Showing 24001 words to 27000 words out of 47324 words
gsky ba yadda za‘ai kamar ni ace na auri
gurguwa, da harkokina zanji ko kuma da
jiyyanta?
Kafin na taho munyi magana da dad dina
kuma ya fadawa da duk wadanda a
bangarenmu muka gayyata cewan an fasa
bikin nan.
An fasa??
Daddy ya tambaya ckn kaduwa.
kwarai na hakura da ita don bazan iya zaman
KADDARA ba, daddy ya kara sanyaya murya
yace “haba TIJJANI abin fa ba wani me muni
bane likita ya tbbtr min zata dawo normal ckn
y‘an lkt kankani.“
Tijjani ya mike tare da cewa “Alhaji kaga
tafiyata, na isar maka da sakon daya kawoni.“
Ya gyara zaman suite din jikinsa ya juya ya
nufi hanyar ficewa duk da kiran da daddy ke
masa TIJJANI!! TIJJANI!!!.
Amma ina! ko alamun waiwayowa baiyi ba
dai-dai lkcnne nida momi muka fito ina zaune
bisa keken guragu irin na zamani a hankali
momi ke 2rani har muka karaso tsakiyar falon
momi tabi kofar fitar da kll ta dawo da kllnta
ga daddy tace “Tayaya kake tsammanin zai
dawo??
Bayan dama ba don Allah yake sonta ba??
Koda ma ace anyi auren idan kaddara irin
wannan ta sameta juya mata baya zaiyi!
Amma abin tambayar me yasa shi mahaifinsa
ya ki tilasta masa ya aureta a haka??
Shi ya manta amincin dake tsakaninku??
Na tbbtr yana sane amma zai iya danne
wannan ya nunawa dansa syy abnd kai ka
kasa yi kuma ka kasa ganewa kenan.“
daddy ya 2nbuke hular kansa ya jefata kan
kujera gaba daya ya rikice dakyar ya karasa
kujerar da tafi kusa dashi ya zauna ya dago
kamar ya fashe da kuka yace “kinga shugaban
kasar CHAD yanzu haka ya sauka a hotel
kuma don daurin auren nan yazo, banda
wadanda suka 2ro wakilansu, ga sanatoci ga
gwamnoni banda abokaina manyan y‘an
kasuwa na duniya duk sun hallara abin
kunyane na 2nkaresu da maganar an fasa
bikin nan, inna-lillahi wa inna-ilaihir raji‘un....“
Yakai maganar dakyar.
Hmm... Zaune kawai nake ina binsa da kallo
bama ta tawa yake ba ta yadda zaiyi ya fita
kunya kawai yake, ba a wanne hali nake ciki
ba.
Hankalinsa ya tashi ma2ka fîye da ko yaushe
sbd abnd baiyi zaton zai faru ba ya faru,
Amma ni a wurina hkn yafi yaimin don gara na
tbbt a yanayin da nake ciki da na auri tijjani.
o-o-ooo!! Ina zansaka raina???
Daddy ya sake fada kamar zai rushe da kuka
don takaici.
Budewar da kofar tayi da karfi yasa duk
hankalinmu ya koma gareta, kamar daga sama
FARUK ya fado da saurinsa caraf muka hada
ido dashi duk da a yadda yake ba‘a farin ciki
yake ba amma bai hana annuri tashi daga
fuskarsa ba.
Yanayin tfyrsa ya canja ya fara takowa a
hankali muna klln juna.
Nayi saurin cewa “FARUK meya kawoka?? me
kazo yi??
Kayiwa Allah ka juya ka tafi karka yarda ka
kara kusanto inda nake sbd ni yanzu bani
kadai bace tafe nake da rakiyar KADDARA,
yayinda BALA‘I da MASIFA ke take min baya.
Yayi saurin girgiza kai yace “Ba wata kaddara
da zata iya sawa na gudu na barki, karki
manta Alkawarinmu na kasancewa a tare duk
tsanani duk wuya.
Da ace ba wata masifa da zata iya riskar dan
adam toda har abada ba za‘a taba iya gane
masoyi na hakika ba, sai kaddara ta afku ne
kawai ake iya gane soyayya ta zahiri da kuma
ta karya don haka yanzu ne yafi ko yaushe
cncnta na nuna miki soyayya.“
Na daga kaina sama wasu sanyayan hawaye
suka gangaro min, ya tako izuwa inda nake ya
durkusa ya dafa keken da nake kai yace
“Sannan idan zaki 2na na taba gaya miki cewa
ba ina sonki don wani abu naki bane ko don
moruwar wani abu daga gareki, ina sonki ne a
matsayinki na humaira kuma zanci gaba da
sonki har abada.“
Ya mike tare da duban daddy yace “Idan har
ka amince ni zan auri HUMAIRA a haka, zan
zauna da ita domin bazan taba guje mata ba
har abada.
Babu bukatar duniya tasan abnd ya faru da ita
bare makiyanmu su sami bakin yi mana
dariya.
Fuskar daddy tayi saurîn washewa, wani sbn
annuri ya saukar mata ya mike tare da cewa
“Lallai faruk ba‘a banza ba humaira ta yarda
da kai yau na gani da idanuna don nayi imanin
ko ni ban fika son humaira ba, laifi nane da
nayi yunkurin hana abnd Allah ya kadarta.
Nagode da kayi yunkurin rufa min asiri da
kuma masoyiyarka.
Lallai samun masoyi kamarka za‘a dade ana
tonawa.“
Faruk ya gyara tsayuwa yace “Don na rufawa
HUMAIRA asiri ba wata bajinta nayi ba domin
kaina nayiwa.“
Daddy ya gyara babbar rigarsa yace “idan
kuwa har kayi min haka nayi Alkawarin baka
dukiya me tarin yawa kuma zan dauki
nauyinku kai da ita ba abnd zaku nema ku
rasa.“
Faruk ya girgiza kai yace “bana bukatar komai
daga gareka indai akan HUMAIRA ne sbd daga
ranar da na samu humaira hakkin kula da ita
da samar mata da farin ciki akaina yake kuma
dole na saukeshi.“
Daddy yayi saurin cewa “uhm!! kaji masoyin
gaske masoyi na hakika yanzu kai kana ganin
a shirye kake??“
Faruk ya gyada kai yace “kwarai kuwa!! abinda
kawai nake so a dauke daurin auren daga
gobe a matsar zuwa jibi idan zai yiwu.“
Ah! kwarai kuwa sosai ma!!
Don dai kwana daya kawai??
Faruk ya kada kansa tare da juyowa muka
kurawa juna ido, ni kaina ya bani mafi girman
mamaki a yau, domin duk yadda nake hango
HALACCIN faruk ya wuce nan.
DAN HALAK farar fuska farar zuciya.
Har yanzu hawaye ke kwararowa daga
idanuna har na fara hango yadda sabuwar
rayuwarmu zata kasance duk da cewa bata zo
mana a yadda muke so ba.
Ya goge hawayen dake idonsa har ya taka
izuwa bakin kofa sai ya juyo yace “kayi hakuri
amma Sai kasa an kwashe wadancan
gardawan banzan daka tara a bakin gate
izuwa asibiti sbd ta karfin tsiya na bigesu na
shigo nan.“
daddy yayi saurin gyada kai yace “KARKA
DAMU KAYI DAI-DAI.“
Ya juya tare da yimin klln karshe ta wani irin
salo kmr zaiyi magana amma sai ya fice, nabi
daddy da kll na durkusar da kaina na fashe da
kuka kmr raina zai fita.
Kukan na abubuwa da yawa ne da suka
cunkushe zuciyata, ko yunkurin rarrashina ma
ba wanda yayi zuwa jimawa MUFIDA tazo a
lkcn ina daki ta zauna a falo momi ta zayyane
mata duk abnd tijjani ya fada da tsananin
mamaki ta dago kai tace “amma TIJJANI anyi
tsinannen mu2m mara mu2nci da bashi da
imani a zcyrsa, ynz momi shikenan komai ya
rushe???
Ta girgiza kai tace “FARUK yazo kuma yace
yaji ya gani ya amince ba abnd za‘a fasa, sai
dai nifa ina jin tsoron al‘amarin nan sosai.“
MUFIDA tadan yi gun2n murmushi tare da
girgiza kai tace “babu abin tsoro momi, 2nda
nake ban taba ganin soyayya irin ta HUMAIRA
da FARUK ba, wlh momi yadda kika san da
son junansu aka haliccesu 2n fil‘azal.
A kyalesu kawai tbbs da abinda Allah yake nufi
a tryyrsu.“
Momi ta kauda kanta kawai ba tare data sake
cewa komai ba, mufida ta mike ta nufo dakina.
Kwance nake na kishingida akan makeken
gadona na zubawa kafafuna ido hawaye na
zuba daga idanuna, mufida tadan rufe min ido
tare da bina da kll tace “haba HUMAIRA meye
haka??
kuka bashi da wani muhimmanci a gareki sbd
bai isa ya dawo miki da abnd kika rasa ba, a
zatona farin ciki zan tarar kinayi Allah ya
kadarta abnd kike buri.“
ckn sheshsheka nace “Dole nayi kuka sbd shi
kadai ne abnd zan iya yi a yanzu, ba haka
naso rywr aurenmu tazo mana ba.“ Shi kuma
Allah haka yaso.
Tayi saurin fada tare da dorawa “Allah na
tsara abubuwansa ne yadda yaso ba wanda ya
isa ya canjasu, amma dai na tbbtr ko a yayane
zakiyi dauwamammen farin ckn zama da faruk
wannan kawai ya wadatar.“ Haka dai kalamai
irin nata na RARRASHI tayi ta jerowa.
*Faruk kuwa isarsa gida keda wuya ya fadawa
wadda take uwa da ubansa kudirinsa da kuma
taimakon da yake so tayi masa, duk da cewa
bata fiya fushi ba amma a wannan karon sai
data canja.
Tabishi da kll tace “A zatona kana da hankali
amma ka canja.
HUMAIRA ce kadai mace a duniya??
ka manta abnd suka yi maka kenan??
sai yanzu da suka shiga wani yanayi sun kada
gabas da yamma basu da me rufa musu asiri
shine suka taho wurinka kai sbd kafi kowa
wauta ka yarda ko??
kai wannan bai zama abin kunya bama a
gareka??
Mutumin nan bakai kawai ya wulakanta ba
harda iyayenka wadanda su zasuyi maka
wakilci su kuma dame zaka 2nkaresu da yarda
su dawo su shige maka gaba??
2n wuri ka cire wannan daga ranka don bame
yiwauwa bane.
Fuskarsa ta canja kmr ya fashe da kuka yace
“amma ummi mahaifinta ne yayi mana laifi ba
humaira ba, ni kuma yanzu humaira nace zan
aura ba mahaifinta ba laifin wani yana shafar
wani ne??
Ta dan zaro masa ido tace “EH yana shafa!
indai ina na isa na fada ka dauka to ka rabu
dasu da y‘arsu idan a jibin kake son auren ni
ina da wadda zan baka gasu nan da yawa
ma.“
Faruk yayi saurin girgiza kai yace “ni
HUMAIRA nake so ita zan aura kota yaya ni
naji na gani 2nda ni zan zauna da ita.“
Ta daga kai sama tace “TO!! tashi daga kasa
ka dawo kan kujera muyi magana 2nda ka
zama abokina.“
Ummi ba haka nake nufi ba amma...
Ta katseshi da fadin “wai Yaushe ka koyi
musu da gardama irin wannan to bani da lkcn
musayar zance akan maganar banza tashi ka
tafi.“
Dole tasa ya mike ckn nuni da hannu yace
“don Allah ummi ki.....“
Ka bacemin nace ko??
Ta katseshi.
Ya saki hannunsa kawai ya bita da kallo
kawai.
“Allah ya wuci zcyrki.“
Ya fada sanda ya wuce izuwa sashinsa,
bangarene me zaman kansa da falo guda gefe
guda kuma ga dakinsa gdn nasu dai-dai
gwargwado na rufin asiri ne.
Ya zauna jim kadan ya zaro wayarsa ya lalubi
lambar bbn abokinsa NAZIR yana dagawa yace
“kazo gida don Allah yanzu ina son ganinka,
............
Ah lfy kadai zo yanzu.
................
OK sai kazo.
Ya mike ya wuce dakinsa min2na kadan yaji
motsin zuwan nazir yana fitowa nazir wanda
2ni ya dare kujera yace “HUMAIRA!!
HUMAIRA!!! kllm zancenka kenan wai da gaske
kai ahaka zaka aureta...?
Faruk yadan tsaya a hankali ya tako tare da
bata rai yace “Eh a hkn ko zaka hana nine??“
Yayi tambayar sanda ya wuce izuwa karshen
falon ya dauko lemon juice da kofi ya juyo
izuwa inda nazir ke zaune yace “idan
munafuncin daya kawoka kenan ka tashi ka
tafi.“
Nazir ya warto kofin da faruk ya dora a dan
karamin tebirin dake gbnsa ya zuke lemon
cknsa yace “haka akeyi? ka gyyceni kuma ka
koreni??
kawai dai nayi mamakin yadda kayi haka anya
baka nuna rashinzuciya ba??“
Faruk ya grgza kai yace “Nazir ba haka bane
ni HUMAIRA bata taba yimin laifi ba, bada
yawunta, sonta ko yardarta abubuwan da suka
faru suka faru ba hasalima jajircewa tayi sai ni
sbd tana da yakini akaina, don haka idan na
juya mata baya yanzu ita nayiwa ba wani ba.“
nazir ya jinjina kai yace “kazo da zance kaima,
ynz dai me kake so ayi??“
Faruk ya gyara zama yace “So nake pls ka
sanar da kowa jibi daurin aurena kowa ya
shirya ba, nasanka da zafin nama a shirya
komai ckn lkc nasan zai yiwu??“
Ah! kwarai me zai hana?? ai ko gobene
bazamu kasa kintsawa ba bare jibi.
Faruk ya dago yace “Na sani, zan 2ra maka
isassun kudi a account dinka yanzu so nake
komai ya kintsu ckn kwana biyu kmr anyi shkr
biyu ana shiri, ga mukullin nan (ya jefa masa)
na gdna ne nasan kasanshi shima a gyarashi
gyara bana wasa ba a shiryashi a kintsashi
kada ya rasa komai da ake bukata.“
Nazir ya mike tare da sarawa yace “an gama
‘leader‘ yayi kasa da murya yace “amma dai
UMMI fa dole...“
faruk yace “karka damu shawo kanta a guna
bame wuya bane kai dai ka zartar da aikinka
ka barni da nawa ka hanzarta kaga dare ya
taho yi .“
Nazir ya taka kmr zai fita sai kuma ya juyo ya
rike baki yace “um!! gskyne gaf kake da kafa
record fa saurayin daya zama ango ckn kwana
biyu.“
kana gaf da zama MAI GIDA.....
Faruk ya nunashi yace “kai! bana son iskanci,
na.... yayi kmr zai bishi.“
Nazir ya kyalkyale da dariya ya fice da sauri.
Faruk ya koma dknsa.
*WASHE GARI da safe faruk ya fito byn ya
gama duk abnd zaiyi a falo ya tarar da ita
zaune a kujera ya gaisheta ta amsa sama-
sama.
Faruk ya gyara zamansa yace “Ummi gameda
maganar nan ne ta jiya ina so....“
Kace game da maganar banzan nan ce ta jiya,
ta mike tare da juyawa zata bar falon, faruk
yayi saurin mikewa ya tsaya a gbnta ya saki
hawayensa data fi tsanar gani fiye da komai
ya durkushe bisa gwiwoyinsa yace “Don
girman Allah ummi ki taimakeni ki fahimceni,
kin sani ban isa na aiwatar da komai ba sai da
izininki kuma bazan taba bijirewa umarninki ba
domin kece komai nawa.
Ina so nayi wani abu ne guda daya dazai
gyara abubuwa da yawa kuma ya samar da
alkhairai da yawa, ciki harda ladan taimakon
wanda yake bukatar a taimaka masa wanda
kin dade kina kwadaitar dani akan haka,
kinsha fada min na zama me juriya da yafiya a
koda yaushe.
Humaira batayi mana laifin komai ba hasalima
keda kanki yabonta kike kuma itama bata so
akai mana haka ba idan na gujeta a yanzu ba
wani nayiwa ba ita nayiwa, na tbbtr idan na
barta zata shiga kangi da takura fiye da ko
yaushe a rywrta nasan kuma kema ba zaki so
a gujeni don wata kaddara ta fada min ba!!“
Jin tayi shiru yasa ya kara tausasa lafazi yace
“2n ba yanzu ba kin dade kina fada min yadda
karshen rayuwar masu HALACCI, CIKA
ALKAWARI da RIKE AMANA take yin kyau ki
taimakeni na zama daya daga cksu don Allah.“
Ta bishi da kll da alama kalamansa sun
ratsata ma2ka, da dawo da baya izuwa kan
kujerar jim kadan tace “kai yanzu wane shiri
kayi??
Shirina bame wuya bane umarninki kawai nake
jira.
Ina ka shirya kaita to byn auren??
Ta sake tambayarsa.
Ya bata amsa da fadin “Gidan da kika fada
min cewa shima nawa ne dana gada a wurin
mahaifina kuma kika bani mukullinsa da komai
nashi da hnnki can zan kata mu zauna idan kin
amince.“
Shikenan ya zanyi da yin Allah?? Na amince
Allah yasa hkn shi yafi alkhairi.
Fuskar faruk tayi gaggawar washewa yayi
saurin mikewa ya dawo gbnta ya zauna tare
da cewa “Abinda nake so ki fada kenan ummi
nasan kuma zaki amince shi yasa nake
godewa Allah daya bani ke NA GODE sosai
ummina, amma kina ganin su kawu zasu
amince kuwa??“
Ba dole ba??
Tayi saurin fada.
Kaifa maraya ne kowa so yake yayi maka
abnd zaisa kayi farin ciki ko don ya sami lada
ka bari zamuyi magana dasu kaje kawai.
ckn farin ciki faruk ya fita daga gdn.
Hakika abnd Allah ya kadarta faruwarsa babu
abinda ko wanda ya isa ya dakatar dashi.
Da ana SO da ba‘a SO, Ana kuka ko ana
dariya, dole aka daura aurena da faruk a ranar
da lokacin a kuma inda aka shirya.
Ranar da bazan manta da ita ba a rayuwata,
daga waje biki yayi armashi ma2ka sbd ba
wanda yasan halin da ake ciki, kai ko a gdn
wadanda ya zama dole su sani ne kawai suka
sani.
A gdnmu kam naira jknta ya gaya mata, daddy
masu sakin famfon kudi haka kawai ma bare
da dalili.
Kowa yayi mamakin faruk da irin abubuwan da
yayi a sannan ne daddy ya tbbtr faruk ba irin
talakan da yake tsammani bane!!
Washe gari byn komai ya lafa dare nayi aka
kaini gdn faruk, gdn sabuwar rayuwa, gdn farin
ciki, gdn jin dadi da walwala.
Ba wasu mutane masu yawa bane suka rakoni
hakan yasa ba jimawa kuwa kowa ya watse
ya zamana daga ni sai MUFIDA, ina zaune
bisa shimfideden gadon da a yanzu nake jinshi
fiye dana sarauta ma daya zarce na alfarma.
Mufida na zaune sai zuba take ta inda ta
shiga ba tanan take fita ba, da yake uztaziyya
ce a nasihar tata harda ayoyi da hadisai,
maganganun nata na ckn ratsani naji tayi shiru
jim kadan ta mike tare da jawo mayafinta da
jakarta zata fice, nayi gaggawar dago kai na
damko hannunta wasu hawaye sukayi saurin
gangaro min nace “MUFIDA kema tafiya zakiyi
ki barni ni kadai??“
Ta bini da kallo tausayina ya bayyana karara
fuskarta, ta dawo ta zauna gaf dani tace “dole
zan tafi sbd nan gdnki ne ba namu ba, gasu
can a waje ni kadai suke jira mu tafi FARUK
yananan tafe KIYI HAKURI.“
Ta banbare hannunta daga nawa ta fice tana
waigena.
Daga nan sai naji ni a wani irin yanayi, ba
wanda zai zauna??
Wace irin rayuwa na shigo kenan??
Kodai basa sona shi yasa kowa ya tafi??
Tunanin da yayi ta yawo a zcyt a wancan
lokacin..!
Hmm da kina tunanin xasutayaki xamane...
Koya wannnan zaman aure zekasance..? Se ku
biyoni INSHA ALLAH..!
Ina nan zaune ni kadai bisa tsakiyar makeken
gadon da nake kai, jikina na sanye da kaya na
alfarma kaina na kasa kirjina na dukan uku-
uku na rashin sabo.
Sallamarsa da naji tasa naji wata nutsuwa
tazo min sautin muryar tasa ya daki
kunnuwana kai tsaye ya fara zagaye a
kwakwalwata, ban dago kai ba shi kuma baiyi
magana ba ya zauna ta salo na fuskantar juna
ya kura min ido kawai.
Na dan dago kai a hankali na dubeshi nayi
saurin mayar da kaina, yayi murmushi tare da
cewa “yes dago mana ya kika fasa my
AMARYA!!
kodai