Showing 27001 words to 30000 words out of 47324 words

Chapter 10 - AL AJABI COMPLET BOOK HAUSA NOVELS .pdf

Unknown   

15 Jul 2025

3410

tsorona kike ji??
Na girgiza kai nace “Koda ace za‘a wayi gari
kowa ya zama abin tsoro a gareni na tbbt
banda kai.“
To ki dago kanki.
Na yace mayafin dake kaina tare da dago kai
fuskata wadda hawaye ya gama jikata sharkaf
ta bayyana.
FARUK yadan yi baya da kansa kmr yaga abin
tsoro yace “Kuka kuma?? Maimakon murna da
farin ciki??“
Na girgiza kai ckn sheshsheka nace “ni nafi
cncnta nayi kuka fiye da kowa, mafi yawan
amare nayin kuka amma na munafunci ne ni
kuwa nawa kukan na dolene sbd rayuwa bata
zo mana a yadda yakamata ba, laifin me
mukaiwa duniya da tayi mana wannan horon

FARUK...??
ya kauda kansa tare da cewa “ki daina fadan
haka HUMAIRA ba muka iya da yadda Allah ya
kaddara, Ai dai gamu a tare matsayin
MA‘AURATA wannan shine bbn abu mafi jin
dadi daya kamata ki rinka 2nawa. Na kara
kasa da murya nace “ma‘auratane mu amma
ba kmr saura ba 2nda mu muna da nakasu ta
bangarori da yawa kowacce amarya takan
zauna ne a tankwashe amma ni kafuna kaga a
mike suke daga sama har kasa ba wani motsi
da zasu iya yi, kaga kenan ni nakasashshiya
ba wani amfani da zanyi a garek......“
Yadan zaro min ido tare da katseni yace
“HUMAIRA!!“. yabini da kallo ya dora da fadin
“don Allah ki daina fadar haka, idan baki
manta ba a baya na taba sanar dake cewa ba
ina sonki ne don bukatuwar samun wani abu
daga gareki ba, ina sonki ne a mtsynki na
humaira gnnki a kusa dani kawai ya wadatar
dani.
Kuma ai larurarki ta iya wani lkc ce ba‘a ce ta
har abada ba don haka zaki warke kuma muyi
rywa kmr sauran MA‘AURATA.
Tarayyarmu bata wani dan lkc kankani bace ta
har abada ce, babu wani dalili dazai rabamu
har abada.
Ki rinka 2na wannan a koda yaushe.“
Ckn sheshsheka nace “a baya na dade ina
hango yadda rayuwar aurenmu zata kasance
ckn farin ciki walwala da jin dadi sai gashi
tazo mana akasin haka, tazo da babban
nakasu.“
faruk yace “ki daina kawowa zamanmu babu
farin ciki sbd kawai kina da larura, duk inda
HUMAIRA da FARUK suka kasance tare akwai
tbbcin farin ciki a wajen a kowanne irin yanayi
ne.“
nadan bishi da kallo nace “Me yasa ka hana a
bamu y‘ar aiki da zata taimaka mana, alhalin
sanin kanka ne ba abnd zan iya yi.
Yayi saurin girgiza kai yace “babu bukatar
wani ya shigo ckn rayuwarmu ya taimaka

mana mu zamu taimaki rayuwarmu da kanmu
kuma mu tafiyar da ita yadda muke so, zamuyi
zama irin wanda ba‘a taba yin irinsa ba.
Na tbbt Allah daya haliccemu zai taimakemu.“
“girki, goge-goge, share-share, wanke-wanke
duk waye zaiyi wadannan ayyukan??
Na tambaya ina dubansa.
ya mayar min da amsa da cewa “duk nine.“
Idanuna sukayi saurin tafiya yawo sbd
AL‘AJABI!!!!!
kai kuma??
Naka aikin kuma fa ko shikenan a gida
zakayita zama??
“A‘A! aikina yana nan amma bazai shafi
wannan ba.“ Wasu sababbin hawaye FIL suka
sulalo min.
Lallai bana jin za‘a samu mu2m irinka duk
duniya!! ka sarayar da hakkinka da duk wani
ango ke buri idan yayi aure sannan ka dauki
alhakin aiki mafi girma akanka duk sbd ni.
Ina rokon Allah ya kawo sababin da nima zan
nuna maka HALACCIN da kayimin duk da
nasan zaiyi wuya nayi maka irin abnd kayi min
sai dai na kwatanta.“ Na kwantar da kaina
bisa cinyoyinsa na fashe da kuka.
Mun dau tsawon lkc a haka dakyar faruk ya
rarrashe ni na iya yin shiru, da kansa ya tashi
ya zubo min abnc ya tilasta min sai da naci
sosai.
Ya dauke plask din da sauran kayan ya mayar
dasu wajensu ya tako a hankali yace “To kinga
yanzu lkcn kuka ya wuce ki kwanta kiyi barci
isashshe kada kiji komai a gdn masoyinki
FARUK kike..
yakai karshen maganar dai-dai sanda ya
zauna a dan karamin tebirin dake gefen gadon,
nabishi da kallo har yanzu hawayen idona
basu kafe ba saima kara gudu da sukeyi.
Na dubeshi nace “amma wannan rana tazo
mana ba yadda yakamata tazo ba, me yasa
ma haka zata faru??...“
Faruk ya dan kauda kai ya dawo ya dubeni
yace “ki bari!! zakiyi sabo fa! idan kika ce me

yasa, kai tsaye Allah kenan fa kike tambaya.
Haka Allah ya kadarta mana koda a haka
zamu tafi har mu2wa ni bani da kaico, kada ki
karya zuciyarki da yawa duk wanda yasanki
yasanki akan dakakkiyar zuciya me zai hana ki
dawo ki cgb da zama a haka??“
Na girgiza kaina nace “zaiyi wuya koda zai
yiwu badai a ynz ba.“
Ya bini da dogon kll yadan zunburo baki yace
“Zamu bata idan baki daina kuka ba.“
Na goge hawayen idanuna.
Yace “yauwa ko kefa??
Sai ki kwanta kiyi barci ki samu isashshen
hutu kinji??
Na gyada kai kawai nabi gadon na kwanta
nace “kai kuma ina zaka??“
Zanyo alwala nazo nayita sallah na godiya ga
ubangijina daya bani ke.
Zan bika muyi tare.
Na fada ina dubansa.
Ya girgiza kai yace “A‘A my amarya aike kina
da lalura barci shine mafi dacewa a gareki a
yanzu.“
Ka daina kirana da amarya sbd lalura ta hana
na amsa wannan sunan, ban kuma san sanda
zata barni na warke harna amsa sunan ba.
Na fada.
Yayi saurin cewa “manta da wannan“ ya jawo
bargo ya lullubeni har zuwa wuyana yace “kiyi
nutsatstsen barci da safe zaki fada min kalar
mafarkin da kikai.“
Yakai maganar murmushi na tashi daga fskrsa,
fuskata ta fadada da murmushi nima na gyada
kai kawai.
Ya juya ya dauro alwala akan idona ya fara
sallah sautin kara2n da yake yi yana ratsa
kunnuwana har barci ya kwashe ni.
*WASHE GARI da asuba faruk ya tasheni nayi
sallah a zaune kmr yadda na saba yi barci na
koma sbd akwai shi a idona sosai.
Misalin 8:15 na safe faruk ya tasheni a karo
na biyu, cak ya daukeni ya dôrani bisa kekena
ya seta kafafuna a matokarar keken dake kasa

ya 2rani a hankali muna hira kai tsaye muka
fito falo ya wuce dani gefe falon inda aka
tanadi wani faffadan tebirin cin abinci zagaye
kujeru ya 2rani har izuwa gbn kayataccen
tebirin ina zaune bisa keken da aka halitta sbd
irinmu.
faruk yace “yauwa kinga ke y‘ar baiwa ce ba
ruwanki da kujera, ni kuwa bin tebirin kawai
nake da kll zagaye yake da abinci kala-kala
irinna breakfast kuma dafawar yanzu sai tiriri
suke kana gani kasan yanzu aka hada su.
ckn AL‘AJABI nace “waye ya dafa duk wannan
abubuwan??“
Yayi murmushi yace “Nine!! kina mamakine??“
Ya fada dai-dai sanda ya ajiye kofin tea a
gefena tare da cewa “bismillah! sai ki fara da
duk wanda kike so.“
A ido kawai nasan duk abinda ya dafa zasuyi
dadi ma2ka sanda nakai bakina dazan hadiye
har wani lumshe ido nayi, na bishi da kll nace
“a jami‘o‘in koyon girki wacce kayi??“
Yayi dariya yace “A jami‘ar ummina mana, 2n
ina yaro tare muke yin komai gashi kuma
yanzu hakan ya fara amfani.“
Haka dai muka cgb da cin abincin ckn nishadi
muna hira har muka gama, faruk ya fara shiga
dani loko da sakon na gidan.
*Haka dai muka cgb da rayuwa har hu2n faruk
ya kare ya koma wajen aiki sai ya zamana
kafin ya tafi duk abinda zan bukata ya aje
minshi bisa faffadan tebirin dake gaf da
makeken gadona.
Abinci, ruwa, magungunana da komai suna
kusa dani sai kuma uwa-uba wayata wadda
da ita muke tare a ko yaushe.
kllm sai ya dawo ya koma, da la‘asar tayi
kuma ya dawo gida ya shiga kitchen da kansa
ya dafa mana abinci.
A wasu lktn tare muke shiga ina zaune bisa
dan kekena muna hira har mu gama hada
abnd muke so, rayuwarmu abin sha‘awa ckn
sauki muke gudanar da ita cike da walwala da
aminci wanda hakan ya samu ne ta silar

tsantsar SOYAYYA ta gsky.
Anya kuwa...za daure..
A wasu lktn idan na dubi a yadda rayuwarmu
ke tafiya sai naga kmr a mafarki don ban taba
zaton zan tsinci kaina a hali kwatankwacin
haka ba, da ace shekaru biyu kacal da suka
wuce wani zai fada min cewa haka zata faru
koda zai nutse a kasa don rantsuwa bzn yarda
ba.
Amma gashi na tsinci kaina a wata irin rayuwa
daba haka nayi zato ba, sai dai ko ba komai
wasu darussa ne na koya na rayuwa da
bazasu taba gushewa daga kwakwalwata ba.
*da yake zancen duniya baya buya a ckn dan
kankanin lkc maganganu suka fara zagaye
gari, nan fa kasuwar gulma da tsegumi ta
bude masu mamaki da rike baki nayi masu
salati da sallallami nayi, masu jinjinawa faruk
nayi masu tausaya masa nayi.
A fahimtar wasu kuskure ya tafka babba
dazaiyi dana sani a gaba, wasu kuma na
kllnsa wanda kuruciya tayiwa yawa.
Amma ko kadan bai kula da hkn ba saima
kwarin gwuiwa da yake kara samu na kyautata
min da nuna min soyayya iyakar iyawarsa, hkn
yaba mutane mamaki ma2ka da gaske. Wato
ni kaina idan na kalli faruk ina mamakinsa
musamman yanzu dana kara kusanta dashi
banyi kuskure ba idan nace ba kmr kowa yake
ba tbbs shi daban ne wanda samun mu2m
kmrsa zaiyi wuya.
A kwana a tashi kwanaki sai kara garawa suke
zaman mu na kara daukan lkc, syy da kulawa,
kauna da shakuwa na daduwa.
Mu kadai muke gudanar da rayuwarmu kmr
yadda faruk yace haka yake so mu kasance,
ko ziyara ba wanda ke kawo mana harta da
momina sai dai kawai muna yin waya wasu
lktn, ba‘a zancen daddy dama amma banga
laifinsu ba da wane ido zasu kll faruk??
Wanda suka batawa da mummunan sharri ya
saka musu da mafi kyawun alkhairi.
hmmm... Abin da kunya ai.

**kmr kllm yauma zaune nake bisa gadona na
kishingida misalin karfe 4:45 na yammaci
tsammanin dawowar faruk kawai nake nama
yi mamakin yadda yau bai dawo da wuri ba
don mafi yawa ana kiran sallar la‘asar yake
dawowa, a hakan har barci ya kwasheni.
ban jima da tafiya nahiyar baccin ba faruk ya
shigo da sllmrsa yayi shiru sanda ya tbbtr ba
yadda zanyi na amsa don bansan yana yi ba.
ya dan tsaya ya bini da kallo kawai murmushi
ya tashi daga fuskarsa ya rankwafo tare da
sumbatar goshina ya dago yace “ohh!! my
lovely wife Allah ya kara miki lfy.“
bai tasheni ba Ya juya ya wuce izuwa
bathroom.
Byn wasu y‘an min2na na farka, na dubi
agogo 5:05 lallai yau faruk ya dade bai dawo
ba na fada a zuciyata, ta yiwu wani muhimmin
abu ne ya tsayar dashi.
Nayi saurin bawa kaina tbbs akan haka domin
bisa al‘ada baya kaiwa haka don wasu lktn ma
ana kiran la‘asar yake shigowa.
Kmr na kirashi sai kuma na fasa, da yake da
wata kishirwa na farka matsowa nayi bakin
gadon na jawo ruwan SWAN dake ajiye bisa
dogon tebirin dake gefen gadon gaf da fuskar
gadon wanda ke dauke da abubuwa da yawa.
Irin daukowar gaggawar da na yiwa robar
ruwan yasa ta subuce ta fadi kasa tare da
gangarawa nesa sosai da gadon, gashi ina
bukatar ruwa sosai hakan yasa na matso
bakin gadon tare da kwantawa na mika
hannuna don dauko robar, sai dai ina!!
hannuna ya gaza kaiwa inda take.
Nayi iya kokarina na mika hannuna iyakar
mikawa amma ya gaza kaiwa, 2nanin dana
fara yi shine wai yau nice ga abu ina so amma
na gaza iya daukarsa kuma ba wanda zai
bani.
Musamman idan na 2na rywr baya yadda zan
hantara inyi tsawa a aikata min koda ba‘a so
sai gashi yau wanda zan yiwa magiya yayi min
ma babu shi a kusa.

Nayi wani spring ta gefe na koma zaune
hawaye wadanda suka zama sabo na suka
gangaro min, na zuba tagumi na rasa abnd
kemin dadi a duniya.
Dai-dai lkcn ne FARUK ya dawo daga inda ya
shiga izuwa dakin fuskarsa tayi saurin canjawa
ya bini da kallo, jimawa kadan yace
“HUMAIRA!!“
firgigit nayi kmr wadda ta farka daga barci
muka hada ido, kll daya nayi masa nasan ba
yanzu ya dawo ba nayi saurin goge idanuna
nace “Uhum!! dama ka dawo??“
Lfy?? meye ya faru kuma??
ya tambaya yana dubana.
na girgiza kai nace
“uhm..uhm ba komai meka gani??“
Ya tako a hankali yace “koda banga hawaye a
idonki ba kll daya zanyi miki nasan da wani
abu, abin mamakin min2na 15 da suka wuce
ma dana shigo barci kike yi ko kinyi wani
mummunan mafarki ne??“
Na girgiza kai alamar a‘a.
Ko don ban dawo da wuri ba??
Sake tambaya yana dubana.
Nayi saurin sake girgiza kai a karo na biyu.
ya bini da kll da fadin “meye ya faru to??“.
na dan kauda kaina a hankali nace “ba komai.“
na fada idona nakan robar ruwan data fadi 2n
dazu, faruk yabi inda idona yake da kll idonsa
yakai ga inda take ya kalleni ya kalli robar tare
da takawa ya daukota, ya dawo inda nake da
fadin “mu2m najin kishirwa yana ganin ruwa
ya gaza samu abin da ciwo kam.
Ya zauna a tebirin dake gaf da gadon muka
yadda zamu fuskanci juna sosai ya juya ya
dauko kofi ya tsiyaya min ruwan tare da miko
min, ba gardama kuwa na amsa tare dakai
kofin bakina na zuke ruwan.
yace “abinda yasa ya fada kasa wai yanayi
miki nuni da cewa na shigo ne, wanda
yakamata ya baki da hannunsa ya shigo don
me zaki wahalar da kanki don Allah ki bari
faruk ya baki da hannunsa. abinda naji robar

na fada kenan yanzu dana daukota.
Duk da gun2n hawayen dake idona saida nayi
murmushi har dariya ta kwace min.
hmm... me kwantar da hankali yayinda ya
tashi kenan.
Ya gyara zama yace “idan kina kuka ko sai in
rinka ganin kamar ba humairar dana sani a
baya bace, HUMAIRA y‘ar kwalisa me jin kai
da girma da martaba komai nata da isa take
yinsa, ga taurin zuciya da juriya komai na
kasaita ne.
Bata taba karaya bare har tayi kuka
hawayenta su zuba, me yasa kika canja????
Na bishi da kll kawai nace “rayuwa ce ta canja
ni sbd naga abubuwan AL‘JABI masu yawa da
suka koya min darasi a rayuwa wanda indai
zan rinka 2nasu hawayena ba zasu daina zuba
ba har abada.“
Zasu daina mana.
Ya fada tare da cewa “Dole sai kin manta
abinda ya wuce zaki samu nutsuwar fuskantar
abnd zai zo a gaba, kefa daban ce kuma
babba ce, mahaifinki babban dan kasuwa me
arziki ma2ka, ke kuma kina da baiwar ilmi,
fahimta da alfarma me yawa.
Na kada kai nace “OK na zaci girman ta
bangaren hikima, hazaka, tausayi, alkawari da
amana kake nufi dasai ince sai dai kai!!
Domin kai sai bayan shekaru ashirin ake sake
haihuwar irinka a duniya.(hmm anya kuwa
koni abdool aina fishi.)
Ya dan daga gira kadan tare da mikewa yadan
taka, nace “ina zuwa??“
Ya juyo tare da cewa “zan shiga kitchen baki
ga nayi dress din girki.“
nabi y‘ar karamar rigar dake jknsa da kll hade
da wando wanda da kadan ya wuce gwiwa, irin
kayan nan ne masu yanayin jersey da basu da
nauyi sai P-CAP dake sanye akansa 2n daga
sama har kasa duk launin yellow ne dasu nayi
murmushi nace “To a fito lfy amma ka tbbtr
ka kula da wuka sbd tana da kaifi, snn ka kula
da wuta sbd tana da zafi.“

Ke kuma ki kula da ruwanki sbd kada ya kara
fadowa. Ya fada tare da juyawa.
Nabishi da kll kawai nadan kada kaina dariya
ta kwace min.
Ya yaje bakin kofa sai kuma ya juyo tare da
takowa yace “my queen me kike sha‘awar ci
ne yau??“
kmr bazan ce komai ba sai kuma nace “Fried
rice idan ka iya.“
Yadan kara takowa a hankali tare da
maimaitawa “fried rice! fried rice!! kai gsky.....“
Rabu dashi kawai kayi koma meye.
Nayi saurin fada. Ya girgiza kai tare da cewa
“ba za‘ai haka ba 2nda shi kike so to sai mun
cishi yau, abnd za‘ai ba dake zamu je kitchen
idan ni ban iya ai ke kin iya, sai zama director
kina zaune a kekenki na sarauta kina bada
umarni.
Daga yau kinga nima sai na kara ilmi ko??
Ya karasa fada sanda ya karasa inda kekena
yake ya 2roshi dai-dai bakin gadon.
Haka kuwa akai a hankali ya 2rani bisa keken
izuwa kitchen muka fara aiki.
Ina daga zaune ina yi masa nunin abubuwan
dazai hada don yin fried rice ckn nutsuwa, idan
bai gane bama 2rani yake har inda abin yake
nayishi da kaina. A haka har muka gama
hadawa tare muka dawo izuwa falonmu.
Irin wannan shine taimakon kanmu da kanmu
da mukeyi kuma muyiwa kanmu komai ba
wanda yakeyi mana.
Kwanaki nata zuwa suna shudewa sannu a
hankali, kulawa daga faruk babu alamun
raguwa saima karuwa a koda yaushe.
**BAYAN SHEKARA DAYA**
zai yiwu bazai yiwu ba, zamu jure ba zamu
jure ba, zai iya faruwa ko bazai iya ba da
wasu keta cece-kuce duk sai yazo ba yadda
da yawan mutane suka zata ba.
sai da muka shafe tsawon shekara daya cif a
haka yadda muke.
Abin sha‘awar babu korafi ko canjin yanayi a
tare damu sai ma karin karfin gwiwa da muke

samu da kuma tbbs soyayyarmu da tbbs na
rayuwa tare har abada.
Wato mun riga mun zama daya na zama faruk
ya zama ni domin idan na fahimta dai-dai ko a
fuska kamanninmu sun juye sun zama daya.
dangane da larura ta A kllm jina nake akwai
alamar sauki a tattare dani sai dai bana yarda
da hakan, a yanzu ina jin cewa akwai kafafu a
jikina sabanin baya.
A kllm kuma sai nake jin suna kara karfi har
nakanyi 2nanin me zai hana na gwada mikewa
amma idan na 2no da gargadin likita acan
baya sai na hakura.
Abinda na tbbtr shine akwai ranar da zata zo
zan mike na tafi akan kafata don na dade da
fara jin alamun haka.
*Kamar kllm yadda ya saba fita misalin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login