Showing 30001 words to 33000 words out of 37941 words
Chapter 11 - BABBAN YARO book 3 Book End Complete by Binta Umar Abbale .pdf
kwanta Shikkenan magana ta wuce na amunce. "
innah ta mike tana fadin "Allah ya tashe mu lafiya kaji yaron kirki gobe sai kara tusa maganar da
tsayar da ranar d'aurin aure."
Wuce wa yayi ba tare da ya tanka mata ba yana mamaki ta sosai shi yanzu babu maganar aure
a gabanshi sai bayan za'be tukkuna kome ye sai ayi ya amunce mata ne kawai domin a zauna
lafiya sosai yake mamakin rigimar mata.
Ina jin motsin shigowar sa 'karamin Parlor na nayi saurin hayewa bed wasu masifaffun hawaye
masu tsananin zafi suka kwaranyo min a fuskata.
Asma'u yini tayi cikin fargaba sanin da tayi cewar mijinta ya tafi yawon kafen dole tasan akwai
ma'kiya da suka saka shi a gaba mafi a kasari ba'a futa a dawo Lafiya shiyasa ta yini tana yi
masa addu'a samun nasara da dawo wa lafiya hankalin ta bai kwanta ba sai da taji shigowar
motar sa gidan sannan ta saki ajiyar zuciya taje ta d'aga labulen window tana le'ken sa har sai
da ya shigo sannan ta sauke ajiyar zuciya ta zauna tana jiran sa ya shigo shuru har kusan minti
ashirin tayi tunani ko yana d'akinsa zai yi wanka mik'ewa tayi da nufin zuwa kawai ta zo bude
kofa taji maganganun su da Innah Amjad yayi wa Innar sa alk'awarin auran Hafsa auran ta
dashi tun baije ko ina ba zai yi mata kishiya ita kuma tata 'kaddarar kenan haka Mimi Tasha
wahala akan shi itama gashi ko sati bata cika a gidan sa ba abubuwa sun cakud'e ta mata
Innalillahi wa'ina ilahi raji'un. "!
Cikin wannan hali ya shigo ya same ta fitalar dakin ya kunna yaganta zaune daram kan bed!
Asma'u duk kokarin ta na hana hawayen ta zubawa ta kasa zuba kawai suke yi sharrrrrr!
Zuciyar ta sa wani irin Tara tsatsin kishi take yi."!
[12/13, 9:32 AM] BintuUm@rAbb@le: Cikin yanayin tafiyar shi ya 'karaso kusa da ita sam bai
fahimci kuka take ba sai da ya kusan ci jikinta sosai yaji shashshekar kukan ta.... Jikinshi na
kyarma ya zube wayoyinshi gefen bed din ya rugumota jikinsa yana sauke ajiyar zuciya tare da
tambayar ta kukan me take, shifa ya tsani ganin zubar haweyen ta.
'Kokarin kwace jikinta take shi kuma ya rike tam! Yana rarrashin ta Sam baiyi tsammanin taji
maganar su da Innah ba tambayar ta yake yi me ya same ta take kuka.... Cikin zafin zuciya ta
gartsa masa cizo! A hannu sosai yaji zafi a hannunsa ya ki sakinta duk ya rikice! Da kyar ta
samu ta bude bakinta tace"Ka k'yaleni ni, tunda na lura kai kan ka kawai ka san...... Katse ta
Yayi ta sauri yana rawar jiki yace." Me nayi miki ne nifa bana son wannan kukan kiyi shuru ki
min bayani ki daina magana kina kuka kinji."! Yana maganar yana goga mata fuskar shi a tata
wannan d'abi'ar shi ce da alama shu k'okari ma yake ya had'e bakin sa da nata.
Tace." Duk maganganun da kuka yi da Innah naji su Kai ko kunya baka ji ba har da amincewa
zaka auri hafsa wallahi bari in fad'a maka abunda baka sani ba zaka mai da gidan ka sansanin
ya'ki domin tuntuni bama zama inuwa d'aya da wannan kucakar yarinyar me warin hammata! Ni
kam na fad'a maka sai dai ka za'bi guda cikin mu ni ko ko ita domin wallahi bazan had'a miji da
ita ba."!
Yanda take fad'an maganar zaka San da 'k'uruciya a tare da ita bayan nan Kuma tsananin kishi
ya rufe mata ido Sam bata tunanin maganar da zata fad'a.
Maganar ta ta bashi dariya sosai amma sai ya dake baiyi ba sai ya sauya al'amarin ma ta wata
sigar....... Haushi ya turni'ke ta tana yi masa magana yana wani Abu daban, ture shi take daga
jikinta shi kuma yana 'kara sakar mata nauyin sa har sai da yayi nasarar danne ta gaba d'aya ya
tsira mata rukittatun idonsa masu kashe mata jiki.
Kauda fuskarta take yi ganin yana shirin yi mata abunda ya saba lallai ya raina mata hankali, sai
ta fara ya kushe masa jiki tana turje-turje da 'kafafun ta duk ta turje bedshirt din...... Yaso ya
sanya mata 'karfi kawai sai ya k'yaleta hade da sauka daga kanta... Toilet ya nufa domin yin
wanka yana mamakin tsananin kishin ta a kansa.
Jikinsa daure da towel ya futo ya tsaya gaban dressing mirror ya feshe jikinsa da turare kana ya
sanya Riga mai gajeran hannu..... Asma'u har yanzu tana zaune ta hade kai da gwiwa tana
kuka, bai CE mata komai ba ta futa daga d'akin...
Mintuna biyar yayi ya dawo hannunsa rike da 'karamin Cup Wanda yq had'o coffee a ciki ya
zauna kusa da ita yana kurba yana latsa wayarsa.
Haushin sa kamar ya kashe ta wato ba zai rarrashe ta ba ma balle yayi mata musu akan
maganar da ta kawo masa wayar shi ma yake dubawa ta tabbata kenan abunda kunnen ta yaji
ye mata gaskiya ne.
Zuciya ce ta ciyo tace"Wallahi INA sane da masu sona da wa'inda basa so na Ni a rayuwata
babu abunda zan cewa granny domin ta nuna mana 'kauna dani da 'yar uwata Mimi Allah ya.
jikanta, duk abunda wannan matar take yi min baka cewa komai babu irin 'kazafun da bata yi
min ba dukol kayi shiru. To ni kuma nace bazan zauna da 'yarta ba wallahi sai dai ka zab'i guda
cikiin mu kuma duk wani Abu da take min taje na barta da Allah zai saka min."
[12/13, 10:03 AM] BintuUm@rAbb@le Fuskar sa a had'e ya d'ago kansa yana kallonta "Kina da
hankali kuwa Asma'u? Innah kike kokarin fad'awa magana a gabana uhumm."!? Ya fad'a
muryar shi babu dad'i!
Ba tare da na damu ba nace" Ai itace ta jawo meye ruwan ta dani a gidan mijina a matsayin ta
na babba bai kamata ta shiga hurumin da bana ta ba tun da tazo gidan nan take zagina." Cikin
kuka take maganar....
Ido ya tsira mata fuskarsa babu wasa yace." Ke Matsalar ki kenan tsaurin ido! Shiyasa kowa ya
tashi zai fad'i aibunki ke baki bar yara ba baki bar manya ba uhumm ? Idan da mutumci ya dace
ki fad'awa Innah Suwaiba wannan maganar ko da kuwa cewa tayi in auri mata uku a lokaci
guda ai tana da iko dani ne."
Asma'u taji kamar ya watsa mata barko no a ido idonta a rufe tace." To sai me idan tace ka auri
Hafsa bayan ita ka 'kara da wasu biyu ko a kwalar rigar Asma'u wallahi ni dai nasan ta siya
maka tashin hankali a cikin gidan ka, Wanda nasan idan Maman ka ce ita ta hak'ika baza ta so
kayi rayuwa cikin tashin hankali ba, ita dai akwai wata manufar ta ita kad'ai ta sani."!!!
Sama-sama take maganar....
Babu wasa a maganar shi yace." OK da kike yin wannan fuffukar kina tunanin zaki hanani
abunda nayi niyya ne? Ko kina tunanin zan bujerewa maganar Inna Suwaiba akan taki, Wallahi
ki shiga hankalin ki ni nan da kika ganni bana daukar raini gurin ko wace mace zan 'bata miki rai
Wallahi! Daga yau sai yau ki San irin maganar da zata dinga futowa daga bakin ki akan Inna
domin duk rintsi Uwata ce ke ma haka dole ki girmama ta kamar yanda nake yi "you have to be
serious."! Ya fad'a cikin 'bacin rai!
Asma'u kuka kawai take yi cikin zuciyar ta kuwa babu irin addu'ar da bata yi wa Innah Suwaiba
Allah yayi mata katangar k'arfe da sharrin ta ubangiji Allah ya rusa maganar tun kafin aje ko ina
ita tana ganin idan abun ya tabbata to babu shakka Zama Lafiya ya 'kare tsakaninta dashi tana
mugun sonsa Wanda shine ya jawo mata tsanin kishin sa.
Sosai take kuka Yana jinta Yayi mata shiru kurbar Coffe dinshi yake gefe guda kuma yana latsa
wayarsa a zahiri ka kalleshi sai kace kukan NATA baya cin ransa cikin zuciyar sa kuwa shi kadai
yasan yanda yake jin zafi da kukan ta, ranshi ya 'baci ne da jin irin bak'aken maganganun da
take fad'awa Innah Suwaiba ko kunyar idonsa bata ji ba, idan da zai bude mata zuciyarsa ta
gani zata yi mamakin girman son ta da kaunar ta a ciki kawai yana dannewa ne saboda sanin
halinta, shafa ya amsawa Inna ne kawai amma Sam bai shirya auran Hafsa ba yanzu bai sani
ba ko nan gaba.
Asma'u ta gaji da kukan ta bacci me nauyi ya d'auketa cike da mafarkin 'yan gidansu
musamaman Ummansu ta ganta cikin farin ciki da walwala.
Jin saukar ajiyar zuciyarta ya gane tayi bacci shima ajiyar zuciyar ya sauke kana ya kashe
wayar sa toilet ya shiga ya wanke bakinsa ya futo kai tsaye bed din ya nufa ya kwanta hade da
shiga blenket din ya rungume ta jikinshi yana sauke a ajiyar zuciya k'amshin da jikinta yake futar
wa ne ya gigita shi tuni ya fara ya mutsata yana kaiwa ko wanne shashe na jikinta kisses masu
zafi! A rikice yake kokarin cire mata Riga... Furgit ta bude idonta ta ganshi yana kokarin hawa
jikinta da sauri tayi nufin tashi ya mai da ita da hannu daya daya hannun kuma ya zare mata
rigar jikinta tuni ya gigice ganin lafiyayyun Brest dinta masu gigita shi take ya rungume ta a
jikinsa yana sauke ajiyar zuciya.
Asma'u duk buge-bugen da take yi. Sai da Amjad yayi nasara a kanta ya samu biyan bukatar
shi.
*13/12/2019*
[12/13, 10:27 PM] .: *BABBAN YARO*
*88*
Haka suka tashi da safe ita dashi kowa na d'acin rai! Tunda ta gaishe shi bata 'kara kula shi ba
shine ma yake janta da hira tana basar dashi haka suka had'u suka yi breakfast har shi uban
gayaar ya d'ora baby a cinyar sa sai shirme suke yi shi da ita ya koma kamar wani 'k'aramin
yaro yana biye mata sai faman dariya suke kyalkyalawa.
Granny bayan tagama karyawa mi'kewa tayi ta nufi d'akin da take suka bita da kallo Sam basu
kawo komai ba, minti biyar tsakani sai gata ta futo cikin shiri ta yafe jikinta da mayafi kirif tayi
hanyar futa ba tare da tacewa kowa komai ba."
Da sauri na mike naje na tari gabanta ina marairaice fuska nace"Granny ina zakije inace jiya
mun gama magana dake kince kin fasa tafiya."
Jin abunda Asma'u take fada ne yasa shi mik'ewa da sauri ya karaso gurin yana tambayar
menene."?
Granny tace"Dama yau na shirya tafi gidana." Amjad ya 'boye dariyar da take 'kokarin subce
masa yace." Wani abu aka miki a gidan. " ? Gyada kai Tayi tace"Ba'ayi min komai ba kawai zan
baku guri Ku wataya."
Dariya yasa ya kama hannunta guda yace." Rayuwata baza ta tafi dai-dai ba idan babu ke a
gidan uwargidana ta kaina idan mun yi miki laifi ki hak'ura. "
Granny tace" babu laifin da kuka yi 'k'ato nice naga ya dace in tafi." Amjad yace." Ni kuma ban
sallame ki ba sai kiyi hakuri idan kuma kika ce dole sai kin tafi kin San kina futa zan sanya a
saki karnuka sai muga ta inda zaku tafi."
Cikin sababi! Granny tace." Sai kace zaman nawa dole ne iyi yanzu nace nafi son zama a
gidana nagaji da jin iface-iface! Cikin dare."
Saurin barin gurin nayi ina mamaki tsohuwar ko me take nufi oho.! Ina Juyawa Inna Suwaiba ta
watsa min mugun kallo tana gyada kanta... Bedroom dina na shige ina fadin"Allah Yayi min
gatangar k'arfe da sharrin ki."
Kwanciya nayi kan bed din ina sa'kawa da kwance wa har bacci me nauyi ya d'auke ni.....a
takaice dai ban San sanda su Inna Suwaiba suka bar gidan ba domin bacci na shirga sai daf da
sallahar azahar na tashi a gurguje nayi wanka da alwala na futo simple make up nayi na zura
doguwar Riga mai hula humra na shafa a jikina sannan na hau dadduma na tada sallah
Ko da na futa parlor granny kad'ai na gani zaune suna hira da Iyami na saki wata irin ajiyar
zuciya mai sanyi, yanzu na tabbata Innah Suwaiba sun bar gidan cikin zuciyata nace mata 'yar
bala'i kurrum tazo zata d'aga mana hankalin gida. Zama nayi cikin kujera cikin sakin fuska na
dinga sanya musu baki a hirar tasu kafin mu zauna cin abunci granny kam cewa tayi Iyami ta
had'a mata ta kawo mata inda take domin baza ta iya zaman daining ba. A cewar ta 'kafar ta
tsami take ni da Iyami muka sanya mata dariya... Yanzu wani irin nishadi nake ji a zuciya idan
na tuna cewar me takura min tabar gidan wallahi d'an zaman da Tayi na kwana biyu jina nake yi
a takutey gefe guda kuma idan na tuna al'kawarin da Abban baby ya daukar mata sai gabana
ya dunga fad'uwa.
*******
Al'amura sun tsananta ga me girma governor gobe wato *Amjadu AbulAbbas mainasara* Yanzu
kwata-kwata baya zama a gida kullum suna can suns taron siyasa ya tsai da mataimakin sa
Engineer Jabir Hamid shine ya yarda da alkairin sa da kulawar sa kana da yanda ya tsaya
tsayin daka akan jam'iyyarsu tabbas Engineer Jabir Hamid tsohon d'an siyasa ne Wanda yake
da a 'kida Amjad tun yana da 'kananun shekaru yasan da mutumin domin. A haife ya haife shi
idan kididdiga ma za'ayi ya girmi mahaifin shi, to dashi ya yarda ra'ayin shi shi jama'ar jahar
kano suke bi lokaci guda al'amura suka dai-dai ta yayin da 'yan bakin ciki da hassada suka 'kara
yawaita sharri kullum yin sa ake yi ga amjadu amma yak'i tasiri jama'ar jahar kano sun Riga
sunyi nisa a 'kaunar sa, Nima nace tabbas zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana
shawo sai yayi Amjadu sai dai fatan alkairi
Kullum zai dawo gida cikin dare a gajiye amma saboda tsabar futuna komai baccin da Asma'u
take yi sai ya turme she ta ita kuma tayi ta masa sangarta da shagwab'a salo-salo abunda yake
'kara gigitashi kenan yake 'kara dilmiya cikin kogin sonta, sun ringa sun saba ita dashi kullum
sai sunyi sex kuma basa tab'a yin sau d'aya a rana duk rintsi kafin ya futa sai 'kara wani da safe
ko da asubah.....aikuwa Asma'u tayi wata irin lafiyayyar 'kiba fatar ta murje sosai Sam bakye ce
mata baka saboda tana samun kulawa kullum oga nayi mata feshi tayi 'kiba sosai ta samu
Lafiya ita dashi duk sun mance da wani zancan Inna rayuwar su suke yi tsaftacciya....Asma'u da
kanta ta fuskanci tana da ciki domun wata biyu kenan bata yi al'ada ba kunya ta hanata fad'a
masa, shi kam gogon NAKU hankalinsa ya d'auke gurin harkokinsa Sam bai fahimci komai ba
tabbas yasan dai Ta 'karayin Sugar ta inda Idan yana sex da yake iface-ifecn da ya saba Wanda
Granny take 'k'orafi akai Asma'u ce take rufe masa bakin sa wani sa'in amma Amjadu hauka ne
kurrum baya yi mata a gado.
****
Granny ce ta fahimci abunda yake faruwa aikuwa farin ciki duk ya isheta shiga futa d'ari sai tayi
zancan ciki motsi kad'an Asma'u zata yi zata hau fad'a wai ta dinga yin komai a hankali da
nutsuwa ita dai sai dai tayi dariya kurrum...cikin wannan yanayin za'be yazo gari ya hargitse ya
hautsine ko ina ka duba police ne sosai aka sanya matakan tsaro a garin na kano, ana ya gobe
za'be Alhaji Hashimu da Yarshi Hibbah suka shiga gidan redio domin ayi hira dasu.
Dama tun safe ake maganar cewar za'ayi hira da tsohon d'an kasuwar nan Wanda yaga jiya
yaga yau a fannin kasuwanci wato Alhaji Hashimu mai citta mutanan gari suka dinga dariya
suna fadin ko me zai fad'a oho kowa ya 'kaugauta lokaci yayi ya saurari hirar har shi kanshi
Amjadu wayar sa na hannun Rambo yana jiran lokaci ya kunna masa.
Alhaji Hashimu mai citta ya zage yana shirya karya kan Amjadu har da fad'in cewar mahaifin sa
da bashin mutane ya mutu kuma bayan haka shi ba d'an gari bane yazo gari zai mulke su yana
da kyau jama'ar kano su farka kar su zab'i bara gurbi Wanda zai tarwatsa jahar kano daga
k'arshe ya koma garin su na gado maganar 'k'arshe da ta girgiza mutane shine abunda Alhaji
Hashimu yace."Amjadu yayi wa yarshi ciki gashinan wata hudu a jikinta suna da shadar haka
koda jama'ar gari zasu karya ta...... Wannan zancan ya jawo kace nace a garin inda kowa yake
fad'ar ra'ayin da akan Amjadu dim wasu suna ganin hakan zata iya faruwa tunda dama tsohon
Dan bariki ne yana da hotel har guda biyu tabbas ba asan iya adadin matan da ya lalata
ba......wasu kuwa a take suka karya ta maganar tare da cin alwashin sai sun ragargaji mai citta
shi da shegiyar yar tasa sai ta fada musu Wanda yayi mata ciki da bakinta, a rake su ka dauki
gorori cikin shirin ko ta kwana suka nufi titin gidan redio na *Komai da ruwan ka* lamfu suka yi
daga nesa suka hango motar Mai citta ta futo daga cikin gidan redio aikuwa suka futo da gudu
suka tsaya kan titi... Cike da tsoro mai citta ya ci birki hankali a tashe! Yake kokarin bude motar
ya futo Hibbah kuwa har ta saki futsari a wando tsabar furgita da tayi kafin su Ankara suka ji
taratsatsa!!!! Gilashin motar ya fashe d'aya daga cikin matasan ne yake dukan gilashin motar
yana fad'in "Futo tsohon banza da shegiyar kilakin 'yarka ogon namu zakuyi wa 'azafi duk bakin
cikin Ku k sai ya zama governor!
Mai citta ya futo daga mota a gigice! Yana sa'be babbar rigar