Showing 15001 words to 18000 words out of 47324 words
dawo nan
as temporary time kafin me kujerar ya dawo
ya karbi wurinsa, ya dago idonsa yace “cire
kudi, turawa ko kuwa kawai yawon
shakatawa???“
Na dan yi dariya nace “Ah haba yawon
shakatawa a banki kuma?? Bama dai zaka ji
abinda ya kawoni ba......
Me yasa?????
Ya tambaya yana dubana.
Nace “sbd ba wajen ka aka turoni ba wanda
aka 2roni wajensa baya nan kaga kuwa a
matsayina na y‘ar aike dole na koma na fada
idan ance na dawo wajenka na dawo!!“
Yayi murmushi yace “Nima zanyi farin ciki ki
koma din 2nda na tbbr idan aka tambayeki wa
kika tarar zaki ce masoyinki FARUK kika gane
a wajen, kinga ko tanan na fara samun shiga a
wajen momi da dadynki.“
Na zaro cak a jakata da biro na dora a tebirin
dake gabana na fara rubutawa nace “Tayaya
kake tsammanin zan fadi haka???“
Sbd nasan ba zaki taba yin karya ba.
Na tura masa cak din bayan dana gama
rubutawa ya kira wani jami‘in banki ya
umarceshi daya je ya ciro min kudin muka cgb
da hira ckn nishadi, Na dubeshi nace “Lallai
bayan kokari ma harda daukan dala ba gammo
kake yi, AIKI irinna banki + KARATU irinna
computer ba hu2 kenan???“
Ya kwantar da kansa jikin kujerar da yake kai
yace “Aikin ne ya jawo kara2n kuma duk tare
suke tafiya basu shiga lokacin hutu ba, Muna
da rauni ta bangaren masu ilmin computer
shine dalilin da yasa aka 2rani na karo sani
akanta don cgbn wannan bankin, kinji dalili.“
Na bishi da kll nace “yanzu na gano dalilin da
yasa bana ganinka in nazo, wato dan lele ne
kai a bankin.“ ya daga kai yace “of course
kamar yadda na zama dan lelen zuciyar
humaira.
Nayi saurin girgiza kai nace “Waye ya gaya
maka? Baka samu wannan damar ba ba kuma
zaka taba samu ba har abada sbd ni zuciyata
FARUK ne kawai a cknta kuma daga shi na
rufe ba wanda zan sake bawa dama ya shiga
bare ma har yayi tasiri.“
Ya dan lumshe ido ya dago kai yace “ faruk na
godiya hade da alkawarin rike amana bata
shekaru kawai ba ta HAR ABADA.“
Na jinjina kai nace “A wasu lktn alkawari nada
saukin dauka amma saukewa nada ma2kar
wahala“.
Ya gyara zama yace “Ina da tbbcn duk nauyin
alkawari ma2kar ke na daukowa shi to zan
sauke sbd ni akan SOYAYYA..... ni kaina
mamakin kaina nake yi.“
Na bishi da kallo kawai, nima na dade da
yarda yana da zafin soyayya, jim kadan jami‘in
nan ya dawo ya dora leda bisa tebirin dake
gbnmu tare da cewa “Sir, gasu an ciro.“
Ok thank you, koma bakin aikinka.
Ya 2ro minsu yace “An cika aiki.“
Na kauda kai nace “OK a takaice dai kora ta
kake ko??“
Ya girgiza kai yace “Mezai sa na koreki??
Alhalin kece fitilar dake haskawa zuciyata
hanyar daya kamata tabi?? Gani dai nayi
kawai kin samu abinda ya kawo ki.“
Na juyar da kujerar da nake kai izuwa gefe
nace “Amma ban gaji da klln faruk ba“.
Yayi murmushi yace “Shima bai gaji da ganinki
ba sai dai idan kuka kwantar da hankalinku
wannan rabuwar ta wucin gadi ce domin zaku
hadu a rayuwa ta har abada.“
Na saki murmushi kawai.
Yayi saurin matsowa gaban kujerarsa yace
“yauwa ni kuwa na manta ban karbi lambar
sarauniyar tawa ba, na dago wayar dake
hannuna kaina na kanta nace “ Ai da farko na
zaci itama zaka canka ne 2nda shi yafi komai
sauki a wajenka.“
Yace “Eh don dai kawai idan kika bani da kanki
zata fi martaba ne a idona, amma da sai dai
kawai kiji kira.
Na 2ra wayata izuwa gabansa nace “ai ko
ifritu ba yadda zaiyi ya canki lambarnan
dai~dai.“ Yayi dariya kawai ya 2ro min wayoyi
biyu na dauki tashi lambar na mike tare da
rakiyarsa na fito daga bankin.
Na dubeshi nace “kaga me girma manager nifa
bance kayi min rakiya ba.
Yayi murmushi yace “bai dace ba ace
sarauniya kamarki tana tafiya babu dogari ko
daya a gefenta.“
Na girgiza kai nace “A yanzu ai ba sarauniya
da dogari bane ke tafiya, SARKI da SARAUNIYA
ne.“
murmushi ya fadada a fuskarmu har zuwa
sanda muka karasa jikin motata, ya bude kofar
gaba tare da dora hannunsa a goshinsa ckn
salo na sarawa tamkar wani soja yace “shiga
da lfy tauraruwar taurari.“
nayi murmushi kawai na shiga na zauna ya
mayar da kofar ya rufe da yake glass din a
sauke ya dafa kofar da hannunsa biyu yace
“murmushinki ya dace da fuskarki
kwatankwacin yadda ni dake muka dace da
juna, sai mun hadu next time farin ganina.“
Ya juya ya koma ckn bankin nabishi da kallo
murmushi na tashi a fuskata har sanda na
daina ganinshi a hankali na daga glass din
motar tare da takata na nufi gd.
Wannan shine tarihin asalin fara soyayyata da
FARUK.
************ ************ ****
Daga ranar ne kwanci tashi alakarmu na kara
karfi har takai soyayya me karfi ta shiga
tsakanina da FARUK wadda tafi gaban a
kwatanta, har takai mun zama ababan misali
domin bawai tsakaninmu kawai ba kowa
yasan alakarmu da kuma karfin syyrmu.“
Musamman a makarantarmu wanda kowa yayi
mamakin ganinmu tare rana tsaka muna
soyayya tamkar bani ba, daga nan ne kuma na
zama ta mutane muka fara kulla abota da
mutane daban-daban ta silar faruk.
Ban taba jin son wani bil‘adama a duniya kmr
FARUK ba kuma ban zaci zan tsinci kaina a
hakan ba, takai ga bana iya yi masa musu a
duk abinda ya fada, bana ganin rashin dai-
dainsa a duk abinda yayi, Sa‘a daya da nayi
da shima yana ma2kar sona domin idan son
da yake min baifi nawa ba to nawa bazai fi
nasa ba.
Kasantuwar kusanci da karfin syyrmu yasa har
aka fara kiranmu da sunaye daban-daban
wasu suce LAILA da MAJNUN, wasu suce
ANGELICA da MACIOLA dadai sauransu.****
FARUK ya kasance haifaffen garin kano kmr ni,
ckkken sunansa UMAR FARUK MUHAMMAD
yayi primary, secondary da university duk a
garin kano, ya karanci irin abnd na karanta
mathematic economics a BUK. Lbrn rayuwarsa
daya bani wanda nafi tausaya masa shine
kasancewarsa maraya.
Ya rasa mahaifansa 2n yana karami ta silar
hatsarin mota, ya taso ne a hannun kishiyar
mahaifiyarsa me suna hajiya amina, yana
yawan ambaton sunanta a koda yaushe domin
a cewarsa itace gatansa a duniya ita zame
masa uwa da uba ta rikeshi tamkar dan data
haifa a cknta har izuwa yanzu.
Ni kaina na yaba da halayenta da kirkinta
ranar farko da faruk ya kaini gdnsu muka
gaisa da ita, ba shakka yayi sa‘ar samunta
matsayin wacce ta rikeshi har izuwa grmnsa.
A duk ma‘aikatan gdnmu ba wanda baisan
FARUK ba domin sai da takai idan direba yakai
ni makaranta FARUK ne ke dawowa dani a
motarsa sannan ya wuce, kai harta da momi
ma tasanshi kuma tayi farin ciki da ganinsa ta
yaba dashi sosai duk da ban fada mata ba
amma ta fahimci abinda ke tsakaninmu.
Kwanci tashi har lokacin gama makarantarmu
yayi bayan tsawon lkc da muka shafe, ranar
karshe ta rufe laccarmu bayan mun fito na
nemi faruk banganshi ba mufida kuwa na can
ckn kawaye suna irin sallamar nan tasu ta
kawaye, nima nayi sallama da iya wadanda na
sani da yake yunwa nake ji kai tsaye
restaurant na dosa domin gani nake kmr
bazan iya kaiwa gd ba, zamana keda wuya na
umarci dan matashin saurayin dake jigilar
kawo abinci na gaya masa abinda nake so ya
kawo min.
A hankali FARUK ya karaso tare da zama a
kujerar dake fuskantata ya dubi me kawo
abincin tare da cewa “kai kawo min abinci da
sauri.“
Na dubeshi nace “wane irin a kawo maka
abinci baka ga na riga ka bane??“
Ya dubeni ya tabe baki yace “ina ruwana ni??“
ya juya gareshi yace “ kai aje a kawo min ka
taho da juice me sanyi.“
Na kara hade rai nace “baya yiwuwa wlh na
riga ka don haka dole ni za‘a fara kawowa.“
Me kawo abincin ya tsaya kawai ya kasa tfy
ya dubemu yace “to ai ni na rasa yadda zanyi
daku ai duk kun rudani, pls daya ya hakura a
fara kawowa daya mana.“
Faruk yace “kai manta da ita dallah jeka kawo
mana.“
na kauda kai nace “a manta dani ko a manta
dakai.“
Ya kalleni ya bata rai yace “karki ce zaki raina
ni fa don bana wasa da yarinya ranki zai baci
yanzu.“
Na zabga masa harara nace “sai dai naka ya
baci wlh.“
Ya hade rai tare da mikewa ya nuna ni yace
“KE!!“
Na mike nima na nunashi nace “KAI!!“
Muka dan dubi juna na tsawon lkc jimawa
kadan muka kyalkyale da dariya yace “gsky kin
iya fa sai kace gaske??“
Na zarce da dariya nace “Na iya koka iya gsky
dakai actor ne zaka kwashi yan kllo“.
Kai! dama ba fadan gaske kuke ba???
Me kawo abincin ya fada ckn AL‘AJABI.
Faruk yace “kai dai je ka kawo mana abinci
don sarauniyar tawa yunwa take ji.
Har aka kawo mana abincin hira muke kafin
mu gama mu tashi.
Daga ranar mukai sallama da makarantar
domin mun kammalata sai dai koda NI da
FARUK kllm sai munyi waya ta tsawon lkc, ko
mu kasance muna hira ta WHATSAPP wataran
kuma har gdnmu yake zuwa.
Haka muka cgb da rayuwa ckn jin dadi kafin
KALUBALE ya biyo bayan soyayyarmu wanda
yayi sanadin zubar hawaye na HAR ABADA.
Wannan wani QALU BALENE..?
Bari in barku haka kar kuce nacika surutu
**** BAYAN WATA BIYU DA KAMMALA
MAKARANTARMU ****
Ranar wata juma‘a da bazan manta ta ba tun
misalin 4:30pm dana kwanta a dakina na
kishingida kaina bisa lallausar katifar gadona
sanyin A-C na ratsani ta ko‘ina daga na‘urorin
sanyaya dakin, fuskata fresh ba wani abu dake
damuna musayar sakwannin soyayya kawai
muke yi ni da faruk. Murmushi ne kawai ke
tashi daga fuskata a wasu lktn ma nayi dariya
har da samba2na ni kadai, FARUK nada
barkwanci sosai abune mawuyaci kuyi magana
ta min2na dashi bai saka dariya ba.
2nda muka fara hirar ba wanda ya gajiya a
cknmu sai da aka kira sallar magariba sannan
mukai sallama a hakan ma ba‘a son ranmu ba,
Na tashi nayo alwala na fito falo momi na
zaune har ta idar da tata sallar na jawo
darduma nima, kiran sunana da tayi yasa na
dago kai tace “wai lfy naji ki kina samba2
harda dariya ke kadai?? Na danyi kasa da
kaina nace sambatu kuma??
Ah momi da Fa..ruk... muke hira....“
Nakai karshen maganar a kunyace.
Tadan harareni ckn murmushi tace “OK hira ce
tayi dadi ko??“
Na danyi dariya kawai na tayar da sallah ta.
Bayan na idar baifi da min2na biyar ba daddy
ya shigo da sallamarsa duk muka amsa masa,
zamansa keda wuya muka zarce da hira ckn
nishadi da walwala.
Zuwa can daddy ya kwantar da kansa bisa
kujerar da yake kai ya dubeni sosai yayi
murmushi yace “My daughter yanzu ne lkc
yayi da yakamata ace kin samu mijin aure
domin mutane sun dade suna cece-kuce
akanki amma na toshe kunnuwa na,
Alhamdulillahi kin samu duk kulawa daga
garemu da kuma gata lkc kuma yayi da dole
muma zamu aurar dake domin ke macece
babu wani gata na karshe daya rage muyi miki
kamar aure.
Momi tayi murmushi ta dubeni tace “gskyne
musamman da yake takai munzalin da ba
abnd ya rage mata sai aure.
hmm... Kwanci tashi kenan ba wuya yau
daddy da kansa na zancen ya aurar dani, a
raina sai naji wani dadi domin damar da nake
jira kenan gata tazo burina na daf da cika.
daddy ya gyara zama yace “akwai babban
abkn kuma aminina wanda tsohon shugaban
kasar nan ne to yana da dansa me suna tijjani.
bansan a inda ya ganki ba to dai yasa uban ya
fada min wai yana sonki kuma harma mun
tsayar da rana gobe zai zo ku tattauna ko
Allah zaisa ku fahimci juna.
Kirjina ya buga da karfi na dago kai na dubi
daddy kawai nama kasa cewa komai har ya
tashi izuwa dakinsa, na koma kan kujera na
zauna na tabe baki nace “Momi me yasa ba
zaki gaya masa ba??“
In gaya masa me???
Ta tambaya tana dubana.
Nace “amma kuma kinsan ni ina da wanda
nake so ta yaya.....“
Ta harareni tace “rufa mana baki mara kunya
da akai ki tashi kije ki fada masa mana, ko ni
kin taba fada min kina son wani??
Na kara mirgina kai nace “amma dai nasan kin
gane ai don Allah ki fada masa kinji“.
Momi ta mike tace “KE! nifa a wannan harkar
taku ba ruwana kinji.“
Ta wuce tabar falôn, nabi ta da kallo kawai na
zamar da kaina na kwanta bisa kujerar da
nake kai, to ma wai meye zaisa na dami
kaina?? Nasan dai daddy ba yadda za‘ai yayi
min auren dole.
Na dauko tantsamemiyar wayata kirar
blackberry, zuwa can na kauda wayar daga
idona a abinda daddy ya fada ya dawo min,
nayi y‘ar gajeriyar dariya.
hmm... tab! wai dan tsohon shugaban kasa,
to ai ni ko dan shugaban kasa me ci yanzu bai
isheni kll ba.
Na lalubi lambar FARUK muka dora daga inda
muka tsaya.
**Washe gari 2n misalin karfe 11:30 na safe
jerin gwanon motocin alfarma har kusan guda
goma suka shigo harabar gdnmu kowacce na
takewa y‘ar uwarta baya, a dai-dai lkcn ina
can sashin saman bene sbd inda na saba
hawa kenan duk sanda nake bukatar kadaici a
gdn namu.
Na bude labulen tagar dakin da nake ciki na
hangi fitowar wanda na tbbtr shine tijjanin sai
wani shan kamshi yake yake yana hura hanci
cabinets na take masa baya, bansan sanda na
zabga masa harara ba 2n daga nan inda nake
alamar fara jin haushi da tsanarsa 2n yanzu
kenan.
Na mayar labulen na koma kan katafaren
gadon dake madaidaicin dakin na kwanta
Allah-Allah nake kawai barci ya daukeni.
Jim kadan wata y‘ar aikin gdnmu ta hawo
izuwa inda nake ta karaso tare da cewa “Ranki
ya dade momi ce tace a gaya miki bakon ki
yazo.“
ji nayi kmr na bigeta don haushi.
Inda a dah ne da tasha tsawa da fada intayi
wasa ma harda mari amma da yake yanzu na
canja daga kwance nace “salama kyaleni kinji,
je kice mata kawai barci nake.“
Ba wata gardama kuwa ta juya.
Na jawo filo tare da gyara kwanciyata a raina
nace ‘indai nice ya hada kansa da wahala‘, ko
2nanin na fito ma bana yi. Sai bayan akalla
min2na 30 dan ni har na fara barci ma naji
momi na kiran sunana.
Na dago kai na dubeta a jikin kofar dakin ta
tsaya hannunta a kugunta ta hade rai zuwa
can tace “baki san tijjani yazo fiye da min2na
talatin yana jiranki ba?? ko ban aiko a fada
miki ba?? wato sbd wulakanci shine kinsan da
zuwansa kikayi kwanciyarki ko?? To ki tashi
maza ki sauka kasa yana falo ke yake jira.“
Momi nifa..... Zaki fito ko zaki fito ba??
ta katseni tare da tsareni da ido.
Dole tasa na mike na sakko daga kan gadon
na wuce ta gbnta kai tsaye dakina na dosa
maimakon nayi wata kwalliyar kirki saina
dakko katon hijabina wanda mafi yawa sai
zanyi sallah nake sashi nasa har jan kasa
yake ina ma ina da nikab wlh sai nasa haka
dai na fito falon fuskata ba wani annuri nayi
kicin-kicin, shi kuwa yana ganina sai ya wani
bude baki wai murmushi yayi yace “sannunki
da fitowa uwar kyawawa, ai ance min kina
shiryawa ne nace a barki ki gama a nutse.“
Na girgiza kai nace “Ba wani shiri da nake yi
kawai yanzu nayi niyyar fitowa ne.“
Ya dan daga kai tare da cewa “hakan ma ya
birgeni, Ah kamar yadda nasan an gaya miki
sunana TIJJANI nazo ne domin na sanar dake
irin son da nake miki ina fatan zaki karbi syyta
hannu bibbiyu.
hmm.. soyayya! na fada tare da dubansa sosai
nace “kaga mallam tijjani ba wani boye-boye
ko bata lkc da zamu tsaya yi, indai don
wannan ne to ba zaka taba samu ba ka ngd
da zumunci a matsayinka na dan aminin
mahaifina ka tashi ka tafi kawai.“
Nakai karshen maganar tare da kauda kai.
Da alama yayi ma2kar mamakin maganar ya
bini da kallo kawai zuwa can yace “Ah humaira
ni kuma sai nake ganin duk duniya idan ta
fuskar dace ne nafi kowa dacewa dake.“
Na dan saki murmushin rainin hankali nace
“hm.. a hakan??“
of course!! ya fada tare da dorawa.
“Idan kika duba dukkanmu y‘ay‘an masu hali
ne, mahaifina tsohon shugaban kasa ne kuma
yanzu haka yana wakiltar kasar nan a zaman
koli na majalissar dinkin duniya, ke kuma
mahaifinki shahararren dan kasuwa ne aduk
fadin afrika.
Kinga kuwa ko tanan mun dace da juna.
Na dan jinjina kai nace “Ok! dama sbd dukiya
zamu so junanmu kenan daga ranar da
dukiyar ta kare mun rabu kenan??“
Na rufawa tambayar baya da harararsa.
Abin ya kulad dashi sosai ya dago kai sosai
yace “yakamata ki sani nifa babban mu2m ne
a kasar nan me dimbin dukiya ya zama dole ki
girmama ni.“
Dukiya?? Na tambayeshi tare da dorawa da
cewa “da motoci goma ka shigo nan a
matsayinka ma na dan wanda dukiyar
al‘umma ya rike, idan ka fita ka tambaya ina
ma‘ajin gdnnan ya baka mukullin ma‘ajiyar
motoci ka debi 100 idan kana so wadanda da
zunzuru2n kudin halak ma aka siye su.“
Idanunsa suka zaro waje yace “kina nufin ni
mahaifina barawo ne??“
Na kara gyara zama nace “maganar mu2nci
kuwa babu 2nda aka wanko kafa aka taho
barar abinda ba za‘a samu ba sbd alfarma ba
zata samar dashi ba gashi kuma kudi basa iya
siyanshi shine SOYAYYAR HUMAIRA.“
ya danyi shiru jim kadan yace “yakamata muyi
magana ta fahimta pls karki manta daga nesa
nazo duk domin ke.“
Nesa?? sai ka koma ka fadawa nesa da yan
nesa abnd kaje nema baka samu ba, na mike
na dora da cewa “bata lkcn ya isa haka