Showing 21001 words to 24000 words out of 47324 words
wannan ba ni faruk ko kasa ya kawo
min zan dafa mana mu ci.“
Bawai daddy ba har momi sai data dago kai a
firgice, daddy yayi saurin duban momi yace
“wai yarinyar nan da hankalinta kuwa??
Anya talakawan nan ba asirceta sukai ba??“
Na girgiza kai nace “bawai asiri bane hakan na
nuna zunzuru2n SON da nakewa faruk.
na durkushe bisa gwiwoyina na canja izuwa
ynyn da dole a tausaya min nace “Daddy don
grmn Allah ka taimaki rayuwata wlh faruk
nake so domin ina da tbbs akansa kayi min
komai 2n daga kuruciya har izuwa girmana
wannan shine abu na karshe da zaka samar
min wanda zan cgb da rayuwa ckn farin ciki
har abada, FARUK bashi da wani aibu na
yarda kayi duk binciken da kake so akanshi
indai ka samu aibu tare dashi nayi alkwrn zan
hakura.“
Daddy ya gyara zaman bakin glass din dake
idonsa yace “bincike??“
yayi nuni da hannunsa da cewa “Talaka har
yana bukatar wata ne?? Halin talaucin da yake
ciki kadai ya isheshi hujja, Bansan sanda kika
lalace haka ba kika manta ko y‘ar waye ke!! to
idan ke baki da hankali ni bazan biye miki ba.
Ranar auren y‘ata ina saran shugaban kasa
da kansa zai halarta, gwamnoni, sanatoci, yan
majalissu uwa-uba manyan y‘an kasuwa a
kasarnan zasu halarta kawai sai ace ina ango
aga wani talaka ya shawo kwana??
Kema kinsan bazai yiwu ba akwai masu sonki
da yawa y‘ay‘an gata ki zabi wanda kike so a
cknsu amma dole ki hakura da wannan FARUK
din.“
Ban taba sanin daddy haka yake ba sai yanzu,
a wannan lkcn ji nake duk duniya ba wanda
yakaishi rashin imani, zuciyata tayi harzukar
dana kasa dannewa na mike kawai nace “ni
kuma bazan rabu dashi ba kuma bazan auri
wani ba face shi ma2kar dai ina numfashi a
dorôn kasa, hakki nane a barni na auri wanda
nake so tunda bashi da wani aibu, hawayen
idona ya karasa zubowa ckn sheshshekar kuka
nace “wlh ko a kotu saina kwaci hakkina ba
wanda ya isa yayi min auren dole!!!!“
Na juya nabar falon, daddy yabini da kll tare
da mikewa, momi da bata tsoma mana baki ba
tace “amma Alhaji....“
Ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu
yace “tace ba wanda ya isa ko? ya kada kai
yace To zata ga isar tawa.“
Ya gyara babbar rigarsa ya wuce dakinsa.
*Daga ranar komai ya sake sakwarkwacewa
dady ya shiga amfani da damarsa da krfnsa
wajen rabani da faruk.
sai da takai ya hana faruk zuwa gdnmu, kullin
da yayi na cin mu2ncin iyayen faruk yasa
shima suka masa lamba akan lallai sai ya
rabu dani.
Soyayyarmu na karuwa kalubale na daduwa,
takaicin safe daban na rana daban na dare
daban.
Soyayya nada koguna da yawa nikam na
ruwan zafi na fada, ga tarko ya rike min kafa
hagu da dama na rasa yadda zanyi na kwance,
sama da sati daya ko a waya na daina samun
FARUK hakan ya gigitani ma2ka har sai da
takai abinci ma ya gagareni ci duk na rame
tamkar bani ba, rayuwar da ban taba zaton
zata juya min ba.
Cikin bakin ciki kmr yadda na saba nake zaune
a yau ma, zaune nake ni kadai a tafkeken
kayataccen falon gdnmu wanda yanzu ya
zame min tamkar kurkuku na zauna bisa
doguwar kujera dan karamin filo na dora bisa
cinyoyina tare da dafashi sbd 2nani idona ma
baya kiftawa hankalina 100% baya jikina.
Dafa nin da momi tayi yasa nayi firgigit
tamkar wacce ta farka daga barci nabi momi
da kallo da jajayen idanuna tamkar gauta,
nasan danniya kawai takeyi ita kanta amma
abin ya dameta.
Ta zauna tace “Humaira me yasa kike
hakane??
Kefa ba karamar yarinya bace da zaki mayar
da kuka mafi tasiri akan komai naki.
wannan 2nanin da kike yawan yi baki san
babbar illane a gareki ba??
Akan hakan gara kiyi addu‘ar Allah ya zaba
miki abnd yafi alheri.
Momi in auri faruk kawai shine alheri.
Tabini da kll tace “FARUK!! FARUK!!! FARUK!!!!
Kllm maganarki kenan???
Uhmmm nima allah ban wadda xatasoni
kaman haka..koda wata tacemin she love me
morther dt bet amma bataso wai asan tana
sona agidansu..its a true love..?lolxxx
AJABI part 13
NA ABUBAKAR A.MUH'D
tare dani--->Aßu Fer'ezerh
Duk maganar da za‘ai dake sai kinyi kokarin
dangantata da FARUK??
zaifi yi miki kyau ki hakura da soyayyarsa...
Fuskar momi ta canja ma2ka irin yanayin da ban
taba gani ba tace “amma Alhaji rashin tausayin
da rashin imanin yayi yawa wlh, a ina aka
taba....“
DAKATA!!
ya fada sanda canja fuska, yace “ince dai y‘ata
ce ko??
nina haifeta??“
Auren dole fa kake shirin yi mata!! Haka na
gadama.
Daddy yayi saurin mayar da martani. Nabi daddy
da kll wasu hawaye masu zafi tamkar
tafashashshen ruwa suka gangaro bisa kuma2na,
na mike muryata na rawa nace “Kayi zabinka da
kake ganin yayi maka, amma hkn ba lallai ya
zama zabin ubangiji ba wanda zabinsa shine
mafificin zabi don haka har yanzu banji a jkna na
rabu da FARUK ba.
Na taka a hnkl izuwa dakina.
Momi Ta kada kai tare da cewa “wannan matakin
naka Ba komai kake sonyi ba face cutar da ita
wlh, ta tashi 2n daga kuruciya bata san meye
takaici ba bata san meye damuwa ba lkc guda
kana kkrn tusa mata su toka sani idan humaira
ta haukace karka zargi kowa face kanka,“ Ya
hade rai yabita da kll kawai ya doka tsaki ya
koma kan kujera ya zauna ya zaro jaridarsa ya
fara karantawa.
*A kwana a tashi kwanaki sai kara matsowa
suke, Abu kmr wasa yana nema ya zama gaske,
ckn kankanin lkc zance ya karade ko‘ina cewar
bikina saura y‘an kwanaki ai kuwa duniya ta
dauka kmr guguwar yaki.
Ban kara tbbtrwa abin gaske bane sai da ya rage
sati daya, wasu akwatina dana iske sunyiwa
falonmu tsinke da ni kaina bansan adadinsu ba
aka ce wai kayan lefe nane, hakan ya girgizani
ma2ka lallai daddy da gaske yake.
Kmr a mafarki haka nake ganin abin gashi kuma
yana nema ya tbbt gaske, kuka 2n hawaye na
zuba har sun daina ma zuwa.
Ba komai nake hangowa ba sai rayuwar da zata
zo min a gaba ta shekaru masu yawa da zanyi
ckn takaici da damuwa watakila na har abada,
abinda na dauka shine aure shine last distination
na duniya a wurin mace walau ta dace da
rayuwar farin ciki ko takaici na har abada.
Illolin mace ta auri wanda bata so sun wuce a
misaltasu, a yadda nake jin tsanar TIJJANI wlh a
duniya ma bana son ganinsa yana rayuwa ina
kuma ga ace mu zauna har abada???
Wadanda ke waje basu san meke faruwa ba gani
suke ai hadin ya dace har tayani murna akeyi ta
waya, ciki harda wadanda bansansu bama abnd
ke kara min takaicin kenan.
Wasu ma ganin da suke yi ni na juyawa faruk
baya sbd dan uwana me kudi yazo, dadai sauran
zan2ka ire-iren wadannan.
ba wanda yasan gskyr abinda ke faruwa sbd ba
wanda na sanarwa, abune da nake zaton cewa
nafi karfinsa yazo yafi karfina, abnd nake ganin
bazai yiwu ba yake nema ya yiwu.
Lkcn daya rage saura kwanaki uku sai ya zamana
duk gdn T.V ko radio daka kamo ba sai ka samu
ana sanarwar DAURIN AURENMU, jaridu da
mujallu duk an baza gari ya dauka auren y‘ar
gata AISHA HUMAIRA ISMA‘IL yazo, harabar
gdnmu har ta fara cika da mutane anata kafa
runfunan alfarma na manyan baki da kanana.
a dai-dai sanda ya rage saura kwanaki biyu da
safe ina kwance nayi nisa a duniyar 2nanin dana
saba ban sani ba ashe mufida tazo ta shigo har
dakina kuma ta zauna ban sani ba, ta dade tana
kllna sannan ta tabani da cewa “KE“.
Na kakalo yake wanda yafi kuka ciwo nace “Ah
mufida yaushe kika zo??“
Ta bini da kll kawai tace “HUMAIRA 2nanin me
kikeyi haka??“
Nayî kasa da kaina kawai zuwa ca na girgiza kai
tare da cewa “ba komai“.
Karyane wlh, ta fada tare da dorawa da fadin
“Naji sanarwar aurenki rana tsaka, kuma abin
mamakin da wani me suna tijjani ina faruk din
kuma?? nidai a sanina shi kike so.“
Nayi kokarin hana hawayen da suka taho zuba
amma na kasa, “bakisan abnd ya faru ba??“
na tambayeta.
Tayi saurin mayar min da amsar “Na sani amma
zatona ke kika canja ra‘ayi da kanki don banyi
zaton duk duniya akwai me tilastaki ba.“
Na girgiza kai nace “Daa kenan amma yanzu ta
canja daddy ya daina kaunata ya tsaneni yafi son
mu2 da bakin ciki akan na rayu.....“
Tayi saurin rufemin baki tare da rike hannuna ckn
nata tana me grgz kai tace “karki ce haka, may
be a ganinsa gata yake sonyi miki, addu‘a
yakamata kiyita yi kawai a yanzu amma ba kuka
ba sbd ba maganin dazaiyi miki a ynzu.“
taci gaba da tsara kalamanta wasu na gane inda
ta dosa wasu ma na kasa ganewa har dai mukaî
sallama.
y‘an min2na wayata tadau ringing
Na jawota a hankali nayi arba da sunan TIJJANI!!
me kuma ya bugo ya fada min??
kmr bazan daga ba amma Na daga tare da kaita
kunnena, dariyar da yayi ce ta fara dukan
kunnuwa na, yanzu fa kin hakura ko har yanzu
kina da ja??
abnd ya rage dai bai fi awanni 48hrs ki tbbt
amaryata“.
Duk yadda naso na danne kuka na sai daya fito,
tijjani yayi dariya yace “irin dan kukan nan na
al‘ada a gurin amare ba sbn abu bane“.
Amma kai mugu ne wlh ba tausayi ko imani a
zcyrka ko kadan, Ya kara fashewa da dariya na
saki wayar ta fado bisa katifar makeken gadon da
nake kai, nayi ruf da ciki kawai na rufe idona
sautin kukan ma baya fitowa.
Tsawon lkc na kwashe a haka har sai da wayar
dake kusa dani ta sake daukan sabuwar kara,
Nayi wata irin dagowa a fusace na warto wayar a
zatona tijjani ne sai kuma fuskata ta canja.
Faruk ne nayi saurin dagawa tare da kaita
kunnena sautin sheshshekane kawai ke kaiwa da
komowa, dakyar nace “faruk shikenan mun rabu
ko??
ki jirani zanzo har gdnku yanzu.“
A firgice na dago kirjina ya buga da karfi, gdn
suwa?? karka zo zasu cutar dakai fa!!
FARUK!!
sai dai ina! tuni ya kashe wayar.
Ina ckn frgbr ne kasa da min2na ashrn naji
hayaniya na tashi a hrbr gdnmu, na tbbtr shine
bansan sanda na zabura da gudu na fita daga
dakin ba maimakon na nufi wajen rikicin amma
ba dama kai tsaye saman bene na nufa na tsaya
gaf da farfajiyar saman ina hangen abnd ke
faruwa.
Turewa, hantara harma da dukan da daka-dakan
samari majiya karfin suka farmasa ne yasa na
dafe bangon dake kusa dani ina me miko hannu
hawaye na kwarara daga idona, Tausayinsa yai
bala‘in kamani.
Faruk me yasa kazo?? Nayi tambayar badon a
bani amsa ba.
Da yake umarnin da aka basu kenan a knknn lkc
sukayi masa lilis!!
Wani layi da naga yana yi ne ya kara rikitani
karfa su kasheshi, zuciyata ta fada min.
nayi wata irin juyawa da gudu na biyo hanyar da
zata sadani izuwa inda abin ke faruwa sai dai
bisa tsautsayi dora kafata bisa matattalar benen
keda wuya na zame tare da rikitowa 2n daga
kololuwar saman benen zuwa kasa......Zamewar
ce tasa ba shiri na rikito gadan-gadan izuwa
kasa, a maimakon na mirgino ta matattakalar sai
jikina ya zamo nayo kasa kacokan. Tazarar dake
tsakanin kasa da sama nada yawa na kwarara
uban ihu wanda shine iya abinda na sani ban
kara bude ido ba sai a gadon asibiti.
Awanni masu yawa ne suka shude ina ckn yny na
suma, lktci sunyi nasarar ceto rayuwata daga
halaka bayan tsawon lkcne kuma na farfado.
A hankali idanuna suka bude tamkar wadda ta
farka daga barci ni kaina abinda ya fara fado min
kenan barci nayi, nayi saurin karasa bude idanun
nawa a sanda na tbbtr nan ba inda na sani bane
a ina nake meya faru dani??
Nayi yunkurin tashi naji an danneni a sannan ne
nabi inda nake da yanayin da nake lkc guda duk
abinda ya faru ya fado min, Na dubi kafafuna
dake mike a dai-dai gwuwoyina ansa wani
kurunbon roba daban san ko meye ba.
Sai fuskata dake kunshe da ciwuka na kujewa
dama sauran sassan jikina, Na daga kaina mukai
ido hudu da momi sai kuma MUFIDA dake zaune
a gefena.
bana jin bakina zai iya furta komai hakan yasa
banma yi yunkurin cewa komai ba, naci gaba da
jujjuya idanuna ina kallon faffadan dakin asibitin.
A wane hali faruk ke ciki kada dai ace sun
kasheshi?? Abinda yayi saurin fado min kenan,
Wasu hawaye suka gangaro min.
budewar da kofar dakin tayi da saurine yasa
muka kalli hanyar shigowar daddy ya fado a
firgice, nayi saurin dauke kaina daga kllnsa.
Ya karaso inda nake yana ganin yanayin da nake
ciki ya dafe kai tare da doka salati ya juya ga
momi a rude yace “wane hali ake ciki??
me likitan yace muku??
momi ta girgiza kai tace “Ba abinda ya fada
mana yadai ce kawai idan kazo yana son
ganinka.“ Inna-lillahi wa inna ilaihir-raji‘un.
Daddy ya sake nanatawa ya gyara zaman babbar
rigarsa tare da juyawa ya wuce izuwa ofis din
babban likitan dake kula da sashen.
Zaune lukutin bakin mu2min yake yasa faffadan
tebirin dake gabansa a gaba sai rubuce-rubuce
yake, shigowar da yaji tasa ya dago kai.
Sannu da zuwa Alhaji ya fada tare da mikewa don
girmamawa.
Doctor wane hali yata ke ciki?? meya sameta??
fuskar likitan tayi saurin canjawa ckn nuni yace
“bismillah Alhaji zauna“
Ya fada dai-dai sanda shima ya zauna.
Koda daddy baiso ba dole tasa ya zauna a
kujerar dake fuskantar likitan ckn tsananin
zakuwa da son jin abinda zai fada masa.
Likitan ya gyara zama yace “Alhaji kasan ita
fadowa daga sama irin wannan na zuwa da
abubuwa daban-daban wani lkcn a sami karaya,
rauni koma a rasa rai dungurungum.
Anyi sa‘a bata rasa ranta ba ba kuma a samu
karaya ko daya ba, hakan ya farune sbd sanda
tazo kasa da gwiwa tazo shine yasa....“
Shine yasa me.....
Daddy yayi saurin tambaya a firgice.
Likitan ya gyara zaman farin gilas din dake
idonsa yace “ Kasan a yadda gwiwa take ita ke
daukar dawainiyar iya taka kafa gaba daya ko
kuma iya karyata a zauna daidai sauransu.
Magana da gsky kokon gwiwarta dukkansu sun
sami matsala munyi kokari mun dai-daitasu daga
gocewar da sukai amma sunyi sanyi ma2ka sbd
buguwar ba y‘ar kadan bace hakan yasa zata
dau dogon lkc bata iya taka kafarta kamar yadda
kowa yake yi ba.
Doc..tor me kake...nufi ne??
Daddy yayi saurin tambayar.
Abinda nake nufi shine a yanzu kafafunta basu da
maraba dana karamin yaro don haka za‘a dau lkc
bata iya taka su ba.“
Ckn kallo me kama da harara daddy yace “kada
dai kace min ta zama gurguwa??“
Kayi hakuri alhaji amma ta zama, sai dai kawai
na wani dan lkcne zata dawo taci gaba da tafiya
kmr kowa.
Daddy baisan sanda ya cire hular dake kansa ba
ya sake doka salati tare da goge gumin dake
kwaranyo masa ya matso gbn kujerar tare da
dafa tebirin dake tsknnsa da likitan yace “doctor
yanzu ba yadda za‘ai?? kasan kudi ba matsalata
bane ko nawa ne zan iya biya kada ta zama
nakasashshiya doctor.“
Wannan ba magana bace ta kudi 2nda kokai
nasan baka taba jin inda akai dashen gwiwa ba,
dole sai dai ayi hakuri ba abnd za‘a iya yi kuma
duk inda kaje ina da tbbcin haka abin yake.
Kuma da yake ynyn larurar tata ba wadda dole
jinyarta sai a asibiti bane nan da wasu y‘an
awanni idan komai ya dai-daita muna iya
sllmrku.
ku koma gida aci gaba da kula da ita a kula kada
ku sake tayi yunkuri na taka kafar sbd a yanzu
kafarta tamkar ta jariri take.
Daddy ya dago tare da dafe kai yace “ynz
shikenan ckn y‘an awanni y‘ata ta zama
gurguwa???“
Sai dai hakuri.
Likitan ya fada.
A sanyaye daddy ya dawo dakin da muke, ina
kwance nabi fuskarsa da kll har izuwa sanda ya
zauna yaune karon farko da naga hawaye a
idonsa.
Kmr yadda likitan ya fada haka kuwa akai domin
a ranar aka sllmemu, abnd yafi bani mamaki
shine nidai bana jin wani ciwo a kafata sai dai
kawai ji da nake tamkar kafafuwan ba ajikina
suke ba.
Ko kadan bazan iya motsa su ba, KADDARA
kenan idan tazo babu me iya canjata kasa da
awa 12 na zama gurguwa.
Rayuwa ta kara juye min bangare mafi baki da
muni, na shiga kangi na bala‘i da masifa da ko a
mafarki ban taba 2nanin zan shigesu ba.
WASHE GARI tijjani yazo har gdnmu ko dakina
inda nake bai karaso ba a falo ya zauna anan
daddy yazo ya tarar dashi ya zauna tare da cewa
“TIJJANI kaga abnd ya faru ko??“
Wlh naji Alhaji.
Ya fada fuskarsa a daure, babu alamun walwala
tare dashi.
Daddy ya gyara zama yace “amma KADDARA baki
iya zuwa ba, um-u-um!! yanzu ya za‘ai tijjani??“.
Game da me fa??
Ah game da harkokin bikin nan mana kasan
duniya ta gama sanin gobe ne ga manyan baki
sun hallara an gama shirya komai bai kamata ace
anji kunya ba.“
Ban gane ba Alhaji.
Tijjani ya fada.
Daddy ya gyara zama tare da matsowa gab da
kujerar ckn kasa da murya yace “a bari a daura
auren nan idan yaso koda tarewar ne sai a daga
ya zama dai an fita kunya...“
Allah ya kiyaye!!
Tijjani ya fada tare da dorawa da fadin “wani
zancen aure gsky a barshi Alhaji me za‘ai da
HUMAIRA bayan ta zama NAKASASHSHIYA?????“
hmmm ALLAH YASA KUNA KARANTA SHIRINMU
NA "BANBANCIN SHA'AWA DA SOYAYYA"wata
kila kugane meyasa tijjani keson humaira
uhmm allah hadamu damasoyanmu nagaskiya
badon wani abu namuba..!
Dan samun posting dinmu akodayaushe
sekashiga blue rubutunnan kayi like(y)
Like(y)ßADI ßA RAI.
Tijjani yacigaba da cewa Ina dai jajanta maka
na
abnd ya samu y‘arka amma ba2n aure babu