Showing 15001 words to 18000 words out of 37941 words

Chapter 6 - BABBAN YARO book 3 Book End Complete by Binta Umar Abbale .pdf

24 Jul 2025

468

suka futo
dashi 'yan jarida da suke zaune a reception suka mik'e dama duk abunda yake faruwa suna
kallo ta CCTV Camera aikuwa suka yi caaaa! Kan alkanawi suna so suji ta bakinsa, ido jazur
yace." Sharrin shad'ain ne kawai da zugar mutane gashi sun kaini sun baro da k'arshe ina
Neman afuwa ga al'umar jahar kano bisa ga abunda ya faru."!! Daga haka yayi shiru idonsa yayi
wani irin jaaa sojoji suka tasa shi a gaba.

To hakace ta kasance kan Amjadu manya manyan 'yan jarida suka sanya shi a gaba dole sai
yayi magana , babu yanda ya iya cikin turanci yace." *Hak'ika wannan ranar bani da kamar ta a
duniya saboda Allah ya nuna min gaskiya ga gaskiya CE, Allah ya wanke ni bisa ga zargin da

jama'a suke min Na tabbata ubangiji baya bacci kuma shi sharri d'an aike ne sunyi nufin cutata
ubangji ya mayar da abun kansu saboda bani da hakki a Kansu nagode wa Allah da na tsalle ke
wannan sharrin nasu kuma ina jinjina ga me girma shugaban kasa tare da mataikan sa hak'ika
sun cancanci yabo da godiya a gare ni nagode k'warai da hallancin su a kaina."* Abunda ya iya fada kenan ya wuce masaukin sa tare dasu doh-doh da Ali da yake cikin farin
ciki da murna domin yana ganin dole ma ayi masa Karin girma gurin aikinsu saboda namjin
kokarin da yayi.

Kafin kace kwabo garin kano ya hargitse da Sowa da murna gari ya hautsine da hayaniya
kowa na fad'ar ra'ayin sa kan abunda ya faru, matasa dattijai duk sunji dadin wannan hukunci
da shugaban kasa ya dauka dama sun gaji da mulkin Alkanawi don haka sai suka yanke
shawarar tsayar da Amjadu a matsayin mai mulkar jahar su, take wasu suka futar da hoton shi
a matsayin governor mai jiran gado nan da wata biyu suka dinga bin jikin gidaje da kan titina
suna manna kasuwanni da shagunan mutane suka dinga manna hotonan amjadu a matsayin
governor.

Duk abunda yake faruwa mun gani labarai Ya Aminu ya kirani a waya yana fad'amin min wai
nasan abunda yake faruwa kuwa nace"Gani a labarai Ya Aminu ni bana son siyasa nan fa." !
Yace." Kiyi hakuri ki taya shi addu'a kinji ko."! Ni dai shiru nayi kawai hankalina duk a tashe
burina kawai ya dawo gida gashi na kira wayarsa ya kai sau ashirin bai d'aga ba..... Daki na
shiga nayi kuka na mai isata na futo na tadda Granny ta jurawa TV ido inda suka nuno Amjadu
lokacin da yake bayanin godiya a fadar me girima shugaban kasa. Ta kalleni idonta ya Tara
k'walla tace"Zo kiyi min bayani me suke cewa ne naga sojoji sun kewaye shi, ga mutanan masu
nacin tsiya sun kewaye shi da na'ura fadamin me yake ce musu jikina duk yayi sanyi.."!

Nace"Granny suna so ne ya zama governor kano babu wani damuwa sai Karin daukaka da ya
samu kuma shine yake da nasara a tafiyar wannan 'yan jaridar da kika ga sun kewaye shi duk
murna suke taya shi suna so su ji ta bakinsa ne."

Granny tace"Alhmdullahi Allah nagode maka dama nasan addu'a ta baza ta fad'i 'kasa ba
nasan 'kato bashi da hakkin su amma ni kam bana sha'awar siyasar nan akwai zube war
mutumci da dai su k'yale shi kawai."

Nace"Wallahi nima haka granny bana so amma gashi tun bai dawo garin anji ta bakinsa ba
jama'a sun fara fidda hotonan sa a matsayin d'an takara governor ." Granny ta sauke ajiyar
zuciya tace"To Ubangji Allah ya dawo dashi lafiya muji ta bakinsa ni dai sanin da nayi wa 'kato
baya sha'awar siyasa ban sani ba ko yanzu."

Shiru nayi mata zuciya ta nacan tunanin wani Abu. Mik'ewa nayi na koma bedroom dina waya
ta na d'auka ina 'kara kira shi cikin sa'a ya d'aga, ajiyar zuciya na sauke cikin damuwa
nace"Abban baby sannu."! Muryar shi bata futa sosai naji yace." Yawwa ya gida babu matsala
ko."? Nace"Eh nayi ta kiran wayar ka kana gani ka'ki dagawa." Ajiyar zuciya yayi yace." Sorry

sai yanzu wayar tazo hannuna mybe lokacin da kika kira tana gurin Doh-doh."""" Shuru nayi
yace." Shikkenan ko."!? Da sauri nace"Amma yau zaka dawo ko."? Kai tsaye Yace."A'a."! 'Kasa
nayi da murya ta nace"Meyasa kasan fa ba lafiya gare ka ba." Kwanciya yayi kan bed yana
lumshe ido yace." Menene damuwar ki da lafiya ta bayan idan ina nan d'in bakya kula ni. " Naji
wani sanyi na shigata jin yanayin yanda yayi magana nace"Baby na kuka abbanta."

'Karya kike yi sai dai idan kece kike kuka kina so in dawo ai na gane. " ya fada yana siriryar
dariya , cikin jin nauyi nace"Da gaske nake don Allah yaushe zaka dawo."? Ajiyar zuciya ya
sauke yace." Idan na dawo d'in me zaki bani. " ? Shiru nayi masa, yace." Ok bari in kashe
wayata." Da sauri nace"Sai dai ka dawo d'in komai kake so." 'Yar dariya yayi yace." Kinyi alk'awari ko." ? Lumshe idona nayi ina jin wani fleengs nace"Eh"
yace." Ok sai jibi zan dawo zan huta anan tukkuna hayaniyar gari tayi sau'ki kinsan in na shigo
gobe zasu takura min ko baki San abunda yake faruwa bane."!?

Nace"Na sani munga komai a labarai Abban baby na taya ka murna kuma ina maka fatan alkairi
har 'karshen rayuwar ka."!. Sosai yaji dadin addu'ar ta yaji yarinyar ta 'kara samun wani matsayi
a zuciyar sa yace." Thank you my wife I will not leave you forever."!

Naji dadin abunda yace cikin jin kunya nace "Thank u my life patner."!! 'Kit!!! Na kashe wayar
cikin jin kunya gabana sai dukan uku-uku yake ina mamakin yanda na sake har nake magana
dashi haka.... Nashi 'bangaran kuwa rike wayar yayi yana sakin wani irin murmushi Wanda shi
kad'ai yasan ma'anar shi, ya mike da kuzari a jikinsa ya shige toilet domin gasa jikinsa saboda
wani irin ciwo yake masa ni kam nace" Dole ne ko don dambe da kasa kai da Kumurci!

********

Washe garin ranar Innah Suwaiba ta dira cikin gidan ita da 'yar ta Hafsa had'e da 'kullikan kayan
su wai sun dawo gidan da zama domin labarin duk abunda yake faruwa ya isa gareta don haka
arzikin d'anta ne tunda d'an 'yar uwarta ne itama ta dawo kusa a ci da ita.... Mamaki kamar ya
kasheni na dinga kallon matar na marasa a wane matsayi zan aje ta, gaisuwar da nayi mata ma
a banzace ta amsa, Hafsa kuwa ido ne tsakanina da ita granny tace"Haba Suwaiba ai ko wani
kika kawo cikin gidanan kikace yana so ya zauna zai zauna saboda darajar ki ba sai kin dinga
tashin hankali ba don Allah ki dinga yin komai cikin nutsuwa da fahimtar juna." Wannan magana
da granny ta fad'a sai Innah tace"ai ta fad'a mata ba'kar magana ta inda take shiga ba tanan
take futa ba. K'arshe dai granny bar mata parlor tayi domin baza ta iya da jarabar Suwaiba,
dakinta na bita na tadda ta a zaune nace"Granny wannan matar tana so ta d'aga mana hankali
a gida." Tace"Sai hakuri Suwaiba taki sanin abunda ya dace Wallahi kiyi hakurin zama da ita ni
kam 'kato na dawowa zan tattara in tafi inda nafi kauri."


Nace"Babu inda zakije granny kina gidanan domin ni dake zan zauna gaskiya. " tace"Yanda
nake da matsayin a gidanan haka Suwaiba take dashi domin a matsayin uwa take ga mijin ki
saboda haka ki kula da kyau." Kuka NASA nace "Wallahi kin San Allah bazan zauna da ita ba

sai dake domin ina ganin idan ta cigaba da yimin wannan halin nata watarana zan rama ko in
zage ta."


Ganin ina kuka yasa granny fadin "Shikkenan kiyi hakuri mu Bari tukkuna mai gidan ya dawo sai
muji ta bakin sa." Hawaye na nagoge nace"Me zan girka miki na rana." ? Tace"ki bari Iyami sai
tayi ke kije ki huta mana." Nace"A'a ki fad'a min dai." Tace"yi min towon alkama da miyar kuka."
Nace" Tom" futa nayi daga d'akin na tadda Innah Suwaiba ita kad'ai ta d'au 'kafa daya ta d'ora
kan d'aya kicin na wuce ta Bini da banzan kalo tana Jan tsaki .!!


Me zan gani Hafsa na tsaye ta kunna gas sai fasa 'kwai take yi gefe ga Uwar doya nan ta tsame
ta cikin wani kwando ta d'ora mai zata fara soyawa..... 'Bata fuska ta nayi nace"Hafsa meye
haka kikeyi min a kicin duba don Allah gurin a gyare duk kin bi kin zubar da 'bawon 'kwai da
doya Haba don Allah."!!

Hafsa da ada take bala'in tsorona itace yanzu ya juyo tayi min wani banza kallo ta d'auke kanta
daga kaina ta cigaba da abunda take..... Wani irin zagi na kurma cikin zuciyata amma a zahiri
nace"Ko bakyajin abunda nace ne."!!! A wula'kance tace"Ina ce da akwai me aiki da zaki wani
dame ni da surutu, idan na gama aikina sai ta zo ta gyara."

Gyad'a kaina nayi nace"Yayi kyau."! 'Karasa wa nayi kusa da ita kawai na murd'e gas d'in na
kashe had'e da dauke man da take soya na aje kaskon gefe kana na kalleta fuskata babu
annuri ko na kwabo nace"Futa ki bani guri in gama abunda zanyi in yaso sai ki dawo kiyi kome
Nene. """
"Baki isaba."! Tafad'a kanta tsaye gashi ta tsare ni da ido har da ri'ke 'kugu gaskiya nayi
mamakinta nace" OK sai inga yanda zakiyi min iko a gidana."!
Wata irin shewa ta buga tace"Masu gida manya, hahahahaha da dai bamu San komai bane sai
kice wani abu, to mun San komai aure ne akayi shi dake da My love d'ina bisa 'kaddara da har
zaki dinga wani famkama da hura hanci kin auri me kud'i tom bari kiji ba a sanja 'yan uwa har
karshen rayuwa ke kuwa fa my love zai iya sanja ki har abada ya kawo wata saboda haka ni
nan da kika ganni jinin mu d'aya da Amjadu za'a iya tsaga jikinsa a tsaga nawa a ga jinimu yazo
d'aya saboda haka ki iya bakin ki Wallahi idan ba hakaba wannan gallafirin auran naki zamu iya
yin sanadin sa."

Naji wani irin takaici ya rufe ni jin abunda Hafsa take cewa danne zuciyata nake yi ina kokarin
hanata aikata abunda tayi niyya nace"Hafsa kin San halina ba tun yau ba bani da kyau ke kanki
kin sani bana so muyi irin wannan zaman daku ki iya takunki ki bar shiga hurumin da bana ki
ba, idan kin 'kiji zaki sha mamaki wallahi."!!

A hasale tace"Ke kar ki kawo min maganar banza da wofi da dai da kikayi min abunda kike so a
skull lokacin ki ne yanzu baki isa ba wallahi kutumar ubanki zanci la'ada waje kuma in
zauna....... Kafin ta 'karasa na tsinke ta da wani irin gigitacan mari! Ta rike kuncin ta da sauri
tana kallona da ido jazur tace" ni Kik....... Kafin ta 'karasa na kifa mata wani a d'aya kuncin nata,
nace"Ina fatan yanzu kin tuno wacece Asma'u Sulaman 'yan a waki."!!! Ihu! Hafsa ta kurma ta
d'auki soyayyan man dake cikin kasko ta watso min da sauri na kauce saboda nasan da zafin
sa zai iya 'kona ni. Kaina tayo aikuwa santsin mai da 'bawon doya ya kayar da ita cikin man
dake da sauran zafi kafin kace kwabo fatar hannunta ta kwailaye! Ina tsaye ina kallonta tana
kuka.
Granny da Innah Suwaiba suka shigo kicin d'in hankali a tashe! Innah Suwaiba kaina tayo tana
fad'in"Shine kika 'kona min yarinya saboda kina ba'kin cikin zata zama kishiyar ki shine tun
yanzu kike so ki nakasta min ita Dan ubanki! Mari ta kai min a fusace.!!!








*8/12/2019*
[12/9, 10:38 PM] .: *BABBAN YARO*

*80*



Nayi saurin dafe kuncina ina kallon matar cike da d'umbun mamaki! Ta cigaba da
cewa"Shikkenan kawai saboda ta shigo tana soye-soye a gidan d'an uwanta sai ki 'kona ta da
mai saboda sharri da ba'kin ciki to Bari kiji wallahi ki sanya a ranki sai kin zauna da ita a
matsayin kishiyar ki, domin ita tudu biyu taci ga aure ga 'yan uwan taka."! Ta 'karashe maganar tata cikin kumfar baki.

Hawaye masu zafi ne suke zurarowa a daga idona tace"Kina tsatsare mutane da idon ki na
rashin kuny...... Kafin ta 'karasa granny ta katse ta ta hanyar fad'in"Wannan ba girman ki bane
Suwaiba abunda ya kamata kiyi kafin ki yanke hukunci shine ki fara tambayar su me ya had'asu
ba ki za'bi taki ba Asma'u ma 'yar ki tunda tana auran d'anki." Granny ta 'karashe maganar cikin
sigar rarrashi.


Botsarewa tayi tace"Kina kallo fa ta 'kona mun yarinya wane irin ba'asi zan tsaya tambaya anan
ga gaskiya a zahiri duk bakin cikinta baza ta ci arzi'kin ita kad'ai to kaji."!!

Cikin saurin na futa daga kicin d'in ina ji zuciya kamar zata fashe saboda takaici tabd'ija lallai
akwai rigima mutu'kar matar nan tace zata zauna min a gida domin na lura bata 'kauna ta ko
kad'an nima take naji wata irin tsanar ta ta shiga zuciya ta, zama nayi gefan bed ina tunani
matakin da zan d'auka kan Hafsa babu shakka tayi ganganci tace zata had'a miji dani... Aure
bazan hanashi yayi ba, kuma Hafsa 'yar Uwar shi CE bazan rabasu ba amma ko da wasa
bazan d'auki raini daga gurin kowa ce shegiyar ba ciki kuwa har da ita Innah Suwaiba.



Waya ta dake kan drawor ta fara ringing Sam banyi tsammanin shine ba ina dubawa nagan my
one and only da abunda nayi serving d'in numbar shi kenan.

Murya 'kasa nayi sallama inajin ya sauke ajiyar zuciya kana ya amsa sallama ta, shiru nayi
domin har yanzu akwai sauran 'bacin ran su Innah Suwaiba a tare dani.... Yace." Me kike cewa
d'azu kika kashe min waya."?

Shiru nayi ina tunani nace" inajin shi yace." Kat ki 'kara kashe min waya daga yau." A hankali
nace "Tom."!! Ina baby."? Ya fad'a cikin wani irin voice Wanda ya sanya ni jin wani yanayi nace"
sun futa cefane da Iyami. "

Yanayin yanda yayi magana ya nuna min ransa ya 'baci yace." A kan me za ki bari a futa da ita
kasuwa dole ne cefe nan." ! Na sassauta murya ta tare da fad'in"Dole ne mana tunda bamu da
wasu a bubuwam a kicin Rambo bayan nan, Doh-doh kuma kun tafi tar...... Kafin in 'karasa ya
katse ni a hargitse yace." Kada ki kuskura ki 'kara bari a tafi min da yarinya kasuwa ko ina gari
ko bana gari Wannan si shirme ne ita Iyami me yasa baza je ita d'aya ba."

Cikin zuciyata nace "Ikon Allah ."! A zahiri kuwa ha'kuri nake bashi ina fad'in " Baby ce take
kuka dole sai Iyami taje da ita." Aiko saurara ta baiyi ba ya kashe wayar sa......
Wayar nake bi da kallo cike da mamakin hakinsa Sam shi idan ya d'auki zafi baya tsayawa ya
saurari mutum... Na fi minti goma rike da wayar a hannuna, kana Naji motsin shigowar Iyami
parlor na futo kamar babu abunda ya faru nace"Iyami kin dawo ne."?

Tace"Na dawo yanzu baby nayi ta min kuka s hanya." Nace." Sakkota mu gani." 'Kokarin
sakkota take daga baya ta sanya kuka Iyami tace" barta kawai a bayan nawa." Nace"Ke da zaki
shiga kicin yanzu." Tace"Hakane fa yanzu da na shiga kicin din aje kaya nace"Ba'ki mukayi a
gidanan ken..... Innah Suwaiba ta katse ta ta hanyar fad'in"Mu ba ba'ki bane 'yan gidane sai dai
kece ba'kuwa." Iyami tayi saurin fad'in"A'a sannu Innah Suwaiba Ashe kece." Banzan kallo tayi
mata tazo ta zauna kan kujera hannunta rike da wani plate cike da doya da 'kwai ta zauna ta
fara cin abunta.


Iyami kicin ta nufa ni kuma na wuce d'akina rungume da baby domin nayi alk'awarin banza

'k'ara shiga har Kar matar ba gaisuwa ma don ta zama dole ne."


Waya ta na d'auka ina kirashi tana ta ringing ya'ki dauka har ta katse na 'kara kira ta katse bai
dauka ba, sai da na kira sau uku bai d'auka ba na hak'ura nace Fushi yake yi kenan take naji
zuciya nima nayi min zafi nace karfa wannan guy ya samu hanyar wula'kantani don yaga na
saki jiki dashi dashi har yake mun fad'a domin a rayuwata na tsani in kira mutum a waya ya
kashe ko ya'ki dauka.... Wata zuciyar tace min Kin manta Irin zaman da sukayi da Mimi dama
kuma granny ta fad'a miki shi mutum ne me d'aukar zafi amma bashi da rik'o, lokacin sai naji
zuciyata tayi sanyi saboda nasan zuwa dare ya sakko dole zai nemi ya kira waya ko don yaji
gwalantun babynsa da ya saba. Ranar haka na yini sukuku sai bayan sallahar Isha'i sannan na
futo parlor. Granny Iyami Innah da Hafsa duk suna zaune suna kallo Cikin kwanciyar hankali
abunsu.... Kai tsaye daining na nufa domin cin abunci granny tace"Kin futo kenan." Ina tafiya
nace"E Granny sannun Ku da hutawa. " hankalinta na kan TV tace"Yawwa kinga hankalina ya
d'auke gurin kallon Wannan wasa Dad'in mu ko dad'in kowa ina son kallon diramar nan. " ta
k'arashe maganar tana dariya... Ina kokarin zama nace"Ba kya kad'ai ba granny shirin dadin
kowa ya shiga zuciyar mutane sosai." Hira muke tsakani mu Innah Suwaiba na makamin harara
ko kallonta banyi ba nagama abunda nake yi na bar gurin bayan nayi wa Granny sallama.


Ko da na shiga d'akinta wanka nayo jikina duk babu kuzari na duba wayata ya Kai sau biyar
banda ko misscal d'insa ba, haka dai nayi shafe-shafe jikina sanyi 'k'alau na shirya baby cikin
kayan baccin ta kwantar da ita nayi saman cikins na kwanta rigingine waya ta na d'auka na
lalubo numbar Munnu wacce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login