Showing 27001 words to 30000 words out of 37941 words
Chapter 10 - BABBAN YARO book 3 Book End Complete by Binta Umar Abbale .pdf
yace." Zaki sumbace ni ki gudu to na
kama ki idona biyu kiyi min yanzu Ku kuma in 'bata wannan kwalliyar."
Asma'u ta diririre "Ni fa b... ba wani Abu Zan.... Maka ba." Tafad'a cike da kunya.
Yace." Ok zaki gyaramin kwanciya ne kika rankwafo kaina kome ."? Cikin sigar tambaya ya
fada."
Kunya duk ta isheta fuskarsa ya cusa tsakanin wuyanta yana gogo mata gemunsa tuni tsigar
jikinta ta fara tashi da kyar tace." Abban baby ka bari ba babu dad'i Wallahi."
A hankali yace." Kike rantsewa babu dad'i.'' Daga kanta tayi a shagwabe!! Babu zato taji ya
damk'i dukkanin Brest din nata da hannunsawa biyu yana murzawa yace." To Wannan fa."!!.
Hannunsa take kokarin cire shi kuma yana kokarin d'age rigar Yana so ya zura hannusa sosai
yaji laushinsu cikin hannunsa duk ya wani burkice mata kokari kurrum yake ya kwantar da Ita ita
kuma ta turjewa.... Da kyar ta samu ya sake ta ta mike da sauri tana gyara rigar Dan har
biriziyar ta balle daga baya.... Hararsa tayi kasa-kasa ta zumb'ura bakinta hanyar futa ta nufa
yace." Kizo kar ki futa nace." Kin zuwa tayi ta bude dakin ta futa da sauri tasan halin futunar shi
jiya idan ba matantawa tayi ba sai tace sau kusan uku yana yin rileazing a jikinta da ya kawo
yake 'kara wani 'k'arfin kamar wani doki
Kicin ta nufa tana baza kamshinta mai dad'i gaske Innah Suwaiba da Hafsa ta Tarar a tsaye
suna yiwa Iyami masifa kamar wasu iyayen ta
*12/12/2019*
[12/12, 10:23 PM] .: *BABBAN YARO*
*86*
'Kamshin turaran ta ne dauki hankalin su, suka juyo da sauri suna kallon bakin 'kofa. Asma'u ta
hade fuska sosai domin taga irin kallon da Innah ta watsa mata, cikin ladabi tace"Innah kin tashi
lafiya." ? Innah Suwaiba tace"Da ban tashi ba zaki ganki, don baki da kirki zakiyi min irin
wannan gaisuwar kamar wata sa'ar ki, ko kuma shi mijin naki bai fad'a miki matsayi na a gurin
shi ba." ?
Cikin kwantar da harshe nace"Inna kiyi hakuri don Allah ba sai Abban baby ya fad'a min
matsayin ki a gurin shi ba na sani dani dashi duk muna karkashin ki kuma ke a matsayin
mahaifiya kike a gurinm...... Inna Suwaiba ta katse ta hanayar fad'in.
"Ke bana son kinibibi da iya samun guri da kin dauke ni a matsayin uwarki ai baza kiyi min irin
wannan gaisuwar ba."!
Shuru nayi mata ganin yanda take magana a hasale bana so ina fada tana fada babu mutumci
yin hakan.....Iyami na kalla cikin taushin murya nace" Iyami me ake had'awa na kalaci."?
Iyami tace"Yanzu dai zan fara aikin." Cike da mamaki nace"Yanzu kuma."? Tace" E wallahi na
shigo kicin din ne nagansu suna aiki shine kika shigo wai bazan ta'ba komai ba sai sun gama."
Raina ya 'baci sosai Iyami macace mai 'kokari da ganin girman mutum Sam bata raina mutum
tana da mutumci bazan so abunda zai "bata mata rai ba. Nace''Innah da kinje kin huta Iyami
zata hada komai na kari kamar yanda ta saba kome kike so ki karya dashi ki fad'a zata miki."
Hafsa ta hasalo! Ta inda take fad'in"Babu wata banza da zamu tsaya ta yi mana iko da abunda
muke da iko dashi ke kibar wani hura hanci a gidanan kina wani baza 'kamshi ke kanki mu
muke da iko dake saboda haka ki iya takunki."
Duk 'kokarin danne zuciyarta da nake yi abun ya faskara na kalli Hafsa fuskata a had'e
nace"Kiyi shuru tunda ba dake ake ba."! Innah tace"Baza tayi shurun ba sai ta saka baki domin
itama watarana mai bada doka da oda ce a gidanan.""
Na bude baki kenan zanyi magana granny ta shigo kicin din tana fadin"Hayaniyar me nake ji ne
a gidanan da safiyar Allah." ? 'Kasa nayi da kaina INA 'kokarin mayar da hawayen da suke
'kokarin min...... Innah tace"Yarinyar 'kankanuwa ta tsaya a kaina tana 'kokarin zagina da
safiyar."! Granny ta kalleta cike da mamaki tace"Asma'u baza ta zage ki ba Suwaiba don Allah
mu zauna lafiya ki k'yale yara suyi abunsu."
Innah Suwaiba ta hau matse hawaye tana fad'in " Yau kam zan bar gidanan domin yafi k'arfin
na duk da ina da iko da meshi kin nuna min ni bani na haifi Amjadu ba, Aisha ce Uwar shi
abunda baki sani ba kuwa shine abunda yayi Aisha shine yayi Suwaiba. "!! Ni da granny muka
bita da kallo cike da mamaki! Ta futa daga kicin din tana kuka.
Hafsa tabi bayanta bayan ta gama watsa mana mugun kallo dani dasu granny da suke tsaye
suna mamakin wannan al'amarin..... Granny tace"Asma'u ko kinki ko kinso Dole yau in bar
gidanan domin ni bazan zauna in tayar miki da hankalin gida ba dama dalili ne ya kawo ni
gidanan saboda haka na bar zaman shi daga yau.''.
Hawayen da nake 'kokarin danne wa ne suka zubo min na kasa cewa komai har granny ta futa
daga kicin din..... Innah Suwaiba kuwa tana shiga parlor suka yi kicibus da Amjad ya futo daga
dakin Asma'u yana dauke da baby a hannuna ganinsa sai ta 'kara rururcewa da kuka tana fadin
"Dole in bar gidanan yau domin an nuna min matsayina a cikinsa, kamar ni Suwaiba 'karamar
yarinya ta nemi fada min magana."! Ta k'arashe maganar cikin kuka.
Amjad yace." Inna wai me ya faru ne kike kuka kiyi shiru ki fada min." Karaf Hafsa tace"Asma'u
ce ta zage ta wai akan me zamu shigar mata kicin."
Wani irin kallo yake watsa Hafsa kana ganin kallon kasan na tsana ne yace." Yi min shuru ke na
tambaya ko ita."? Hafsa tayi 'kum! Da bakinta tana sinne kai wani irin bala'in kwarji guy yayi
mata take jikinta ya fara kyarma!
Inna kuwa jin tsawar da ya dakawa Hafsa yasa ta 'kara kyami gurin kukan tace"ai ba karya Tayi
maka ba, matar ka dai zagina tayi kuma a Gavan granny ta zage ni ta nuna mai aikin gidan ka
tafi ni daraja dole in bar gidanan yau.
Amjad yaji kansa. Yana Sara masa Sam ya tsani hayaniya a rayuwar sa shi da zata tafi ta bar
masa gidansa ma yafi son haka.. Amma don ya kwantar mata da hankali yace." Innah kikace
Asma'u ta zage."!? Tace"Ba wai kuma babu karya a ciki naga ka tsaya kana mamaki dama
yarinyar bata da tarbiyya shiyasa kowa yake gudun hada jini da ita."
Karaf a kunne na, raina yayi mugun b'aci sosai jin irin kazafin da Innah take min har kokarin
'bata suna idona ya rufe Sam na manta wacece ita, da kausarshiyar murya nace"Kiji tsoron
Allah baiwar Allah sai fad'a kike yi na zage ki da girman ki da kome karya dai haramun ce babu
kyau a cikinta na d'auka dani da Hafsa duk d'aya muk.........."Asma'u. "!!! Cikin tsawa ya katse
ta yana mata wani irin kallo fuskar shi a mugun had'e!!
Innah Suwaiba tace" Koda naji ka gani ai a gabanka dai Yarinyar nan bata duba furfura ta ba
take cewa ina 'karya oh! Duniya kenan Nasan inda ta dauke ni a matsayin uwarta bazata fada
min haka ba, hummm ko da yake duk laifin ka ne da baka nuna mata matsayina ba, Innah
Suwaiba ta kare maganar tata tana me rurucewa da kuka. "!!!!
Asma'u ma hawaye ta fara sharewa tana mamakin wannan masifar daga yin aure yau kwana
uku Shikkenan ta kasa samun nutsuwa wai yaya zata yi ne."!?
A kausashe taji Muryar sa yace." Ki bata ha'kuri yanzu."!
Kallon fuskar sa tayi ta ganta a murtuke! Ya wani tsatstsare ta da ido, granny tace"Ba wai zan
hana ta tabata hakuri bane amma ina so kafin ka yanke hukunci ka dunga bunkice ni dai da
kunne na banji lokacin da Asma'u ta zagi Suwaiba ba, amma tunda abun ya zama haka ke
Asma'u bata hakuri domin a zauna Lafiya. "! Hannu nasa na goge hawayen fuskata na kalli
Innah Suwaiba dake zaune cikin kujera tana matsar hawaye nace" Innah kiyi hakuri don Allah."
Tace." Oh-oh aike zan bawa hakuri ke da akazo gidan ki za'a takura miki." Amjad yace.'Innah
mu bar wannan maganar don Allah Insha Allah Zaku koma gidana dake Rijiyar Lemo da zama
na bar muku kome kike bukata kiyi mun magana ni dan ki baki da banbanci da mahaifiyata
Kuma Asma'u ma 'yar ki ce tunda iyalina ce don Allah kiyi hakuri magana ta wuce."
Inna Suwaiba bata so haka ba amma babu yanda ta iya tace"To nagode K'warai da gaske Allah
yayi maka albarka ya jikan mahaifiyar ka, amma da nake cewa ko zamu je gidan gomnatin tare
ne."!
Cikin 'kosawa yace." Innah ki bari tukkuna in zama governor din sai a shirya shawarar abunda
zai faru yanzu dai idan anjima zan sanya Doh-doh ya kaiku can gidan akwai kome a ciki babu
abunda zaku nema." Inna sai was he baki take yi tana shi masa albarka tace"To kafin mu tafi
INA so muyi muhimiyar magana dakai.".
Yace. " tom Shikkenan ni dai burina ki kwantar da hankalin ki kuma ki dauki Asma'u kamar ni."
To Dan albarka kome ya wuce a gurina...... Ni kam tuni na bar musu gurin zuciyata kamar zata
tsage saboda takaicin su gaba dayan su.... Kuka na zauna naci sosai a dakin.. Kafin ya shigo
cikin shirin futa. Dauke kaina nayi daga kansa har ya karaso kusa dani ya sanya hannu ya dago
fuskata hade da tsira min idonsa, lumshe idona nayi hawayen da nake makalewa suka zubo .....
Tsugunawa yayi ya tallafo fuskata ya fara aikunshi sai da ya tabbatar ya lashe ruwan hawayen
da suke zubo min a fuskarta sannan yace." Nasan Halin Innah Suwaiba da tada futuna Asma'u
inaso kiyi hakuri da ita kamar yanda nake yi da ita ki dauke ta a matsayin uwa kinji ko kiyi min
wannan alfarmar don Allah duk abunda zata tayi miki ki daina mayar mata da magana."!!!
Rungumeshi nayi sosai ina jin wani irin tausayin shi nace"Abban baby kayi hakuri don Allah
Wallahi raina ne ya 'baci shiyasa na mayar mata da magana amma insha Allah bazan sake
ba."!! Bayan ta yake bubbugawa cikin sigar rarrashi yake fada mata kalamai masu sanyaya
zuciya har ya samu tayi shuru kana ya fada mata abunda zai futar dashi yanzu.... Asma'u tayi
masa addu'a da fatan alkaro hade da samun nasara a rayuwa, bai futa daga dakin ba sai da ya
ya mutsa mata jiki da salon soyayarsa ya futa ya barta da kewar sa.
****
Amjadu ne tare da dumbun jama'ar gari suke zagaye a birnin kano da kewayen ta dukanin wasu
local goment da suke karshin jahar kano sai da suka zagaya yawon kamfen alhamdullahi babu
wata local goment da shiga a ka jefe shi ko aka yi masa ihu! Ko wace local goment sun bada
goyon baya, cike da samun nasara suka dawo gida.
*12/12/2019*
[12/13, 10:14 AM] .: *BABBAN YARO*
*87*
Amjad bai shiga gida ba sai da ya tabbatar da komai ya kammala a cikin gidan da ya mallakawa
Mahaifiyar Asma'u gidane plate mai kyau sosai ginin zamani gida cikin jama'a kuma 'yan boko
dama yana da ire-ire wannan gidan yake ginasu saboda mabukata to gaskiya Wanda ya saka
Umma a ciki nagani na fada ne komai na jin dadin rayuwa akwai shi a cikin gidan sannan yayi
musu sallama Umma albarka kawai take shi masa ko a mafarki bata ta'ba tsammanin zata
zauna irin wannan gidan ba na wane da wane, yanzu sun ringa sun gane cewar magauta ne
hade da 'yan siyasa masu Neman kujerar governor suka had'a wannan kutungwilar domin a
tozarta Amjad din, a cewar su idan jama'ar gari suka ji cewar iyayen matar shi na yawon yaya
zasu zage shi, to shima Amjad din tun kafin aje ko ina ya gane sharrin abokan adawa ne.
A ranar bai shiga gida ba sai kusan sha daya na dare domin sai da yaje ya dubo Rambo dake
kwance asibiti yana samun kulawa sosai kuma bashi da wata matsala tunda Amjad din yana
tsaye a kansa.
Yana shiga parlor yaga mace a zaune kan kujera tayi kirif da hijab! Ya tsorata domin baiyi
tsammanin ganin kowa ba sanin da yayi dare yayi dukanin su basu yi bacci Ba.
Cike da mamaki yake kallonta yace." Innah bakiyi bacci b." ? Hamma! Ta buga Muryar ta da
alamun bacci tace"ta ina zanyi bacci ina jiran ka ka dawo muyi muhimiyar magana wannan
yaron yazo ya matsamin da lallai sai nazo mun tafi sabon gida wai Kaine ka umarce shi yazo ya
dauke mu." Amaj ya zauna cikin kujera cikin gajiya yace." Nine nace Yazo ya kaiku gidan tunda
mun gama magana dake tun da safe."
Inna Suwaiba ta gyara zaman ta sosai tace"Har ka manta maganar da nace zamuyi da Kai ko."
Sosa kansa yayi yace." Wallahi na manta Innah kin San abun da yawa kiyi hakuri."
Tace"Ai ya wuce kam har kullum muna yi maka fatan alkairi da zamowa shugaba me adalci."
Yace." Godiya nake Inna."
Cikin kwantar da murya Innah tace"Dama Alfarma ce nake nema a gurin ka wacce nasan kana
da damarta sai dai Idan baka yi NIYYA ba ko kuma matar ka ta hana ka amma abunda nake
nema a gurinka Allah da manzon sa sun hallata maka shi kuma Kai kan ka zaka kara yin
kwarjini ka zama cikkakan namiji mussaman yanzu da nauyi zai hau kanka yana da kyau ka
amin cewa 'bukata ta "
Cikin. "Kosawa sa maganar ta yace." Innah idan muna magana dake tsakanin mu ne don Allah
ki daina sako iyalina a ciki Asma'u bata isa ta sani nayi abunda ban yi niyya ba wannan
tsakanina dake ne ji fad'i ko wace irin alfarma kike so insha Allah idan da hali ni zan miki
alfarma innah ke kin wuce ki nemi alfarma a gurina." Innah Suwaiba ta saki fuskarta sosai jin
abunda Amjad din yace Tace." Dama ina so ka auri 'yar uwarka Hafsatu insha Allahu baka da
matsala da ita nayi mata tarbiyya sosai zasu zauna lafiya da ita Asma'u mutukar wata futuna ta
'bullo to babu shakka daga 'bangaran ita Asma'u ne domin ni nasan yarinya ta me tarbiyya ce ,
bayan haka kuma Hafsa a kanka ta'ki sauraron d'imbun samarin ta da suke sonta da aure Tace
dole kai take so, lokacin babu irin magiyar da banzo nayiwa kakar ka ba a kan mu hadaku aure
ta bujere tare da fadin"Ita baza tayi maka dole ba katsaham! Muka samu labarin auran ka da
wannan yarinyar me rasuwa ina nufin mahaifiyar baby 'alamarin ya 'bata mana rai sosai ganin
muna a matsayin iyayen ka, ka kasa zuwa ka sanar mana shiyasa muka yi fushi muka koma
gefe guda hade da zuba muTo. ido sai bayan ta mutu kuma shima katsaham! Muka ji auran ka
da ita wannan d'in to da nayi bunkice sai na tabbatar da cewar kaima baka sani ba Allah ne ya
nufin haka, to sai muka dauki abun a matsayin kaddara yanzu dukanin abunda ya faru a baya
mun YAFE maka."!
Ta k'arashe maganar ta ta tana sauke ajiyar zuciya.
Dama tun kafin ta fad'i maganar ta ya fahimci inda ta dosa, don haka bai wani furgita ba yace."
Innah idan muna magana dake a tsakaninmu ne don Allah ki daina sako sunan kowa ciki naji
kina maganar cewa granny ta hanani auran Hafsa ki gafarce ni anan wallahi ba laifin ta bane
granny tayi iya bakin kokarin ta gurin ganin ta 'kulla auramu Allah bai nufa ba, idan tuhuma
zakiyi to ni zaki tuhuma domin ni na nuna bana ra'ayin yarinyar Sam bana sha'awar auran
zumunci, kiyi hakuri don Allah ki bar zancan ni Hafsa a matsayin 'kanwa na dauke ta, insha
Allah zan tsaya mata a kan kome idan ta samu miji zan yi mata aure kuma zan gantata amma
maganar aure tsakanina da ita ki aje ta gefe.
Innah Suwaiba ta fashe da wani *Mashahurin* kuka tana fyace majina tace"Ta tabbata bani na
dauki cikin ka ba yau tabbata ta bani ce na tsuguna na haifeka yau ta tabbata bani ce na shayar
da Kai ba! Yau ka nuna min *Aisha* ce uwarka domin nasan ita baza ta ta'ba umartarka da abu
ka bujere wa bu'katar ta ba, Alhmdullahi Allah yasa nima na Haifa da yau nasha takaici."! Cikin
kuka me futar da sauti ta 'karasa maganar.
hankali a tashe yace." Innah! Yi shiru don Allah ki daina wannan kukan da kike yi bana so,
wallahi dukan abunda kika fada ba haka bane na fada miki a Yanzu bani da wata uwa da ta
wuce ki kiyi hakuri kiyi shuru muyi maganar please."!!!
Inna Suwaiba ta fyace majina kamar ba dare ba sai d'aga murya take yi ta cigaba da cewa"Idan
da ka dauke ni a matsayin uwa ai baza kayi min musu a kan magana ta ba hummm."!!
Amjad yace." To kiyi shuru muyi maganar kinga dare ne kar ki tashi mutan gidan kiyi shuru don
Allah." Innah Suwaiba ta goge hawayen ta tana fad'in "To kai nake saurare."!?
Ajiyar zuciya ya sauke ya dafe kansa mintu biyu tsakani yace." Bukatar ki kawai in auri Hafsa
ko.? Ko numfasawa bata bari yayi ba tace" Shine bukata ta yaron kirki." Kallonta yayi idonsa
yayi ja yace"Shikkenan Allah ya sanya alkairi. " washe baki tayi tana zabga masa godiya tare da
fad'in"Insha Allahu zaka yi alfahari da wannan auran tunda kayi min biyyaya."
Mik'ewa yayi yace." Innah ya kamata kije ki