Showing 9001 words to 12000 words out of 47324 words

Chapter 4 - AL AJABI COMPLET BOOK HAUSA NOVELS .pdf

Unknown   

15 Jul 2025

3406

nufin a

makarantar matsiyata??“ Dariya ta kwace min
na girgiza kai nace “ a‘a akwai wata reshen
AL-KHRAMY ta kasar saudiya da suka bude
anan kano next week za‘a fara lecture,
MUFIDA ma can zata fara zuwa kaga na sami
abokiyar tafiya.“
Daddy ya gyara zamansa yace “kwarai naji
lbrnta, to karki damu my daughter a ckn satin
nan za‘a shirya miki komai next week dake
za‘a budeta.“ Nayi murmushi nace “Thank you
my dad“.
Daddy ya mike “bari in karasa ciki, ya juyo ga
momi yace “a ina kika saka min jakar nan ta
jiya??“ Har yanzu takaicine akan fuskarta tace
“ tana nan cikin lokar dakinka“. daddy ya sabi
jakarsa ya wuce. Ni kuwa wani farin ciki ya
lullubeni, gsky daddy na sona ni kaina nasan
haka.
Hararar da momi keyi min ce tasa ban takalo
wata hira da ita ba na jawo novel dina tare da
kwanciya bisa luntsimemiyar kujerar da nake
kai na cgb da kara2n da nakeyi a baya.
******** ******* ******* ********
Sati daya dai-dai da faruwar haka na fara
zuwa lecture a katafariyar makarantar AL-
KHRAMY computer training school, 2n daga
sanda na hangi makarantar a shigata ta farko
naji a raina tayi min sbd tsarinta. fasalin
gininta kawai abin kallo ne banda kuma zubin
cikinta.
Tana da ma2kar fadi da girma da kuma
wadatar dakunan kara2, akwai bangaren da
aka ware musamman don hutawa a lkcn da
ba‘a lacca wanda ya kunshi kujeru a jere daf
da wasu kyawawan bishiyu da kuma filawowi
dalilin da yasa iskar dake kadawa a wajen ta
zama me kamshi, wajen dai ya dace da
hutawa ga wanda ya debo gajiyar kara2.
Gefe guda akwai daki na musamman da aka
ware aka cikashi da littattafai kala-kala da
suka shafi darasin computer da mutum zai iya
zuwa ya bincika wanda yake so, nesa kadan
kuma akwai wurin cin abinci da aka ware

musamman ga masu bukata.
Da yake makarantar mallakar larabawa ce an
ware bangaren maza daban na mata daban.
Ga yadda ake kaffa da dalibai ake maidasu
y‘an gata.
kamar yadda aka saba ranar juma‘a 12:00pm
mun tashi zaune nake bisa wani dan
dandamali ina jiran mufida ta fito mu tafi
kaina na kasa na kurawa laptop din dake bisa
cinyoyina ido ina tayi, sallamar da naji anyi ce
tasani dakatawa kamar na dago kai na dubi
wanda yayi sallamar sbd muryar tasa ta
ratsani sosai amma sai girman kan ya motsa
na cgb da abinda nakeyi ko sallamar ban
amsa ba.
Kyakykyawan saurayin bai gajiya ba yace “ pls
na gaji da tsayuwa in zauna??“
Na cilla idona tare dago fuskata nace “ka
zauna mana idan ka gadama“.
Mai makon ya bata rai sai yayi murmushi yace
“godiya nake.“
Ya zauna bisa dandamalin nesa kadan dani,
kaina na kasa amma zuciyata na sake-sake, ji
nake kamar na dago kalli mu2min daya fara
birgeni karo na farko a rayuwata.
Jim kadan mufida ta fito ai kuwa tana kyalla
ido taga wannan saurayin dake kusa dani sai
ta bude baki tare da fadin “ Ah leader manyan
gari kaine anan haka??“
Yayi murmushin daya kara masa kyau yace
“nine wlh kinga su nazir nake jira basu fito ba
dama tare kuke da wannan??“
yayi nuni dani.
Eh tare muke da ita wlh ni take jira......
Na rufe laptop dina tare da diban littattafaina
dake ajiye a gefena na doka tsaki na wuce
nabarsu anan.“
mufida tabini da kallo kawai ta juya tare da
yin murmushi tace “sai gobe ko??“
Ya gyada kai kawai dai-dai lokacinne
abokansa su uku suka karaso wanda ya riga
kowa karasowar yace “kai wai ya akai harka
2nkari wccn yarinyar ta barka ka zauna kusa

da ita??“
Ya bishi da kallo yace “kasanta ne??“
Kwarai kuwa shugaban y‘an girman kai,
takama da gadara ta duniya kenan.“
duk sukai dariya, saurayin ya shafi gashin
kansa yace “kai! nazir yarinyar fa ba karya wlh
ta hadu“, wanda aka kira da nazir din yace “
ana fada maka matsalarta kana cewa ta
hadu??“
ya harareshi yace “ mace idan batai takama da
gadara ba waye zaiyi?? girman kan ne kawai
matsala.... ya sake bin inda muka bari a mota
da kallo.“
Ni kuwa 2nda muka tafi mufida nata bani lbrn
saurayin wai mu2min kirki ne kaza-kaza nidai
ban kulata ba, don kasa gane me take nufi da
hakan....
Ammafah....koda baxance komaiba..senaga
iya gudun grman kannata....
Yanxu ne aslin komai ze fara..sekucigaba
dabina.. amma fa bada gudu ba
Isata gida keda wuya na ketawa ma‘aikatan
gdnmu rashin mu2ncin dana saba harma sai
dana mari me baiwa fulawowi ruwa sbd yayi
sakacin watsa min ruwa duk kuwa da cewa ba
yana sane bane, kai tsaye dakina na wuce nayi
wanka naci abinci na jawo laptop dina hau
aikin dana saba.
Bayan kwanaki biyu da haduwa da
saurayinnan da ko sunansa ban sani ba ina
zaune a bakin harabar makarantar tamu a
wannan karon wayata ce kawai a hannuna
sakamakôn laptop dina tana hannun mufida,
zuwa da wurin da nayi ne yasa a gabana dai-
daikun dalibai ke isowa suna wucewa ba
ruwana dasu sai dai su wuce.
wasu lktn zakaga daliban na zuwa ne a group-
group kamar yadda al‘adar rayuwar makaranta
take.
Ana cikin haka ne group din da suka fi
kowanne shahara a makarantar suka zo
wucewa ai kuwa caraf idon saurayinnan a
kaina ya dakata tare da duban na kusa dashi

yace “nazir“.
Wanda aka kira da sunan nazir din yace
“na‘am leader.“
wuce min da jakar nan na hango mu2niyar,
nazir din ya amshi jakar ya kallo inda nake
tare da cewa “wlh leader kabi a hankali
yarinyar nan big class ce zaka sha mari fa
inkai wasa.“
ya rike kugu tare da cewa “Ta mareni?? haba
dallah sai kace a zamanin jahiliyya?? kudai ku
tsaya kusha kallo.
Ya juyo ya doso inda nake, dirar daddadar
muryarsa kawai naji a kunnena da fadin
“Amincin Allah ya tbbta a gareki ma‘abociyar
son kadaici da hutawa“.
Har ga Allah wani sanyi naji a raina amma da
yake ni din ce kawai sai kauda kai kamar
bansan me yace ba.
ya sake yin murmushi yace “kauda kanki lfy
tauraruwa me haske“, na sake hade rai na kalli
kasa.
woww!! gsky ke daban ce ban taba ganin
wanda fushi keyiwa kyau ba sai ke.
Ya fada yana kallona. Na cije lebena na
dubeshi zanyi magana yayi saurin cewa “ina
ma kiyi magana a ckn fushi daba karamin
kwarjini zaki kara ba.“
Na dan rufe idona a raina nace “BALA‘I“ na
kara hade rai nace “kaga nifa ba shashasha
bace da za‘a zo har inda nake a cikani da
suru2 idan ina son zama a wuri me hayaniya
mezai kawoni nan?
murmushinsa wanda adon fuskarsa ne ya karu
yace “gani nayi zaman kadaici bashi da dadi
shine nazo na debe miki kewa gashi kuma nayi
nasara 2nda a baya bakinki a rufe yake yanzu
kuma gashi yana motsi, na girgiza kai nace “to
bana so idan wurin ne yayi maka zan iya tashi
nabar maka“.
Ya mike tare da cewa “ kinfi karfin kina waje
ace wani ya tasheki amma ki sani babu wata
halitta dake iya rayuwa ita kadai dole tana
bukatar mataimaki Allah ne kawai yake guda

daya baya bukatar abokin tarayya amma bamu
y‘an adam masu rauni ba, yaja da baya tare
da dago min hannu yace “sai anjima“.
Na bishi da kallo ba karya fa gayen ya hadu
wlh, tun daga zubinsa har ya zuwa kalamansa
da halayensa ababan birgewa ne.
Ban jima a zaune ba na tashi na shiga class
ko break ban fito ba sai da aka tashi, abinda
ya kara bata min rai sai dana shafe min2na 15
da tashi direba na bai iso ba bare mu tafi na
zauna bisa dandamalin dana saba zama na
zaro wayata na kira direban yana dagawa na
balbaleshi da fada duk da hakurin da yake bani
sai da nayi na gaji sannan na kashe wayar
hade da doka tsaki, Allah ya wuci zuciyarki
yake tauraruwa me kyalkyali, na dago kaina
muka hada ido da saurayinnan na bata rai
naja tsaki na kauda kai.
Yace “ina bbr aminiyar taki ne na ganki ke
kadai??“
sakanni talatin na dauka sannan nace “ Ta tafi
koyo sallama “
Ya saki murmushi yace “sorry i took the
correction“
Amma me yasa duk ranar da ake kwallawa
baki nemi inuwa kin zauna ba kika zabi zama
a ckn rana??“
Cikin fusata nace “ina ruwanka? wai kai
wanne irin mu2m ne?“
Yace “bakar fata, musulmi kuma bahaushe,
bana fatan kice na takura miki don haka kinga
tafiyata, sai anjima.“
MAYE!!!!!! na fada a raina, dai-dai lkcnne
direbana ya karaso mufida ma ta fito kai tsaye
muka nufo gida, inata zabgawa direban ruwan
bala‘i ta inda na shiga ba tanan nake fita ba.
******* Kwanaki uku da faruwar haka misalin
11:30am mun fito break da yake ban karya ba
naja mufida muka shiga restaurant aka kawo
mana abinci muka fara ci, bamu dauki tsawon
lkc ba muka gama.
Na kira dan matashin bakin saurayin daya
kawo mana abincin nace “yauwa nawa ne

kudinku??“ yayi yar gajeriyar dariya yace “No
ai basai kun biya ba“.
Na zabga masa harara nace “kai nifa bana
wasa da yaro nawa ne kudinku aka ce??“
nakai karshen maganar cikin tsawa.
ya girgiza kai yace “An riga an biya muku fa“,
na bishi da kallo nace “kai kada ka raina min
hankali kaga nayi kama da matsiyaciyar da
za‘a siya wa abinci?? To ai ni ko gaba daya
restaurant din naku nagadama ina iya siya
bare abincin mu2m biyu kada ka batamin rai
ka batawa kanka, nawa ne kudinku??“
fuskar saurayin ta canja yace “haramun ne a
aikina na karbi kudin mtm biyu akan abu daya
amma idan kina musu ga wanda ya biya muku
can, nabi hannunsa izuwa inda yayi min nuni
caraf idanuna suka dira akan saurayinnan me
lakabin leader na dauke kai tare da runtse
idanuna ckn takaici, shit!!! wai wannan wane
irin mtm ne?? Na tambayi kaina naja jakata
dake ajiye akan tebirin dake gabana na doshi
inda yake. Ko sanin nazo inda yake baiyi ba na
tsaya a kansa nace “mallam abin naka kuma
yana neman yayi yawa fa, daga ina dan
saurararka kuma sai raini ya shiga??
cikin rashin fahimta ya ajiye kofin juice dake
hannunsa ya dago kai yace “ raini kuma?? me
ya faru??“ Na dan harareshi nace “idan ba
haka ba meye na biya min kudin abu mafi
sauki da kowa ke iya siya irin abinci??“
Fuskarsa tayi saurin canjawa zuwa murmushi
yace “ wlh na zaci wani gingimemen laifi na
aikatawa sarauniyar matan wannan karnin,
ashe ma ba wani abu bane “ Na bishi da kallo
nace “ba wani abu ba?? kayi min wulakanci
irin wannan kace ba komai bane??“, ya juyar
da p-cap din dake kansa izuwa baya yace “Ni
banyi miki wulakanci ba a wajena kyautatawa
nayi miki sbd kin cncnci fin haka a wurina
bawai nayi hakan bane don kankantar dake
domin kin wuce haka, kuma ni a wurina kyauta
ai itace mafi girman karramawa!!
Ni kuma a wurina itace mafi girman

kankantarwa, nawa ka basu na biyaka??
Na fada dai-dai sanda na zaro wata yar
karamar jaka daga bbr jakata.
Ya dago da sauri tare da bina da wani irin
kallo tamkar bai fahimci abinda na fada ba
yayi saurin girgiza kai yace “baki yi kama da
wadda zata maida hannun kyauta baya ba sbd
nasan kinsan hakan bai dace ba, abinda nake
so ki gane shine don an baki abu kin amsa ba
yana nufin baki fi karfin abin bane.“
Na tabe baki nace “well!! naji 2nda kai
kagadama kaga zaka iya amma ka sani idan
wai kayimin haka ne don naji dadi to banji ba,
kuma bazan gode maka ba sbd bani na saka
ba.“
yayi saurin sakin murmushi yace “dama badon
ki gode min nayi miki sbd ba nema kikai ba
martabarki ce kawai takai ayi miki abinda yafi
haka.“
Na juya tare da cewa “kai dai ka jiyo“.
Sai dai a zuciyata ba karamin dadin kalamansa
naji ba sbd ni mtm ce me son a zigani.
Na nufi inda mufida take wacce har yanzu ke
zaune kawai tana kllnmu ta mike kai tsaye
muka nufi class muka cgb da lacca.
*** Wato 2nda nake a duniya ban taba ganin
mu2m irin saurayinnan ba, ya hadu ta ko‘ina
kuma ba shakka yasan abinda yake yi
kalamansa kawai ke tbbr da haka, abinda nayi
iya kokarina na gano na kasa shine me yasa
yake burgeni? me yasa yake da kwarjini a
idona? me yasa bana iya wulakantashi kamar
sauran mutane??? tambayoyin dana kasa
bawa kaina amsarsu kenan ***.
Bayan kwanaki uku da faruwar haka, na shiga
inda ban taba shiga ba library don duba wani
littafi me danake ma2kar bukatarsa da wuri,
al‘adata ban damu na duba littafi a library ba
domin waya kawai zanyi a kawo min shima
wannan din don ina bukatarsa da gaggawa ne.
Ni kadai ce a cikin wajen hakan yasa nake
neman nawa ckn kwanciyar hankali, motsin
shigowar da naji yasa nayi saurin dago kai

muka hada ido dashi nayi saurin dauke kai
daga kllnsa, yadan tsaya yana kllna lkc guda
ya tako tare da cewa “Amincin Allah a gareki
ya tauraruwar da haskenta baya disashewa“,
ko kllnsa banyi ba naci gaba da abinda nakeyi,
ya tako a hankali izuwa nesa kadan dani yace
“nayi sa‘a kenan yau zan taya sarauniyar
mata bincike me kike nema ne??“
ko kllnsa banyi ba nace “ Idon matambayi “.
Hmmmm lemme stop here kar mucika cikawa
kuce yayi yawa..!
Ya kyalkyale da dariya yace “ kema fa kina da
abin dariya gaki dai kamar ba zaki yi ba “, ya
zauna a kujerar dake nesa kadan dani ya dora
da cewa “nayi mamaki ma2ka dana duba kaf
makarantar nan ban hango tauraruwar dake
haska wannan makarantar ba ke kinga yadda
duk makarantar tayi duhu kuwa??
akwai bukatar ki fita ko don ki haskata“.
Na dauke kaina daga lttfan da nake dubawa
nace “kai!! ina yin abuna a nitse kazo zaka
rikitani wai kai wane irin mtm ne??
Kai baka rabo da NACI??
Baki, musulmi kuma bahaushe. Ya bani amsa
irin wannan a karo na biyu sannan ya dora da
cewa “ina da naci musamman idan ina so na
isar da wani sako aka kasa fahimtata.
Na tabe baki nace “sako?? wanne irin sako
kake so ka isar??“
Ya danyi shiru jimawa kadan ya mike alamar
wasa ta fita daga fuskarsa yanayi na fadar
magana da gaske ya shigeta ya taka a hankali
izuwa gaba yace “ Akwai wata kalma da ake
kira SO wacce a baya ban santa ba, ban
fahimceta ba hasalima ban yarda da ita ba.
Abinda na dauka shine ba zata iya tasiri
akaina ba sai gashi lkc guda na fahimci ashe
SO gsky ne domin tamkar kwayar virus yake
wajen saurin fadada, yana da ma2kar gudu a
cikin jini hakan kesawa yayi saurin bin sassan
jiki kwatankwacin yadda yabi jinina ya hana
min duk wani sukuni....“
Nayi saurin jan wani dan karamin tsaki nace “

To ni ina ruwana?? “
Ya juyo izuwa gareni yace “abinda kika kasa
fahimta shine na kamu da sonki duk da cewa
ban sanki ba bansan daga inda kike ba
hasalima ko sunanki ban sani ba, wannan na
daga cikin aikin SO ba ruwansa da kyau, muni,
asali ko kuma banbancin akida.
INA SONKI!!! kalmar da bana shayin fadarta a
ko‘ina domin na tbbtr shine abinda ke ckn
zuciyata.
Nayi saurin dago kaina idanuwana suka zaro
tamkar zasu fado, Kana sona??
Tambayar dana fara yi masa kenan na dora da
cewa “ Ban taba tsammanin jin wannan
kalmar daga bakinka domin wadanda suka fika
komai ma ba wanda ya taba 2nkarata da
wannan maganar...“
hakan na nuna miki irin son da nake miki
kuma yana tbbtr miki ni masoyi ne gaske bana
yaudara ba.
ya fada kyakykyawar fuskarsa na kaina.
Na ajiye littafan dake hannuna na mike da
dubeshi tare bata hade rai wanda ban taba yin
irinsa ba nace “ kaga leader kake kowa??
wasanka yana yin yawa yakamata kasani
akwai wasan da kakanni kawai ake yiwa
irinsa....
Ya katseni da cewa “Wlh ba wasa nake ba
idanuna kadai sun isa su tbbtr miki da haka,
amsa kawai nake jira daga kyakykyawan
bakinki wanda ta yiwu shine danbar fara
sabuwar rayuwata“.
Amsa kake jira?? na tambaya ina kllnsa nace “
kana tsammanin amsata zata zo a yadda kake
so ne?? to kayi kuskure, babu wata maganar
soyayya tsakanina dakai kayi gaggawar janye
wannan maganar ko don tsira da mu2ncinka a
idona.
ya gyara zamansa izuwa kallo na sosai yace “
Bazan taba janye kudirina ba sai dai idan har
zaki fada min shin wani mummunan hali
gareni da za‘a ki sona sbd dashi??
Na girgiza kai nace “ba wani mummunan hali

amma koba komai banbancin class... kuma ma
kawai bana ra‘ayin soyayya yanzu.“
amma.............
Nayi saurin katse maganar tashi da tsawa
nace “Bana sonka!! nace bana yi!! karka kara
zuwar min da zan2ka irin wadannan sbd nafi
karfin jinsu bare na yarda dasu.“
Fuskarsa ta sauya ma2ka ckn yanayin da ban
taba zaton akwai ranar dazai zama haka ba a
yadda nake ganinshi, yace “ Naji na amince
kuma na hakura amma zanso kiyi abinda idan
na tafi bazan zargeki ba sai dai na zargi
kaina.“
Kamar yaya?? na tambaya ina kllnshi.
Yace “ kiyi min duk irin jarabawar da kika
gadama a duniyar nan da kowacce nau‘in
tambaya kîka gadama idan har na fadi to
shikenan na hakura kuma bazan taba zarginki
ba sai dai na zargi kaina.“
Idan kuma ka amsa fa??
Nayi saurin tambayarsa.
Yace “sai ki dauki kaddara ki yarda muyi
soyayya.
Na bishi da kallo na koma inda nake a baya na
zauna nace “ ba tambaya daya zanyi maka ba
sai dai guda uku kuma cikin kwanaki uku a jere
idan ka fadi a daya ko kayi tsallaken rana daya
shikenan dole ka rabu dani.“
Na amince.
Ya fada ba tare da jinkiri ba....
Na bishi da kallo ckn mamakin yadda bai
tsorata da komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login