Showing 18001 words to 21000 words out of 47324 words
zan
shiga daga ciki“.
Ya dan marairaice yace “bai kamata kiyi min
haka ba yakamata ki bani dogon lkc muyi
magana ko dôn kasancewar nayo doguwar tfy.
Na juya tare da cewa “yanzu ma ai ba korarka
nayi ba, ga T.V nan kayi kllnka son ranka
amma idan ka gama karka kashe can an jima
zan kalli wani program.
Na wuce kai tsaye na doshi dakina kan ma
nabar falon shima ransa a bace ya mike ya
fice, na juya na kyalkyale da dariya KORA DA
KALAMAI kenan na tbbr bazai taba yin
marmarin dawowa ba, dama ba SON gsky ya
kawoshi ba kalarshi ma tafi kama data
munafukai don duk abinda yake fada babu
alamun har zuciyarsa hakane.
Na wuce dakina ban kara komata takansa ba
** Misalin karfe 8:00 na dare ina zaune bisa
dardumata byn na idar da sallar isha‘i, kwala
min kiran da naji ana yi kuma yasa na saurara
dakyau.
Bisa mamaki daddy ne abinda bai taba faruwa
ba kenan sai yau na jefa dardumar kan gado
na tare da nufo falon, daddy na tsaye ckn
fusata ya hade hannunsa biyu ta baya.
Na zauna tare da cewa “daddy barka da
dawo.....“
Tun kafin na karasa Ya katseni da cewa
“Menene dalilin da mu2m zai taso 2n daga
katsina domin ke, kuma na gaya miki
matsayinsa da kuma ko waye shi amma
maimakon ki karramashi saima ki
wulakantashi??
Me kika fishi??
Anji ma bakya sonsa ki mu2ntatashi mana
idan nazo sai ki fada min baiyi miki ba insan
yadda zanyi na sanarwa mahaifinsa amma sai
ki bishi da bakaken maganganu??
Shekararmu 40 da mahaifinsa ke baki isa ki
shiga tsakaninmu ba.“
Na danja da baya a kujerar da nake zaune
nace “kayi hakuri idan hakan ya bata maka rai
gsky bana sonshi ne ina da wanda nake so
kuma shima ai da laifinsa don me zai......“
Tsawa daddy yayi min a karona farko a
rayuwata da fadin “Ki rufa mana baki, ki shirya
TIJJANI ne mijinki nan bada dadewa ba za‘a
saka ranar aurenku.
Sbd girgiza bansan sanda na mike tsaye ba
kaina yayi wata juyawa sau daya, na maimaita
abnd daddy ya fada “TIJJANI ne mijina??“
Kwarai!! daddy ya fada.
Nace “koda hakan na nufin bakin cikina da
tbbt a takaici na har abada??
Daddy ya amsa da “koda hakan na nufin
mutuwarki da tbbt a kabari na har abada.“
Duk da matsananciyar damuwa data bayyana
a fuskata, idanuna suka fito waje kamar zasu
fado.
ba AL‘AJABIN mgngnunsa kawai nake ba,
amma yadda idonsa ya rufe yake zazzaga min
ruwan bala‘i ta inda ya shiga ba tanan yake
fita ba.
Ya kara da fadin “da bakinsa yake fada min
kince masa MUMMUNA, BANZA, DABBA!!
kmrsa ki fada irin wadannan maganganun??
Kawai ji nayi kmr an sare min gwiwoyi, lallai
TIJJANI munafuki ne lamba daya abin nasa
harda kage da sharri kenan??
Wasu hawayen takaici irinsu na farko a
rayuwata suka gangaro min, Na gyada kai
nace “ eh na fada masa haka sbd ya cncnci
fiye da haka ma kuma zan kara gaya masa
haka duk inda muka hadu, ckn sheshshekar
kuka nace “daddy karka manta ka bani ilmi me
yawa wanda yasa nayi wayewar da nafi karfin
ayi min auren dole.
Bana sonsa!! Bana sonsa!!
Ina da wanda nake so kuma shi zan aura bana
jin akwai wanda zai hana ni don addini ma ya
bani dama.
Kuka na ya karasa fitowa na juya izuwa
dakina, ina zuwa a hankali na zauna a gefen
gadona na hada kaina da gwiwa naci gaba da
ku kan da nake yi. Tijjani ne mijinki....
Koda hakan na nufin mu2warki da tbbt a
kabari na HAR ABADA.
Kalaman dake kara yawo a zuciyata kenan,
ashe har akwai ranar da daddy zai fada min
maganar da zata sani damuwa? Akwai ranar
da zai aje dunbin son da yake yimin a gefe ya
fada min bakaken maganganun da zasu sani
kuka??
Na dade a zaune a haka har zuwa sanda naji
an dafa ni, nayi saurin dagowa muka hada ido
da momi. Na kwantar da kaina bisa cinyoyinta
ckn kuka nace “momi daddy ya daina sona
yanzu,“ Ta dago fuskata muka fuskanci juna
tayi saurin grgz kai tace “ba haka bane ransa
ne ya baci kuma kema da laifinki bai kamata
ki yiwa TIJJANI haka ba“.
Wlh momi abnd yace na fada masa duk karya
yake yi ban fada ba.
momi tabi ni da kll tace “amma me yasa kika
cewa daddynki kin fada??“ na goge hawayena
nace “Sbd ya tbbr bana son TIJJANI.“
momi ta jinjina kai tace “yanzu dai kiyi shiru ki
share hwynki, dadynki ba wanda yake so a
duniya kmr KE duk abnd ya fada nasan bazai
taba aiwatar dasu ba.“
Na karasa goge dukkan hawayen dake idona
nace “ba lallai ya saurareni yanzu ba momi“.
Tayi murmushi tace “nafi kowa sanin halinsa
bashi da wuyar sakkowa duk irin fushin da yayi
jeki kinji??“
Na bita da kallo kawai a hankali na mike na
doshi dakinsa gwiwata a sanyaye, Zaune na
tarar dashi a tsakyr dakin bisa dardumarsa ya
idar da sallah, na karasa inda yake na zauna a
gbnsa tare da sunkuyar da kaina kasa ckn
sanyin murya nace “Daddy don Allah kayi
hakuri nasan ban kyauta ba kuma na bata
maka rai dana......“
Nayi shiru sakamakon daga min hannu da yayi
yace “Ya isa haka my daughter koda baki roka
ba ya zama dole na yafe miki kan KUSKURE
DAYA TAK!!.“
Nagode my dad na fada dai-dai sanda nayi
yunkurin mikewa.
Ya dakatar dani da cewa “wanene wanda kike
so din? kuma yaushe kuka hadu?
Ya akai bansanshi ba kuma??“
Na danyi shiru kmr bazan ce komai ba zuwa
can nace “sunansa FARUK, A makarantar
koyon kwamfuta muka hadu dashi kuma har
gdnnan yana zuwa momi ma tasanshi tfyr da
kayi ce ta tsawon watanni yasa baka sanshi
ba.“
Ya kada kai yace “Wajibi nane na baki wanda
kike so amma ki sani mafi girman gatan da
zanyi miki a yanzu shine na tbbr na zaba miki
miji nagari idan har na samu wani matsala
game dashi bazan amince dashi ba.“
Na gyada kai tare da cewa “Insha-Allahu zaka
sameshi duk yadda kake so,“ Shikenan kice
masa yazo ina nemansa“.
Na amsa da fadin “To, Sai da safe my dad.“
Kai tsaye na fice daga dakin nasa na koma
nawa, har yanzu momi na zaune bata tafi ba
na zauna gaf da ita na saki murmushi tare da
dakko hannunta na hada ckn nata nace “Momi
kinsan me?? yace in fadawa FARUK yazo yana
nemansa“
Tayi murmushi tace “Humaira kina son faruk
da yawa fa!! kina barci ma fa kiran sunansa
kike yi.“
Na danyi dariya nace “Ah haba momi a barci
kuma??“
kiyi ta fadin FARUK! FARUK!! FARUK!!!“
Na kyalkyale da dariya, momi ta mike tare da
cewa “idan zaki kwanta ki rinka kashe kwan
nan haskensa yayi yawa.“
Ok gud night my mum.
Na fada ta juya ta fice.
Na karasa kwanciya kan gadon sosai na zaro
wayata na nemi lambar faruk.
Mun dade muna hira dashi har sai da dare ya
tsala sannan mukai sllma dashi byn na sanar
dashi sakon daddy.
***FARUK bai zo gdnmu ba sai byn kwanaki
biyu misalin 5:00 na yamma, daddy na gd a
lkcn da kaina na fita na yi masa jagora izuwa
falo inda daddy ke zaune bisa kujera.
ya amsa sallamar da mukai sai dai daga
shigowarmu na lura da wani kllo da naga
daddy na yiwa faruk anya kuwa....
Ya zauna a kasa daga jkn kujerar dake
fuskantar daddy, ni kuwa mikewa nayi nabar
falon har na shiga dakina hankalina ya gaza
kwanciya na dawo da baya don jin hirar da
zata gudana tsakanin FARUK da DADDY.
daga inda na tsaya ina hangensu tare da jin
abnd suke fada.
*dai-dai sanda na tsaya faruk ne ke cewa
“...cikakken sunana Umar faruk jibrin,
mahaifina mllm jibrin dalhatu da mahaifiyata
hajiya Hauwa‘u sun rasu 2n ina karami
hakan....
Daddy yace “sunan mahaifinka mallam sunan
mahaifinta Alhaji banbanci na (1) kenan,
mahaifanka sun mu2 nata nada rai banbanci
na (2) kenan, ina sauraronka.“
Ba tare da wani damuwa ba faruk yace “na
sami yin kara2 kurewarsa shine degree dana
samu anan bayero university...
Daddy ya gyara zaman hularsa yace “Ita kuma
masters gareta a OXFORD UNIVERSITY
england, another deference kenan.“
Faruk dai bai kula ba ya karasa da fadin yanzu
haka ina aikin banki nakai matsayin activities-
director.
Daddy ya kwantar da kansa ckn kasaita bisa
kujerar da yake kai yace “Akwai banbanci me
yawa tsakaninka da y‘ata wanda ya wuce a
misalta, kasan ko danbe ake akwai wanda kll
daya zaka masa kasan yafi krfnka!! Don
haka.........
Jirin da naji yana neman dibata ne yasa nayi
saurin dafe kaina nabi fuskar masoyina faruk
da kll kawai na juya da sauri na shige dakina
domin kunnuwana ba zasu jure jin
maganganun da daddy ke fada ba, don na riga
na gane inda suka sa gaba.
Ina shiga kofar na mayar na rufe nabi jikin
kofar daga sama har kasa hawaye suka
gangaro min, wai me daddy ke nufi ne?
Nima tan bayana kenan ga masu karatu..!
Medaddy kenune..?¿ Allah sa kuna fahinta..!
SABAHUL KHAIR..!
Tambayar dana fara yiwa kaina kenan
tambayoyin suka cgb da yawo a zuciyata.
wai me yasa daddy ke yimin haka ne??
Sai yanzu a lkcn da yakamata ya samar min
farin ciki fiye dana ko yaushe yake kokarin
dakile hakan??
Na dade a haka zan2kan na karo da juna a ckn
kwakwalwata, dakyar na rarrafa izuwa kan
gadona na kwanta kawai idona a bude karrr
amma 2nanin dana tafi yana kama da ace
barci nake yi, ni kaina bansan yadda zan
kwatanta ynyin da na shiga a wannan lkcn ba.
Allah sarki faruk kawai nake 2nawa wanda ban
taba ganin mu2m irinsa ba, hakurinsa kawai
ya isa yasa na kara kaunarsa dubi yadda
daddy ke fada masa bakaken maganganu
amma ko kadan ba saima ya zamana kmr
kara masa karfin gwiwa yake yi.
Ni dai duk ranar ban ma koda yi sha‘awar
fitowa daga dakina ba. washe gari kuwa da
wani azababben ciwon kai na tashi wanda ina
tsammanin ban taba yin kmrsa ba, sai duk da
wuyar da yake bani ban damu ba don ba shine
a raina ba abinda ya dame ni daban, momi
cema ta rude ta takura min akan lallai mu tafi
asibiti amma naki don ni nasan meye dalilin
ciwon. Can misalin karfe uku na rana ina
kwance abin duniya ya isheni ina son na kira
faruk amma na kasa, ringing da wayata ta
dauka yasa na dago kaina na mika hannu na
jawota ina me runtse ido sbd yadda kaina ke
sarawa.
hmm.. DAN HALAK na fada a zcyt sanda nabi
secreen din wayar da kll a hankali na daga tare
da kaita kunnana sautin muryarsa ya ratsa
jikina na kwantar da kaina bisa gadon na
amsa sllmr da fadin “W salam farin wata sha
kallo.“ Nayi saurin zarcewa da fadin “Don Allah
ya kuka karke da daddyna jiya??“
Ya danyi dariya yace “kina so kiji na jiraki
30minutes koki dan rakoni, na kira wayarki har
sau uku baki daga ba?? sannan baki kokarin
kirana ba a tsawon awannin da aka shafe da
faruwar abin??
Na dan kauda wayar daga kunnena dama a
jiyan ya kirani?? Lallai na shiga wani yanayi
da yawa. Na mayar da ita tare da cewa “uhm!
faruk kayi hakuri da wannan, amma dai don
Allah ka fada min ya akai??“ Yayi murmushi
tare da cewa to kin shirya??
Da sauri harda gyada kai nace “EH“.
Ya fara zano min hirar 2n daga farko duk
yadda na jita haka yake fada sai da yazo kan
gabar da nake so nayi saurin mikewa zaune
duk da karuwar da sarawar da kaina keyi
amma na jure duk don naji abnd banji ba, ya
karasa daga dai-dai inda na tsaya da ji da
fadin:
“.....don haka bawai zan yarda ka auri
humaira don kun dace bane ta bangaren
dukiya ko alfarma ba sai dai don kun dace da
son junanku, dôn haka lallai ka 2romin
magabatanka ckn kwanaki uku rak!! domin
muyi magana.“
Idona yayi saurin budewa kaina dake
mummunar sarawa ya daina, bugawar da
zuciyata keyi na fargabar abnd zanji ya daina,
Nayi saurin gyara zamana nace “Faruk da
gaske??“
“Kwarai“ ya amsa tare da fadin “kina mamakin
daddy ya bani ke ko da kina tsammanin zai
hanaki wanda kike so??“
Wani yalwataccen murmushi ya fadada a
fuskata farin ciki sabo ya ziyarci zucita na
koma kan gadon na kwanta tare da cewa
“Baka san yadda akai bane!!“
Sai dai idan kin fada min, yace.
Na kada kai nace “To ai ni jiya labewa nayi ina
sauraron hirarku farkonta kawai naji hankalina
ya tashi 2n jiya ba‘a dai-dai nake ba wlh.
Faruk yayi dariya yace “To banda ke wa yake
hukunci da farkon abu ba tare da yaji
karshensa ba?? Ashe ni ban sani bama
tauraruwata bata ckn walwala?? Nifa duk nayi
2nanin farin ciki ne yayi miki yawa.“
Na gyara kwanciya nace “INA!! ban taba yin
barci harda mafarki alhalin idona yana a bude
ba sai jiya, Ga wani ciwon kai da nayi me taba
kwakwalwa.“
Ya sake yin gajeriyar dariya yace “TO!! amma
ina fatan kin warke??“
Na gyada kai nace “Eh mana kana fada min
lbrnnan naji na warke.“
Dukkanmu mukai dariya.
Kina sona da yawa fa!!
Ya fada.
Na dan zunburo baki nace “kai kuma fa??“
Yace “Ni? hm.. bawai SO kawai ba akwai
KAUNA da SHAKUWA da BEGE gareki a koda
yaushe gami da ALKAWARI wanda bazai canja
ba duk rintsi duk wuya ba wani dalili na
rabuwa har mu2wa.
Na lumshe idona kawai muka cgb da hira ckn
frn ciki da walwala na tsawon lkc sannan
mukai sllma.
Sai sannan naji wata YUNWA ta taso min
domin duk yinin yau dama banci komai ba.
lallai na dawo hyycn na fada sanda na mike na
wuce izuwa kitchen.
*duk da cewa ina da shakka akan daddy amma
lkc guda duk wani bakin ciki ya fita daga
zuciyata naci gaba da harkokina ckn walwala,
2nanin zan iya rabuwa da faruk kawai na
sawa in kwanta rashin lfy ina kuma ga an
rabamu din?? Shine kawai abnd na tbbtr bazan
iya jurewa ba.
** Kamar yadda daddy ya nemi faruk ya 2ro
haka kuwa akai bayan kwanaki uku da daddare
suka zo, ina dakina na kishingida bisa tafkeken
gadona fuskata fresh ba kyalkyali kawai take
tana walkiya, zuciyata tayi fari, wayata nakan
WHATSAPP messenger muna hira da faruk.
Ina jin alamun hirarsu sama-sama sai bana
iya fahimtar abinda suke cewa, har sanda suka
gama tattaunawarsu suka tafi.
Farin ciki kmr ya kasheni idan na 2no gaf
muke da fara sabuwar rayuwa wadda nake
hangowa 2n daga yanzu, farin ckn nawa bai
yanke ba sai washe gari da naji abinda ya
wakana tsakanin daddy da iyayen faruk.
Faruk ne ke fada min ta waya, 2n da naji yana
cewa in nutsu kada hankalina ya tashi nasan
da matsala, ashe daddy rufe ido yayi ya
zabgawa iyayen faruk rashin mu2nci hade da
bakaken maganganu tare da yin alkawarin
yarsa tafi karfin tozarcin auren talaka kamar
dansu (FARUK).
Tunda ya fara fada min maganar na mike
tsaye, sanda yakai karshen lbrn kuwa zcyt ta
gama harzuka, kwakwalwata ta dimauce,
idanuna suka kada sukai jajir duk a ckn kasa
da sakanni 30.
Wayar ta subuce daga hannuna izuwa kasa ta
tarwatse komai nata ya rabu da jikinta amma
ban kula ba.
Abin kuma harda yaudara??
Wato daddy na ganin idan ya biyo ta haka
iyayen faruk su zasu fara tilastawa ya rabu
dani.
Nayi dawurwura a guri daya na juya da karfi
na bangaji kofar dakin ta bude na fito da gudu
na izuwa falon momi na tarar a zaune bisa
kujera tayi saurin dago kai tace “Lfyrki
kuwa??“
Na tsaya a gbnta nace “wai momi me yasa
daddy keyi mana haka ne??
Koda yana son rabamu ne bai kamata yaci
mu2ncin iyayen FARUK ba!!
Ashe daddy na falon rufewar da idona yayi ne
yasa na gaza ganinsa.
Yace “kaji shashasha talaka har yana da wani
mu2nci ne???
Nayi turus kawai nabi daddy da kallo wani
takaici da bakin ciki suka rufeni, wlh badon dai
ubana bane a wannan lkcn Allah ne kadai
yasan abnd zanyi.
Na dawo da baya a hankali izuwa tsakiyar
falon duk da cewa ckn fushi nake ma2ka
amma nayi kokarin sanyaya zuciyata na saita
harshena ckn salo na marairaicewa nace
“amma daddy bai kamata ka gyyto mutane da
kanka kuma ka tozarta su ba, idan har kasan
haka zakayi 2n farko gara ace FARUK din ka
fadawa amma ba iyayensa ba.“
Daddy ya matso da hularsa gbn goshinsa yace
“Ok! kina nufin muyi sulhu dashi kenan na
bashi hakuri ko??
Ai hakan da nayi shine kawai abnd yafi a
gareni domin iyayensa sunji zafin wutar
maganganun dana watsa musu dole ma su
tilasta masa ya rabu dake.“
RABUWA!!!
kalma mafi daci a gareni kenan har sai da
takai na kauda kaina kadan lkc guda na dawo
da fuskata gareshi nace “daddy talauci, arziki
ko wata daukaka duk na Allah ne shike bada
su ga wanda ya gadama a sanda yake so
kuma ba abnd ke tbbt face kudirar ubangiji
muma arzikin da muke takama dashi Allah ne
ya bamu kuma badon munfi kowa bane.“
Daddy ya kwantar da kansa jikin kujerar da
yake kai yace “EH!! nafi ki sanin wannan ai.“
Na dan matso gaba kadan nace “Ashe kenan
ba wata hujja da za‘a ce yar me kudi ba zata
zauri dan talakawa ba? tunda duk Allah ya
haliccesu ya.....“
Kaji shashanci banza!!
Daddy ya katseni tare da cewa “har akwai
wata alaka tsakanin mai arziki da talaka da
har zata kai ga aure??
Ai a doka ma hanyar jirgi daban ta mota
daban ba yadda za‘ai na siyar da akuya ta
dawo tana cimin danga ba.“
Na danyi yaken takaici nace “Indai don
wannan ne to karka damu domin dai-dai
gwargwado FARUK nada rufin asiri zai iya
sauke duk wani nauyi na dake wuyansa kuma
koma ba