Showing 3001 words to 6000 words out of 47324 words

Chapter 2 - AL AJABI COMPLET BOOK HAUSA NOVELS .pdf

Unknown   

15 Jul 2025

3416

daga barci, tab inda take
da kallo kamar wacce ta ganta a sbn waje. Lokaci
guda tayi kokarin goge hawayen dake idont ta
kakalo yake ta maye gurbinsa dashi tace "
Ah....Ahmad yaushe ka shigo??" Ya dan bita da
kallo yace " Humaira kukan me kikeyi??" Tayi
saurin girgiza kai tace " kuka kuma? ni... ba kuka
nake yi....ba." Ahmad ya danyi guntun murmushi
yace " Humair a rayuwa damuwa bata taba buya
domin ita abac da ba a zuciya kawai take zama
ba rubutu takeyi da manyan baki akan fuska
wanda kowa sai ya gani, kuma koda ma tana
buya to ta yiwu girman taki damuwar ta wuce a
boyeta don da zata boyu da kin boyeta. Ya
rankwafo da kansa gareta yace " Me zai hana
bani dama nasan wani abu a rayuwarki, ta yiwu
in da hanyar taimakonki koda da addu'a ne." Idan
kana yiwa Allah ka daina yimin wannan maganar
ba wani dalili da zaka damu sai kasan labarin
rayuwata, Aikine kawai ya hadamu dakai k tsaya
a iya haka ko don tsare mu2ncinka a idona.
Ahmad ya daga kafadarsa kadan yace " 2nda ba
zaki fada min ba shikenan, dama nazo ne na san
dake gobe muhimman kayan aikinki zasu karaso
saiki shirya." ya mike tare da cewa " see U next
time ".
.
Ahmad!! Ta kira sunansa dai dai sanda yake gaf d
ficewa, ya tsaya cak a hankali kuma ya dawo
izuw gabanta. Ta dago kai tace " Don Allah kayi
hakuri kayi min uzuri kwakwalwata ce ba zata juri
tuno dukkan abinda ya faru dani a baya ba, amma
ta yiwu wat rana ka sani." Ahmad ya zauna bisa
kujera yace " Humaira wasu lokutan kunshe abu a
rai cuta ne furtashi kuma warakane, yana da kyau
na rike wani hujja koda guda dayane wadda zan
rika nayi miki uzuri idan na ganki a yanayin dana
ganki yau.," Hawaye suka sake gangaro mata

idanunta suka bude karrr tace " Tunda uwata ta
haifeni ban taba ganin mutum mara yarda ba
irinka, baka taba yiw mutum uzuri? kai kawai
abinda kake so shine a ranka?? To bazan fada
maka ba, tunda baya cikin sharadi abinda dole
sai ka sani kafin ka zauna dashi, idan ka kara
yimin wannan tambayar ba zaka kara ganina ba
har abada. Akan me?? Ta fada da karfi sannan ta
dora " Na zabi nayi aiki ne badon kudi ko don na
samu wani abu ba sbd nafi karfin wannan, sai
don ina tunanin hakan zai rage wani yanki na
damuwa idan kuma kace takurata zakai kake
bijiro min da wata damuwar abu me sauki na
hakura." Takai karshen doguwar maganar tata da
ajiyar zuciya. Ahmad yace " Nida kike ganina
mutum ne me so samun labarai musamnan na
al'ajabi, daga cikin labaran dana samu akwai a
2nanina naki shine za zamo na farko a ban
al'ajabi, baki da wani zabi dolene nasan labarinki
a yau." yakai karshen maganar cikin daga murya.
Lokaci ta kara sauyawa ta hade rai ta kara
fusata gami da harzuka ta kauda kanta domin ta
gama zuwa iya wuya, Dame wannan mutumin
yake takama daya isa yayi mata dole. Ta mike ta
rufe laptop din dake gabanta ta jefa masa
mukullin ofis din ta jawo babbar jakarta ta rataya
cikin tsawa tace masa " Don ina aiki dakai ba
yana nufin ka cutar da kwakwalwata bane, idan
badon na kaskantar da kaina ba kai nafi karfin ka
min dole wlh. Ga mukullinku nan tafiyata itace
mafi sauki daga wannan matsin lambar taka.
.
Ta ture kujerar kusa da ita cikin sauri ta nufi
kofar ficewa. Ahmad ya jawo mukullin ya rikeshi
a hannunsa cikin sauri ya waiga kafin ta fice yace
" Ba wani abu bane idan kin tafi hakan shine ma
ya tabbatar min da mummunan zargin da nakeyi
akanki." Duk da batai niyya ba amma sai da tayi
saurin waigowa duk da cewa daf take da ficewa.
Ahmad ya juyo sosai ya dora da cewa " Na yarda
da cewa ke MUGUWA CE, tabbas ke ba mutuniyar
kirki bace, a rayuwarki babu komai sai ta'asa da
rashin kirki, na tabbata wani mummunan abu

kika aikata wanda yake bibiyarki kuma ya hana
miki kwanciyar hankali......" Ya dakata da
maganar yana kallonta. Idanunta suka zaro
kamar zasu fado 'iiihhhhhhh!!!! bakinta ya fada
dai dai sanda ta rike bakin nata, zuciyarta ta fara
saka mafi munin maganganun da aka fada mata,
lokaci guda kwakwalwata ta gaza jurar amsar
kalaman, kanta yayi nauyi tayi saurin dafeshi,
idanunta suka fara juyewa wanda yazo dai dai da
sanda kafafuwanta t gaza daukar ganga jikinta,
cikin sauri kwakwalwarta ta tuno mata abinda
yace......
.
Na yarda da cewa ke muguwa ce, tabbas ke ba
mutuniyar kirki bace, .......... na tabbata wani
mummunan abu kika aikata daya hana miki
kwanciyar hankali...... Dai-dai lokacinne ta
karasa sulalewa kasa cikin yanayi na suma....
Wai wai wai wannan al'amari akwai rikici.
.
Kubiyoni anext..
Tsaye yake kofar dakin kula tare da yin aikin
gaggawa na asibitin yana kaiwa da komowa,
mintuna talatin kenan da kawowa kuma likitoci
suka hau aiki amma ba wani bayani har izuwa
yanzu.
Zuciyarsa nata yi masa sake-sake kala-kala,
me yasa zaiyi haka?? Don me ma ya ma zan
takura akan abun da bai shafeni ba?? Kada fa
nayi silar kashe yar mutane ko na jawo mata
w...........
Hango fitowar likitan daga dakin da yayi ne
yasa ya dakata daga zancen zucin da yake yi
ya tunkari inda yake da gaggawa, doctor ya
akai?? ya ake ciki?? zata lafiya kuwa??
Ya tambaya cikin tashin hankali.
Likitan ya dubi nurses din dake tare dashi yace
" kuyi ku samo abin nan yanzu ".
To suka fada tare da wucewa.
Ya juyo ga ahmad yace " Karka shiga damuwa
da yawa zata sami sauki bada jimawa ba
insha Allah, mun shawo kan abin sai dai har
yanzu bata farfado ba.

Idan mahaifinta ko mahaifiyarta sunzo ina son
ganinsu a ofis."
Ya wuce da sauri.
Ahmad baiyi wata-wata ba ya fada dakin kai
tsaye izuwa gabanta yabi ta kallo cikin sanyin
jiki, ALLAH SARKI humaira zuciyarsa ta fada.
Ya danja da baya ya zauna a kujerar dake
gefen gadon da take kwance har yanzu idonsa
akanta yake.
Abinda ya fara fado masa arai shine: Tayaya
za'ai iyayenta ko wani nata yasan halin da
take ciki tunda bashi da zabi dole sai hakan ta
faru.
Tuno da wayarta da yayi wacce ke rike a
hannunsa yasa yayi saurin dagota kai tsaye ya
shiga contacts dinta, abin mamaki ba wasu
lambobi ne da yawa a ciki ba, ya tsa ya a dai
dai lambar da aka sa MY MUM, ya danyi jim
kamar me jin tsoron kiran bisa dole ya danna
kira tare da karata a kunnensa.
Yayi shiru ya kasa magana har sai sanda
wacce ta daga wayar tace " humaira lfy shiru
har yanzu??
Ahmad dakyar yace " ba ita bace ni sunana
Ahmad ina fatan kece mahaifiyarta??"
Ehh... nice.... mahaifiyarta lfy dai ko??
Ta tambaya da sauri.
Humaira ta yanke jiki ta fadi yanzu haka muna
asibiti...."
Subhanallahi!!!! Ta fada cikin rudewa tare da
cewa kuna wane asibitin ne??
Ahmad cikin sanyin murya yace " ALBARKA
HOSPITAL dake nan cikin........."kafin yakai
karshen maganar ta katse wayar.
Yabi wayar da kallo lokaci guda ya juya ga
fuskar humaira yabi ledar ruwan da aka jona
mata da kallo izuwa inda yake a rataye can
sama, ya dafe kai, ko kadan baya son kallonta
musamman idan ya tuno abinda ya faru kafin
shigarta halin da take ciki.
mintuna talatin ya sake shafewa kafin
mahaifiyarta da wata da baisan ko wacece ba
suka zo, da tambayarshi suka fara.

Ahmad yace " muna cikin magana to sai ta
mike lokaci guda kuma ta yanke jiki ta fadi.
mahaifiyartata tace " to yanzu me likitan
yace??"
Ahmad yace " cewa yayi idan wani yazo daga
cikinku yana bukatar ganinsa.
Mahaifiyar tata ta dafe kai tace " humaira ban
taba ganin mutum irinki ba, ace ke ba zaki
taba manta baya ba? ba zaki taba daina
tunanin abinda ya wuce ba? Wasu hawaye
suka gangaro mata, wacce suka zo taren ta
fara rarrashinta, Ahmad kuwa binsu kawai
yake da kallo.
Ta juyo ga Ahmad tace " sai kayi kokari ka tafi
tunda munzo kada dare yayi maka.
Ya gyada kai kawai ba tare daya motsa ba, ya
dade kafin ya tashi ya mika musu wayar
humairan kamar mara laka a jiki a haka ya fita
daga dakin.
zuwansa motarsa keda wuya yayi arba da
jakar humaira ya dago ta tare da jujjuyata a
hannunsa yasan tabbas tana ji da kyakyawar
jakar tata sbd kusan kowanne lokaci da ita
yake ganinta.
Kamar ya fita yakai musu ita sai kuma ya fasa
ya jawo kofar motar tasa ya kunnata yabar
harabar asibitin.
Jikinsa a sanyaye yake tukin, jinsa yake kamar
sabon mara lfy a haka ya iso gida, da sauri ya
wuce izuwa ciki yadda yake so kuwa momi
bata falon sai saudat kadai kwance tana
danna wayarta.
Ta amsa sallamar tasa kanta nakan wayar
tare da cewa yaya ka dawo??
Ehh... na dawo ya fada tare da wucewa da
sauri kafin ta dago kai izuwa dakinsa, dai dai
sanda ta tashi zaune tabishi da kallo a ranta
tace " Wannan lfy?"
jim kadan ta dan daga kafada tare da komawa
ta kwanta.
Yana shiga dakin nasa ya mayar da kofar ya
rufe ya jingina a jikinta idonsa ya ciko da
kwallah a hankali ya karasa ya jefa jakar tata

kan makeken gadon dake dakin, fadawar jakar
keda wuya ta bude abinda ke cikinta ya fito
wanda yayi saurin canja fuskar Ahmad.
Wani katon littafi ne me tsawo, fadi da yawan
gaske.
Ya zauna a gefen gadon a hankali ya jawo
littafin ya kare mai kallo a haka a hankali
kuma ya bude bangon littafin idonsa yayi
saurin kara zarowa sanda yaci karo da hoton
humaira me matukar kyau da haiba a kasa an
rubuta AISHA HUMAIRA ISMA'IL ya karewa
hoton kallo sannan ya bude shafin gaba anan
ma hoto ne amma ba nata ba, wani
kyakyawan saurayi ne da shekarunsa basu
haura Talatin da daya 31 ba, kyakyawa ne na
gaske a kasan sunan nasa ansa UMAR FARUK
ABUBAKAR, Ahmad ya dade yana kallon hoton
nasa ya sake bude shafin gaba nan kuma
hotuna ne nata da wancan faruk din a
samansu ansa FARUK & HUMAIRA, tsakiyarsu
kuma dan gaf fin dake tsakaninsu ansa ONE
LOVE!! daga kasa kuma ansa LIFE TOGETHER
DIE TOGETHER.
Littafin ya subuce daga hannun Ahmad sbd
mamaki, dama halin da take ciki akan soyayya
ne??
Waye kuma wannan faruk din??
Tambayoyin da suka fara zuwar masa kenan.
Ya sake cakumo littafin da sauri ya bude
shafin gaba na tafkeken littafin yaci karo da
abinda yasa shi saurin gyara zama CIKAKKEN
LABARINA.
labarin humaira kenan?? ya tambayi kansa,
yayi saurin gyara zamansa ya karasa karanta
abinda aka rubuta a kasa, labarin farin ciki na
gajeren lokaci daya jawo bakin ciki na har
abada.
Labari me tsuma zuciya da sanya shauki.
Labari me tare da tarin Al'ajabi.
Ahmad bude shafin gaba ya fara karanta
labarin humaira daya dade yana burin ya sani.
Cikakken SUNANA Aisha humaira, sunan
mahaifina Alhaji Isma'il ishak daya daga cikin

hamshakai kuma fitattun yan kasuwa a africa.
Haifaffiyar garin kano unguwar
hausawa......kuma SABAHUL KHAIRI...
Shine yadace da masu karatu..
Se ku qara gyara xama dan sauraro da
karanta labari me cike da AL-AJABI....
.
CIKAKKEN LABARINA. labarin humaira kenan??
ya tambayi kansa, yayi saurin gyara zamansa
ya karasa karanta abinda aka rubuta a kasa,
labarin farin ciki na gajeren lokaci daya jawo
bakin ciki na har abada. Labari me tsuma
zuciya da sanya shauki. Labari me tare da
tarin Al'ajabi. Ahmad bude shafin gaba ya fara
karanta labarin humaira daya dade yana burin
yikakken SUNANA Aisha humaira, sunan
mahaifina Alhaji Isma'il ishak daya daga cikin
hamshakai kuma fitattun yan kasuwa a africa.
Haifaffiyar garin kano unguwar
hausawa......kuma Ya kasance sananne wanda
sunansa ba boyayye bane sbd Allah yayi arziki
na gaban kwatance, hakan yasa ya tara
mutane masu yawa matuka kama daga
ma'aikata, abokai da yan maula daban daban
dake kaiwa dake nanike dashi a kowanne
lokaci. Ni kadai ce wacce mahaifina ya mallaka
a matsayin Y'A hakan yasa na taso cikin gata,
so, kauna da kulawa. Tun daga yarintata ba
abinda nake nema in rasa, komai nace ina so
sai an mallaka min ban taba yin kukan rashin
wani abu ba. a kowanne lokaci mahaifina na
nuna min ba abinda bazan samu ba sai dai
idan bana so, tun dai bana yarda har na yarda
domin kwakwalwata ta gaza tunano min
abinda zan nema dukiyar mahaifina ta gaza
samar min shi. Saboda son da mahaifina keyi
min yasa kowa ke nan-nan dani da nuna
kulawarsa akaina don ya samu abinda yake so
a wurinsa, duk kuwa wanda ya kuskura ya
taba ni to kashinsa ya bushe a wurin
mahaifina. Matsala daya dana tashi da ita
itace na raina mutani da nayi musamman
talakawa da marasa galihu, gashi ko kadan

bana son kula mutane bare na girmamasu sbd
bana ganin kan kowa da gashi. ban damu na
shiga harkar kowa ba kuma mafi yawa idan
aka shiga tawa raine ke baci, hatta kawaye
ban damu nayi ba sbd yadda nake jin nafi
kowa. Ba wadanda nafi rainawa na taka yadda
raina ke so irin yan aikin gidanmu kuma dole
su kalleni don suna tabani sun san hukuncinsu
kora ne don haka dole suka kyaleni nake cin
karena ba babbaka, mutum dake da karfin
taka min birki a wasu lokutan itace
mahaifiyata da nake kira da MUM.
.
Wani lokacin idan na dauko rashin mutuncin
daya wuce hankali takan kwabe ni wadda ita
kadai ke yin hakan domin mahaifina komai
nayi dai dai ne a wurinsa.
.
********* ************ *********
.
Tun ina da shekaru hudu aka saka ni a nursery
ta musamman ba kamar saura ba, me tsadan
gaske ce da kudin da ake biya a shekara daya
kawai ya isa a dauki nauyin karatun yayan
talakawa guda uku tun daga primary har zuwa
jami'a. Direrba aka tanada don kaini kuma ya
daukoni, idan ya kaini baya tafiya har sai an
tashi ya dawo dani. Shekaru biyu kacal nayi
aka matsar dani izuwa hamshakiyar
makarantar da duk wani dan me akwai ke
burin ganinsa a cikinta, wadda tun daga
sunanta kasan tafi karfin talaka koma uban
talaka, makarantar nada kyan yanayin data
burgeni har yakai ban taba korafi da ita ba.
Ina daya daga cikin dalibai abin alfahari a
makarantar sbd kwakwalwata ta saurin gane
abu wanda hakan ke kara min girman kai
matuka. Duk da cewa makarantar kowa naji da
kansa domin ba dan talaka a cikinta kowa ka
gani daga gidan arziki yake, amma fa nawa
girman kan yafi na kowa domin ko kawa daya
ban yi ba sbd a ganina duk babu me aji dai dai
dani. Sai dana shafe shekaru goma sha biyu

anan primary & secondary, da shekaruna 18 na
gama ta.
.
A dai- dai wannan lokacinne kuma kari kan da
ZUNZURUTUN KYAU ya kara bayyana,
Wohoho!!!!!!!!!!! Kai idan ka ganni sai ka rantse
da Allah ni balarabiya ce domin kadan zubi na
bana hausawa bane, kamar yadda ake fada
kuma nake gasgatawa a duk sanda na dubi
kaina babu kamata a wannan zamanin indai
fagen kyau ne. Nasha jawo accident idan ana
tafiya dani a mota ban daga glass ba, nasha
jawowa mutane karo da juna idan ina tafiya,
duk wadda ke ji da kanta idan ta ganni sai ta
fashe da kuka don taga karshen kyau, wasu
fashewa suke da kuka suna cewa ina ma su
sami 1/10 kyawu na. Kwalliya ma bata wani
dameni ba sbd a cewata idan kyau bai cika
bane ake neman kwalliya ta karasa cikashi
amma idan kyau ya cika babu bukatar hakan.
Mafi yawa harkar sharwoliya bata dameni ba
koda a shigata nakanyi kokari na rufe jikina,
mafi yawa kayan da nafi sawa ba wadanda
basu kamata bane sbd ni ako yaushe na yarda
na tsare mutuncina kuma a ko'ina. Bayan na
kammala secondary a nigeria mahaifina ya
nema min admission amma fa a oxford
university dake kasar england, nayi murna
sosai sbd ina da buri na bar kasata izuwa
wata musamman kasashen turai. Da yake
harka ce ta kudi nan da nan komai ya
kammala kuma aka saka ranar tafiyata domin
fara degree na farko a fannin kimiyar tattalin
arziki wato (economics) da kuma lissafi. Ana
gobe zan tafi ne bayan komai ya gama
shiryuwa zaune nake nasa tafkekiyar
televission din dake manne a jikin bango nesa
kadan dani a cikin katafaren falon alfarma na
gidanmu, cikin kwanciyar hankali nake kallon
ba wani abu dake damuna. kaso 99% na
hankali ya tafi ga kallon film din na DHOOM
yadda jarumin film din ke raina hankalin yan
sanda da dabaru daban daban, wucewar da

daya daga cikin yan aikin falon tayi ta gabana
yasa banga karashen abinda ya faru ba abinda
ya tunzira ni kenan wulakancina ya motsa na
kira sunanta da karfi.
.
HANNE!! Ta juyo da sauri tana kyarma, nace "
Zo nan" Ta fara matsowa a hankali a hankali
na daka mata tsawa nace " gidan uwar wa
zaki je??" Tace " uhm... haji..ya ce ta kira...ni.
". Nace harareta nace " kuma don ubanki shine
ta gabana zaki wuce ko? Duk nan ba hanya
bace??" Tayi shiru kawai tana makyarkyata
bata ankara ba na zabga mata mari hade da
fadin " ba tambayarki nake ba??". Karfin marin
sai daya sa ta fadi kasa lokaci guda ta zarce
da kuka." Ahmad ya kauda littafin daga
karantawar da yake yace " Lallai wannan
wulakanci har na siyarwa kina dashi ya gyara
kwanciyarsa tare da mayar da idonsa ya dora
da karantawa.......
.
Karar data kwalla ne ya jawo hankalin mum ta
fito da sauri tana tambayar lafiya kuwa?? Ta
tsaya kawai tasamu a gaba tana kallo hade da
hararata cikin takaici.......
AL'AJABI part 6
NA ABUBAKAR A. MUHAMMAD
wth--------->
Aßu Fer'ezerh
MUM ta dade tana kallona cikin takaici jim kadan
tace " Me tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login