Showing 36001 words to 39000 words out of 47518 words

Chapter 13 - HALAL VEER Book Complete end by Chuchu .pdf

06 Jul 2025

1311

shirya ma abunba so i bought the gift in a rush I just wish you like it"..

Bude box din tayi finally inda taci karo da car key na Maserati "
Hannunta ta dora kan bakinta tace how do you know my favorite car ,
Omg thank you very much abidin best gift danayi receiving so far ,

I really really appreciate thank you"
Murmushi ya kumayi tareda jin dadin ta yaba da kyautar nasa tun kannta gani "_

The white maserati look stunning "
Muryan adeel ya jawo hankalinsu gareshi"
Thank you very much little man yakarasa maganan tareda masa dukan wasa a arm dinsa
"mungode da sabon car din da kasiya mana"

Nasiyama aunt dina dai abidin yayi saurin gyara masa cikin wasa "

Guri adeel yasamu yazauna kusa da ita yace madam kinjifa mai kanin nan naki yake cewa wai
motankine ke kadai"

Murmushin da bai kai ciki ba kawai ta bashi kafun tace abidin muje naga new car dinnawa "
Abidin ne yafara fita kafun ta bishi a baya"
Bai maganaba kuma bayyi kokarin binsuba"

*************************
Washe gari da safe tana shirin zuwa gida domin rananne ranar liyafan da su abba suka hada
mata '
Hayaniya taji a harabar gidan nasu wanda kaman kar ta fita amma sai ta fita domin ganin mai
yake wakana cikin gidan nasu tunda su basuda geji ga jamaar gidan in tasu ta tashi kaji
hayaniyarsu"

Mai babban daki tagani zaune a gurin shan iskan su na sarauta a farfajiyan gidan nasu inda
gefenta kuma kuyanguntane guda biyu,batayi mamakin rashin shiganta tareda birkin da tayiba
dan yanzu wannan jamaar gida sun daina bata mamaki ,

Karasawa tayi cikin nutsuwa tareda zama daga gefe ta kwashi gaisuwa ,
Fadada faraa mai babban daki tayi tareda amsata inda tace "ina kokarin sawa ashiga ciki a miki
iso bayan an gama hada miki gurin zama kuwa ashema kinji mu".
Alamu tayima wasu bayi tace kuzo ku taimakawa gimbiya ta zauna akan kujeran alfarma ,
Itadai takasa cewa komai sai gyara gyalen da ta yafo kan ta fito take '
Algaita taji anfara busawa daga bakin gate dinsu irin wadda akanyi a gidan lokacin farin ciki
then gradually sautin yana nufota ,
Kuyangune gaba dauke da wata kwarya sai bayansu kuma masu wannan busan ,
Gabanta aka aje kwaryan inda aka umarceta da ta wanke hannunta ciki,
Batayi musuba ta saka hannu cikin ruwan da yayi mata kama dana lalle sannan wani kamshi na
daban ke tashi a cikinsa ,
Bayan ta wanke hannunne aka sake umarta da ta saka kafafunta ,
Kamar yadda aka bukata din haka tayi batareda tayi gardama ba"

Bayan sun gama ne sukafita da abun inda nan mai babban daki ta umarci kowa da ya fita ya

basu guri kana tasa nuayma ta dawo inda take a zaune "
Cikeda faraarta tace congratulations ina taya gimbiya da yarima farin ciki samun rabo a tsakani
wanda da fari nayi tunanin kuna boye mana ne then da result kuma ya fito na tabbatar da
bakusan da shiba domin cikin wata dayane da sati daya ,
Kuma sai kinyi hakuri da yanayin gidan sabida nasan zakiyi tunanin yarda aka miki katsalandan
kan personal life dinki amma wannan ba personal bane a cikin gidannan domin hatta mai
martaba baida burin da ya wuce ya ga jikan sa daga gurin yarima adeel "
Yanzu tsarin cin abincinki ma zai dawo hannuna sabida kinga abunka da farko sai kuciyo
abunda zaizo not healthy for the unborn child at all,
Allah ya miki albarka ,da haka tamata sallama inda hajiya nuayma ta kasa tashi daga inda take
zaune ,
Wani kululun bakin ciki da wasu zafafan hawaye suka fara mata gudu a fuska,
Ciki!!
Ciki!!!?
Nashiga uku ni nuayma ,cikifa ta fada a fili then kuma procedure din da akabi dan sanin tana da
cikin yakara dawo mata take taji wata sabowar tsanar adeel da tsanar gidansu da aladarsu ya
darsar mata .

Koda ta shiga daki wayarta ta tarar tana kara ,
Da hanzari ta dauka ganin sunan ummi na yawo kan screen din ,
Saita kanta tayi gudun kar ummi din ta gane  wani abu na damunta ,
DA sallama ta amsa wayan inda ta tsikayi muryan ummi da alamun damuwa tace "ayma mai ya
samu wayankine tun dazu ake ta kira ,
Na kira
Abbanki ma nusayr ma sannan ibi ma yakira amma shiru lapia dai ko?
Munjiki shiru "

Share hawayen da suka zubar mata tayi tanajin ina ma zata iya sharing damuwanta da
mahaifiyar tata amma ina ta janye kudirinta na fada musu tukunna sai ta zubar da wannan cikin
domin babu mai sakata ta haifeshi, ba dai jikan soyayya ba to zata zubar dashi inyaso mutanen
gidan sa saka ya saketa da hujja ba sai ta bama kanta wata wahalaba "
!!Ummi bacci ya dan daukeni walh kuma wayan yana silent shiyasa tashina kenan amma
yanzunnan zan taho hope ummi kin aje mun favorite dambun accan da namiki magana jiya "
Ta tsinci kanta da fada".

Daga daya bangaren ummi tayi dariya dan ta fahimta sarai nuaymanta takusa bata jika dan
haka tunda ta fara maganar dambun accan tashiga kasuwa da kanta domin hado kayan hadi"
"Kedai sai kinzo har sai kin gaji da dambun acca "
Tabata amsa "

Hanging wayanta keda wuya taji anyi hugging dinta ta baya then kuma kaman wata mota ya
juyo da ita tareda mata kiss a goshi ,

Cikeda murna yace "thank you very much sweet heart
Nayi matukar farin ciki da labarin da na iske cikin gidan nan, that's the best gift i could ever ask
of you "
Naso na miki babban surprise na graduation Dinki amma wannan labarin dana iske ya ruguza
mun komai ,i dont even know what to give you "
Hannunsa ya saka tareda shafa cikinta cikeda farin ciki ya kuma cewa thank you babe "

Yana kokarin sake taba cikin ta turesa wanda sai a lokacinne ya kula da yanayinta.

C

hu chu.

Halal veer❤
45
Cikeda rudani ya kalleta yana kada kai yace "nuayma no"
Please no"_
Kar ki min haka,nasani i did you bad amma babu ruwan abunda ke cikinki dan Allah kar laipina
ya shafi babyn mu"

Wani side smirk tayi tace aw yau kuma sabida abunda kakeso for a long time a jikina ya
bayyana shine zaka na wani nuna farin cikinka desperately?

Tsk tsk little prince kayi murna da farin ciki a banza dan haka shawara daya zan baka ba biyu
ba shine ka ma yi kamar bakaji cewa inada cikiba ,
Kai ba kai kadai ba har wadanda suka mun katsalandan a rayuwa yakamata su sa a ransu
cewa nuayma batazo da ciki gidannan ba domin wannan ciki da kake gani sunansa zubabbe "

Wani zaro idanu yayi lokacin da tafadi hakan inda itakuma ta daga masa gira daya tareda sake
fadin "yes zubabbe domin am aborting this child,
Idan na haifa jininkama sunana yar iska kenan"
Kai dan Allah a tunaninka farin ciki zanyi sabida ina dauke da cikinka?
Gangan ma kenan"

Hannunta tasaka guda daya tana tapping kirjinsa tace "keep on dreaming spark "
Keep on dreaming "

Jakanta ta dauka har ta kai bakin kofa ta juyo tace oopz na manta zanje gida duk da i told you
amma wai kasake sani kar na fita malaiku suyita tsine mun "
Da haka ta sakai tafita tareda barinshi kaman dolo a gurin
Lokaci daya kuma abunda ta fada suka fara dawo masa ,kada kansa yayi cikeda rudewa yace
no she can't do this to me , bai masan unknown hawaye sun fara fitar masaba ,
Bai kara gigicewaba sai da yaji karar fitar motarta ,

Car key dinsa ya fincika tareda fita da gudu gudu dan take mata baya domin gani yake idan ta
fita zataje ta cire masa cikinsa ne wanda idan duka duniya zata hadu bazai yarda ba "
Yayi saa kuwa yana fita ya hango ta tana hawa babban titi ,binta ya farayi abaya wanda saida
yazamana mota biyu ke a tsakaninsu amma yanayin gudun da takeyi shine abunda yake kara
bashi tsoro ."

..........tunda ta hau kan babban titi ta taka kan motan amma abun mamaki motan yafara mata
wasu funny abubuwa wanda ta kasa gane kansu ,
Yes funny abubuwa domin a iya shekarun da tayi tana tukin mota tasan zaiyi wuya mota ta bata
kashi saidai in wani ikon Allah,

Gani tayi funny thing yana kokarin zama gaskiya so a take tafara kokarin taka burki dan tayi duk
yarda zatayi motan yayi slowing down yaki and wani abun mamaki shine burkin motar ya bace ,
Tirkashi ita dai tasan tana hawa maserati din ummi kuma lapia lau akwai burki to whats wrong
with this ?
Motar dake gabanta taga ta nufar ma haikan da nakin dan haka ta kama sitiyarin motar domin
kaucewa motar wanda hakan yayi dai dai da kwace mata da motar tayi tareda yin kiss da wata
katuwar katangar makaranta"
A take balloon ya fito amma a banza dan tariga ta bugi kanta da karfi inda da taimakon glass
din motan da ya fallatsa cikin motan wanda ya haifar mata da zubar jini"

Kaman a marfarki taji ihunsa inda a take kuma komai ya koma mata blank and black..

*****************************************
Sarkin yaki ka tabbatar wannan yaron naka da ka kawo yayi aikinsa yarda ya kamata"?

Washe baki mutumin da aka kira da sarkin yaki yayi tareda kamo hannun yaron nasa da aka
ambata yace "ranki shidade na yarda da aikin zaki dari bisa dari domin ba yau yafara mun
aikiba daga kisa zuwa kan duk wani kazamin aiki dan haka kar kiji wani wai ko dar aikinki
kaman anyi angamane"
Juyowa tayi daga bayan da ta basu tace yayi kyau zan tura maka kudi a account dinka sai ka
sallameshi sannan kasani wannan abun yazama daga ni sai kai sai shi wannan zakin ,
Kar ka kuskura naji sunan gwaggo amarya ya fita abakin kowa sabida idan hakan yafaru zaka
mutune kuma mutuwa mai tsanananin radadi"

Alamun zip yayi da hanunsa a bakinsa inda itakuma ta kada kai tareda fadin zaka iya tafiya "
Suna kokarin fita Abba yana shigowa kallon kallo sukabi da juna kafun suka matsa masa
yashigo.
Kallon mahaifiyar tasa yayi yace mai wannan tsohon shuumin kuma yake a nan,
Hade rai tayi dan kar ya fahimci wani abu tace kace kome zanyi yanzu sai nafada maka tunda
kaine ubana to taimakon da muke ma marayu duk shekara yazo mu tattauna akai"

Kada kai kawai yayi dan yafi kowa sanin halinta sannan a rayuwarsa babu abunda ya tsana
kaman ta jefa kanta kan yakin neman mulkin gidan wanda yasan dole sai kabi ta kazamar
hanya bugu da kari sayeed din da take ma wanann fighting din ya bata rayuwarsa da shaye
shaye wanda yake ganin shine hanyar bullewarsa " Allah ya kyauta kawai ya iyacewa kafun ya fita a gidan inda ita kuma tabishi da tsaki tareda
kiransa da sallamamme"

..tunda ta tsinci labarin cikin nuayma a yau din hankalinta yayi mutukar tashi ,ta tsorata dan
wannan karanne bokanta yataba samun sabani a aiki dan haka tuni tashiga rudani,
Sake sake tafara yi aranta na yarda zata zubar da cikin dan karyazo duniya ,tana tsaka da
wannan tunanine babbar baiwarta talle ta shigo tareda kara bata labarin da yafi komai mata
daci wato na zuwan mai babban daki gidan adeel domin tayasu murna"

Karyar da kai talle tayi da ta fahimci uwar dakin nata na cikin rudani tace "ranki shidade ga
shawara ,maizai hana anemo sarkin yaki yanzu amiki aiki kaman yankan wuka kinsan ba yau
aka fara ba.

Zama gwaggo amarya ta dawo tayi kusa da talle tace talle kina nufin me kenan kinsan shifa
sarkin yaki abunda aiki dashi yake nufi"
"Kwarai kuwa talle ta bata amsa "yana nufin mutum zai mutu kuma ranki shidade a ganina
gwanda nuayma ta mutu da mu zubar mata da ciki sabida idan muka zubar zata iya samun
wanine amma idan muka kashetafa "?

Sai tai ciki akiyama "gwaggo amarya ta karasa tareda saka wata bakar dariya "
"Maza je ki kira mun sarkin yaki"

Mintuna da basu wuce biyar ba saiga talle da sarkin yaki ,batayi wata boye boye ba wajen
shaida masa bukatarta inda shi kuma ya bata tabbacin ai aiki kaman anyi an gamane in
nuayma bata mutu yauba to zata mutu duk ranar da ta hau motar da yarima abidin yabata a
matsayin kyauta"
Yana fita yakira yaron dake masa irin wadannan kazaman ayyukan ,
Babu tsoro ko shakka zaki yay shigar bayi tareda sajewa da mutanen mai babban daki  inda su
sunanta hidimunsu shikuma ya nufa inda aka tanada domin aje motocin gidan ya bata birkin
motar nuayma ta kwarariyar hanya ,abunka da tsohon hannu a aikin,
Sannan bayan haka yakuma dawowa tareda sajewa da sauran bayin inda yayi nasarar fita
lokacin da mai babban daki ta umarce kowa da ya basu guri...

********************
Kai Kawo adeel kawai yake a kofar dakin theater wanda anfi hour kenan da shiga da nuayma ,
Addua kawai yake ga ubangiji kan yabama nuayma lapia ,

Bakaramin tsorata yayi ba lokacin da yaga motar nuayma tana wasa akan titi ,ya firgita ainun
amma bai gama tsorata ba sai da yaga ta nufa gini,baisan lokacin da ya faka motarsa ba tareda
karasawa gurin da gudu wanda lokaci daya yasaka ihu da idanunsa sukayi tozali da ita ,
Kokari yafara na bude murfin motar sakamakon hayakin da motar ta fara,da kyar ya iya balle
murfin Idan ya cirota cikin karfin hali.

Cikin lokaci kankani aka taru a gurin inda shi kuma adeel babu abunda ya iya banda kuka da
rokanta kan ta tashi ta daina masa wasa'
Wani matashin saurayi wanda dandazon yajawo hankalinsa gurin ne yayi kokarin kiran 911"

Komawa yayi da sauri motarsa tareda dawowa da wani dan box da hand gloves then ya umarci
adeel da rike mata wuyanta kar tayi twisting shikuma bari yayi kokarin tsayar mata da bleeding
din da take"

Yana kokarin examine vein dinta adeel ya ture hannunsa tareda fadin " who are you"

A doctor" saurayin yabasa amsa tareda nuna masa id card dinsa yakarada doctor saleem
topah"

Bayan lokaci kalilan ambulance ta zo inda dr saleem ya bisu a motarshi dan yasan definitely
asibitinsu zaaje dan shine nearby"....

***
A hanzarce ya nufa kofar dakin ganin danjar ta dauke yasan likitocin nanan fitowa "
Dr saleem ne a gaba jikinsa sanye da korayen kayan likitoci inda bayansa kuma mutum uku ne
suma cikin kayan,
A kidime adeel ya rike hannun doctor saleem tareda tambayarsa "doctor matana fa "
Dafa kafadarsa dr saleem yayi yace matarka lapian ta kalau Alhamdulilah munsamo kanta
sannan "miracle happened" sabida dana fahimci matanka nada ciki sannan ta gamu da
wannan-----
Da sauri adeel ya katse shi dan sai a lokacinne ma ya tuna wai nuayma na da cikin shi ,cikin
kidima yace doctor how is the baby?

The baby is fine mr adeel kar ka damu as i was saying Allah ya cece babyn cikinku dan hardly
ayi irin wannan accident din da ciki kuma cikin yayi surviving so kawai mubarshi ace wa matarka
da abunda ke cikinta suna da saa domin buguwa kawai tayi sai karaya a hannu wadda akayi
taking care of nothing serious so mugode ma Allah sannan zata iya farkawa anytime soon
yanzu dai zaa sake mata daki then ka iya ganinta"

Da haka yatafi inda adeel babu abunda yake masa sai godia kaman shi yayi mata rai"

A hankali nutsuwa ta fara zuwar masa ,guri yasamu yazauna tareda ciro wayansa dan kiran
abba ,

"Yakamata ace sun Sani"
Bayan ya kira abbane wanda ya shaida masa zuwansu kana yakira mai martaba shima ya
shaida masa.

*
Ya  jima zaune a gabanta a dakin da aka chanza mata yana kallon yarda fuskanta yayi pale
kaman ba itane tagama masa tsiwa dazuba yanzu gatanan kwance kan gadan asibiti hanunta
nannade da bandeji"

Wata soyayyarta yaji tana kara fizagarsa ,ya tabbata yau da yarasata baisan inda zai saka
rayuwarsaba "
Da sallama yaji anbude kofan inda yafara jiyo sautin kukan ummi ,
Yana kokarin tashi domin juyawa garesu yaji ta damke hanunsa da hannunta mai lapia"
A take ya maida hankali gareta tareda fadin  sunanta murya cike da murna ,
Idanunta ta sauke akansa ,wani zafi ya ziyarci kanta ,kara kallonsa tayi kafun ta bude baki da
kyar tamasa tambayar da ta kusa wargaza duka maths din dayake kansa "
WHO ARE YOU?




I'm chu chu

Halal veer❤
46

WHO ARE YOU?
Kaman shock yakamasa haka yaji tambayar tata da hanzari ya matsa da baya inda itakuma ta
bishi da kallon "wannan kuma lapia"

Kallonta ta maida kan ummi wadda tashin hankaline karara a fuskarta inda hawaye ke gudu a
fuskarta fargabar ta daya da tsoranta shine kar kwallin yartata tace wacece ita kaman yarda
tama mijinta amma ga mamakinta sai cewa taji tayi"
"Ummi Mai nakeyi a gurinnan ,
Abba why are we all here"

Da sauri adeel ya matsa gareta tareda rike hannunta cikin kuka yace" nuayma kar ki mun haka
please,
Nasan kina fushi danine,nakarba amma karki hukuntani ta hanyar nuna kaman baki sanni ba
,we can leave here muyi rayuwa a wani gun dagani saike sai unborn baby dinmu,please
nuayma karki mun haka"

Wani kallon daurewar kai ta bishi dashi kana ta kalla ummi da alamun tambaya na wanene

wannan kuma"
Hannunta ya saki ya fita a dakin inda bai tsaya ko ina ba sai office din doctor Saleem"
Saida yayi knocking sau biyu kafun ya basa izinin shigowa ,
Batareda yayi masa iziniba ya ja kujera ya zauna tareda dafe kansa cikin matsananciyar
damuwa"

cikeda nutsuwa Dr saleem ya zagayo gareshi tareda zama kan kujerar dake facing

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login