Showing 39001 words to 42000 words out of 57176 words

Chapter 14 - NIDA MALAMATA BOOK COMPLETE BY Fatima Batula.pdf

16 Mar 2025

5528

fuskan ta waje kamar yadda suka shigo.

Wata irin rikitattan ihu yayi mai tsoro ta zukatan bayi.
Sauka kaɗan haulat da zuba da gudu momy ta riƙo ta.

Wata dariyar yayi sanan ya ce,"An baku izinin zama."

A Hankali suka juyo suka zauna,cikin tsoro haulat ta ɗauke kanta,sakamakon ganin munin
halittar shi,gaba ɗaya idanuwan shi a waje su je,girman su ya kai girman ƙwai,ga su jajir,haƙura
zakwa-zakwa suma jajir wani ƙazamin miyau ne wawwara ke dilaluwa daga bakin
shi,mummuna ne fiye da tunanin ko,ni kai na ban iya ganin shi ba,sai jaruma bloody ce ta tsaya
ta kalle shi ta siffan ta min yadda yake.

Tun da ya kalle Haulat ya ƙura mata ido harda lasar harshen shi.

"Me kuke so ai mata? ya faɗa cikin wata irin mummunar murya wacce zata iya tsorata dodan
kunne.

Cikin rawar jiki Momy ta ce,"Muna so a haukata ta,sanan kuma ta bar garin gaba ɗaya tayi can
wata uwa duniya."

Razananniyar dariya ya ƙara yi,"Wanan ƙaramin aike a gurin jabarun ƙaranjuuu na saman
dutse."

Saida ya ƙara bashewa da dariya sanan ya ce cikin kausassiyar murya,"kin san sharaɗin farko
kafin a fara aiki,ya kalle haulat ya lace baki,ƙaranjuuu yana vukatar ki,ya nuna haulat da
munanan hannuwan shi kamar na kutare,saida gaban ta yai mummunan faɗuwa a razane ta
kalli momy.
Cikin ihuuu ya ce,"Ba'a ma ƙaranjuuu musu duka ce dukk wanda ya tako nan zai yabi umarnin
ƙaranjuuu,kuna ɓata ma ƙaranjuuu lokaci ."

"Na shiga ukku yanzu wanan mummunan kazamin zai kwanta da ni."

Idanuwan ta har sun ciki taff da kwalla,har lokacin idon ta yana kan momy

Cikin raɗa momy ta ce mata,"Minti nawa ne ki ɗaure kawai kar ran ƙaranjuu ya ɓace ya fasa
aikin kuma ya hukunta mu." tana gaba faɗa ta bar ɗakin kamar yadda ta shigo da baya-da baya.

Waiyo ni tirrrr da irin wanan ƙazamar rawuyar ya allah ka kare mu ka tsare imanin mu ba mu da
wayau ba mu da dubara ya allah.

Ko da momy ta koma ɗakin ita ma haulat ta fito cike da ɓacin rai.

Ita ma momyn kwanciya yayi da ita sanan ya basu umarnin wuce wa...

.
[12/23, 2:17 PM] �° � D°�⭕Y: _ �σѕт у �яσυρ � � �уρє �αυѕα
�σνєℓѕ σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/23, 2:19 PM] �° � D°�⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*


*By*
*fatima* *Batula*

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*
Page 15
..........................................

Addu'ar Saduwa Da Iyali:
ِ
مْسِب ِهللا َّمُهّللا اَنْبِّنَج ،َناَطْيَّشلا ِبِّنَجَو َناَطْيَّشلا اَم .اَنَتْقَزَر
Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana.

Da sunan Allah. Ya Allah! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan
daga abin da Ka azurta mu da shi.

__________________

Kallon Haulat Momy tayi sanan ta maida hankalin ta gurin tuƙi ta ce,"To baga shi ba mun wuce
gurin minti nawa ne?yanzu wa yasan munyi ,ko shi bai sani ba tunda umarnin ƙanjuung
ne,kuma yanzu zaki ga aiki cikin gaggawa."

Duk yadda Momy ta ke ba Haulat baki abin yaƙi dan jikin ta ya mutu,ranta bai so ba,ta so ta
hakura amma tsoran abinda zai yi musu idan suka ƙi yarda yasa ta amce amma har ranta ta so
hakura.

~~~~~~~~~~~~~
Kiran Sallar farko Sabreen ta miƙe,haɗe da addu'a a bakin ta,sanan ta dirgo daga kan gadon
bayi ta shiga ta ɗauro al-wala sanan ta fito,har lokacin yana kwance yana sharar barci abin
shi,kusa da shi ta matsa daff hannunta saka a kan shi tana shafa kwantacciyar zumar shi,a
hankali kamar mai raɗa ta ce,"Miji na!ka tashi lokacin sallah."
Kamar daga sama yake jin muryarta cikin kunnan shi,a hankali ya fara buɗe ido,har ya ware su
kan fuskarta idanuwan suka sauka,sun daɗe suna kallon s
juna,har wani lumshe ido yake yi,ta shi tayi zubur tabar inda ya ke.

"Ka tashi kar a tada sallah ka rasa jam'i."

Lumshe ido kawai yake yi,yana son macce mai riƙon addini tana ɗaya daga cikin ra'ayin shi.

Sallaya ta shimfiɗa ta tada iƙama raka'atanin fijjir zata yi,yana kallon ta birge shi ta ƙara yi,dan
yasan ba'a tada sallah ba nafila ta ke yi,ganin ta fara yi yasa ya tashi ya shiga bayin,saida yayi
kwankan tsarki kamar yadda ya saba yi ko wacce safiya.

Lokacin da ya fito da idar tana zaune akan sallayar yana kallon bakin ta yasan tasbihi ta ke yi
,bai ɗau lokaci gurin kallon ta ba,dan karya rasa sallah kamar yadda ta faɗa mishi,farar jallabiya
ya saka ya ɗaura hula akan shi sanan ya fice.

Bayan sun idar da sallar saida ya zauna jin huɗuba,abinda bai taɓa yiba kenan tun dawowar shi
daga india,ya rage abubuwa da yawa, a rayuwar shi wanda da ba hakan ya ke ba.

Tun yana falo ya fara jin sautin karatun al-qur'ani yana tashi,mamaki ya gama shi jin muryar
sabreen,kasa yarda yayi har saida ya shiga ɗakin ya ganta tana karantawa,zama yayi yana
sauraran yadda ta ke karantun cikin natsuwa kamar wata balarabiya.

"Kai daman yarinyar nan ta iya karatun haka mai daɗin gaske,to a ina ta koya?,a garin su,tun
tana shekara tara dady ya gayamishi ta sauke al-qur'ani kuma tun a lokacin tana da hadda izufi
goma,amma ban taɓa jin tana yi ba? to a gaban ka zata yi,yadda ta ke da rawar kai da ƙiriniya
ba zaka ɗauka haka ta ke da ilimi ba."
Duk shi da zuciyar shi su ke wanan zancen ya tambayi kan shi sanan kuma yaba kanshi amsa.

Ya daɗe yana sauraran zazzaƙar muryarta,wanda bai san lokacin da barci ɓarayo ya ɗauke shi
ba.

Saida ta haɗa izufi biyar sanan ta rufe al-qurnin ta yi addu'o'in naiman tsari kamar yadda addinin
ya zo mana da su sanan ta tashi ,ganin yayi barci yasa ta fita a ɗakin ,ɗakin ta,ta wuce wanka
tayi dogowar riga ita ce kayan da tafi so a rayuwarta,ta atamfa da saka orange colour da ɗan
ratsin brown sai fari,kayan sun mata kyau ainun ɗauren gwaggwaro tayi ganin kicin zata shiga
yasa ba tai komai a fuskarta.

Karin kumallo ta haɗa musu kunon gyaɗa sai soyayyan danganin turawa sai ferfesu hanta,sai ta
soya indomi da kwai da sayayyan kwan sai lipton.

Bayan ta haɗa komai sanan ta koma ɗakinta,ta ƙara yin wani wankan dugowar riga ta ƙara saka
wa,ƙirar dubai pink ne kalar rigari sai akai adon rigar da blue ɗin stone,rigar ba irin me kama jiki
ba ce,amma duk da haka ta amshi jikin ta kuma kirarta ta baiya na,ɗan ƙaramin gyalen rigar ta
yafa sanan ta feshe jikin ta da turaren da shi ne turaren da ta saba saka wa,light makeup tayi
sai plat shoe kalar blue,tayi kyau ainun.

Safa da marwa yake yi a cikin bedroom ɗin shi ,"Me ya kamata nayi? Savreen zaɓin iyaye na
ce,kuma bata da matsala ko kaɗan nabi umarnin mahaifana na zauna da mata ta,to amma ba
ra'ayina bace,meye matslar hakan zan iya rayuwa da ita,inah da kamar wuya ita Haulat fa? ba
da aure ta ke so na ba,na ƙyale ta kawai,a'a taya bayan ina son ta,ita ma tana so na,soyayyar
ƙarya tunda ba auran ka ta ke son yi ba."

da ɗan ƙarfe yake maganar yana girgisa kai,"Taya? ba zan iya rayuwa da ita ba,to ya zanyi."

Marar shi tai wani irin murɗawa dafe ta yayi ,ya dawo ya zauna,"Ina bukatar macce,wata zuciyar
ta ce mishi,"To ai kana da ita halal ɗin ka ce,ba zaka sha wahala gurin shawo kan ta ba."

"Zata raina ni."

Wata zuciyar ta ce mishi,"Wani raini mutuni na sai girman ka da zata ƙara gani,kayi tunani mai

kyau."

"Assalamu alaika!

Bai tsaya tantance muryar ta ba ya amsa sallamar.

ƙarasowa ciki tayi saida ya lumshe ido dan wani irin asirtaccen ƙamshi da ya doki hancin shi,a
hankali ya buɗe idannuwan shi ya sauke su akan ta,wani irin baƙon yanayi ya siyar shi zuciyar
shi.

Ita kuwa ganin hakan yasa ta ƙara faɗaɗa fara'arta harda fari da fararan idanuwan tayi,ƙara
takowa tayi daff da inda yake zaune ,ta duƙa cikin wata irin muryar ta ce," Ka tashi lafiya? ya
gajiya?

Har lokacin bai ɗauke idanuwan shi a kan ta ba,wani irin abu zuciyar shi ke mishi.

jin yayi shiru yssa da ɗago kai wani murmushin ta ƙara sakar mishi,bai san lokacin daya maida
mata martani ba.

"Tana gama kwarin kumallo ka sauko mu ci."

Ɗaga mata kai kawai yayi,ta tashi ta fara gyara ɗakin har lokacin yana nan ya kafe ta da ido,duk
inda ta je binta da ido yake yi.

"Kayi wanka ne?

"A'a." ya faɗa a taƙai ce.

"Ba zaka yi yanzu ba ne."

"Zanyi."

"To ka tashi dan Dady ya kira ni wai muje yana naiman mu."

Tana rufe baki ya tashi,gyara gadon tayi sanan ta fita.

Bayan ya fito daga bayin yaji wani irin ƙamahi wanda duk lokacin daya ji shi yakan ji wani iri a
ranshi.

Wanan shi ne sirran turare Naufal hatta so yana tsufa komai yana tsofa kuma yana gundura
amma turare baya tsofa baya gundura kullum ka ji ƙamshin shi sabo ya ke zuwa kamar baka
taba ji ba.

Kallon ɗakin yayi tsaf komai a kimtse yadda yake ganin sabreen da sakuwa bai taɓa tunanin
zata iya aiki ba,yana son tsafta a rayuwar shi.

Tuno zasu je gida yasa ya saka shadda blue tasha aikin sama ,ta mishi kyau ainun da hula ita
ma blue takalmi blue saida ya gyara fuskar shi sosai da kayan kwalliyar maza san ya feshe jikin
shi da turarruka ma su ƙamahin gaske,zai yanzu ya tuno da wayar shi naiman ta yayi bai
gane,bai damu ba dan yasan sabreen zata san inda ta ke tunda ita ke gyara ɗakin.
ƙasa ya sauko tun daga kan matattakalar ya hango ta,har ya iso cikin falon idan shi yana kan ta.

Jin ƙamshin turaran shi yasa ta waigo haɗa ido suka yi ,ta sakar mishi wani amintaccen
murmushi shi ma sakar mata yayi.

"yawwa muyi sauri kar ya gaji da jiran mu."

Bai ce mata komai ba,gurin abincin ya wuce ya ja kujera ya zauna,ita ta zuba mishi gunun
gyaɗa ta zuba mishi har saida ta kusa shika cup ɗin dan tasan yana son gunun gyaɗa sosai.

"Sabreen!

Saida ta ɗago ta kalle shi sanan ta ce,"Na'am miji na!

"Kin dafa lipton?

"Eh gashi nan shi zaka sha?

"Eh plss ki matsamin lemon tsami a ciki."

"Baka da matsala."

Kicin ɗin ta koma ta matsu ruwan sanan ta dawo,ta haɗa mishi da lipton ɗin.

"gashi sai me zaka ci?

Dan galin turawa da kwai su kama kaɗan ya iya ci.

"Sabreen ina waya ta?

"Wayarka tana ɗaki."

"Ki ɗauko min ban ganta ba."

Tashi kawai tayi ta dufi ɗakin nashi inda ta ajiye nan ta ɗauko,kunna wayar ta,pic ɗin shi ne

wanda ya ɗauka a india a gaban wayar saida ta kalli pic ɗin sosai sannan ta taɓe vaki,"Ko kyau
ina farin namji ya ga kyau kamar wani macce,dariya tayi ta ƙara cewa,"Uban yan iyayi zaka ga
aikin Sabreen lokacin da ka ji ka manta wata haulat a rayuwar ka."

Number Haulat ɗin ta shiga naima,"My dear", ta ga an rubutu blocking ɗin number tayi.

Tai murmushin mugun ta sanan ta ce,"Hm malama ta nasan ke wacece,amma ke baki san ko ni
wacce ba,ba taƙamar yana son ki ba idan ya manta da ke zanga tsiyar da zaki iya yi."

A falon ta same shi,miƙa mishi wayar tayi,"Gashi!.

Amsa kawai yayi,"Muje ko."

"Eh.

Kamar wasu masoyan gaskiya haka suka jeru sun yi kyau gashi kayan su iri ɗaya.

~~~~~~~~~~~~~

Tun a hanya Haulat ke kiran number shi wayar a kashe kamar tayi kuka.

"Momy tun jiya wayar shi a kashe ya zanyi momy?

"Ki kwantar da hankalin ki,ai na daɗe ina gaya miki kaidin mata da yawa,halan ma duk ita
ce,amma yanzu za'ayi maganin ta dan uban ta shege idan ta fara bin bola sai mu ka tsiyar
abun."

Duk yadda Momy ke kokarin kwantar mata da hankali ta ƙasa,dan hankalin ta ya kasa natsuwa
duk wani iri ta ke ji a ranta,wanda bata san ko meye ba.

~~~~~~~~~~~~~

Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gidan su Dady,cikin natsuwa da sallama a bakin su ,su ka isa
cikin falon.

Suna isa dady ya taso da kan shi ya tarbo Sabreen riƙo hannun ta yayi su ka dawo inda ya ke
zaune kan cinyar shi ya zaunar da ita,ba yau ba ne ranar farko da dady ya taɓa zaunar da ita
kan cinyar shi ba,amma ba ta taɓa jin kunya irin na yau ba,kasa gaida shi tayi dan kunya.

"Sabreen ya kike? ina fatan komai lafiya,idan yana miki wani abu da baki so ki gaya min karki ji
komai,kinji Sabreen."

Saida ta ɗago kai ta kalle shi,shi ma kallon ta yayi yana son jin amsar da zata gayawa dady.

Ƙasa tayi da kan ta,"Ba komai dady."

"Kin tabbatar."

"Eh!

Ajiyar zuciya ya sauke sanan ya ce,"Masha allah komai daɗi,haka ne ke,kallon Naufal dady
yayi,ƙasa naufal ɗin yayi da kai yana shirin gaida shi ya tari hanzarin shi.

"Naufal ka haifu,Lallai ka nuna min kai ɗa ne,na gari mai tarbiyar,naji daɗi Naufal na gode ma
ka,da ka riƙe min Sabreen da kyau allah ya biya ka na god...

"Dadyn dan allah ka daina godiya,ni ya kamata nayi godiyae."

Farinciki da jin daɗi ya ƙara mamaye dady,ƙarara fuskar shi ta nuna irin farincikin da yake ciki.

Duk wanan abun da ake yi Momy da Farrah suna zaune a ɗakin.

"Nima zan ma godiya Naufal ka cika min burina,Jibe insha allahu za ku tafi honeymoon kasar
turkey..

.
[12/23, 2:19 PM] �° � D°�⭕Y: _ �σѕт у �яσυρ � � �уρє �αυѕα
�σνєℓѕ σσк нαтѕαρρ 08064400100_
[12/23, 2:22 PM] �° � D°�⭕Y: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*


*By*
*fatima* *Batula*

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

Page 16
_________________________

مالسلا_* مكيلع ةمحرو الله اكربو *_هت
مسب*_ الله نمحرلا _*ميحرلا

_*Sayyiduna Aliyu yace; Manzon Allaah(ﷺ)* *yace min; KA RI'KA (ADDU'A KA NA) CEWA;
{YA ALLAAH KA SHIRYENI, KUMA KA DAIDAITA NI (A KAN HALAYEN 'KWARAI.}*_
°

```[Sahihu Muslim;2725]```
~~
_Muma sai mu dage da yin wannan addu'ar neman shirya da kuma hali na kwarai. Allaahu
a'alam._

```Allah ta'ala yasa mudace```

ﻚﻧﺎﺤﺒﺳ*_ ﻢﻬﻠﻟﺍ ,ﻙﺪﻤﺤﺑﻭ ﺪﻬﺷﺃ ﻥﺃ ﻻ ﻪﻟﺇ ﻻﺇ ،ﺖﻧﺃ ﻙﺮﻔﻐﺘﺳﺃ ﺏﻮﺗﺃﻭ _*​​.ﻚﻴﻟﺇ

........................................................................

Gaba ɗaya jikin Naufal yayi sanyi tunanin halin da zuciyar shi ta ke ciki yake yi.

Ganin yayi shiru yasa Dady ya ce mishi, "Naufal ko ƙasar ce ba ka son zuwa?

Murmushi yayi sanan ya ce,"A'a ina so sai dai ban san ko Sabreen ba."

Kallon Sabreen Dady yayi wacce har yanzu tana kan cinyar shi,cikin murmuahi mai ɗauke da
farincike dady ya ce,"Sabreen ba ki son zuwa ƙasar ne?

"Ina so."

Ai nasan ba zaki ƙi ba my Sabreen."

Haba Alhaji ka barsu mu gaisa mana,tun zuwan ta ka janyo ta jikin ka,ka hana ta zuwa guri
na,Sabreen ta so kin ji."

Dariya dadyn yayi ya ce,"ba gwara ke ba kuna haɗuwa ni fa tun bikin sai yau ba abin ki ce ta
zauna a guri na ba ne."

"Ah...Momyn zata yi magana ya katse ta.

"Sabreen ta shi ki je gurin momy ko."

A kunyace ta miƙe ta isa inda momyn ta ke,jikin jin kunya ta gaida ita.

Bayan zun gaisa ta koma inda farrah ta,cikin raɗa ta ce mata,"Oh su Aunty Sabreen manya,to
ki tabbatar kin dawo min da baby a cikin ki." Cikin dariya da zolaya tayi maganar.

Muntsinin ta Sabreen tayi har saida tayi yar ƙara sanan ta gyale ta,taja bikin ta tai shiru kamar
ruwa ya ci ta.

Dady ya ce,"Sai kun dawo ne za'a yi maganar makarantar Sabreen ko kuwa,"ya faɗa yana

kallon Naufal.

"Eh a bari mu dawo kamar zai fi,amma yadda ka gani dai."

Sai da Dady ya ɗan murmusa sanan ya ce,"Naufal kai fa mijin ta ne,ka fi ni iko a kan ta yadda
ka ce ɗin hakan za'a yi."

Fira sosai suka yi harda Naufal ɗin dan tunda su ka zo basu fita ko ina ba har Dady ,sai lokacin
sallah su fita su dawo har la'asar sanan suka fito,sai sun biya gurin hajia kafin su wuce.

Kafin su tafi saida Momy ta bata magangunan mata kala-kala tun daga zamfara da sokoto ta
saka aka siyo mata,ta kuma ce mata kar ta yi amfani da su sai sun je honeymoon sanan ta sha.

~~~~~~~~~~~~~

"Kin san meye honeymoon kuwa? bai kalle ta ba yayi maganar.

Saida ta kalle shi sanan ta ce,"Eh ba shi ne mata da miji ke zuwa wata ƙasa ba,cin amarci."

"Shi fa zamu je."wanan ƙaran ya kalle ta.

"Eh ko baka so ne,ni fa matarka ce ta sunna."

Ta taɓo mishi idan yake mishi kaikayi,zuciyar shi ta fara dan bugawa zuciyar shi ta mishi
ce,"Tsoran me kake ji Naufal wanan ne gaskiyar lamari ita matar ka ce ta sunnah."

Da sauri ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login