Showing 6001 words to 9000 words out of 47324 words

Chapter 3 - AL AJABI COMPLET BOOK HAUSA NOVELS .pdf

Unknown   

15 Jul 2025

3404

miki kika mareta??"
Na koma kan kujera na zauna nace " zuwa... tayi
ta giftani ina kallo ta kare min ban gani ba kuma
tambayarta tayi min shiru."
ta kada kai tace " lallai humaira rashin mutuncin
naki yakai, kawai daga na kirata ta gifta ta
gabanki shine abin duka??"
Na zunburo baki nace mum " kare min fa tayi
kuma......."
Ta katse ni da cewa " ke dalla can rufa mana baki
kice kawai wulakancinki ya motsa to kin daketa
kinji dadi, idan kinfi karfinta ai akwai Allah."
Ta nufi inda hanne ke zaune har yanzu bata tashi

ba sai kuka da take yi.
Na dan kara bata rai tare da gyara zama nace "
ni mum wlh bakya yimin adalci a komai ba zaki
taba goyon bayana ba kullum nice me laifi a
wurinki akan wadannan banzayen."
Nakai karshen maganar da kauda kai.
Mum tace " anki a goya miki bayan wace gsky
gareki?? Ke ko kunya baki ji ba don Allah?? ki
rasa wacce zaki zage kwanjinki akanta sai yar
aikin gdnku wadanda yakamata ace kin jasu a
jikinki ki nuna musu kauna."
Na kalli hanne na zabga mata harara nace "
wadannan shashashan matsiyatan zanja a
jikina?? Allah ya kiyaye.
Mum tace " to tunda ba zaki kyalesu susha iska
ba ba ruwanki dasu basu shiga rayuwarki ba kada
ki kara shiga tasu idan kuma kika ku wlh zan
basu dama idan kika dakesu su rama suyi miki
dan banzan duka ai ba karfinsu kika fi ba. Taja
hannunta suka wuce, nabi mum da kallon
mamakin jin abinda ita kanta tasan bazai yiwu
ba, nace " Su dakeni fa kika ce?? "
Ta juyo da sauri tace " Eh don ubanki ".
Nabita da kallo ganin abin ya dau zafi da yawa ta
juya suka bar falon da nake a zaune.
Na gyara zama na hade rai nayi kicin-kicin kamar
na fashe da kuka, wai ni ake zagi akan wannan
banzar yar aikin? lallai zamanta yazo karshe a
gidan nan bari dady ya dawo.
BAYAN AWA DAYA naji motsin dawowar dadyna
na kakalo sabon fushi da takaici, dady yana
shigowa yayi ido hudu dani cikin fushi, yayi saurin
ajiye jakarsa tare da tunkaro inda nake zaune "
my daughter ( daya daga cikin sunayen da yake
kirana dasu ) menene ya faru haka? waye ya taba
min ke?"
Nayi shiru na kara hade rai kawai na juyar da
kaina.
Dady ya zauna gaf dani cikin kasa-kasa da
murya yace " fada min mana waye ya taba ki?
uhummm?"
Cikin shagwaba na mirgina kai nace " ba mum
bace......."

Me kuma tayi miki??
Ya tambaya da sauri.
nace " wai..... zata sa yan aiki su rinka dukana "
dady har wani dan babban motsi yayi tare da
mai-maita abinda na fada " su dakeki??".
na gyada kai.
Ya juya da sauri ya fara kwallawa mum kira.
Hajiya!!!!! Hajiya!!!!!
Da saurinta ta fito izuwa falon da faddady yace "
Me yasa kika batawa humaira rai, wai ke hajiya
me yasa kike haka ne don Allah.... to to yanzu
me kike nufi yar aiki tafi yar da kika haifa da
cikinki kenan??"
Mum ta tabe baki tace " au wai da akan wannan
ne kake kwala min kira haka sai kace wani tashin
hankali??"
Au kina nufin shi wannan ba komai bane kenan??
kinga hajiya ran kowa zai baci a gidan nan fa.
Mum tace " rainin nata ne yayi yawa nace zansa
a dai daita mata zama.
Na tsandara ihu nace kaji ko dady??
Dady ya kara rudewa ya fara zabga bala'i ta inda
ya shiga batanan yake shiga ba.
Zuwa can nace " dady kawai a kori yan aikin nan
dukansu ".
dady ya juyo yace " kwantar da hankalinki, abinda
za'ai kenan suna ina ne??"
Mum tace " Wai suwa za'a kora?? bazai yiwu ba
sbd duk cikinku ba wadda kuka dauka kuma baku
kuke biyansu ba nice don haka babu me korar
minsu ina jin dadin aiki dasu......
Munji tafi kici gaba da harkokinki kada ranmu ya
baci duka, Allah ya baka hakuri.
Ta juya ta nufi sashinta, dady ya juyo gareni ya
fara rarrashina ni kuwa sai wani kara hade rai
nake.
Kinga manta dasu kinji humaira na, ba wanda ya
isa ya taba ki duk wanda ya kara bata miki rai
wlh tamuce ni dashi.
Kada ki manta fa gobe iwar haka kina kasar
birtaniya kin bar musu kucakar kasar tasu zaki
fara rayuwa cikin turawa ba wanda zai takura
miki inda iskar da zaki shaka ma ba irin wannan

bace.
Jin hakan da nayi yasa nadan saki raina kadan,
yace " to danyi murmushi mana "
Na saki rai sosai yace " Yauwa ko ke fa! gobe kiyi
kokari ki tashi da wuri sbd jirginki na safe ne an
gama duk wasu shirye-shirye kina zuwa direct
zaku daga shuuuuu!!! sai london."
yakai maganar da murmushi.
Na dan tabe baki cikin shagwaba nace " dady nifa
dakai zamu tafi idan muka je sai ka dawo."
Ya dubeni yace " to ke banda abinki ina naga
lokacin binki har london kuma na dawo? kedai
karki damu jirgin na musamman ne zaki samu
duk abinda kike bukata kuma za'a kula daku
sosai musamman ma ke yar lele.
Nayi murmushi kawai.
Daddy ya mike ya dau jakarsa bari na shiga ciki
ko?
"To dady" Na fada idona na kasa ya wuce.
Na daga kaina na dubi katafaren agogon dake
manne a jikin bango karfe 6:15pm sallar
magaribar ma ai da saura na mayar da kaina ga
t.v din naci gaba da kallo.
$$$$$$$$$$$$
in Alhaji lfy irin wanWashe gari misalin karfe
8:00am na safe zaune muke mu uku, mum da
dady na zaune a kujeru daf da juna yayinda nake
zaune a kujerar dake fuskantarsu.
faffadan tebirine a gabanmu kayan abinci kala-
kala jere bisa kansa wadanda suka dace da karin
safe, babu wanda ke magana a cikinmu.
Humaira!!!!!!!!!!!!!
dady ya kira sunana, na dago a hankali na
dubeshi.
yace " misalin 11:30 na safen nan zaku tashi,
abinda nake so dake shine kibi a hankali kuma ki
kula sosai sbd kasar da zaki je ba taki bace ba
wadda kike ciki bace kuma ba wadda kika saba
da ita bace, kiyi abinda yakai ki kawai shine
karatu ki samo abinda zanyi alfahari dashi sbd
ina da comfidence 100% akanki kuma ba zaki
bani ba.
Insha-Allahu dady. Na fada tare da mayar da

kaina ga kofin tea dake hannuna.
Daddy ya mike yace " bari inje na shirya na fita
ina da meeting karfe tara hajiya ina takardun nan
dana baki ajiyansu jiya??
Ta dago kai a karon farko tace " Suna nan cikin
lokar sama." Ok " ya fada tare da dubana yace "
yar lele na Allah ya kiyaye hanya, da zarar kun
sauka zanyo miki waya."
To dady na fada ya juya nudi dakinsa.
Na mike na koma kan kujerar dake gaf da mum
nace " Momina banji kince komai ba."
To me zance???
Ta fada kanta na duban abinda take ci.
Nace yakamata kice wani abu saboda kinga tafiya
zanyi ta shekaru da yawa kodai bakin cikin
rabuwa dani kike yi da yawa haka har ya hana ki
magana??"
A'A ta fada tare da cewa " nifa haushinki kawai
nake ji "
Na bita da kallo lokaci guda nayi yar gajeriyar
dariya nace " da gaske??"
ta gyada kai kawai.
Na kwantar da kaina a jikinta nace " sorry my
mum ai nasan da wasa kike ba zaki taba jin
haushi na ba, uhmm! mum pls sarkar nan don
Allah ki bani zanyi amfani da ita acan.
Ta girgiza kai tace " kefa kika nuna halin ko in
kula da ita sai yanzu zaki ce kina so??"
Mum dama can ina sonta wlh zan kula da ita,
Zaki bani??
nakai karshen maganar da kwantar da murya.
Mum ta dubeni kadan ta kauda kai tace " Zan
baki ".
Na saki fuska hade da alamar jinjina nace "
Thank you MUM bari naje na fara shiri. "
Na nufi dakina.
Misalin karfe goma 10:00am mufida tazo kawowa
momi sako ta iske ina gaf da gama shirina ta
tayani muka karasa na tilasta mata ta tsaya don
yimin rakiya izuwa airport.
MUFIDA y'a ce a wurin haj. jameela kawar mum
kuma aminiyarta, mufida ce kadai zan iya cewa
kawata a duniya don da ita kawai na yarda muyi

kawance sbd ta wasu bangarorin halinmu yazo
daya duk da muna da banbanci da ita sosai a
wasu bangarorin.
Misalin karfe 10:15am Nayi sallama da momi da
sauran wadanda zan iya sallama dasu sauran yan
aikin gidanmu kuwa da rashin mutunci muka rabu
don ban hakura ba sai da nayi final.
A jibgegiyar mota kirar PRADO muka fito, mufida
na gefena sai kuma mutum biyu har direba dake
gaba.
Mukanyi hira jefi-jefi da mufida, kaina sai wani
kumbura yake waini zani kasar turai.
Cikin kankanin lokaci muka isa AMINU KANO
international airport, tunda naga jirgin dazai daga
damu na yarda bana yara bane saboda
haduwarsa, ya isa a nunashi a ko'ina.
Ban dauki lokaci ba aka gama tantanceni na juyo
na karbi jakunkuna na mukai sallama da mufida...
****************************
Shigata jirgin ya tabbatar min da abinda dadyna
ya fada, tsaruwarsa daga ciki yafi yadda nake
ganinsa daga waje domin ya wuce duk yadda
nake tsammani.
kai tsaye sit dina na wuce na zauna duk da cewa
yaune karon farko dana shiga jirgi irin wannan
amma ban yarda na nuna hakan ba don kada
wadanda ke cikin jirgin su raina ni.
Abinda na lura dashi shine kowa naji da kansa a
cikin jirgin sbd daga manyan attajirai masu tafiya
kasuwanci sai yayan attajirai masu zuwa karatu
irina, babu ma zaton samun dan talaka a ciki
bare a samu din. Kamar yadda aka shirya
11:00am dai dai jirgin ya daga kai tsaye izuwa
birnin london tafiya mafi tsawo dana fara yi a
rayuwata, jami‘an cikin jirgin kuwa sai nan nan
ake damu duk abinda muka bukata ba bata lkc
ake bamu.
Awanni nata shudewa 2n ina sha‘awar tafiyar har
sai dana gaji amma bamu iso ba, duk na kosa
sbd wannan ne karon farko dana taba yin tafiya
irin wannan daga karshe madai wani nannauyan
barci ne ya kwashe ni ban farka ba sai AIRPORT
na birnin londôn, A hankali daya bayan daya

muka sakko daga cikin jirgin.
wowwww!!! Nan fa naga abin mamaki domin ba
birnin ba airport din kadai abin kallo ne ban taba
tsammanin akwai wuri me kyau da kawatuwa irin
wannan lallai duk yadda ake bada lbrn birnin nan
ya wuce nan, duk yadda nakai da ji da kai sai
dana zama kamar wata yar kauye a wurin.
saukowarmu keda wuya jami‘an filin jirgin suka
yo kanmu nan fa aka shiga secreening kala-kala
harda wanda ban taba ji ba ko a lbr, bayan na
cika duk wani sharadine aka bani damar ficewa
daga airport din, ban jima ba kuwa wata
jibgegiyar mota me matukar fadi da tsawo ta iso
like take da banner din OXFORD UNIVERSITY
bamu dauki tsawon lokaci ba ta debemu tare da
mutane daban-daban da muka zo daga wurare
da kasashe maban-banta, Anan ne fa naji kwalta
tamkar ita ta shimfida kanta, duk inda motar tabi
titine luwai-luwai ba gargada bare rami.
Shuuuuuuu!!!!! A haka motar ke tafiya tamkar
jirgin sama ban-bancin kawai ita wannan a kasa
take tafiya ba‘a sama ba.
Gefe guda tsarin gine-ginen birnin wanda keda
matukar tsayi tamkar zasu tabo can kololuwar
sama sun kawatar dani matuka.
gashi kowa irin rayuwar da nafi so yake yi ta ba
ruwan kowa da wani, kowa ka gani harkar
gabansa yakeyi. jim kadan muka iso katafariyar
jami‘ar daya daga cikin mafi girma, daukaka da
suna a duniya, bayan komai ya kammalu kuma
kai tsaye aka yimin jagora izuwa masaukina.
Ni kadai ce a sashin nawa wanda ya kunshi duk
abubuwan da nake bukata.
************************* Nan fa na shiga karatu
gadan-gadan kasancewarsa wajene da ko baka
so sai kayi karatu, da farko na dauka a nigeria ne
naci gaba da jiji dakai da takama sai naga ina!!
domin a banza wajene da kowa keji da duk
abinda nake ji dashi shima. Dole tasa na sakko
na fara maraba da kowa nan da nan kuwa na
tara kawaye masu yawan gaske tamkar bani ba,
na saki jiki da mutane sosai. Da yake ba karatu
ne irinna na nigeria ba cikin shekaru biyu kacal

na kammala degree na na farko a hakan ma don
mun sami dan tsaiko ina daya daga cikin
wadanda suka sami sakamako me kyan gaske
hakan yasa makarantar ta bani damar yin
masters degree kyauta kasancewar ina jin dadin
zaman yasa na amince na zarce cikin ba tare da
jinkiri ba. shekara daya kuma na kammala
masters, degree biyu cikin shekaru uku kacal,
wannan shine tarihin kara2na da yadda na samu
masters degree a kasar birtaniya.
“hmmm..... Lallai gskyr Bahaushe da yace ‘Talaka
bawan Allah‘ domin talakan nigeria ne zai kwashe
shekaru hudu yana neman diplomer bai samu ba“
Ahmad ya fada sanda ya kauda kansa daga kan
littafin lkc guda ya mayar da kansa ya dora.
kammaluwar komai tasa na tattaro inawa-inawa
nayo nigeria, ranar laraba misalin 12:00pm
jirginmu yayo nigeria.
dirarmu keda wuya dady ya iso tare da wasu
daga cikin yaransa aka daukeni direct mukai gida,
nan fa girman kai, takama, gadara da raina
mutane ya dawo sabo fil. Na fara jin nifa yanzu
nafi kowa kuma samun kamar ni sai an tona kai
zaiyi wuya ma a samu mace kamar ni da tattara
abubuwan da nake dasu.....
Hmmm'un yanxu akapara shirin..!
BARKAN KU DA ASUBAH..!
Bayan kwanaki uku da dawowata ina kwance
bisa doguwar kujera hannuna na rike da wani
novel daya daga cikin abokan hirata a london
me suna HAPPINESS DAY na prof. christiana
wolein dan kasar holland, kyakykyawar fuskata
nakan littafin wanda fararen idanuna ke kallo,
hankalina, tunanina da duk wani nazarina ya
tafi ga karanta daddadan lbrn da nake yi
wanda nake matukar son karasashi ko don naji
yadda karashen lbrn zai kasance.
Magribar da nake ganin ta doso yasa na kara
kaimi, Momi ta fito daga sashinta rike da wani
dan madai-daicin kaskon turare wanda wani
daddadan kamshi ke tashi ta hanyar farin
hayakin dake fita daga kaskon, ta fara zagaye
faffadan falon domin kanshin ya isa ko‘ina

kafin ta dawo ta ajiye shi a tsakiyar falon.
A dai-dai lkcnne dady na ya dawo, cikin fara‘a
yayi sallama kasancewar ya ganni a falon, ya
karasa ya aje jakarsa tare da zama. Kamar
hadin baki nida momi muka amsa sallamar, na
dago daga kwanciyar da nayi tare da aje novel
din a gefena nace “Wellcome back my dady“.
Yauwa yar lele na da fatan dai komai normal
ko? na gyada kai kawai, momi dake gefe ta
bimu da kallo tare da jinjina kai tace “uhm..
gsky ina ganin kabilanci a gidannan, wato
Alhaji yarka kawai ka sani ni ba mu2m
bace??“ Daddy ya kyalkyale da dariya yace
“kinji ki hajiya da wani zance gani kikai na
tashi daga nan bance miki komai ba??“ Da
sauri tace “zaka iya don ba karamin aikinka
bane kace bama ka ganni ba 2nda ka shigo
sai da nayi magana.“ Dady ya sake yin dariya
yace “ A haba sai kace wani makaho? kawai
dai........“ Y‘arka ce a ranka!! momi ta karasa
masa zancen.
ya gyada kai yace “anji muje a hakan“. Momi
tace “gashi kuma duk daran dadewa sai ka
shigo falon nan ka tarar batanan koka manta
macece dole ka aurar da ita??“ Dady yayi
murmushi yace “kinga hajiya duk takaicinki
kyayi ki gama ai ba akuya bace ita bare kice
zan kaita kasuwa na siyar mun rabu kenan har
abada.“
Duk muka fashe da dariya, dady ya kwantar da
kansa jikin kujerar yace “ yauwa ni na tuna
ma, humaira!!
Na dago kaina a nitse domin nasan indai dady
ya kira sunana kai tsaye to maganar da yake
son yimin me muhimmanci ce.
Yace “kasancewar kinyi kara2 me tsada a wuri
me tsada kuma akan abu me tsadan gaske
izuwa yanzu na sami request daga wurare
daban-daban akan anaso ayi aiki dake, daga
ciki akwai central ban.k da me gwamnan
bankin da kansa ya rubuto min takarda akan
cewa suna bukatar karin kwararru da suke da
sani akan tattalin arziki, akwai FIRST BANK,

GTI BANK, DIAMOND BANK da sauransu.
Ma‘aikatar kudi ta tarayya ma na bukatar kiyi
aiki dasu, sannan jami‘o‘i kamar B.U.K, A.B.U
da sauransu na bukatar kiyi musu aiki a
matsayin lecturer, ke harda wasu hukumomi
daga kasashen waje sai kin zaba kin darje.
A maimakon nayi farin ciki sai na hade rai,
dady ya dubeni tare da gyara zama yace “Ah
ya naga kin bata rai?? lafiya??“
Na dan kumburo baki nace “dady nifa bazanyi
wani aiki a duk wuraren nan ba.“
dady yace “sai a ina?? ko a bankin duniya kike
so kiyi aiki??“
Na girgiza kai nace “ A‘A ni bazanyi a ko‘ina
ba.“
Kafin yace wani abu momi tace “ba zakiyi ba
kina nufin duk kara2n da kikai ya tashi a
banza kenan??“
Dady ya dubeta yace “haba hajiya kibita a
hankali mana, ya juyo gareni yace “Yar lelena
me yasa bakison kiyi aiki??“
Nace dady nifa banyi kara2 don na wahalar da
kaina ba, nawa ne duka albashin da za‘a
biyani? duka fa bai kai kudin da gyaran gashi
na keci ba.
Yayan talakawa da matsiyata sune keyin kara2
don su sami aiki amma ba irina ba.“
Daddy ya kyalkyale da dariya kamar zai
tuntsiro daga kan kujerar yace “gskyrki fa
y‘ata.“
Momi tace “ Au wai kaima ka biye mata a
hakan??“
Daddy yace “To karya tayi??, ya juyo gareni
yace “ yanzu ke me kike so ayi??“.
Na tabe baki kamar ba zance komabi ba daga
bisani nace “ daddy nifa a duniya ba abinda
ban iya ba irin kwamfuta don haka ina son na
samu certificate akanta.
Cikin sauri daddy yace “Tooo!!! a germany ko
japan ko america zabi daya......
Na tabe baki nace “NO daddy duk basai ankai
ga haka ba, anan kano nake so nayi.“
Daddy yabini da kallo yace “kina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login