Showing 1 words to 3000 words out of 37941 words

Chapter 1 - BABBAN YARO book 3 Book End Complete by Binta Umar Abbale .pdf

24 Jul 2025

461

[12/3, 9:02 AM] .: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR BINTA UMAR*


*71*


Daurewa kawai yayi ya karasa kusa dasu cikin yanayin tafiyar sa ta jarumin namiji, baby Aysha
ya dauke daga jikinta kawai ya fuce daga dakin. Kallo granny tabi shi dashi itanan ta kira shi ne
tayi musu fada shi da Asma'u gashi ya futa, cigaba da rarrashin Asma'u tayi kusan mintuna
ashirin tukkuna ta futa daga dakin, parlor ta same shi ya tasa baby a gaba yana kallo. Tace"Kai
da zaka rarrashe ta kuma sai ka dauko 'yar ka ka futo Asma'u tana bukatar Dan rarrashi." Da
Jan ido ya kalleta yace." Granny nima Neman Wanda zai rarrashe ni nake domin bata fini jin
ciwo ba." Tace"Ai kai namiji ne kana da jarumta ita kuwa macace don Allah ka rike yarinyar nan
amana k'ato kar ka hofintar da ita zakaji dadin zama da ita domin jikina na bani akwai alkairi a
auran Ku da ita."


Shuru yayi kawai ta cigaba da cewa a yanzu tana cikin damuwa saboda haka duk wani bori
da zata yi maka kayi hakuri kar ka biye mata domin an shiga hakkin ta ne.... Ranshi a Dan bace
yace." Granny wato ni ba a shiga nawa hakkin ba kenan? Hararasa tayi zata yi magana ya
katse da sauri yace." Nifa bani nace ina son ta ba domin ni yanzu babu maganar aure a tsarina,
gaskiya amma dai tunda kun kulla Allah ya sanya alkairi, amma kiyi mata fada sosai duk wasu
halayen ta da nasa ni a da to ta sauke su domun bazan zauna da ita dasu ba."


Granny tace." Insha Allahu zaka ji dadin zama da ita kuma zan ja mata kunne da kyau kai dai
ka zama namjin duniya a gidan ka." Shiru yayi mata ita kuma ta cigaba da yi masa fada har
sanda Jahid ya shigo, ya same su. Kusa da Amjad din ya zauna yana fadin "Ya zamu yi ne
gasu Khalid can sun shirya walima kamar yanda aka saba sai ka kimtsa bayan sallahr magariba
zamu fita." Gyada kansa kurrum yayi Jahid din yaji babu dad'i yace." My friend nasan nayi maka
katsalandan cikin rayuwar ka amma ina me baka hakuri don Allah idan hakan bai maka dad'i
ba, hak'ika banaso in rasa Asma'u saboda kyawawan haleyen ta tunda Allah ya kaddara cewa
ba matata bace shine nayi maka sha'awar auran ta ko don baby nasan gaba zaka ji dadin
wannan abun insha Allah kayi hakuri ka sasssutawa zuciyar ka idan ka saki ranka na tabbata
itama Asma'u zata saki nata Ku zauna lafiya.


Amjad ya dafa kafadunsa cin kyakyawan lafazi yace"Jahid babu abunda zance maka wallahi
sai dai fatan gamawa lafiya ka nuns min kulawa a rayuwata babu shakka zan karb'i Asma'u
saboda kai zan rike ta amana dalilin ka, insha Allah." Jahid yaji dad'i sosai hannu ya bashi suka

yi musabaha kana ya mike yana fadin bari inje in sanya a kara gyara guri yanzu." Amjad din
yace." Zan fito Yanzu insha Allah. "


Granny ma mik'e wa tayi ta nufi kicin gurin Iyami dake had'a abunci na tarb'ar amarya nan
granny ta sanya mata hannu suna yi suna hira da yadda abun ya faru har suka kammala tsaf
Iyami ta fito ta gyara daining lokacin Amjad ya tashi daga gurin yana bedroom d'insa shi da
baby Aysha da take was an ta kan bed din sa, wanka ya fito daure da towel ya tsane jikin sa
tsaf gaban dressing mirror ya tsaya ya gyara sumar kanshi hade da shafe ta da Maya mayai
masu asalin tsada jikinsa ya shafe da turare kana ya shafa mai sama-sama , wardrobe din shi
ya bude ya dauko sabbin kaya cikin ledar su, yadin plitex ne blue black dark yana da taushi
sosai sngjilet ya sanya fara kal kana ya Dora rigar a kai wacce ta sakko masa har kasa din ki
Muhammad Abacha kenan tsaf ya gyara links ya d'aura a gogon shi Dan Asali turare ya fesa a
jikinsa. Ya aje inda yake zuciyarsa na tuno masa shararran k'amshin Asma'u Wanda yake
kwadayin sake jin shi, amma ya lura kamar yarinyar da rigima ta shigo gidan dole ya kiyaye kar
ta raina shi, zai yi kokari gurin ganin bai shiga harkar ta ba, baby ya gani na kokarin saukowa
daga bed yayi saurin d'aukar ta yana fadin"Kin fiye kiriniya Momy sai kinje kin fad'i ko." Dariya
take bangala masa tana wasa da kwantaccan sajan sa dake shek'i, haka suka futo parlor shi da
baby suna dariya.

Granny ya samu zaune cikin kujera zaune ta k'urawa TV ido yana futowa tace"Yawwa dama kai
nake jira ka futo ka shiga gurin Asma'u nayi-nayi ta fito taci abunci taki kaje ka rarrashe ta."
Zama yayi cikin kujera ba tare da ya bawa maganar ta muhimanci ba yace." Ba sai ki k'yaleta
ba cikin ta ne idan taji yunwa zata futo taci." A"a baza ayi haka ba ka shiga dai ga lallab'ata. "
Cikin mamaki yake kallon Granny yayi 'yar dariya hade da Sosa kansa yace." Granny ni baza ki
rarrashe ni inci abunci ba sai wata daban ni kike sawa ma in rarrashe ta alhalin nima Neman
Wanda zai rarrashe ni nake ni babu inda zanje idan ta gadama ta futo taci kanta tayiwa." Bata
fuska granny tayi tace"Bana son gaddama yarinyar nan amana ce a gurin mu bana son abunda
zai kuntata mata da wanne zata ji." Shiru yayi ganin ranta ya b'aci sai ya zab'a baby a kafad'a
suka shiga dakin da Asma'u take.

Ina kwance har yanzu ina sak'awa da kwance wa naji an turo kofar dakin an shigo tun kafin in
d'ago kaina naji k'amshin turaran sa rintse idon nayi da sauri Sam! Bana son mu hada ido dashi.
Idonshi a kanta har ya k'araso gurin, baby ta dinga zillo wai ya sauke ta, yana aje ta ta fara
kokarin hawa bed din da kansa ya d'ora ta jikin Asma'u dake kwance rif da ciki. Hucin
numfashin sa naji a dai-dai wuyana, tsigar jikina ta mike k'amshin sa duk ya baibaye ni. Gabana
fad'uwa kawai yake. Shima nashi b'angaran hakan yake domin wata irin sha'awar ta ce ta bijiro
masa mai zafin gaske. Yanayin kwanciyar da tayi ya ya sanya shi cikin halin k'aka ni kayi......
Gyaran murya yayi had'e da had'e fuskar sa sosai ya ambaci sunan ta sama-sama." Asma'u.'!!
Yarrrrrr!! Naji a jikina domin bai tab'a kirana da irin wannan muryar ba.... Shiru nayi. Tsaki yaja
hade da fad'in"Nasan kina jina kika min shiru Ok ina so ki shiga hankalin ki ki nutsu sosai ki San
da wa kike zaune naji na karb'a an lak'aba min saboda gujewa sharrin ki jama'a suke gudun
had'a zuria dake ni don an raina ni sai a wani d'aura min aure dake.... OK naji na karba amma ki

kiyaye wallahi domin bana son shirme da gatsali nayi rashin matata mai biyayya kiyi koyi da
halin 'yar uwarki Mimi sai mu zauna lafiya dake ina fatan kin gane ko."!!!!?

*Ikon Allah mutumin da aka turo yayi rarrashi shine yake gasa wannan maganganun masu zafi
Wanda zasu iya sanya zuciyarta ta buga a take babu shakka Kalmar da malam bahsushe yake
fad'i gaskiya ne Namiji tabarmar k'aya ne waiii*

Tun kafin ya karasa maganganun sa nake wani irin kuka yayin da nake jin wani irin zafi da
zugi a cikin zuciya ta, ji nayi bazan iya kyaleshi ba, domin a ganina idan na barshi ya saba min
da wannan cin mutumcin to babu shakka nice zan sha wahala da sauri na mike zaune ina goge
hawayen fuskata da gefan lifayar dake jikina. Ido muka hada dashi yaji gaban shi ya fad'i ganin
yanda idanunta sukayi wani irin ja!! Dama gasu masu girma..! Kauda kansa yayi da sauri! Yana
wani ya mutse fuskarsa..... Murya ta bata futa sosai nace"Ni ake gudun had'a zuri'a dani."?
Daga kafad'a yayi yana kallona. Na cigaba da cewa "Saboda ana gudun mugun halina, shi
Jahid din ne yace maka haka." !? A d'age ya kalleta yace." Idan shine ya fad'a min ke Baki isa ki
na fad'a miki E ko A'a ba." Cikin takaici da ciwon zuciya nace"Ni nasan Jahid don an fi k'arfin
shi ya sanya ya hak'ura dani, amma babu shakka soyayyar da yake min babu algus a cikin ya
nafi tunanin wannan maganar daga bakin ka ta fito saboda mugun sharrin ka da b'ata sunan ka,
ita kanta mahaifiyar Jahid din da ta hana faruwar auranmu bata yi min wannan mummunan
kazafin fa sai kai.! Tom nagode K'warai amma nima ina fada maka cewar "Wallahi irin zaman da
kayi da Mimi kai baka isa kayi irin shi dani ba, sharrin ka zai koma kanka! Kuma baka isa ka
kashe ni da bakin Cikin ka ba, ko Mimi ma itace ta sa kanta har ta mutu ta sanadiyar ka ni baka
isa kayi sanadin mutuwa ta ba, sai Allah."


Ranshi yayi mugun b'aci jin kausasan lafuzan ta, dama hausawa sun ce baki in yasan abunda
fad'a to bai San abunda za a mayar masa ba... Take yanayin fuskar sa ya sauya sai wani huci
yake yi yana kallonta tana kallonsa... Gyada kansa yayi yace." Kinci albarkin baby Aysha dake
jikin ki Yanzu amma da baby shakka sai na miki abunda Baki tab'a tsammani ba." Da sauri
nace" Bans so inci albarkacin kowa kayi min abunda kayi NIYYA don Allah."!!! Bai saurare ta ba
ya bude kofar da sauri ya fuce kamar kububuwa. Granny na zaune taga futowar sa yayi waje
kamar zai tashi sama da sauri ta shiga dakin Asma'u sai ta tadda ita ta rungume baby tana
gursheken kuka har da majina. Hankali a tashe ta karasa dakin tana fad'in " innalillahi ASME me
yayi miki kike Wannan kukan nagan shi shima ya futa da b'acin rai ki daina kuka ki fada min
damuwar ki."! Cikin kuka nace"Granny zaman mu da abban baby bazai yi wu ba."" Hankali a
tashe! Tace"kan wane dalili kika fad'i haka." Kasa fada mata komai nayi sai kuka domin ji nake
kamar in mutu ya ilahi wai same zanji ne."!!? Kuka ta fashe dashi itama sosai take fad'in "Kiyiwa
girman Allah da Annabi kiyi hakuri babu shakka nasan abunda ya faru tsakanin ki dashi ba me
dadu bane da nasan zai shigo yayi b'arna da ban turo shi ba, kiyi hakuri ki dubi wannan yar
lab'ub'uwar yarinyar dake jikin ki ki zauna da ubanta ba don halinsa ba, nasan yana da fushi
amma ba shi da rik'o don Allah dukan abunda kika San zai hasala masa zuciya ki guji yin sa kin
ji ko." Duk cikin kuka take wannan maganar.
Sosai tsohuwar ta bani tausayi goge fuskata nayi ns rike hannunta dake karkarwa nace"Granny

ki daina kuka don Allah insha Allahu zanyi abunda kika ce din zanyi kokarin ganin na kawo
zaman lafiya s zamantakwar mu dashi insha Allah nasan ni tawa kaddarar kenan kuma zan
karb'e ta hannu biyu." Tace"Yawwa ko kefa Allah yayi miki albarka." Ameen nace. Ina jin wani
irin kaunar tsohuwar Cikin zuciyata. Tace"Muje kici abunci don duk ga alamu nan sun nuna ba
kici abunci ba." Nace"zan fito yanzu insha Allah ." Mik'ewa tayi tana kokarin d'aukar baby dake
wasa kan bed yarinyar ta sa kuka Granny ta fuce tana fad'in "Ja'ira kawai yau ni din kike gudu
saboda kin ga uwarki." Murmushi nayi kawai na mike ina warware liffayar jikina toile na shiga na
wanke fuskata kana na dauro alwala na futo k'arfe hudu da rabi na yamma, dadduma na
shimfid'a na tada sallah cikin nutsuwa bayan na kammala addu'a ne na mike a nutse na tsaye
gaban wani dressing mirror dake cike da kayan shafa, fuskata na kalla naga duk ta kode dama
ban yi wata kwalliyar kirki ba aunt Hauwa babu yanda batayi dani ba naki raina babu dad'i na
futa daga dakin. Da babu a hannu granny da Iyami da wasu mata uku s zaune a parlor suna
magana sama-sama da suka ga na futo sai suka yi shiru, Kai tsaye gurusu na nufa a nutse na
gashe da matan kana na mike na isa gurin cin abunci ina mamaki kallon banzan da d'aya daga
cikin su take min....... Magana suka cigaba da yi Wanda bana fahimtar me suke fada na dai lura
kamar ransu a b'ace yake dukanin su, kad'an na zuba abuncin ina ci kamar magani baby nake
bawa àbinci kad'an kad'an ganin tana so taci babu laifi taci kad'an hankalina na mayar kan su
granny jin abunda matar nan dake hararata take cewa"Yo!! Da kike wannan maganar idan
Hafsatu ya aura kina nufin ita bazata kula masa da baby ba, ai kusancin sa da Hafsatu yafi
Wanda ita take da Uwar yarinyar, ni dai wannan al'amari bai min dad'i ba kuma an munafurce
ni."!! Iyami da bata so a tab'a mata granny tace" Haba ke kuwa da girman ki da komai kike
magana irin ya yara k'anana shi ga aure nufi ne na Allah kuma babu laifin Uwar dakina anan,
tunda ba itace tace Dole sai anyi auran ba Allah dai ya kaddara za'ayi.....! Cikin hayagaga Inna
Suwaiba mahaifiyar Hafsa tace"Kinga bana son munafurci da iya samu guri Yaro dai danmu ne
mu muke da magana a kansa ba ke kar ki kara sanya mana baki anan, ai INA zaune a gurin
nan har Amjadu ya shigo gidan a matsayin na uwarsa yan umarce shi da iya yi min Abu kuma
sai yayi, Granny tace"To idan ya shigo sai ki umarce shi kina da iko dashi duk hukuncin da kika
yanke a kansa dai-dai ne dank'i... Matan da suka rako inna Suwaiba suka ce K'warai kuwa
maganar ki hakkun kamar yanda kike da iko dashi muma haka nake dashi..........











*3/12/2018*
[12/3, 9:57 PM] .: *BABBAN YARO*

*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA
CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO
MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA
SAI TA CI SHI*




*72*





Wani irin mamaki ne ya lullub'e ni jin abunda yake futowa daga bakin matar wai tana da iko da
Amjadu zata sanya shi ya k'ara aure Ikon Allah idan Amjadu zai hada mata uku ni na zama ta
hudu a halin yanzu bai dame ni ba, saboda Sam ba shine a gabana ba, abincin nake ci babu
dad'i ina tunanin lamarin mutane. Tare suka shigo da Jahid da Khalid Jahid yana rike da wata k'atuwar leda mai tambarin
Muddansir&Broths kai tsaye inda nake ya k'araso ya dauki baby yana mata wasa. B'acin rai da
bakin ci bai sa na kalli inda yake tsaye ba.... Amjadu da Khalid kuwa gaisawa suke da su Inna
Suwaiba dake zaune suna jiran shigowar sa... A hankali Jahid yace." Amarya kin sha kamshi
nasan nayi miki laifi a ganin ki, amma na tabbata nan gaba zaki zo kina alfahari dani a rayuwar
ki, Asma'u Allah ya tabbatar da alkairi a rayuwar ki." Wata irin k'walla me zafi ce ta cika min
kwarmin idona Hak'ika Nayi rashin mosoyi na hak'ika Momy Jahid ta cuce ni a rayuwa ta
Tabbas duk macan da tasamu Mujahid a matsayin miji ta more wa rayuwar ta... Ledar dake
hannunsa ya aje a cinya ta yace." Ni yanzu a matsayin yaya nake a guri. Ki Asma'u ba don ni
ba don Allah ki tashi ki kimtsa jikin ki zamu futa walima Wanda muka shirya muku ke da angon
ki.." Yana gama fadin maganar shi ya bar gurin dauke da baby a kafadar sa. Mik'ewa nayi jiki
babu kwari na dauki ledar na nufi bedroom din da na fito yanzu. Daf da zan shiga naji Inna
Suwaiba na fad'in"Ni dai na fada maka magana ta ta k'arshe har in dai ka dauke ni a matsayin
uwa to kabi umarnina kamar yanda nace din. Saboda bamu da muhimacin a rayuwar ka ranar
auran ka sai dai muji a gari bare ma yafi mu daraja a gurin ka, iyi ga yarinya 'yar Asali zakaje ka
daukowa kan ka kara da kiyashi! Ai duk mun San komai mu baza a rufe mu ba... Itama
mahaifiyar Abokin naka ta guji hada zuria da mugun iri ne shiyasa ta ruguza auran, kai kuma
saboda baka da wayo ka karba to baza mu lamunta ba.."!!! Maganganun Inna Suwaiba sunyi
tsauri da yawa shi kanshi Amjad din yaji rashin dad'i ga Asma'u a tsaye taji komai ga abokan

shi Innarsa take wannan surutun tabbas Jahid zai ji babu dad'i cikin zuciyar sa. Aikuwa Hakane
ta faruwa granny ji take kamar ta gaggaurawa Suwaiba mari ganin yanda take kokarin bata
al'amari wannan ai cin fuskane take a matsayin ta na mace mai hankali dattijuwa bai cancanta
tayi irin wannan maganganun ba.
Da gudu na fad'a dakin nayi kwance kan bed rumutse idona nayi da k'arfi hawaye suka fara
gudana a fuskata Shikkenan Amjad ya gama zubar mun da mutumcin na, a duniya ni kuwa me
nayi wa mutumin nan me zafi a duniya ya b'ata min suna gurin jama'a a takaice ma yanzu na
rasa wane irin kallo jama'ar gari suke yi min. Innalillahi wa'ina ilahi raji'un. "!!!! Bude kofar dakin
aka yi, nayi saurin goge hawayena domin na dauka granny ce.... A hankali ya k'araso har bakin
bed din hannunsa cikin aljuhu ya tsaya a kanta k'ikam!!! Yafi minti biyar yana kallonta kana ya
sauke ajiyar zuciya hade da Jan siririn tsaki yace." Kukan me kike yi."!!!? Shiru babu amsa..
K'afar shi guda ya Dora kan bed din ya d'ago fuskata da hannun shi, da sauri na kwace ina
kauda kaina...

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login