Showing 12001 words to 15000 words out of 47324 words
ba saima wani karfin gwiwa
da yake da ita, ya tsareni da ido jiran irin
tambayar da zanyi masa kawai yake.
Allah ya sani yana ma2kar birgeni sbd ya hadu
sai dai kawai ji da kai da takamata ta hanani
na amince da ainihin abinda ke zuciyata,
wacce tambaya ma yakamata nayi masa?????
Tambayar dake ta yawo a zuciyata kenan ckn
salo na nazari.
Zuwa can na dago kai nace “tambayar yau me
sauki ce ina so ka canki sunana wanda
mahaifina ya rada min, sau daya kawai zaka
fada idan ka fada ba dai-dai ba ka fadi.“
Yabi ni da kallo tare da gyara zama yace “
Sunanki?? Haba ranki ya dade ta ina kika taba
ganin an fadi sunan mtm daga ganinsa???
SUNAYE na daga abubuwan da suka fi komai
yawa a duniya don haka amsa wannan
tambayar is impossible a ko‘ina, a zatona
zakiyi min tambayane wadda kwakwalwa zatai
aiki wajen gano amsa amma ba canke-canke
ba.
Na danyi gun2n murmushi nace “daga farawa
harka fara karaya?? wannan itace mafi sauki
daga wadanda nayi maka tanadi, koka manta
kai kace duk irin tambayar da nake so??“.
ya kauda kai daga kallo na a hankali ya dan
jima baice komai ba zuwa can yace “bari
kwakwalwa tayi aiki“.
Ya mike daga inda yake zaune ya fara takawa
a hankali yana kaiwa da komowa hade da
kallona a wasu lokutan, yanayin na nuni da
zuzzurfan nazarin daya shiga, ni kuwa har
wani murmushi nake yi idan na kalli halwar
daya shiga, yau dai zan rabu da kaya.
Abinda naketa darsawa kenan domin ina da
yakini 100% bazai iya amsawa ba.
y‘an min2na kalilan ya kwashe ya juyo gareni
yace “A mafi yawan lkt suna nayin tasiri a
kamar mu2m da yanayinsa, idan har an sami
haka a kanki to ina da tbbcn sunanki ba me
guda daya bane irin sunan nan me guda biyu
ko ince tagwaye kamar “fatima-bintu, zainab-
abu, halimatus-sadiya! sai dai duk bakiyi kama
da wadannan sunayen ba.
Ya dan taka da kafarsa dake sanye da wani
kyakykyawan farin takalmi ya juyo gareni ya
kalleni na dan lkc yace
“AISHA HUMAIRA!!!!!!!“
Ya fada tare da sake mai-maitawa da fadin
“yes nafi yarda sunanki Aisha humaira....“ ya
zarce da kllna don jin abinda zan fada.
Ni kuwa 2ni idanuna sun kwalalo waje sbd
AL‘JABI, ya akai kasan sunana??
tambayar dana jefa masa kenan, fuskarsa
tadan fara saki yace “ kina nufin Na fada dai-
dai kenan??“
Bansan sanda na gyada kai alamar eh ba, ya
kawo gwauron numfashi hade da murmushi ya
koma ya zauna tare da cewa “Step one done
saura na gaba, ita dama SOYAYYA hadin Allah
ce idan yaso koke baki da ikon hanawa kuma
ina da yakini da karfin gwiwar yin nasara sbd
ina ji a jikina akwai alkhairi a tarayyarmu.“
Ya mike tare da ja da baya fuskarsa cike da
yalwataccen murmushi yace “Nima sunan
nawa me tagwayene UMAR FARUK!! sai an
jima farar tauraruwa me farin haske.
Ya juya ya fice.
Na daki tebirin dake gabana kamar na fashe
da kuka, gsky ya birgeni amma naji haushin
yadda yayi kaca-kaca da tambayata mafi
tsauri irin wannan domin ba canka kawai yayi
ba hankalinsa ne yayi aiki a wurin.
wai wannan anya kuwa mu2m ne???
dakyar na karasa abinda nazo yi na tafi class.
°ranar sai ya zamana duk na zama wata iri
2nanin irin zazzafar tambayar da zanyiwa
faruk kawai nake wacce zata gagareshi
amsawa, koda ace zan yarda da soyayyar
faruk amma bana so ya kureni, sai dai duk
tambayar data fado min sai naga kamar kwaf
daya zaiyi mata°
Washe gari 2nda na shiga makarantar bamu
hadu dashi ba har aka tashi na fito daga class
na hangi driver na sai dai dole na jira mufida
wacce bata fito ba har yanzu, na karasa jikin
motar na bude bayanta na zauna ba tare dana
rufe kofar ba saima kafafuna dana ziro waje,
salon sallamar dashi kadai keyi tasa nasan ya
iso, na dauke kai kawai.
Ya dubeni sosai yace “sorry for the late, Allah
ya taimakeni baki tafi ba da shikenan na fado
ina fatan dai baki manta tambayar da kika
tanado min ba??
Na kalleshi nace “bana so saina kayar dakai ta
karfin tsiya ka hakura kawai zaifi maka sauki
daga jin tambayar da miliyoyin mutane suka
gaza amsata masu ji da basirar, hikima da
hazakar da tafi taka..Mai-makon kalaman
yaudarar da nake amfani dasu suyi tasiri
akansa saima ya kyalkyale da dariya ya dan
taka kadan izuwa jikin kofar motar dana bude
ya dafashi da daddadar muryarsa me ratsa
zuciya yace “Humaira kenan kada kiyi
tsammanin kautar da 2nanina akan abinda
nake so kuma nake da yakinin zan sameshi,
na kasance ina da baiwar yin abubuwan da
miliyoyin mutane suka kasa, wannan kamar a
jinina ne don haka karki damu kiyi min kawai
ni abinda na dauka shine abinnan da muke yi
kamar istahara ne a gareni indai tarayyarmu
dake alherice to zan amsa tambayoyinki koda
sun kai 100, idan kuma babu alheri a ckn
soyayyarmu to bazan taba iyawa ba.“
Nabishi da kallo kawai nace:
*“ Akwai wata halitta a doron kasa wacce
yanayinta ke caccanjawa.
Idan tana karama tana tafiyane da kafa hudu,
idan ta girma kuma sai ta koma tafiya da kafa
biyu, yayin da kuma ta tsufa sai ta koma
tafiya da kafa uku, wacce halitta ce wannan???
*
Yayi saurin sakin kofar daya rike yabini da
wani irin kallon da ni kaina sai dana tausaya
masa, yaja da baya kadan lkc guda ya fara
kaiwa da kawowa a wajen hankalinsa in yayi
dubu ya tashi, na saki yalwataccen murmushi
nace “kaga faruk ba iya amsawa zakai ba
ka.......“
Ya daga min hannu yace “ karki katseni “.
Na daga ido tare da tabe baki a raina nace
‘ayi dai mugani‘.“
Ya dan dakata kamar zaiyi magana sai kuma
ya fasa ya shafi gashin kansa yace
“DANKARI!!“
Na kyalkyale da dariya kawai na dauke kai na
fara latsa wayar dake hannuna sbd a yadda
nake ji a jikina na gama dashi, sai dai ta ciki
na ciki don kuwa kirjina dif-dif kawai yake don
bansan yadda zamu karke dashi ba. tsawon
lkc muka shafe amma babu alamun ya karaya
da amsa tambayar saima dada kaimi da yake
wajen 2nani da nazari, jim kadan yadan yi nuni
da hannun tare da gyada kai ya saki murmushi
kyansa ya kara fitowa, ya tako a hankali izuwa
inda yake tsaye 2n dazu yace:
“ idan har 2nanina da nazarina sun bani dai-
dai-dai to ina da tbbcin ba kowacce halitta
bace wannan face MUTUM wato
bil‘adama.dalili kuwa mu2m sanda yana yaro
da kafa hudu yake tafiya shine RARRAFE,
gwiwoyi biyu hannaye biyu.
Yayin kuma daya girma ya iya tafiya sai ya
koma tafiya da kafa biyu kamar yadda ni dake
muke tafiya yanzu.
Lokacin kuma da mutum ya tsufa sai ya
zamana kafa biyu ba zata iya daukarsa ba sai
ya kara da sanda a matsayin kafa ta uku.“
Bansan sanda wani irin murmushi ya kwace
min ba wanda shine ya nuna ainihin abinda ke
zuciyata nake dannewa, yadda yake zano
abubuwan tamkar me karantawa a littafi ya
birgeni ma2ka.
Shima yayi murmushi tare da cewa “ zan iya
cewa wannan murmushin tayani murnar cin
nasara a karo na biyu ne??“
Na gyada kai tare da cewa “kwarai kuwa da
alama gaf kake da cina da yaki faruk akan
haka dole na jinjina maka domin kaine mu2m
na farko daka fara neman ka kureni,
murmushin da kaga nayi na tayaka murna ne
da kuma tausaya maka domin ka kai matakin
da dole kayo kasa domin gobe koda kai
aljanine baka isa ka amsa tambayar da zanyi
maka ba.“
Ya dago kansa ya fashe da dariya yace “kina
birgeni sarauniya sbd komai naki me tsari ne
kuma da karfin gwiwa hakan na daga ckn
abinda yasa muka dace da juna, idan wai kina
tsorata nine to sai ince miki kima hutar da
kanki don kuwa ma2kar ina tuna cewa
soyayyarki nake nema to zanyi abinda aljani
ma bazai iya yi ba.
Na gyara zamana dai-dai sanda na hangi
mufida tare da kokarin shigo da kafata ckn
motar nace “can dai da yawarka“.
Yayi dariya ya gyara doguwar jakar dake
rataye a kafadarsa wadda ta hadu da dressing
din jikinsa tayi masa kyau yaja da baya a
hankali yace “Ki shiryawa fara sabuwar
soyayya a gobe......“ Nayi saurin katseshi da
cewa “ko kuma ka shiryawa bakin cikin
faduwarka a gobe ba“. Ya dan dakata yace “
to shikenan zan iya cewa duk mu jira FINAL
din don ganin yadda zata kaya, ya dora
hannunsa a gefen goshinsa ckn alamu na
sarawa tamkar soja yace “sai gobe farin
ganina“...
Hmmm mumadai allah yakaimu GOBEn muji
wannan wata tanbayace haka..zata hada ko
zata raba..?!
Mufida na isowa direban wanda har ya fara
barci na daka masa tsawa ya farka ya juyar
da motar muka nufi hanyar da zata sadamu
da gida, Mufida ta dubeni tace “amma fa nayi
mamakin yadda naga kuna hira da faruk harda
dariya sai kace ba ke ba??“
Na kwantar da kaina kadan nace “manta da
wancan faruk din lamarinsa sai shi.“
mufida tayi dariya tace “Ah kidai fadi gsky
tbbs akwai wani abu“.
Ganin yadda take kokarin kureni yasa na
kautar da zancen ban bari yayi nisa ba, har na
isa gida.
*Abinda na kasa ganewa game dani shine:
Nidai faruk na birgeni ma2ka, komai nasa
naban sha‘awa, shine kawai a duniya da bana
iya tozartawa ko in wulakantashi koda nayi
niyya sai hakan ya gagara yiwuwa a wajena.
Ga yawan 2naninsa da nake yi a koda yaushe
banda son kasancewa dashi a kowanne lkc da
nake yi!! Shin wannan shine SO?? tambayar
dani bansan amsarta ba kenan.*
Washe gari misalin karfe tara na safe tsaye
nake a jikin wata faffadar bishiya dake harabar
makarantarmu nesa kadan da inda dalibai ke
zama, kasancewar yau an tashi da lullumi ga
iska me dadi na kadawa yasa nake jin dadin
wurin.
Gefe guda dalibai ne group-group masu hira
nayi masu kara2 nayi, Ni kuwa littafine a
hannuna ina karantawa hankalina gaba daya
tafi ga kara2n, jin sallamarsa yasa dole na
tsagaita daga kara2n da nakeyi duk da cewa
ban dago na kalleshi ba.
Amincin Allah a gareki ya ma‘abociyar son
kadaici da hutawa, Ya fada 2n yana nesa
kadan dani. Dan kwalisan saurayi kllm kara
kyau yake ya karaso inda nake tsaye yace “ina
fatan dai kin shirya tambayar dazan bige a
karo na karshe??? Nayi banza kmr banji
abinda yace ba. Yayi murmushi yace “ Kinyi
shiru kodai kin karaya ne??
Nayi yaken karfin hali nace “baka isa kasa na
karaya ba, yau so nake ka fada min ranar da
aka haifeni da watan da shekarar kayi jumulla
ka fada min shekaruna nawa??
da wata nawa??
kuma da kwana nawa??
Nayi karatu a kasar waje ka fada min wace
kasa ce kuma wacce university??
Na kumbura baki sanda nakai karshen
maganar ckn gadara da takamar cewa na
gama dashi.
Ya kura min ido kamar baisanni ba.
na kalleshi nace “yadai ka kasa cewa komai
kodai ka karaya ne??“
Yayi murmushi yace “gskyrki da kika ce ko
aljani yayi kadan ya amsa tambayarki tayau
sbd shima baisan gaibu ba amma ina so ki
sani SOYAYYA ba karya bace don haka duk
abinda naji a jikina game dake to gskyne,
zuciyata bata taba gaya min karya akanki ba
don haka zan jaraba idan har son gsky nake
miki na tbbt Allah zai bani nasara.
Ya taka kadan gaba da inda yake yace:
Irinku rayuwarku na tfy ne ckn tsari ba a
hargitse ba don haka ina da tbbs idan nace, an
saki a primary shekara shida sannan kika
samu shekaru shida a ita primary din, kin
secondary da shekaru 12.
kika gama secondary da shekaru 18 kika wuce
university kika yi shekaru 3, jumulla shekarunki
ashirin da aya (21) yanzu.
Tofa!! 2n daga nan idanuna suka zaro waje
sbd AL‘AJABI.
Ya kara gyara tsayuwa yace “idan har jikina
dai-dai yake bani an haifeki 1/6/1994 kuma
kinyi kara2 a OXFORD UNIVERSITY ta kasar
england domin itace burin duk wani dan gata
irinki.“
Hmm... Nifa tun kafin ma yakai karshen
zancen nasa bansan sanda duk abinda yake
hannuna ya subuce ba naja da baya a dan
tsorace, idan har faruk ba aljani bane to yana
harka da aljanu.
Kallo daya yayi min ya tbbr ya amsa dai-dai
ya tako inda nake tare da durkusawa ya
tattaro kayana da suka zube kasa ya mike
muka fuskanci juna yace “karki AL‘AJABI ko
mamakin abinda ya faru a maimakon haka ki
yarda Allah keson tarayyarmu, nasan kina
sona tun tuni don na dade da gani a idanunki
amma kina dannewa abnd kika manta shine
zuciya ba‘a yaudararta akan soyayya yau dai
wasa ya kare zamuyi soyayya abar kwatance
indai da tsawon rai.
na karbi laptop dina da littafina harma da
wayata daya miko min yaja da baya yace “Yes
ki shirya daga yau an fara, I LOVE YOU.“
ya juya izuwa ga abokansa dake can gefe
nesa sosai da inda nake, nabishi da kallo
kawai na kwantar da kaina a jikin bishiyar da
nake, wani murmushi ya kwace min Allah ya
sani ina so kauce-kauce ne kawai irin nawa
yau kuma karya ta kure.
Nadan dade ina cgb da tsayuwa a wurin har
zuwa sanda lkcn shiga class, ko break yau ban
fito ba yau sai da aka tashi na samu naja
mufida bamu bata lkc ba muka tafi, kai tsaye
gd muka nufa bayan da muka sauke mufida a
gdnsu.
Isowata keda wuya da yake da yunwa na
dawo kai tsaye kitchen na wuce na zubo abinci
naci nayi sallar azahar sannan na jawo laptop
dina na shîga aikina. Zaune nake bisa
luntsumemiyar kujerar falon namu na
tankwashe kafafuna laptop din na ajiye bisa
cinyoyina gaba daya hankalina ya tafi ga
laptop din sai shiga da fita nake, television
dake yi ma kasheta nayi sbd karar ta dameni.
Tunda na fara ba kakkautawa sai naji an kira
sallar la‘asar sannan na rufe na sakko tare da
shimfida darduma na jawo katon hijab dina
dana tanada musamman don yin sallah nasa.
Idarwa ta keda wuya momi ta fito falon ta
zarce izuwa kujera ta zauna ta danna remote
din dake rike a hannunta tafkekiyar T.V din
dake manne a jkn bango ta dawo taci gaba
dayi. Gamawata keda wuya na mike na koma
kan kujera na zauna na jawo laptop dina na
budeta, momi tace “aikin kenan bakya gajiya
bakya daga kafa.“ Na danyi dariya nace “momi
ai computer tayi, uhm don Allah momi dan
rage karar t.v dinnan tana takura min, momi
tace “don kina wannan shiriritar sai nabar jin
abu me muhimmanci irin wanda nake kll
yanzu??“
Nadan kumbura baki nace “ momi shiririta
kuma??“
Eh an fada shiririta ai ni wannan makarantar
taki da ita da shirme duk dayane a wurina.“
Na dan hade rai nace “ai kuwa momi ba
shirme bace don kara2n computer na daya
daga ckn mafiya tsada a duniya, kuma wlh
yadda nake jin dadin makarantar nan ko
OXFORD banji dadinta haka ba.“
Momi ta kauda kai tace “karyar banza!! yanzu
dai ki tashi kije banki ki ciro min kudi zanyi
baki gobe ba kudi a hannuna kinsan dadynki
sai jibi zai dawo,“ Na dan cilla hannu nace
“kayyyy!! momi kina gani aiki nake yi
kuma.....“
Ta katseni tana kallona da cewa “OK ba zaki je
ba kenan???“
Na mayar da kaina ga laptop din dake gabana
nace “Zanje“
to ki tashi maza ki tafi kinga yamma nayi, na
rufe laptop dina na nufi dakina kai tsaye
bathroom na shiga nayi sabon wanka na wuce
ma‘ajiyar kayana na saka wadanda suka dace
dani a yanzu na dawo ga tafkeken madubina
na zauna kujerar dake fuskantarsa zagaye dani
kayan kwalliya ne bila-adadin kala-kala.
Bayan dana gama shiryawa na kalli kaîna
bansan sanda wani murmushi ya subuce min
ba, hmmm... wato ba karya ne ba ni nakai
mafi kololuwa fagen kyau bama kyau kawai ba
komai nawa daban ne domin abinda kesa
wasu muni ni kuma kyau yake kara min bare
kuma nasa abu me kyau, Na zama
kwatankwacin zarah a ckn taurari gasu da
yawa amma daka daga kai ni zaka fara gani.
Na fito izuwa harabar kasaitaccen ygdn namu
ina takun isa, takama da gadara.
Direba ya taso da gudu tare da cewa “ranki ya
dade ina zuwa haka??“
Na harareshi nace “Ba ruwanka da yinda zanje
bani mukullin waccan motar,“ nayi nuni da
CR-V din dake nesa kadan dani.
A tsorace ya miko min tare da cewa
“amma.......“ Nayi saurin katseshi da tsawa
nace “Yau nizan tuka kaina inda nake son
zuwa ka koma kuci gaba da zaman
munafuncinku, na warci mukullin daga
hannunsa na shige motar na juyar da ita na
fice nabi titin dazai sadani da inda zanje.
Tafiyar min2na 15 nayi na iso katafaren bankin
nayi parking motata a inda aka tanada na
wuce ckn bankin, Al‘adata duk sanda nazo kai
tsaye wajen manager nake wucewa ya 2ra a
ciro min abinda nake so in juyo na fito sbd
asalinsa yaron dadyna ne.
Zuwana ofis din nasa dai-dai inda ya saba
zama nayi turus don yau wanda nake
tsammani bane ba abinda yafi kenan ba wanda
ke zaunen 2n daga zamansa dress dinsa da
komai nasa ma nasan ko waye.
Na tsaya akansa nace “ Ah!! Ya haka kuma??
Dalibi a wani wuri ma‘aikaci a wani wuri??
Faruk ya dago kai koda ganin nice sai ya saki
murmushi ya gyara zama yace “ kina mamaki
ne??
Na gyada kai dai-dai sanda na zauna a kujerar
dake fuskantarsa nace “yes!! dole da mamaki
mana kodai faruk din biyu ne bayan wanda na
sani??“
Yayi dariya yace “Nine dai wanda kika sani
don ba sunana husaini ba bare kice hassan
dina kika gani, dama kina zuwa nan ne?? Ba
tare dana dubeshi ba nace “shi yasa ma nake
mamakin ganinka don ban taba ganinka anan
ba sai yau.“
Eh gsky ba zaki ganni ba sbd ba anan
bangaren nake ba yau ne kawai na