Showing 39001 words to 42000 words out of 47518 words
dinsa yace
"lapia kuwa "
Sai a lokacinne adeel ya bude fuskansa tareda sauke gajiyayyon idanunsa kan Dr saleem "inafa
lapia doctor ,ina wata lapia matana ta gane kowa a cikin dakinchan amma bandani and you told
me babu wata damuwa kalau take amma mai yasaka ta manta dakoni wanene ,
Could you blv nuayma asked me waneneni"
Calm down "doctor saleem yafara kokarin saukar da shi tareda dafashi"
Hanunsa adeel ya ture tareda fadin "calm down?
Don't tell me to calm down doctor bawani calm down dazanyi ,just go and fucking check what
the problem is"
Fahimtar da Dr yayi nacewa adeel yana cikin damuwane yasaka ko kadan baiji haushinsa ba
illa tashi da yayi domin zuwa aduba lapiyar kanta "
Ana cikin sake binciken kanta mai martaba ya halarci gurin batareda wata alamu ko algaitaba
wadda zata nuna maka cewa sarki yazo gurin ,
No as a normal mutum mai arziki wanda yakeda halin daukan bodyguards biyu"
Bakowa ya maida hankali gareshiba dan haka cikin sauki ya isa inda abba ya musu kwatance
ille nan ya samesu zaune cikin damuwa musamman ma ummi wadda har yanzun take matsar
kwalla"
Cikin girmamawa suka bashi guri ya zauna sannan suka gaisa a yanayi na surukanta "
Shaida masaa halin da ake ciki abba yayi wanda lokaci daga hankalinsa ya koma kan dan nasa
domin duk da cewa a kullum yana fadane a nannade amma yasan irin soyayyar da adeel kema
nuayma ,
Bai tambaya yana ina ba dan yasan he's somewhere within dan haka sai ya tsaya jiran
tsammani kamar bakace sarkiba.
Mintuna kalilan Dr saleem ya fito daga dakin da aka sake dubata ,
A tare ummi da abba suka nufesa dan jin bayani,
Yana kokarin maganane idanunsa suka sauka kan maimartaba wanda yasan bai kuskureba
shidinne dan haka cikeda girmamawa yayi musu iso zuwa office dinsa inda suka tarar da adeel
da hannu a fuska ,
Alamun shigowanne yasaka da sauri ya mike tareda fadin doctor what's the problem?
Then kuma sai yaga mahaifinsa wanda ai nan take wasu zafafan hawaye suka sake fitar masa "
Zaunar da shi mai martaba yayi kan cushion tareda dafasa in assurance na cewa everything ia
gonna be okay"
Dr Saleem baiyi mamakin ganin adeel din prince bane Dan daga ganinsa dama kasan dan wani
babban ne sannan bugu da kari yana masa kama da spark dan wasan kwallon raga ,
Tun ganinsa yake tunanin koshi dinne amma sai ya kawar da tunanin but identity dinsa yakara
tabbatar masa cewa shi dinne "
Cikeda nutsuwa yafara musu bayani kamar haka"
Munyi bincike sosai akan matsalar nuayma amma a zahirin gaskiya babu abunda yasamu kanta
kamar damage ko wata muguwar buguwa haka amma dama normally wanda yasamu accident
kaman nata atttimes yakan samu matsalan traumatic amnesia wanda yake temporary she can
recover within weeks KO months it depends ,
DA sauri adeel ya katsesa ta hanyar cewa "look here likita ina tunanin you don't get what's
going on here"
I told you matana ta tuna kowa bandani ,only me "how can that be possible"
Murmushi doctor saleem yayi yace"nasani" dalilin dayasaka ta manta memory dinka shine
maybe she has the worst experience with you before the accident and memory dinka yafi ko
wane memory hurting a tartare da ita ,ba kai kadai ba ,zaiyyi wuya a yanzu dai halinda take ciki
ta tuna daya daga cikin family dinka "_
Wani dum gabansa ya fadi 'abunda yake kalla a movies yau shi adeel ya faru dashi ?
Inazai saka rayuwansa ?
What if taki tunasa baki daya ?
No
DA sauri ya tashi yabar office din "
Koda ya shiga dakin zaune yasameta inda yabarta saidai wannan karon tana cin grapes
gefenta kuma fasiya ne da maryama wayanda sukayi tsuru suna kallonta "_
Tana hada idanu dashi tasakan masa sassayan murmushi tareda fadin"hey strange man kayi
baki takarasa maganan tareda nuna fasiya da maryama ,
Sunce daga gidanku suke "
Hawayen da ya dade a idanun fasiya ne suka samu damar fitowa lokaci guda ,
A guje ta fice a dakin taana kuka "
Galala nuayma tabi kofan da kallo kafun ta aje grape din tareda maida kallonta gareshi tace
"that's strange tunda nace bansansu ba naga ta nuna damuwa i like the girl amma wallahi I'm
serious bantaba ganinta ba I'm I suppose to pretend a zimmar nasansasu "
Call her I will do that "Takarasa maganar da damuwa sosai a tattareda ita ,
Zama yadawo yayi a kujeran da fasiya ta tashi then ya kalli maryama wadda itama hawayen
keneman hanya yace "bi fasiya "
Ba musu tabi bayan fasiyan .
Kama hanunta biyu yayi tareda zuba mata idanu inda itama in return ta zuba masa nata idanun
deep down a ranta tana yaba kyawunsa ,
Sniffing yayi kafun yafara magana tareda fadin"
The first time I saw you was the most luckiest day in my life ,
Kinshigo rayuwana and baki shigo hakanan ba saida kika taho mun da soyayya da kwanciyar
hankali sannan aurenki yana daya daga cikin daukakata ta rayuwa ,
Hannunsa yakai kan cikinta kana ya cigaba "cikin dake jikin ki kuma yana daya daga cikin
manyan kyautukan da kika taba mun a rayuwa "
Ba dole sai kin tuna memory dinkiba as far as zaki zauna taredani da unborn child dinmu,it
doesn't matter ko baki tuna irin soyayyar da ke tsakanina dake ba tawa ma kadai ta isa sabida i
love you to the moon and back "..
Dan kwace hannunta tayi daga gareshi kafun tace literally kanasan kace ni matan kane since
from the beginning sannan bugu da kari ina dauke da cikinka ?
Dafe kanta tayi tanaso ta tuna wani abu a attareda shi amma ta kasa illa wani ciwo dataji kanta
ya fara "
No I can't be your wife that's impossible I mean ya zaayi nakasa tunaka and suwane
wadancan".
Sisters dinane ".yabata amsa a takaice"
Fasiya and maryama and kina sansu sosai musamman fasiya you were very fond of her "
Take sai taji rashin dadin tunasu sannan wani urge nasan ta tunasu lokaci daya ya ziyarceta,
Murmushi tayi tareda rike hannunsa wanda yin hakan yabasa mamaki dan hatta ita kanta ta
kula dan haka ta kara fadada murmushinta tace ,"its okay as far as zaka taimakamun natuna
,nima inaso na tuna ,
Da sauri yakara matsowa gareta tareda fadin "da gaske?
Kada masa kai tayi alamun eh domin clearly tanajin wani abu a tattareda shi sannan bataji dadi
rashin tuna memory dinsu tare ba amma tasan kowane irin memoryne to mai dadi ne domin
babu yarda zaayi ace wannan tsalelen handsome guy din ya bama mutum bad vibes"
Baisan lokacinda ya rungume taba har saida ta dan saki yar karamar kara saka makon ciwonta
da ya taba,
DA sauri ya saketa yana aika mata sakon sorry wanda hakan ya bata dariya dan haka ta bude
masa hannu a hankali ,
Baiyyi wata wata ba shima ya rungumeta a hankali yana tunani a ransa na tabbas tunda ta
bashi wannan dama dole yasan duk yarda zaiyyi domin kara gina sabuwar soyayarsa a cikin
zuciyarta ,within weeks ,month or months yarda koda tunaninta yadawo rabuwa da shi din zai
mata wuya.
***
Dafatan kunyi sallah lapia?
Chuchu
Halal veer☀
49
Cikeda baccin rai yace to uban wanene yahanasa nuna unknown mutum a cikin su ,
Inasan ganinsa right now*
Dafasa abid yayi tareda fadin"calm down bro Kasan yanayin aikinsu mayhaps zaiyyi tunanin ko
baidade da shiga cikinsu ba amma ansamu wanda yasan shi har an fadan sunansa Zaki we just
have to capture the guy maybe musamu wani abu daga gareshi,
Remember he is just a suspect "_
Kada kai adeel yayi tareda tashi domin dama ya gama ,dafa kafadar abidin yayi yace "thank you
very much abid "
Koda ya shiga gida tarar da ita yayi tana yima fasiya kitso,karasowa yayi tareda zama a kujeran
datake yace"bismillah kice wahalar mun da mata kawai aka zoyi"
Charaf fasiya ta dauke "bro inace nima wahalar mun da Ammi kuka gama yanzun so tit for tat "
Tare shida nuayma suka saka dariya sanin yarda bakin fasiya baya mutuwa,daman a last one
suke so ana kai mata aya tamike tareda musu salama,
Kallonsa tayi kafun tarike hannayensa
"Dear you looked disturbed"
Wani ajiyan zuciya yayi tareda kallonta yace "why won't I look disturbed tunda matana batani
take ba tamaki bani dan abun duniyaan nan ko naja kaya "
Dukan wasa takai masa tareda fadin"stop being naughty"DA gudu ta tashi tashige daki inda ya
bita yana dariya tareda fadin ashedai zaa bani kayan dama mutum ma yana san dan dana
zuma amma yana fulako".....
*******
.....
DA zafi zafi yake hura sigarinsa inda a daya hannun kuma wayarsa ce yanata danna kira amma
baa dauka"
"Okay bazaka dauka ba kenan eh"
To wallahi ba sarkin yaki ba ko sarkin takobine katabo ma kanka danja ,
Inmuku aikin ku hainceni,?
To wallahi zuru batacin zuru sai dai su hadu suci zuru zuru dan baban nan ,
Oh ni shege ZAKI ban fito ba saida na shirya billahilazi bawani dan jaka"
Wayarsa ya kunna tareda shiga recording din da yayi alokacin da sukaje gurin gwaggo amarya
shida sarkin yaki'
Dariya yayi da yaga recording din yana nan,
"Eh yanzu ranarka tazo da wannan daukar nasan idan na kaima yarima adeel zan samu na
wiwi"
Da haka ya nufa gidan adeel ,
Tsabagen dan kwayane shi baiyyi tunanin wani abu da zai biyo bayaba dubada harda shi acikin
wannan danyan aiki, aa shi burinshi yasami yan kudin da zai chake"
Cece kuce suka fara da mai gadin gidan adeel akan zaki bazai shigaba tunda yarima bai sanar
masa da zuwan saba inda shikuma yanace kan cewa ai ganinsa a gun yarima yafi ganin
makudan miliyoyi.
Suna cikin wannan cece kuce abidin ya karaso gurin inda suka dakata atare suka gaishe shi,
Neman Karin bayani yayi "
Bayan maigadi yagama fada masa ne ya maida kallonsa kan zaki yana tunanin inda yasanshi
,then kuma abun yayi masa hitting ya tuna tabbas ya taba ganinshi da sarkin yaki sannan ko a
lokacin bai yarda dasu ba amma sabida adeel yasaka yarabu dasu dan haka ya umarci mai
gadin da ya barshi ya shigo ,
Zama yayi kan kujera a harabar gidan whilst shikuma zaki ya tsugunna ,
Maike tafe dakai,"
Jum zaki yayi kafun yace yareema inasan na gana da yareema adeel ne akan wata gagarumar
magana ,
Kallonsa abid ya kuma yi domin jikinsa bai bashi cewa zaki nada gaskiya "
"Yasunan na ?ya tambayeshi kai tsaye"
ZAKI"..
A hanzarce abidin yakallesa tareda cewa zaki?
Kada masa kai zaki yayi ".
A siyasance abid yace "masha Allah "yanzu dai zaki kafada mun maike tafe dakai ,idan kaganni
kaman kaga adeel ne ai ,kana neman wani taimakone "_
Inda inda ya fara kafun "yace dama dama wani abu mai muhimmaci zan siyar masa amma sai
in zaamun afuwa ranka shi dade "
Mamakin karfin halin zaki yagani sosai dan yasan tabbas abunda ya shafi nuayma ne ya
kawoshi,
Bai masa musuba ya kira adeel a waya wanda minti kadan bai karaba ya fito harabar gidan "
Da izza Zaki ya mika masa video din inda take jikin adeel ya fara tsuma da saida abid ya
rikeshi"
"Ranka ya dade sai lada na "
Kallon zaki adeel yayi cikeda wani makeken bakin ciki yace " kajira bari nasaka a kawo maka ai
kacancanta "
Waya yakira tareda matsawa daga garesu ,
Magana kadan yayi kafun ya dawo inda haji Zaki babu abunda yake sai washe baki "
Kafun kace menene yansanda sun bayyana a cikin harabar gidan ,
Kokarin guduwa zaki yake amma kafun kace wani abu an damkesa"
Ai take yafara "eh yarima bafa haka mukai da kaiba ,wannan ai cin amanane,nayi wasa da
rayuwata danna samu dan nashan shoshe na amma ka kira mun kwalawa ,
Haba ranka shi dade wannan ai yawa ne"
Baibi ta kan zakiba yabada umarnin da ayi gaba dashi inda yakara bada umarnin akamo masa
sarkin yaki within 24 hours"
Kaman wani namijin zaki haka ya shiga cikin gidan wanda hakan sai da ya tsorata nuayma
dake ware kayan da aka kawo daga guga"
Kaman guguwa haka ya shiga cikin dakinsa ,
Aje komai da takeyi tayi tareda binsa ,
Komai dake kan mudubin yayi watsi dashi inda guri daya kuma hannunsa na bleeding "_
Da gudu ta shiga daki tareda rikesa "
What's wrong with you honey ,wane ya
mutu"
Kallonsa ya maida gareta kafun yace "babu wanda ya mutu amma wani zai mutu ,could you blv
gwaggo amarya tayi causing accident dinki ,beside she wanted you dead ,bana tunanin zan
sasasauta mata wallahi ,juyawa yayi fuu zai sake fita,
DA hanzari ta kamo hannunsa tareda zaunar dashi ,a hankali tafara shafa masa bayansa dan
ya samu nutsuwa,
Saida ta tabbatar nutsuwa ta ziyarcesa kafun taje ta dauko first aid box tayi dressing masa
wound dinsa ,
Kafun tace "
Habibi nasan kana cikin babban bakin ciki ,i mean who wouldn't amma kasani cewa daukan
hukunci cikin fushi is not the answer ,you have to do everything accordingly,
Karda kabari zuciya tasaka aikata aikin dana sani mubi komai a hankali ,yanzu kafara kai case
dinan gun sarki shi yasan yarda zai bi da abun kaji mijina "
Idanunsa yasaka cikin nata kafun ya jawo ta jikinsa tareda rungumewa cikeda shauki yafurta "i
love you"
I love you too.
...
A bun ya girgiza kowa a cikin masarautar musamman sarki da baitaba kawo matar da yake ma
kallon mutuniyar aziki zata aikata wannan gagarumin danyen aikinba ,
Sosai hankalin kowa ya tashi a masarautar dan saida ta koma upside down ,
Batareda bata lokaciba sarki yasaka akayi ram da ita sannan cikin hour 24 hudu aka kamo
sarkin yaki wanda ya gudu garinsu dake birnin gabas ,
Yayi mugun dana sani nayima greedy mutum aiki kaman gwaggo amarya,yasan tabbas ba kudi
ne bata dashi ba kawai mugun hali ne yanzu gashi suna zaman zaman su kalau zata ja masa
gidan yarin da bai shiryaba,
Shi yasan Zaki kuma yasan wanene shi akan kudin,dama yasani ta yankin chadi chadi yabi da
tuni yana chan baka lapia ciki lapia,
Babu wanda bai tsorata da hukuncin sarki akan gwaggo amaryaba,.dakin duhu yabada umarnin
a kulleta sannan a ringa bata abinci sau biyu arana ,shima hakan wai sassauci ne sabida ita
din ta taba rayuwa a matsayin matar sarki,
Zaki da sarkin yaki kima hukuncin shekara 20 a gidan yari .
......
Tun wakanar alamarin komai ya dawowa nuayma da adeel daidai,kimanin wata daya kenan"
Soyayya mai tsafta suke zubawa tsakanin su inda kowa yake fatan dawwama da dan uwansa ,
Kwatsam wani wasa ya taso ma adeel a Germany wanda ake bukatarsa da gaggawa ,ai take
nuayma tafara hada kayanta dan tace bataga yarda zaayi yatafi ya bartaba ga kuma masifaffen
laulayi da take fama dashi "
Zaunar da ita yayi ana gobe zai tafi yace look here darling "
Baifii nayi kwana uku bafa ,banasan tafiya dake ki wahala sannan abunda ke cikin kima ya
wahala ,
Namaki alkawari insha Allahu bazan wuce 3 days dinnan ba zan dawo gareki da babyn mu so
now be a Good girl and listen to daddy "
Dukan wasa ta kaimasa jin ya ambaci daddy abunda ke bata dariya kenan idan yace yanzu shi
daddyntane ita da unborn dinsu ,
A haka yashawo kanta washe gari kuma da sassafe abid yakaisa airport dan wucewa Germany.
*****
Chu chu
Halal Veer
50
Zaman gidan taji ya isheta sakamakon bawa ladi hutu da adeel yayi atleast datana nan zasu
dan yi hira ,
Shiryawa tayi ta dauki malullubi dan zuwa sashen Fulani tasan kewan zai ragu koda hira ne tayi
taji dadi ,
Bayi masu gyaran gida ta iske a harabar gidan ,a tare suka zube domin kwasan gaisuwa ,baban
abunda ta tsana kenan,
Amsasu tayi tareda yin gaba abunta "
Tana kokarin fita a gidan wani dakare yakaraso cikeda girmamawa yace "ranki shi dade kafun
yarima yabar garinan ya gargademu sosai akan duk inda zakije mu baki tsaro ,
Kallonsa tayi ta dafe goshinta in frustration itafa last thing abunda ta tsana shine takura"
"Katafi banisa zanyiba "ta umarcesa"
Ranki shidade kimin afuwa "
Ya kara nacewa "
Cikeda fushi tace "inace nidai nace maka katafi ko"i don't need any bodyguard nan da nan din
da zanje,?
Gaba tayi tana cewa "Allah ya taimakeka naga ka biyoni kagani"
Baiyyi gangancin binta dinba dubada bai taba ganinta tayi irin wannan fushin da kowa ba "
Tsaki tayi lokacin da ta tabatar baya binta kafun ta dauki hanyar da zata sada ta da sashen
fulani"
Kamar daga nesa ya hangi gilmawarta "ai baiyyi wata wata ba ya dauki kokaran da bafaden da
ya aika ya aje yayi gareta a sukwane ,
Koda ya isa gareta saida yasaka hannu ya tabata tukkuna,
A zabure ta juyo amma kafun ta furta wani abu koma ya antaya mata gora a tsakiyar kai"
Yana ganin ta zube a kasa sumammiya ya arta a nakare "
Wata kuyangar fulani da abun yafaru akan idanuntane ta kwasa da gudu tayi gun fulani domin
sanar da ita abunda idanunta ya gane mata "
A take Fulani ta fito hankalinta a tashe tana kiran sunan nuayma wadda ke sheme a kasa bata
ko motsi"
DA gaggawa tasaka akira mata abidin wanda ta baro a uwar dakinta yana bacci .
Koda yafito yaga nuayma kwance a kasa kanta na jini bai tsaya wani neman karin bayaniba ya
kwasheta domin kaita asibiti da gaggawa .
***
Zagaye kawai fulani da abid suke a kofar dakin da aka kwantar da ita