daban.
Sabreen tana jin abinda Dady ya faɗa ta ƙara ƙanƙame hajia tana kuka mai tsuma zuciya.
Tashi momy tayi taje da riƙo Sabreen tana san ta rabata da jikin hajia.
"Waiyo hajia Momy dan Allah ,Hajia bazan tafi na barki ba,waiyo hajia ki riƙe ni,momy momy
kiyi hakuri na fasa auran bana so Allah na fasa bana son ya naufal,hajiyata bazan tafi ba...
Duk da yanayin da suke ciki saida suka yi ƴar dariya,musamman Naufal da farrah A ran shi ya
ce"Banza daman haka kike amma kika ce kina son aure n..
"Naufal zo ka jata"
Dady ya katse mishi tunani.
Hajiya ya fara ja dan baya son ya taɓa Sabreen.
"kai ita zaka ja", Dadyn ya taɗa.
Hannun shi yakai kan kafaɗar ta,ya fara janta ,ita kuma momy taja hajia.
"Yawwa kamata ku fita",cewar dadyn
Kuka Sabreen take yi tana ihu "Waiiyoo! wllh Dady na fasa bana so,dan allah ku barni,na
zauna da hajia bana son auren,Yaya Naufal dan allah ka barni bana so waiyooo"
Dariya ta bashi sosai har ya kasa ɗaurewa zaida yayi,ita ma farrah dariya tai tayi.
"Karka sake ta Naufal."
"To Dady."
Har suka fito daga fallon tana kuka,gurin shiga motor ma,saida momy ta turata da ƙarfi tana
shiga aka kulle kofar,hajia bata fito ba tana chan tana rusa kuka an rabata da ƴar aljanna.
shiga motor yayi direba yaja suka fita daga gidan,Su momy suna nan tsaye har motor ta
fita,sanan suka dawo suyi ma hajia sallama su koma gidan su.
Dariya Naufal ya fara yi sosai da sosai wanda bai taɓa yin irinta ba.
Ƙara fashewa da kuka tayi mai sautin gaske.
"ke dare ne ki mana shiru baki son rabuwa da ita kika ce kina son aure."
ys ƙara fashewa da dariyar shi.
Kuka Sabreen ke yi sosai bata kuma kula shi ba har suka isa unguwarsu,wani katafaran gida
ne,wanan kallo ɗaya zaka mishi kasan ankace dala,dan ya fituno da kyau abin zai wanda ya
gani.
Suna isa harabar gidan direban ya tsaida motor,shi ya fara fitowa"Idan kin ga dama ki sauko
idan baki ga dama ba ya maida ke gidan hajia."
Yana faɗa ya shige abinshi yana tafiyar kasaita da izza.
Kamar ta ce direban ya maida ta gurin hajia sai kuma ta fasa ,ta sauko ta bi bayan shi a falon ta
isko shi,tana kuka ta karasa gurin shi ta ce"Idan na koma zance kaika kuro ni,ka ce na dawo."
A fusace ya miƙe har zaiyi wata magana ya fasa tuno halin Sabreen ba abinda ba zata iya
ba,wani mugun kallo ya mata sanan ya juya ya haye sama.
Har lokacin bata daina kuka ba,kallon falon tayi ya mata kyau sosai,kan gujera ta hau,tana ta
kuka har barci ya ɗauke ta.
Daman yasan gidan ya kuma zaɓa ɗakin shi,yana zuwa ya shige saida yayi wanka yayi sallah
sanan ya kwanta,ya daɗe yana tunanin irin zaman da zasu yi da sabreen sanan shi ma barci ya
ɗauke shi.
~~~~~~~~~~~~~
"mtseww!
"Wai ke wa kike ma wanan tsakin tun ɗazun."
Wani mugun kallo tayi mata sanan ta ce"Ban sani ba".
taɓe baki tayi ta cigaba da yin abinda take yi.
Kallon wayarta tayi ta ce"Naufal meke faruwa ne?
ƙanwarta wacce suke zaune a ɗakin ta kalleta a ƙaro na biyu ta ƙara cewa"Ai daman na sani"
"Kin san me,banson iskancin banza."
Tana rufe baki saƙo ta whatssap ya shigo wayarta,kamar ba zata duba ba,dan baƙowar number
ce.
Sai ta duba, a tsorace ta miƙe tsaye haɗe da zaro idanowa,xuciyarta ta fara bugawa da ƙarfin
gaske"Wa.i..y.."
Numfashin ta ya fara sarƙewa dushu-dushe ta fara gani.
"Aunty haulat lafiya mai ke faruwa? a ruɗe take tambayarta,ko kafin ta ƙarasa gurinta ta faɗi
kasa zummama.
"Innalilahi! momy momy Aunty haulat mun shiga ukku.
~~~~~~~~~~~~~
kiran sallar farko a kunnan Sabreen a ruɗe ta fara tambayar kanta "Nayi Sallah jiya?
"Innalilahi ta faɗa da sauri ta miƙe tuno bata yiba,saman ta hau a ruɗe ,kasancewar bata san
wani ɗaki ba ne tashi ta faɗa dakin shi,bata ma lura da yana kwance akan gadon ba tayi toilet
da Sauri.
Jin ƙarar ruwa ya farkar da shi,kunna guluf mai hasken yayi,"waye a baya" ya faɗa a hankali
saukowa yayi,sautin tafiya taji a tsorace ta ce"Waiyo Allah na waye"
"Ke meye ya kawoko ɗaki na?
"Bansan ɗakin ka ba ne"
"Bakin san ɗaki na ba ne".
"eh!
"To fito nima zan shiga ne".
"Waiyo karka shiga ya hakuri dan allah dan allah".
Dariya ta bashi a ranshi ya ce "Kamar wata wacce zan ga wani abu ƙwaila da ita"
Murmushi ya fara yi tuno hali irin na ta,mawuyacin abu ne ta ba mutum hakuri,amma yanzu
harda wani haɗa shi da allah.
"To na baki minti biyar kafin na dawo ki fito"
Yana faɗa ya juya yana murmushi.
Tana jin ya fita ta fito da sauri,ta faɗa ɗayan dakin wanda ba tazara a tsakanin su da juna,tana
shiga ɗakin ta kulle,kallon ɗakin ta tsaya yi,ganin zai shagaltar da ita yasa ta maida hankalinta
akan abinda zata yi.
Yana dawowa yaga bata nan daman yasan ba ganinta zaiyi ba,shiga toilet ɗin yayi ,saida yayi
wankar tsarki sanan ya fito ya gabatar da ibada.
Zaune yake kan sallayar yana hailala da tasbihi wa ubangijinki,tunanin Haulat ya shigo ranshi
zumbur ya miƙe ya fara naiman layinta...
Ringin wayar tayi har ta katse ba'a ɗauka ba,tsoro ya kama shi,tunda yake da Haulat bata taɓa
ƙin ɗaukar wayar shi,cikin hanzari da zaƙuwa ya ƙara kira,nan ma shiru ba'a ɗauka ba,saida yai
kira biyar abinda bai taɓa yiba ,amma shiru ba'a ɗau wayar ba,jefar da wayar yayi akan gado
ransh a ɓace,haɗe da hura hanci.
"Haulat Allah yasa kina lafiya?
"Taya zata kasance cikin lafiya bayan abinda ka mata."
Da kanshi yayi tambayar kuma ya ya ba kanshi amsar da ta ƙara ruɗa shi,yasan bai kyauta ma
Haulat ba,ya kamata ya sanar da ita koma meye,yanzu idan taji a bakin wani fah.
Tashi yayi ya fara safa da marwa a tsakiyar ɗakin,lissafin shi duk ya dagule,kanshi yayi zafi
tunanin halin da masoyiyar shi take ciki yake yi,wanda ya ɗaura laifin akan Sabreen ko kaɗan
baya jin zai iya raga mata kan abinda da mishi,zumbur! kamar wanda aka tsungula ya fito da
sauri,bibbiyu yake taka matalakar dan sauri,har ya iso cikin falon bai kula da mutanan dake ciki
ba,ya fara ƙokarin fita.
"Ango Naufal ina kuma zaka je ka bar amarya ita kaɗai."
Tsayawa chikk yayi sakamakon jin muryar ko ta wacece,a hankali ya juyo dan ƙara tabbatarwa
zaro ido yayi ganin ba ita kaɗai ba..
"Naufal saurin me kake yi,baka kula da mu ba."
Momyn shi ta katse mishi tunanin shi,kallon su yayi,Hajiaya ce ita da Momy da farrah sai
Sabreen ɗin wacce ke manne a jikin Hajia, "Meye kuma ya kawo su da safe haka? taya zasu zo
mana gida a irin wanan lokacin jiya ne fah muka tare", a ranshi yake wanan tambayar,"To meye
wani abun zamu yi waɗan da ba son juna muke yiba",duk a zuciyar shi yake wanan tunanin,bai
san lokacin da ya ƙaraso tsakiyar falon ba,sai jin shi yayi zaune a ƙasa,cikin harɗaɗiyar murya
haɗe ta aro murmushi ya yafawa fuskar shi ya ce"Ina Kwana momy."
Bai tsaya jiran amsarta ba ya juyo da kallon shi ga hajia ya ce"Ina kwana Hajia ya gajiya."
yana kai aya hajia ta ɗauka"Lafiya lau Naufal ka barni da kewa shi ne ko tambayata baka
yiba,au naga kamar ba baka so ganin mu yanzu ba."
Kallonta yayi ,yana tuhumar kanshi akan maganar da ta gayamishi ,a fili ya ce haɗe da ɗan
guntun murmushi, "Ba haka bane hajia,ya kewa?
"Ba sauƙi jiya ban iya barci ba ,da zan iya da nayi kishi da kai"
Gaba ɗayan su sukai dariya banda Sabreen wacce ta murtike fuska.
"yi hakuri Naufal munzo kawo abinci ne da farrah zata kawo to sai hajia ta ce tana son zuwa."
Murmushi yayi ya ce"Ba komai Momy."
"Amma ina kake ƙokarin zuwa?
"Am..amm..da. amman daman zanje gurin hajia ne na samo mata abinci bata ci komai ba."
ya faɗa yana kallon Sabreen ɗin yana mata guntun murmushi.
Charab hajiar ta ce"Hm to na hutar da kai,amma naji daɗi da kake nuna kulawarka akan
Sabreen na gode Naufal Allah ya biyaka da aljannar shi."
"Ba komai Hajia ko kin manta Sabrewn ƴar uwata ce,zan iya yin komai a matsayinta na ƴar
uwata,sanan kuma matata! daidai gurin yji zuciyar shi ta buga ƙara maimaita kalmar yayi
"Matata!
Wani irin kallo Sabreen ta mishi na mamaki,shi ma ɗago kai yayi suka haɗe ido mugun kallo
suka yiwa junan,amma sai suka yi murmushi.
Wani irin daɗi ya mamaye Momy wanda ta kasa ɓoyewa sai yaƙar baki take yi,kamar Ango.
Ita kanta farrah dake gefe murmushi take yi,dan jin daɗin yadda naufal ya aminta da ita cikin
ƙanƙanin lokaci haka.
Wai kuma kunsan farinciki gurin hajia ba sai ance komai ba.
Sun ɗan taɓa fira kaɗan,sanan momy ta kalli hajia ta ce"Hajia to mu tafi ko,yadda zasu sake su
iya cin abincin da kyau."
Kallon momy yayi a ranshi ya ce"Hm wai mu sake kamar wasu masu cin amarshi."
Sabreen naji abinda momy ta ce,idanowan ta sukai jajir kwalla ta shika su famm,cikin murmuyar
kuka ta ce"Hajia yanzu tafiya zaki yi."
Momy ta ce"Kinga idan kuka zaki dunga yi,xata daina zuwa,muma zamu daina zuwa,kina son
gobe ta zo?
ɗaga mata kai tayi alamar eh.
"Toh idan kina so ta zo gobe,kiyi shiru."
"Tohhh! kawai ta faɗa.
Kallonta hajia tayi ita ma hawayen ne a idonta ta ce"Kiyi shiru kinji ga mijinki nan zai tayaki
zama,kuma baga waya ba,sai ki kira ni mu gaisa."
"Ba zaki xo gobe ba."
"zan zo."
A tare suka fita fita har harabar gidan,suna kallo suka shiga motor,Sabreen sai hawaye shaaa
kamar famfo,ko kallon inda take baiyiba ya juyo ɗakin,yana zuwa ya janyo kulolin abinci ya fara
ɓuɗewa,kunon gyaɗa ne sha madara sai waina da miyar ita kanta wainar sai tashin ƙamshi take
yi,miyar ma haka ga nama zaƙo-xaƙo,sai dangalin turawa soyayye da dafaffe wanda ya haɗe da
hanta, sai kuma farfeson kaza,da soyayyan gwai harda lipton,kallon abincin yake yi yana
yamutsa fuska kamar wanda yai arba da ɗanyan kashi.
Kunon gyaɗan da waina ya xuba ya fara ciki,yana cikin ci Sabreen ta shigo,kallon shi ta tsaya
yi.
"Waya ce ka cimin abinci ai ba kai aka kawo mawa ba."
Bai ɗago ba balle ya tanka ta,saida ya gama ci ,tana kallon shi yana hura hanci kamar warin
abincin yake ji.
Yana gamawa ya tashi saida ya fara goge hannunshi da hankey sanan ya tashi har lokacin bai
kalla inda take ba.
"Ina zaka?
A fusace ya juyo gabanta ya ƙaraso dabb da ita har suna jin fitar numfashin juna,kallon ta yayi
ido cikin ido ya"Momy ko Dady,kuyi hakuri dan allah zani gurin wacce nake so ne."
"Toh ban aminci ba."
Dariya ya fashe da ita sosai yana mamaki hali irin na Sabreen,a lokaci ɗaya kuma ya murtike
fuska kamar ba taɓa dariya ba,rikiɗewa yayi ya dawo ainihin Naufal mara dariya ɗan gilibibi da
iyayi da yatsine isa izza mulki.
kallon ta yayi ya ce"me zan miki idan na tsaya?
"Ai.. dan...
"Hm Sabreen dan kin aure ni,da ƙarfi ba ki da ikon juyani,kin gane yana maganar yana ƙarya
harshe cikin iyayi.
Kallon ƙaramin bakin shi Sabreen ke yi,yadda yake fito da maganar take kallo.
Ƙara matsuwa yayi dabb ta ita ƙokarin haɗe bakin su ya fara yi,tureshi Sabreen ta fara ƙokarin
yi,amma ina ta kasa.
"Yadai ba abinda kike so ba kenan."
"Allah ya kyauta ni ba ƴar iska ba ce."
"Ni kuma ɗan iskane,u know what Sabreen?i cant share anything with you,"
"Ni bana jin yaren india."
Haba me Naufal zaiyi dariya ya fashe da ita harda komawa baya ya zauna kan gujera.
Ta ƙule gurin takaici hararshi take yi ,shi baima san tana yiba,saida yayi me isarshi sanan ya
tsaya ,ɗaure fuska yayi ya ce"u are very funny Sabreen."
Ko kaɗan Sabreen bata gane abinda yake faɗa,ko hausar ma ba ko wani lokaci take ganewa
ba.
Fita yayi yabarta a tsaye tana jin hauci.
"Kai Anya banyi kuskure ba,gashi gurin Haulat zaije kuma sai ya gayamata abinda ya faru ni
nace zan aure shi baya so na,waiyo allah na yanzu ya zanyi? ya zanyi???
Naime naime ta fara yi,chan ta hango abinda take naiman wayarta ce.
"To yanzu wa zan kira?
"Dady nace mishi me?
"Na kira Naufal yawwa shi ,to me zanje mishi ya dawo.
Cikin rashin abinda zata faɗa mishi ta kira shi,yana tafiya a cikin motor shi da tunanin yadda zai
fusanci Haulat a ranshi,jaji ringin ɗin waya,baƙowar number ya gani dan bashi da number
ta,kamar kar ya ɗauka sai kuma ya ɗauka,tana jin ya ɗauka tai shiru.
"Hello! waye?
"Ya Naufal ka dawo gida yanzu Dady ya zo yana son ganinka."
"Ohhh no! Am coming" yana faɗa ya katse wayar ya juyo da sauri a zuciyar shi yana tausayawa
kanshi halin da zai shiga,ya kamata a kyaleshi ya sarara amma yaga alamar ba'a da niyyar
barin nashi.
"To ni yanzu idan ya zo me zan ce mishi,ko na ƙara mishi wata ƙaryar ."
"Ah'ah ba zan kara mishi wata ƙaryar ba,gaskiya zan faɗa mishi."
"To idan yaji hauci fah?
"to sai me ba abinda ya isa ya miki"
Murmushi tayi haɗe da juyo kanta"Hm ni ce fah ƴar aljanna ƴar gata kuma shalelen Hajia da
Dady,sai abinda na ce,baka da yarda zaka iya Ya Naufal zan juyoka"
waiyo aka ce raahin sani yafi dare duhu Sabreen kina da ƙuruciya kuma kinyi kuskure.
Tana gaba faɗa ta haye sama tana jin daɗi,wanka tayi ta saka riga da sikit na atamfa shiff-shiff
suka mata kamar dan jikinta aka yi kayan,ko mai bata shafa ba,ta fito falo ta zauna akan
1seater ta kunna tivi tana kallo hankali kwance.
********************
Kwance take akan gadan ta hannuta ɗauke da drip,barci take yi,tun jiya har yanxu bata farka
ba.
Momynta ta kalli ƙanwarta salma ta ce"Kai salma lamarin Haulat yana ban tsoro ,ban taɓa
tunanin akwai namijin da zata shiga wani hali akan shi ba,tun yaushe nake gaya muku,daga kun
ga abinda yake son ya gagareku ,kuje gurin malam gajere zai warware muku komai amma kun
ƙi jira kuke yi saina kama ku na kaiku".
"Ba haka ba ne momy,shi ma yana sonta dan ya sha matsa mata akan ta bashi izini ya turo."
"Yana sonta shi ne zai aura wata ke baki ga hoton ba,yadda suke wa juna kallon soyayya."
"Wllh momy yana sonta bansan yadda aka yiba,kuma ita ma tana da laifi tunda tun lokacin yake
mata mita ya fito taƙi amcewa."
"Ni na kasa gane abinda kike son faɗi,kina nufin wanan zoƙeƙen saurayin ne zai tsaya a mishi
auran dole,bari kiji yanzu ko wacce mace ba'a zaune take ba ,musamman ma shi wanda
kowacce mace ke buri ,to da ƙyalla ido ta ganshi bazata bari ya ƙuɓuce mata ba,amma ita
dayake bata da wayau shashace ta zauna haka ai gashi nan tana ji tana gani an ƙwace mata
shi,ba yadda zata yi."
"Hm momy kenan ai ko ni kinsan ba hakura zanyi ba,balle Aunty Haulat kuma akan abinda tafi
so a duniya ai wallahi zata iya yin komai akan shi,ba zata haƙura ba."
"To da dai yafi mata,ta ɗau mataki,akwai wani sabon malami wanda ƙawata tamin hanyarshi ya
iya aiki,aikin shi kamar yankan wuƙa yake,idan ta tashi sai muje a san yadda za'ayi"
"Yawwa momyn mu shiyasa muke sonki kuma muke alfahari da ke allah yabar mana ke."
Murmushi tayi ya ce"Hm dole na so ku,ban yarda da rashin nasara ba,shiyasa zanyi komai akan
nasararku.....
.
[12/22, 5:26 PM] ° D°⭕Y: _ σѕт у яσυρ уρє αυѕα
σνєℓѕ σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/22, 5:28 PM] ° D°⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*
*By*
*fatima* *Batula*
*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*
Page 12
.............................................................................................
*FALALAR* *KWANCIYA* *DA* *AL* *-* *WALA* .
_Hadisi ya inganta daka *Annabi Sallallahu Alaihi wasallam* yace:_
نمE→* تاب ارهاط تاب يف هراعش كلم ملف ظقيتسي الإ لاق كلملا مهللا: رفغا كدبعل نالف هنإف تاب *Fارهط
...•
_( Wanda ya kwanta da alwala, mala'ika zai kwana acikin mayafinsa bazai gushe ba yana
masa Addu'a yana cewa "Ya Allah ka gafartawa bawanka wane domin ya kwanta yana da tsarki
(alwala)"_
...•
_*Abdullahi bin Mubarak yaruwaitoshi acikin littafinsa "azzuhudu" (64) ta hanyar hasan bin
Zakwaan, Ibnu hibbaan ya fitar dashi acikin saheeh dinsa (1052).*_
...•