Showing 42001 words to 45000 words out of 47518 words

Chapter 15 - HALAL VEER Book Complete end by Chuchu .pdf

06 Jul 2025

1310

inda likita kuma ke duba
lapiar kanta kafun afara mata aiki domin badaban su din bane bama babu yarda zaayi yatabata
har sai anje anyi hoton kanta amma kasancewar mai asibitin kankat ya kawota da kansa babu
yarda zaayi yace sai anbi wasu procedures"
Kallon abid fulani tayi da damuwa tace abid bazaka shiga kaduba halin da take cikiba kuwa "
Kama hannunta yayi cikeda karfin hali yace "ammi just calm down okay "
Wannan ba bangarena bane amma i trust doctor lakum insha Allahu komai zaizo da daidai ,
Amma tukkunna ma ammi who did this "

Share kwallan da ta taru a idanunta tayi tace wanene fa idan ba wannan yaron ba sayeed
,kasan babu mai aikata wannan danyan aikin idanu na ganin ido idan bashi ba ni yanzu
damuwata daya bansan mai za'a fadawa adeel ba ,but promise me bazaka fadamasa ba tunda
ba dadewa zaiyyi ba zaidawo kar mu raba mashi hankali biyu " Kada mata kai yayi alaman to kafun ya mike yana ayyana maima zaiyyiwa sayeed idan ya
rikeshi "
Kaman fulani tasan tunanin mai yake tace"abid nasan halin zuciyarka to na rokeka karkaje ka
tsare yaronnan kabari babanku zai dauki mataki da kanshi dan already nasaka aje a fada mashi
,banisan abunda zai hadaka dashi komai kan kantarsa '

Dunkule hannusa yayi tareda cije baki ,bahaka yasoba baiso ammi tasaka baki cikin abunnan
ba da wallahi yau mai kwatar sayeed a cikin gidannan sai ya shirya "
Kada mata kai kawai yayi kafun yasamu guri ya zauna tareda dafe Kansa.

Jim kadan dr lakum yafito daga dakin tareda mika ma abid hannu"
" success bro, but tayi narrow escape fa domin saura kadan yataba brain dinta amma all thanks
to the Almighty komai yayi dai dai sannan zata iya tashi a kowanne lokaci,
Man to man hug abid yabashi kafun yafara masa godia domin da ace wani abu yasamu nuayma
yasan definitely his brother won't survive it .

****

Wani amsawa taji kanta yayi lokacin datayi kokarin bude idanunta ,
Batayi kasa a gwiwa ba ta budesu a hankali dan ganin inda take ,
Kaman déjà vu haka abun yafara dawo mata,
Kokarin tashi zaune tayi amma takasa jin wani nauyi da kanta yayi"

Don't stress your self nuayma bari na taimaka miki"
Ta tsinci muryar fulani"

Kamota fulani tayi tareda dagata ta zaunar "
Sannu "tafada cikeda kulawa *

Dafe kai nuayma tayi kana ta kada kai alamun yauwa"
A hankali abubuwa da dama suka fara dawo mata tundaga ranar accident dinta har izuwa
yanzu da ta dauka hanyar zuwa gurin fulani,
Take abubuwa suka fara hadewa a kanta ,
Babu Kalmar da ta ke mata yawo akai kaman ruwa face "

"Bantaba tunanin zakaci bet din auran nuayma ba"
Lokaci daya komai dayafaru ya dawo mata ,wani ihu tasaka sakamakon jin kanta datayi kaman
zai fashe daganan batasake sanin meke faruwa ba,

Hankalin fulani sosai ya kara tashi inda babu shiri tafara kiran numbern abid wanda bai dade da
fita ba adakin,
Koda tagama fada masa abinda ya faru baiyi kasa a gwiwa ba wajen zuwa ga dr lakum dan
sanar dashi abunda ke faruwa ,

Da gudu gudu suka isa gareta domin sake duba lapiar kanta ,wannan karan fulanice kadai tabar
dakin amma abidin yakiya,

Bayan sungama bincike da komai ne dr lakum ya saka mata drip din da yayi ma alluran da zai
rage mata zafin ciwan kan. nema suje office dinshi yayi domin suyi magana"

Cire glasses dinsa yayi yace Dr abidin karka wani damu she's okay "
Tasamu problem din traumatic amnesia right?
Da sauri abid ya gada masa kai yana san jin karin bayani da gaggawa ,
Cigaba Dr lakum yayi "
So masha Allah tayi regaining memories dinta due to dukan da aka mata aka yau but yanzun
zatayi ta famane da migraine  ,the photophobia "and visual disturbance sabida ta daku a kaine
ba sau daya ba amma insha Allah that wont be a problem sabida zan dorata akan magunguna
and insha Allahu with time zata bari"
Godia yayi ta masa kafun ya koma gun fulani domin shaida mata duk abunda dayake akwai "

******
Tunda suka sauka garin yaji komai baya masa dadi musamman dayakira numbern nuayma ba'a
dauka ,
Bai takuraba yayi wanka yaci abinci ya kwanta yadan samu hutu domin washe gari akwai
zazzafan wasa dole yana bukata "

Washegari tunda aka fara wasa yake jinsa gashinan dai domin ko kwallo daya bai saka a raga
ba inda Allah ya taimaki yan team dinsu daya shine da saif a cikin wasan dan haka wadanchan

team din suka ja suma suka ja amma a draw ake har aka tafi half time "_

Dukan kafadansa saif yayi lokacin da yazo inda yake ya dauka ruwa"
Zama yayi ya balle murfin goran yasha fiye da rabi kafin ya kallesa "
What's wrong with you man?

Shafa kansa yayi tare da dan karamin tsaki yace i also don't get it man ,gaba daya hankalina
yayi gida domin jikina yana bani wani abu ba lapia ba ,
Nakira nuayma jiya bata dauka ba and yau da safe kafun mu fara wasannan still nakira bata
dauka ba ,i called abid shima bai daukaba Ammi kawai nasamu amma tace mun komai lapia lau
amma i don't know why nakasa yarda "

Dafashi saif yayi yace"look man tunda kaji ammi tace maka babu komai to babu komai dinne
lets just focus akan wasan nan kasan bakaramin mahimmanchi yake dashi ba kasani,kadaina
bama kanka negative thoughts .
Gada masa kai yayi in assurance kafun suka tashi domin komawa filin wasan..

...Sungama wasa cikeda nasara sakamakon maganganun saif da ya dauka "
Sosai coach dinsu yayi farin ciki da sakamakon ,
Gagarimin party yayi organizing wanda zaayi a daren ranar amma fafur adeel ya makale kafada
tareda cewa shifa yanada urgent  Family issue Da yake bukatansa "

Duk yarda suka so yazauna din babu yadda suka iya sanin halin adeel idan ya kafe akan abu
so haka nan suka barshi ya tafi badan sun so ba.


CHUCHU

Halal veer❤
51
Yana fitowa daga cikin filin jirgi ya hangi abid wanda yana ganinsa ya karaso fuska dauke da
murmushi ya karba akwatinsa kafun yabasa side hug
"Welcome back bro ,how was it"

Dan shafa gefen fuska adeel yayi kafun yace"
It was a success".
Yanada tambayoyi dayake san yayi masa amma sai yabama zuciyansa hakurin ta jure su shiga
mota "
Cikeda nutsuwa abid yafara tuka motan shikansa yasan yayan nasa nada tambayoyi da yawa"

Mai yasa nuayma bata daukan wayana"
Ya tsinci kansa da tambayan kaninnasa duk da yasan wannan tambaya sounds smh tunda abid
ba a jaka yaka yawo da ita ba"

Sniffing yayi kafun yace "well you deserve to know ,dama ammi ta hana na fada maka abunda
ya faru amma right now as we are talking nuayma tana asibiti tho Dr lakum yace a gobe ma
zasu iya sallamanta'

Asibiti?
Ya tambaya cikeda tashin hankali,
Mai ya same ta?
Mai take a asibiti?
What happened and why didn't anyone informed me?

As I told you ammi ce ta hana sabida we have got to the bottom of it ,wannan yaron ne sayeed
ya buga mata gora akai a hanyanta na zuwa gun ammi,amma dad ya masa hukunci daidai
dashi yaturasa palace prison ,
Wai yana ikirarin kan cewa ita taja aka kulle masa mahaifiya "

Dukan gefe kujeran adeel yayi tareda furta "Goddamit"
Shikenan abunda akai masa?
How wish ina kasar nan da wallahi sai yagane shayi ruwa ne dan da sai nayi kasa kasa dashi
yarda gobe idan ance masa ga kwaya ma bazai sha ba '
Dafe goshinsa yayi kafun yace "take me to the hospital"

Koda suka isa asibitin tana tareda nusayr suna hira wadda ga dukkan alamu suna jin dadin hirar
sakamakon yarda suke darawa ,
Da sarsarfa ya karsa gareta tareda manna ta akirjinsa ,
Ganin abid da nusayr ne kadai yahanata turesa tareda kwada masa mari zazzafa"

Gyaran murya nusayr yayi "
Da sauri ya saketa tareda dan shafa Kansa yace sirikina sannu da kokari "
Kada kai nusayr yayi yace "yauwa sirikina naga alamun baka kula dani bane shiyasa nayi
gyaran murya ko asan dani mu gaisa "
Dariya abid yayi tareda mika ma nusayr din hannu suka gaisa ,
Atare suka tashi suka fita wanda hakan yabama adeel daman zama a kujeran da nusayr yatashi
wadda take daf da ita ,hannunta yakama yayi kissing kafun yace"
Hayati I was scared and I miss you so dearly ,how's our baby"

DA zafin nama ta kwace hannunta tareda hade rai "
Don't you ever dare call me hayati again sabida I am not your life ,you better get that stick to
your head and secondly stop dreaming about holding this baby or what so ever, kayi kokari
wajen taking advantage nawa lokacin da memory na ya dauke amma not again honey,
Wannan chance din ya karemaka so just get my fucking divorce letter kafun nabar gurin nan
and yanzunnan kafitamun anan banisan ganinka_
You're a cheat"

Wata irin uwar zuface tafara keto masa lokaci daya"hakan yana nufin nuayma ta tuna memory
dinta like for real?
Tirkashi "
Ana wata ga wata "
Jiki a sabule yatashi ya fita a dakin domin yasan babu abunda zai fada mata ta saurareshi duk
zakin harshen sa "

Abid na ganinsa yayi ma nusayr sallama tareda isa gareshi ,
Saurin kauda kai yayi ya goge kwallar da yake kar abid ya gani"
"Bro harka fito kenan"
Muryan abid ya ziyarcesa "
Gaba yayi tareda cewa "eh mutafi gida i need to shower naga she's okay na dawo anjima"

He ain't getting it sabida tabbas yaji muryan yayan nasa kaman wanda kuka ke shirin kwacewa
amma bai tsaya dogon bincike ba yabi bayansa domin zartar da umarninsa .

**********
Bayan kwana biyu

Yau yakasance ranar da zaa sallami nuayma amma fafur adeel yaki zuwa domin shi tsoran ma
haduwa yake da ita shiyasa tun ranar da yaje bai kara komawa ba wanda hakan ba karamin
damunsa yayi ba".

Tayi tayi tabi ummi da tazo amma ummi taki tace ta zauna gidan ta kamar yarda tayi the first
time ,babu yarda ta iya dole ta hakura tabi su abid'_
Bataji motsinsa ba ko alamunsa wanda hakan ya tabbatar mata da cewa haduwa da itane
bayaso sabida yana gudanma maganan saki amma ita babu komai zataje har inda yake"

Wanka kawai tayi ta sake kaya sannan ta nufa dakinsa dan yau duk balai sai ya sake ta dan
zata tada masa hankaline wanda dole zai saka ya aikata gidansu don ta kudiri niyan yau
gidansu ta kwan,
Taci saa kuwa tana murda handle din dakinsa  ya bude "

Kwance ta tarar dashi yana kallan fankan da ke juyawa a sama ,wani tausayinsa da kaunarsa
taji lokaci daya ya kunno kai cikin zuciyarta amma shaidanin da ke hura mata wutar fitina lokaci
daya ya goge komai,

Baiji shigowarta ba saidai tsayuwarta da yaji a kansa ,
Mikewa yayi zaune fuskansa dauke da faraa ya kamo hannunta domin zaunar da ita ,
Da karfi ta kwace hannunta tareda matsawa daga kusa dashi da sauri kamar wadda wuta ta
taba ,
Cikeda fitina ta fara magana "

Kaga adeel bawai nazo ne muyi wani dogon surutu bane ba ,nazo ne ka mun abunda nake so
maana ka sakeni.

Kai wallahi sai kasakeni ko kanaso ko bakaso ni bazan zauna dakaiba sanan ciki idan har zaa
iya cirewa a mayar maka jikinka muje asibiti ayi ahakan amma wallahi sai ka sakeni "

Gyara zamansa yayi tareda jin wani chargi mai girma akansa ,
Kara juya abubuwan datake fada yayi akansa da yarda take rantsuwar sai ya saketa,
Yasani cewa yayi mata laipi amma tayi tsauri dayawa gani yake kamar an chanza masa
matarsa musamman idan ya tuna zaman da yayi da itana soyayya cikin kwanakin kamar kar ya
kare"

Dakai nakefa kamun shiru idan har kacika namijine kai ka sakeni mana wannan wane irin balai
ne da maita kasakeni ni kadaice mace a duniya ne ,i don't like you Adeel DA wane word
zanfada maka ka fahimci mai nake nufi for crying out loud huh ?
KO saina saka iyayenka cikin maganan sun kwatar mun hakkina tukkuna zaka fahimci bana
sanka yanzun"

Da kyar ya bude bakinsa yace
Baxan sakeki ba nuayma ".

************
Nuayma menene damuwankine?
He is your legal husband for God sake
Akwai masu so inke baki so
Yeye girl.

Chu chu❤

Halal veer
52
Tana kokarin bude baki domin magana ya tareta ta hanyar daga mata hannu.

"Eh ,bazan sakekiba har sai a gaban waliyinki da waliyina sannan saiki fada musu dalilin
dayasaka kikeson na sakeki sannan ki fada musu cewa kinasan kizubar da cikin jikinki nikuma
namiki alkwari idan har sun amince nima na amince kije ki zubar da cikin ,

Hanya ya dauka domin barmata dakin amman muryarta ta tsayar dashi
"
Why do you make it look as if I'm the villain?

Juyowa yayi tareda goge yar kwallan da ta tarar masa ya rike mata hannu tareda cewa "i am
the villain nuayma ,ni nayi miki laipi amma kifada mun how did i harm you,

I loved you in return ,inasanki da duk wani jini dake yawo a jikina a kullum kara sanki nake ,
Nabaki hakuri ,
I apologized not once not twice nuayma ubangiji ma muna masa laipi wanda yafi naki kuma ya
yafe mana,i did all I could to make everything right amma zuciyarki ta kekashe sannan shaidan
yana san cin galaba a kanki i mean mai innocent child na cikinki yayi miki da kikesan kasheshi,

KO kinsan cewa garin neman ramuwa kan abunda namiki kina neman fadawa halaka ,kina
neman fushin ubangiji mai tsananin gaske sabida abunda kike kokarin aikatawa dai dai yake da
kisan kai sannan kisani bai halatta mace ta nema saki a gurin mijinta ba dan yabata mata rai
har sai dai idan yana da mumunan dabia wadda nasani har ga Allah banida ita, Ko kuma yazamana baki kaunata kwata kwata wanda nasan idan kika fadi hakan kinyi karya
sabida nasani ego dinki kawai ke dawainiyya dake"

Akwai hadisi ingantacce wanda manzan Allah sallalahu alaihi wasallama yace "duk matar da
tanemi saki gurin mijinta batareda hujja kwakwaraba  dan kawai yabata mata rai to hukuncinta
shine bazataji kamshin aljannaba "

Halal a Neman Saki shine idan har halitta ta ta daina burgeki,ko kinga ina wasa da addinina ko
ina tauye miki hakki ta hanyan biya miki bukatun aure ,ko kinga ina zina,ko shaye shaye ,ko ina
karya azumi da gan gan,ko ina zaluntarki to ya halatta kinemi saki ta hanyar kul'i wanda ni
nabar miki komai da nayi miki na aure basai kinnema saki ta hanyar kul'i ba , Zan sakeki in har abubuwan da na lissafa maki sun danganceni cikin sauki"
Ki yi tunani zuwa dare amma kisani in har kika kashe abunda ke cikinki Allah bazai taba
ragwanta miki ba"

Sannan babu inda aurena dake ya haramta kamar yarda kike cewa ba aure bane sabida ba
ciyo ki a chacha nayi ba ,wauta ce kawai tsakanin abokai bet din dake tsakanina da shareef
amma babu ta inda hakan ya maida auren mu haramun sabida na aurekine ta tsarkakiyar
hanya ,shaiduna da naki kowa yana nan haka zalika waliyyanmu sannan baatashi a gurin ba
har saida aka shafa fatiha wanda hakan koyarwace ta annabinmu ,dan haka babu haramci a
cikin aurena dake.
Yana kai aya yasaka kai ya fita a dakin .

Wani uban kuka tasaka tareda zubewa kasa inda lokaci daya wata nadama tashigeta,wani kuka
mai ciwo ta fashe dashi tareda dafe cikinta ,
Cikin kuka tafara magana "
Astagfirullah ,ya ubagiji na tuba astagfirullah ,ya Allah ka yafemun nadade akan bata ya Allah
ka yafemun ,na shiga hakkin mijina na kudira mumunan niyya kan abunda yake cikina alhalin
babu abunda nakeso sama dashi ,
Kayafemin babyna im very sorry ,mommy is sorry ,
Ya Allah ka yafemun karkasaka na tashi ranar lahira cikin matan da bazasuji kamshin aljanna
ba ,
Ya illahi what have I done ?

DA Sauri ta tashi dan ta bishi amma ta makara domin yariga ya fita agidan,dakinta ta koma ta
zauna zuciyarta cikeda tsoro da fargabar yanzu idan ta mutu bai yafe mataba wutafa kenan
zata shiga gashi ita ba maabociyar fadan sirrin gidanta bane barantana ta kira daya daga cikin
kawayenta su bata shawarar mai zatayi ,sannan a yanzu dai mutum na karshe da zataso yasan
wannan wautar tata to bazai wuce iyayenta ba ,sannan a duniya babu abunda zai saka ta yada
matsalar gidan aurenta a media koda kowa a matsayin anonymous ne dan haka ta dauki
shawarar da zuciyarta ke bata nacewa ta gyara aurenta ta hanyar neman yafiyar adeel wanda
tabbas tasan yin hakan yana kan hanyar daidai.

*******
Favorite abincin da yake so ta dora around 4 tunda tasan duk inda 6 take zai shigo gidan ,
Tuwon wheat ta tuka da miyan kuka wadda tasha shaki,ganda ,stock fish,and crayfish nan da
nan gidan ya dauki kamshi,bayan ta gama jera komai kan table dinne ta koma ta dauko
soyayyan manshanu ta aje a gefe sannan tafara shiryin hada masa mango lassi wanda bai
dauki lokaci mai yawaba ,tana gamawa tasaka cikin fridge don yayi sanyi duk da ice block din
da tayi blending tareda mango din"

Ajiyan zuciya tayi da ta tabbatar komai ya kamala dama already ta sallami maids dinta domin
wannan ranar ta nuayma ce da adeel ,
Burner ta kunna tareda zuba turaren wuta mai sassayan kamshi kafun ta fada daki domin yin
wanka,

Cikin wani material mara nauyi riga da skirt wadanda suka fito da surar jikinta sosai ta shirya ,
Komai nata yayi dam dam sakamakon cikin daya fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login