Showing 12001 words to 15000 words out of 37941 words

Chapter 5 - BABBAN YARO book 3 Book End Complete by Binta Umar Abbale .pdf

24 Jul 2025

462

tsananin jarumta Amjad ya mike tsaye hannunsa dafe da k'irjina
da yake jin wani irin zafi da zugi a gurin ya rintse idonsa ya bud'e su kan Doh-doh yace." Rambo
yans cikin halin taimako. "!! Cikin tashin hankali doh-doh ya kamshi yana fad'in" Sir kaima a
halin yanzu taimako kake nema, mubar gurin nan domin ns lura mutanan ran ka suke buk'ata!!!

Amjad ya mike tsaye a daddafe jini duk ya bata masa hannu Doh-doh us rike shi suna kokarin
futa cikin jama'a, da sauri d'an jaridar nan ya futo daga mab'oyar sa ya k'araso gurin tare da
kama gefan kafadar Amjad din yana masa sannu kana yace." Yallab'ai insha Allah Kaine kake
da nasara kuma insha Allah karshen mutananan yazo domin duk abunda ya faru a gurin nan
ina dashi cikin na'ura ta insha Allah sai mun tona musu asiri."!


Amjad yaji dadin wannan Abu take yaji k'warin a jikinsa duk da cewa yana jin jiki domin ba
k'aramin suka wuk'ar tayi masa ba daurewa kawai yake yi suka futa cikin dandazon jama'ar gari
dake ta hatsaniya da ta kura sai rigima suke da yaran gidan gomnati, futowar Amjad din ce ta
dauke musu hankali, su kuma suka samu nasarar guduwa bayan sun faffasa galashin motar
Amjad yayi raga-raga!!.... Sam wannan bai dame shi ba, burinshi kawai mai girma shugaban
kasa ya San abunda yake faruwa a jahar kano domin daukar mataki akan governor bisa
wannan danyan aikin da suka yi.

Wasu matasa ya sanya suka dauko Rambo suka sanya shi a mota Rambo saboda tsabar
galabaita da yayi Sam ya kasa magana sai gumi yaki ga jikinsa yayi bud'u-bud'u!!! Shi kanshi
Amjadu din Jikinsa bud'u-bud'u da k'asa saboda tumurmuson da sukayi a kasa!


Yini nayi cikin zullumi da fargaba da fad'uwar gaba misalin biyar da kwata muna zaune a
parlor ya shigo gidan, sallamarshi muka amsa dukaninmu muka bishi da kallo, wata irin
fad'uwar gaba ta rikito min ganin shi cikin jini a jiki duk k'asa!! Salati nake a zuciya ta na mike
zumbur!! Granny kuwa ai kafin ya karasa shigowa ta riske shi bakin kofa ta fashe da kuka tana
fadin "Dama fad'uwar gaban da na yini ina kenan innalillahi wa'ina ilahi raji'un."!!! Kuka take
sosai ta rirrike shi kwata-kwata ta hanashi magana "Hatsari kukayi kome!? Ooh ni jikar mutum
biyu, Asma'u kinga abunda na yini ina fada miki ko watak'ila tunanin abunda kikayi masa ne ya
sanya a ransa don Allah ki kula da mijin ki." Yanda Granny ta hakikance tana magana ne zaka
fahimci ba a cikin hankalin ta take ba kuka take yi ya samu ya shige bedroom d'insa ba Tare da
yace mana komai ba.
Kallo na bishi dashi jikina na rawa!! Granny tace"Kinyi tsaye a gurun baza ki bishi kije meya faru
ba."!? Kafin ta rufe baki har na bud'e d'akin na shiga. Yana tsaye tsakiyar dakin yana kokarin
cire rigar shi na karasa gurin da sauri! Nace"Abban baby men..... Meya faru wai."!!! Shiru yayi
min. Yana cire rigar shi na fasa wani ihu! Ganin naman kirjin shi a waje fatar ta kwailaye jini
jazur Ashe suit din jikinsa shine yake tsane jinin yana cire wa ya fara kwatanya a jikinsa yana
d'iga k'asa." Hawaye shab'e-shab'e a fuskata nake nuna gurin da hannuna na kasa cewa
komai!


Wuce ni yayi zai shiga toilet na bishi da sauri rike hannunsa nayi nace"Kana ganin yanda jini
yake zuba a jikin ka ko ka damu abban baby ba a wasa da rai kaji tausayin tsuhowa kaji
tausayin baby wacce bata San meye rayuwa ba, don girman Allah ka daina wasa da ranka."!!!
Cikin dauriya yace." Yanzu me kike so ayi miki."!? Ina zubar da hawaye nace "Ka bari a duba
gurin nan kar ya zama matsala."!! Murmushi yayi me ciwo yace." Zanyi dressing gurin da kaina
kar ki damu." Girgiza kaina nayi nace"Ka Bari a kira Jahid ya duba sosai wai kai baka ganin
yanda jini yake zuba ne."!!! Kallonta yake cike da mamaki ganin yanda take hawaye duk ta tada
hankalin ta yace." Mik'o min wayata gata can." Da sauri na mike na d'auko.

Jahid ya kira a waya tun kafin ya fada masa komai yace." Ganina akan hanya Aboki duk ina
da labarin komai innalillahi wa'ina ilahi raji'un. "!!? Daga haka ya kashe wayar tasa......shuru
dakin yayi, k'irjinsa na zubawa ido inda ciwon yake ina ji kamar a jikina na mike da sauri ina
neme-neme a dakin dankwalina na cire da sauri na d'ora kan ciwon sam bana son gani.

Wani irin d'as!d'as!d'as! K'irjinsa yake hakan ya tabbatar min Yana cikin tashin hankali da
fargaba na kalleshi sai akayi sa'a shima ni yake kallo mun fi minti uku muna kallon juna daga
bisani nace" Abban baby meye faru don Allah ka fad'a min. "!?

Idonshi tsaye akaina yace." Tsautsayi ne kawai amma dai da da karar kwana da sai dai kuji
mummunar labari." Naji fad'uwar gabana ya karu "Hadari kuka yi da mota."!? Girgiza min kai
yayi alamun a'a! " To menene. "!? Nafada Muryata na karkarwa." Kai tsaye yace." Magauta ne
suke so suga bayana."!! Kuka nasa nace"Allah ya fisu kaima ka daina biye musu idan naso
kake mu rasaka ba, kamar yanda muka rasa Mimi." Shiru yayi mata kawai yana kallonta had'e
da mamakinta sosai lallai yau yaga tsantsar sonsa a kwayar idonta.
[12/8, 1:16 PM] .: *BABBAN YARO*
*78*

Wallahi har ga Allah a lokacin na manta 'yar tsamar dake tsakaninmu dashi, hankalina ya tashi
da yanda naga jini na zuba a jikinsa kuma bai damu ba.. Dankwalina Dana sanya a gurin ya jike
da jini na sanya hannuna na daine gurin hawaye na kwaranyo min, yace." Wai kukan me Kikeyu
ne."? Rasa abunda zance masa nayi kuma ban fasa shashshekar kukan ba, ina jinsa ya sauke
ajiyar zuciya yace." To idan kuma akace miki na mutu yaya zakiyi ? Ki daina min wannan kukan
bana so kina k'aramin zafi cikin zuciyata domin zubar hawayen ki a gabana babban tashin
hankali ne."

Shuru nayi masa dai ina kokarin maida hawaye na gefe guda kuma ina tunanin maganar da
da yake cewa kukana nayi masa zafi cikin zuciyar sa...... 10 minutes Jahid ya shigo gidan iya
parlor ya tsaya ya kira wayar Amjad din. Mik'ewa yayi zai fita na bishi a baya cikin mutuwar jiki.
Jahid nata zayyanewa Granny abunda ya faru, ita kuma sai salati takeyi cike da tu'ajubi
tace"Shikkenan da da karar kwana sai da akawo mana gawar sa, innalillahi wa'ina ilahi raji'un."
Kuka ta fashe dashi sosai da taga Amjad din ya futo duk jini a jikinsa ta dinga fadin innalillahi
wa'ina ilahi raji'un."


Zama yayi kusa da jahid din dake kokarin futo da kayan aiki yace." Granny please wannan
abun fa bana kuka bane ko na tashin hankali don Allah kiyi min addu'a na yarda dukkanin
abunda ya samu bawa daga Allah ne don Allah Ku daina daga hankalin Ku." Tace"Dole ne nayi
kuka k'ato kai kadai nake gani a duniya inji dad'i narasa iyayan ka kaima bana so na rasa ka."!!
Girgiza kansa kurrum yayi, Jahid ya soma yi masa dressing din gurin ciwon yana kara kwantar
wa da granny hankali.


Shuru parlor yayi minti goma ya kalleni dake tsaye kanshi, kasa nayi da kaina zuwa yanzu na
fara dawowa nutsuwa ta yace." Kunna min TV nan ." Cikin sauri naje na kunna masa kamar
yanda ya umarce ni..... "Mik'o min romot d'in mu gani." Yafad'a yana Dan ciji lips d'insa saboda
yanda yake jin zafin ciwon Ga Jahid ya dage sai wanke gurun yake da magani.

Hannuna rike da romt din na karasa gurin na mik'a masa tare da matsawa daga gurin domin
ji nayi tsigar jikina na wani irin tashi gani Kwata-kwata bana son ganin tashin hankali a

rayuwata. Tashar *NTA NEWS* Ya kunna dai-dai lokacin da suke yin labaransu na k'arfe shida
cikin turanci suke fad'ar abunda ya faru a jahar kano tsakanin governor kano d'in da Amjadu
*Young millionaire* hoton governor da Amjad suka hasko lokaci guda suka cigaba da hasko
badak'alar da ta faru a rujajjam company inda mutanan mai girma governor suka dinga b'arna
da sakin harbi hade da tiyagas, da inda suke kokarin k'watar manager , kai har dambe tsakanin
Kumurci da Amjadu sai suka hasko dukanin abunda ya faru da inda Kumurci ya dab'awa
Amjadu wuk'a a k'irji. Da kuma lokacin da suke dariya har suka samu nasarar guduwa bayan
sun jikkta mutane tare da ragargaza gilashin motar Young millionaire. "
Tsakanin ni da granny ban San Wanda yafi wani tsurewa ba ganin hatsaniyar da ta faru lallai
kam da da k'arar kwana da sai dai a kawo mana gawarshi. Iyami ce ta shigo da baby a
hannunta, karb'ar yarinyar nayi na rungume a jikina ina kokarin danne hawayen da suke
kokarin zubo min ayya nawa nake cikin zuciyata da ya mutu Shikkenan baby ta zama marainya
gaba da baya zata taso bata San iyayen ta ba, naji tausayin tsohuwar data kwallafa ranta a
kanshi.... Gabana ya fad'i cikin zuciya ta nace idan ya mutu ke wane halin zaki shiga? Ni kaina
nasan ina masifar son guy mussaman yanzu na San mallakina ne kawai ina share shi saboda
sanin halin shi, nake tunanin gwara in kama kaina tun wuri amma ina ganin dole in sauke nawa
in kula dashi idan ba haka ba abun zai yi masa yawa ko ina babu sauki duniya ga uban makiya
Allah ka tsare min shi. Abunda nake fada kenan cikin zuciyata.

Baby ta dinga yunk'urin sai ta sauka taje gurin shi ina riketa Hannunsa guda ya miko min wai
in bashi.... Nace"Ta yaya zaka iya daukar ta sai ta dauje maka ciwon ."" a hankali yace." Ke dai
ki bani ita nace, kar ki bari tayi wannan kukan ranki zai b'aci. "! Gurin na karasa muka had'a ido
da Jahid kunya ce ta kamani don Wallahi shaf na manta ban gaishe shi ba, nace" Jahid munyi
lafiya yasu Salim." ? Murmushi yayi kad'an yace." Lafiya lau Salim nan lafiya zan kawo miki shi."
Nace"To ina jira." Daga haka nayi shiru ina mik'a masa baby. Kallon fuskarsa nayi naga ta
sauya karb'ar baby yayi ya rike ta da hannu d'aya, yarinyar ta dinga kokarin kai hannunta gurin
ciwon tana so ta jawo bandejin da Jahid yake nad'a masa a gurin. Granny tace"Dama ganganci
ne yasa ka karbeta kasan yanzu hannunta yayi ido komai kamawa take yi."
Wasa yake da baby din bama ya sauraran abunda granny take fad'a. Duk hankalinsa na kan
'yar tashi.

*****

A ranar kiran gaggawa ya samu governor dashi da Amjadu daga fadar shugaban kasa,
hankalin shi ya kai k'oluluwar tashi yasan halin mai girma shugaban kasa da zafi da daukar
Serious ba tare da b'ata lokaci ba ya nufi babban birnin tarraya abuja, cike da ta tsantsar tashin
hankali da nadama.... Lokacin da sak'on shugaban kasa ya samu Amjadu sam ba nuna wata
fargaba ko tashin hankali ba, tabbas yasan gurin da zasu je ba gurin wasa bane dole yaje da
shirin sa duk wasu matakan kare kansa ya tanade su hade da shaidu, yana jin jiki ya kira
doh-doh a waya Wanda yake can asibitin malam Aminu yana kula da Rambo yace." Yazo yana
Neman sa, a daran aka kira Ali wannan d'an jaridar shima Dole zai zama shaida a gurin duk da
ba kutu zasu shiga ba amma yana ganin tafiya dasu tana da amfani...... Nan parlor muka kwana
ni dashi da baby domin babu yanda banyi dashi ba kan ya tashi mu koma daki yak'i hakanan

na zaune kasan kafet shi yana saman kujera a kwance baby gefan hannun shi inda babu ciwon
ko kadan ban rintsa ba kamar yanda bai rintsa ba.

K'arfe hudu na asubah ya mike yana kokarin dauke baby a jikinsa mik'ewa zaune nayi da sauri
na dauke baby na kwantar kan kujera, ya mike zaune, hannun shi na rike hade da tsira masa
ido... A dake yace." Menene. "!? Hawaye ne suka fara sintiri a idona nace" Wallahi ina jin tsoron
zuwan ka abuja nan."
Tsaki ya ja k'asa-k'asa yace." Jiya kin kwana kina kuka ga rashin barci kan abunda bai shafe
ki ba, na fad'a miki tun jiya wannan kukan da kike yi bashi da amfani Sam na tsane shi."
Hannunsa na saki na hade kaina da gwiwa sosai nake zubar da hawaye ni kadai nasan irin
fargaba da take damuna akan wannan al'amarin gani nake yi idan ya tafi kamar yanda ya fada
jiya za' muji mummanan labari!!!


Shashshekar kukan ta ne ya dame shi! Dafe kansa yayi ya yunk'ura ya mike tsaye cikin k'arfin
hali ya tsuguna gabanta tare da d'ago kanta suka fuskanci juna..... Kallon-kallo muke ni dashi!!
Ga hawaye shab'e-shab'e a fuskata.... Fuskarsa yake matsowa da ita, nayi saurin rintse idona
hawaye suka zubo, harshen shi naji kan kuncina yana lashe ruwan hawayen. Nayi saurin bude
idona ina kallonsa shima ni yake kallo kuma bai fasa lashar fuskata ba. Naji wani irin Abu a
jikina lokacin babu abunda nake so illah in jini a jikinsa babu hali da babu ciwo da babun
abunda zai hana na rungume shi. Sai da ya lashe ruwan hawaye na tas! Sannan ya mike a
nutse ya shiga toilet din parlor.


Jiki a mace na bishi da kallo har ya shige dakin , kwanciya nayi a gurin ina zubar da hawaye
ni kaina kukan da nake yi ya ishe ni..... Alwala ya dauro a gurguje ya futa k'arfe biyar da rabi ya
dawo gidan kai tsaye dakin shi ya shiga ya sanya Riga da dogon wando jins shart din mai botira
ce kuma bata da nauyi sosai saboda ciwon sa, a gurguje yake yin komai har ya kammala ya
futo hannunsa rike da wayoyinsa yaji dad'i da ya futo ya tadda Asma'u ba tashi daga parlor
baby dake bacci kan kujera ya mannawa kiss a kumatu yayi saurin futa saboda jin tsoron
rigimar granny.. Yana futa Doh-doh da Ali na tsaye, take Ali ya bude masa mota ya shiga shima
ya zauna kusa da doh-doh yaja motar suka futa daga gidan. Kai tsaye airport suka nufa.
[12/9, 11:02 AM] .: *BABBAN YARO*



*79*



Gabakid'aya wad'anda suke fad'a aji k'asar najeria sun hallara a d'akin meeting na fadar mai
girma shugaban k'asa, Amjadu ne kawai mai k'ananun shekaru a cikinsu, duk sun girmeshi

nesa ba kusa kai harda wandanda suka girmi mahaifin sa a cikinsu kuma dayawa daga cikin su
k'abilu ne saboda haka suke komai cikin hikima da nutsuwa, duk wani bunkice mai girma
shugaban kasa ya gama yi kuma ya tabbatar governor Alkanawi shine bashi da gaskiya duk
wani dauki ba dad'i da ake da a jahar kano ya sani kuma shine ya haddasa ta, bayan yayi
rantsuwa da alkur'ani gaban bainar jama'a zai yi kula da jahar sa zaiyi mulki tsakani da Allah
amma ya karya doka, babu shakka a abunda yayi ba k'aramin Abu bane ya wuce gona da iri ta
inda mai girma shugaban kasa yake ganin dole a hukunta shi, kuma mulki ya bar shi har abada
domin a doka ta siyasar kasa duk governor da aka samu da cin amanar kasa za'a hukunta shi
kuma ya bar siyasa har abada don haka 'yan majalisa da hukumomin zab'e suka yanke
shawarar juyin mulki ga mai girma governor Alkanawi domin su nawa jama'ar kano damar zab'o
Wanda suke so ya mulke su daga nan zuwa wata biyu lokacin zab'e kenan.... Bayan nan kuma
mai girima shugaban k'asa ya sanya dole hukumar Efcc ta tsaurara bunkice a kansa domin
alamun rashin gaskiya sun bayyana a fuskarsa. Wannan shine hukunci da aka yanke ga mai
girma governor Alkanawi... Bayan nan kuma Mai girma shugaban kasa da shauran k'ososhin
k'asa suka jinjinawa Amjadu *Young millionaire* bisa ga NAMIJIN kokarin sa bisa kawo wa
k'asar shi cigaba da jikinsa da kud'in sa da lafiya hak'ika idan k'asar najeria tana alfahari dashi
da wannan aikin nasa. Nan mai girma shugaba ya sanya hannu a wata ta karda dake gaban
shi, ya mik'awa na kusa dashi shima ya sanya hannu haka har sai dai mutum goma suka sanya
hannu a wannan takarda kana takadar tazo gaban Amjadu shima ya karb'a ya sanya hannu ba
tare da ya fahimci me takardar mecece ba.... K'arshe ta kardar ta koma gaban governor
Alkanawi, hannu na rawa ya sanya hannu zufa suk ta jika jikinsa shaddar jikinsa duk ta jik'e
yana sanya hannu wani soja dake tsaye kusa da shugaban kasa ya dauki takardar ya ajeta
kusa da shugaba shi kuma ya had'ata da wasu takkadu ya rufe!!!

Ambassador Aminu Ahli shine ya kalli Amjadu cikin turanci yace." Duk wani Abu da zaka yi a
jahar kano Wanda kake ganin zai kawo cigaban kasa da talakawa mu zamu mara maka baya
kaje kayi kanka tsaye zamu tallafa maka ni cikin asusuna na cire 50 Million's na baka domin
kaje ka k'ara farfad'o da harkokinka da company ka da suka rusa, take jama'ar gurin suka dinga
ma Amjadu kyautar ta bangirma Shi kanshi shugaban kasa sai da ya bashi 50
Millions.....*Innalillahi wa'ina ilahi raji'un* wanin hanin ga Allah baiwa ne *Amjadu Young
millionaire* Ni Binta na taya ka murna hak'ika babu abunda yafi gaskiya a duniya dad'i wani
lokacin akan yi maka Abu domin a kuntata maka amma daga k'arshe sai ya zame maka alkairi,
Fad'ar irin mak'udan kud'in da Amjadu ya samu a gurin b'ata lokacine. Mai girma governor
Alkanawi kamar ya mace saboda bakin ciki.Take Sojoji suka tasa k'eyar Alkanawi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login