Showing 36001 words to 37941 words out of 37941 words
Chapter 13 - BABBAN YARO book 3 Book End Complete by Binta Umar Abbale .pdf
musu tana yi musu bayanin cewar
ita mahaifiyar mai gidan ce suka ce basu San wannan tayi hakuri sai ya dawo tukkuna a lokacin
suna Chadi....Haka suka koma gida jikinsu suk a mace zagi kuwa babu rij Wanda Innah batayi
wa securitys din tana fad'in " Idan governor ya dawo zai nuna muku matsayi na a gurinsa shegu
tsinannanu.!
Da ta samu labarin dawowar shi sai ta sanya Hafsa ta shirya sosai suka nufi government house
din zuciyar cike da kudure-kudure a cewar ta sai ta sa Amjad din ya kori wannan masu gadin da
suka yi mata wulakanci sannan ta umarce shi ya sanya ranar d'aurin auran sa da Hafsa.: Ko da
suka isa gidan sai suka yadda securitys har sun fi na kwanaki yawa tabbatar cewar mai girma
governor yana ciki bai futo ba, taje ta tsaya tana musu magana dukaninsu Hausa bata ishe su
ba domin kadan ne daga cikinsu hausawa turanci suke mata suna zare mata ido! Inna ta tsorata
sai ta koma gefe guda tana haraarau Hafsa da ta tsinci kad'an daga abunda suke cewa tuni ta
tsure! Domin cewa suke maza su bar gurin idan ba haka ba zasu Zane su da bulala! Inna na
gama jin abunda Hafsa take cewa kawai sai ta fashe da kuka Wanda yayi dai-dai da shigowar
Aunt Hauwa cikin gidan cikin dalleliyar motar ta. Ga mamakin Inna taga aunt ta bude mota ta
futo kuma kaitseye ta durfafi securities din babu wani fargaba ko tsoro sai ta dunga mamakin ita
kuma wacece ita? Gani tayi suna gaishe ta suna mata magana da turanci hade da nuna su da
hannu abunda suke cewa shine wai tasan da zuwan su Innah ko kuma tare suke domin sun
San ta saba zuwa gidan da jama'a .
Juyowar da aunt Hauwa tayi sai da gaban Innah ya fad'i ganin suna kama da Asma'u a
zuciyarta tace"Babu shakka wannan yayar ta ce aikuwa hafsa tace"Yawwa inna ga aunt
Hauwa nan sai tq shiga damu gidan." Innah Suwaiba Tayi sakato da baki har aunt Hauwa ta
karaso gurin ta gaishe ta cikin mutumci sannan tace"Kuzo mu shiga ciki gashi munyi sa'a duka
mai grima governor yana nan bai futa ba." Simi-simi suka bi bayan aunt Hauwa tayi musu
jagora har katafaran parlor mai girma matar governor hamshakiya mandiya Asma'ulhusna.
Suna zaune a parlor ita da granny suna shira granny na saman kujera Asma'u na kasa kan wani
irin lallausan kafet ta mike k'afafunta Shi kuma ubangayyar yana matsa mata granny tana fad'in
"nauyin cikin ne yasa k'afar taki tayi kumburi nace anya kuwa Wannan cikin naki bana tagwaye
bane." Fad'ar maganar granny tayi dai-dai da shigowar su Innah Suwaiba cikin parlor
Innah Suwaiba tayi turus ganin abunda yake faruwa Amjad gurfane kamar wani bawa yana
aikin mammatsa k'afafun Asma'u dake zaune da ciki turus a gaba daga ita har Hafsa jikinsu
mugun sanyi yayi tuni Hafsa ta tabbatar wa da zuciyar ta cewar Asma'u tayi mata nisa kuma
tayi mata fintikau ya kowa ne b'angaran tasan ko inna ta sanya Amjad din ya aure ta to tasan
itace zata sha wahala a gidan Saboda tasan irin son da Amjad din yake wa Asma'u bana wasa
bane jikinta yayi bala'in sanyi kamar yanda na innah yayi sanyi cikin sagewar gwiwa suka
karaso cikin parlor granny tana musu barka da zuwa
Ita kuwa aunt Hauwa kunya ce ta ishe ta bata tab'a jin nadamar zuwa gidan ba irin na yau
governor da kansa yana yiwa kanwarta tausa lallai babu abunda zasu cewa Allah tabbas yanzu
ta k'ara tabbatar da cewar kauna da so tsakanin kanwarta ta dashi Amjadu din ajininsu yake.
Bayan sun gaisa da granny dashi kanshi uban gayyar ta wuce dakin Asma'u cikin kunya.
Ita kuwa Asma'u a ladafce ta gaishe da inna Suwaiba dake faman ya'ke tana satar kallonta a
fakaice har ta samu damar mik'ewa tsaye a daddafe Amjad din yana taimaka mata sai da ya
kaita kofar d'akinta sannan ya sake ta ta shiga gurin aunt shi kuma sai sannan hankalinsa ya
dawo jikinsa ya dawo cikin parlor Innah Suwaiba tayi muzu-muzu tana jin Shakkar ta fada masa
abunda ya kawo ta gidan saboda yanda yayi mata mugun kwarjini a ido haka suka gaisa dashi
jikinta sai kyarma yake yi Hafsa kuwa ba yarda ta hada ido dashi ba. Saboda kwarjini gami da
tsoro duk masifar da Inna tazo dashi ta neme shi ta rasa sai ta fara jan granny da hira cikin
rashin abinyi Ita kuwa granny biye mata tayi suka dinga hira kamar wani Abu bai faru ba....
Sunanan zaune Amjadu din ya futo cikin shirin futa...ya tsa Yana fadin''Innah zan futa ofis babu
wata matsala ko."! Baki na rawa tace"Babu komai Dan albarka Duk ka cika mu da abun alkairi
wallahi bama bukatar komai mungode sosai Ubangiji Allah ya jikan mahaifiyar ka." Ya amsa da
""Ameen kana ya futa yana mamaki innah da bata yi masa wani k'orafi ba sai yaga ma kamar
tsoransa take ji..shu kadai ya ke dariya cikin mota Rambo dake gefan sa yana taya shi
murmusawa hummm Rayuwa kenan Amjadu bai zubar da bodyguard dinshi ba a yanzu ma
sune suke take masa baya kasamcewar duk wata gwagwarmaya tare aka sha dasu.
******
Bayan shekaru hudu abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa har da haihuwar Asma'u inda ta haifi
twins duk maza masu kama da mahaifin su Allah bayanda baya al'amarin shi ana ya gobe suna
Hassam din ya rasu sakamakon shakewar nuffashi dalili lokacin an haifi yaran da sanyi a jikinsu
Amjadu sai da yayi kuka saboda ya yana son Hassan din kasamcewar ya Dan d'auko kamanin
Asma'u kadan a lokacin sai Asma'u tafi shi dauriya. Hakadai ya 'karaci kukan shi ya gama ya
barwa Allah to da yake ubangiji sami'uddu'ai ne sai ya kara bawa Asma'u cikin tagwaye lokacin
Husaini na wata goma sha daya ta haife su duk mata kuma masu tsananin kama da ita sai dai
daya tafi daya haske Hasana farace tas kamar ubanta ita kuwa Husaini kamar Asma'u tayi kaki
ta tofar har yanayin jikinsu da saurin bakinta gami da zafin nama irin na uciki Amjad ya Dora
mata son duniya komai Husaina komai Husaina gata da tsokana da Neman fada amma shi a
gurin sa bata laifi idan Maman su ma ta tsananta sai su kwana su yini yana surfa mata masifa
wani sa'in ma sai ya dauketa ma wuta ya daina kulata akan 'yayan sa sai taje tayi banbad'anci
tukkuna zai dawo.... Lokacin baby ta girma sosai yarinya me fara'a da hankali kamar uwarta
yanayin baby sak da na Mimi domin wani lokacin Husaina tayi ta haike mata tana tsagalgale
mata Saboda tasan tana da daurin gindi a gidan... Ko a gaban Amjadu din kuwa abun mamaki
sai yayi shuru ko ya mai da abun wasa ita kuwa Asma'u sai bayan ta tabbatar ya bar gidan take
kama Husaina ta zane tas! Ta kuna mata muhimamcin baby a gurinta abunda zai baka mamaki
ga wannan family shine duk sanda Asma'un take dukan Husaina Saboda halinta babyn ce zata
zo ta rugumeta ta kuka wai sai dai a Doke su tare Asma'u takaici duk ya ishe ta Tayi ta fada
tana cewa duk laifin baby ne da take wasa dasu..... Granny kuwa 'yar kallo tq zama a gidan
domin Sam bata shiga har karsu Saboda sun gama raina ta Ubansu ya gama shagwaba su
baby da Husaini sune c kawai take mutuntata a gidan.
Tsakanin Amjadu da Jahid zumunci yayi k'arfi sosai Jahid ya aje aikin gomnati ya tsayawa
Amjad kan harkokinsa na kasar waje abun sai son barka a lokacin ne kuma mahaifiyar jahid din
ta tabbatar da cewar Asma'u mai k'ashin arziki ce a cewar ta da ta yarda jahid din ya aure ta da
tuni shine governorí ½í¸ƒ
****
Umma ta samu wani alhaji dake nan unguwar da suke yana da mata biyu da yara bakwai sosai
zuciyarta ta amice dashi ta yarda zata aure shi mutumin yasan abunda yake yi a rayuwa kuma
yana tsaye akan iyalinsa sosai don haka akayi d'aurin aure Umma tq zauna cikin gidanta duk
ranan girkinta Alhaji Ayuba nan yake zuwa.
Gaba d'aya iyalan Umma sunji dadin Wannan auran da tayi domin shine cikar mutumci ta a
halin yanzu Ya Aminu yana da yara bakwai saboda shekata hudu da suka wuce ya kara aure
Munnu ta gama boran ta ta hak'ura Yanzu suna zaman Lafiya da kishiyar ta mai suna Amina
itama Aminar lallaba Munnu din take ganin yanda Ya Aminu yake kafkaf da ita.
****
Alina kuwa yawan bariki da shaye-shaye da take yi yasa ta zama kwarkwasino ita kad'ai
sambatu take yi wai itama matar governor ce.í ½í¸ƒ
Hibbah kuwa wani tsohon saurayin ta ne ya ya amunce zai aureta bayan taga yi masa
magajiya da koke kike ya amunce bayan ya kafa mata sharad'ai.
Rambo da doh-doh kuwa dama tuntuni suka yi aure lokaci guda Amjadu ya mallaka musu
komai na rayuwa suna zaune da iyalinsu cikin gidan gomnati.
***
Sai da Amjad yayi shekaru takwas kan kujerar mulki sannan ya sauka ya d'ora Wanda yake
ganin zai Dora daga inda ya tsaya a jahar kano an samu cigaba iri-iri an samu sauyi mutuka a
jahar kano komai yayi sauki ma'aikata da yan kasuwa suna harkokinsu yanda ya kamata
jama'a sai son barka suke yi masa tare da rokansa kan ya tsaya takarar shugaban kasa. Shi dai
bai amsa musu ba kawai yana binsu da abunda suka zo masa dashi.
Rayuwa kenan komai yayi farko yana da k'arshe a yanzu Amjadu da Asma'u sun haifi 'yaya
shida hudu mata biyu maza sai baby take cikin ta bakwai Idan ba fada akayi ba babu Wanda zai
ce itama ba Asma'u ce ta haifeta ba saboda kulawar da take bata ma tafi ta 'yayan da ta Haifa a
cikinta. Rayuwar gidan Amjadu sai son barka nutsuwa da kwamciyar hankali a gidan babu maganar
Karin wani aure a tare dashi duk ya aje gefe guda 'yayan shi ne kawai a. Gaban shi itama
Asma'u sai tayi da gaske sannan yake saurara ta gashi yayi mata mugun sabon da baza ta iya
barinsa ba.
****
Suna zaune Innah Suwaiba tazo ta sanar dasu d'aurin aure Hafsa Amjad yayi mamaki sosai
daga bisani yace." Duk wani Abu da ake bukata innar tayi masa magana zai tsaya akan komai
aikuwa haka akayi bukin Hafsa na zuwa yayi mata hidima sosai da sosai kana ya mallaka mata
k'aton gida hade da motar hawa lallai babban goro sai magogin k'arfe. Kyautar manya kenan
Bayan bukin Hafsa ne muka fara shirye-shiryen kaisu Baby da Husaini saudia domin suyi
karatu a can gaba ki dayamu har granny muka nufi kasa mai girma cikin aminci da yardar
AllahAllah.
*Alhmdullahi*
*Alhmdullahi*
*Alhmdullahi*
Nan na kawo 'karshen wannan littafin mai suna babban yaro ina ro'kon Ubangiji Allah ya yafe
min kusakuraina abunda na rubuta dai-dai Allah kamu ikon amfani dashi baki 'daya
Na gaishe ku real fans d'ina na gruop din babban yaro yawan Ku bazai barni in rubuta sunan
Ku ba ni Binta umar hak'ika INA alfahari daku wallahi nagode sosai da sosai da hadin kan da
kuka bani har na kawo karshen wannan littafin nawa ubangji Allah ya sada mu da alkairin sa
ameen
Sai mun had'u a sabon novel dina mai suna
*MASHAHURI*
_Taku......BintuUm@rAbb@le_