Showing 33001 words to 35284 words out of 35284 words

Chapter 12 - MANYAN MATA BOOK 2 BY HADIZA BARAU GIDAN IKO.docx

ke kashe su wanda da yawan mutane ke sharar baccinsu.

Ban gane hakan ba sai da na koma yin bacci da rana inda zan hango wanda zai mutu, wani in ba shi kyauta wani kuma in shaqe shi kamar yadda nayi wa na baya, wani kuma koda ban ba shi komai ba, ko ban shaqe shi ba koda ganinshi kawai nayi a mafarkina to zan tashi in ji ya mutu.

Maganar kitso da qunshi dama tuni na soke koda ban soke ba ma babu me shigowa gidan saboda tsorona da ake. Ana haka Alh. Bashir Bangis ya diro gare ni da maganar da tasa na tabbatar da hannunshi a cikin abinda yake faruwa a kaina.

“Me yasa ki ka fiye naci ne Beeba? Me ki ke xaukar kanki da girma? Yanzu kin zavi mutane suyi ta mutuwa a kan ki zo muyi aure? Yanzu hakan bai dame ki ba?”

Na dube shi “Ai ka makara Bangis, na rantse maka da Allah in dai sai ka aure ni za ka rayu to ka kusa mutuwa. Abin da kayi min in dai akwai sakayya tun a duniya Allah zai saka min. Kar ka sake zuwa inda ni ke.”

Yayi murmushi ya ce, “To shi kenan, tunda haka ki ka ce. Amma ki sani tunda dai ni ina sonki da aure kin qi tunda kin fi son muyi ta haihuwa babu aure idan na buqace ki zan san yadda nayi ki ka zo hannuna.” Ya tashi motarshi ya yi gaba.

Rannan da rana bacci ya kwashe ni sai kawai na ga wata yarinya me suna Bahijja ‘yar maqwabciyar Hajiya ce wai na bata

kyautar Alkaki. Na farka a firgice inda na jiyo koke-koke a gidan su Bahijja, inda na tabbatar ta cika tunda na gano ta a cikin mafarkina.

Ina zaune ina ta’ajibin lamarina sai ga sallamar Mamar Bahijja idonta sharkaf da hawaye, na dubeta a tsorace don ban san abin da ya kawo ta ba. Hajiya ta ce, “Me yake faruwa ne Maman Bahijja na jiyo kuka?”

Ta ce, “Hajiya ba tun yau muke tare ba amma zuwan wannan baqar daga komai na neman sauyawa, ashe abin da ake ta faxa a kanta gaskiya ne Mayya ce? To ta baiwa Bahijja Alkaki ga shi can Bahijja ta mutu.”

Hajiya ta dube ta “Yaushe Habibar ta ba wa Bahijjar Alkaki? Kin ga fa yanzu ta tashi daga bacci, yaushe rabonta da Alkaki?” Maman Bahijja ta ce, “Wallahi Hajiya yanzu ta bata shi, kuma da waxannan kayan na jikinta ta shigo gidan.”

Na zabga tagumi ina sharar hawaye. Maman Bahijja ta fashe da kuka “Shi kenan an yi min sanadin xiyata, wallahi ba zan tava yafewa ba! Allah ka isar min.” haka ta fice tana sharar hawaye.

Anyi haka da sati biyu na sake gano wasu ‘ya’yan maqotanmu na kusa da gidan su Bahijja, sai dai su ban basu komai ba ina farkawa naji anc e sun mutu su biyun, sai dai su ba a zo min ba amma dai an yayata ni ce na kashe su.

Zuwa wannan lokacin duniyar ta fice min a kaina. Ina zaune ne a cikinta ba don ina jin daxinta ba sai ya zamo ko abinci bana ci na fice a hayyacina, babu abin da ni ke buqata irin in mutu in huta.

Tuni kwana talatin xin da Yayan Hajiya ya xiba suka cika, ashe wai yana umara shi yasa ba muji daga gare shi ba. sai ya zamo duk bayan sati biyar sai an yi mutuwa a unguwar kuma in ba a ganni ba to za a xora mutuwar a kaina.

Ranar da ba zan tava mantawa da ita a kundin tarihin rayuwata ba ita ce, na kwanta bacci in da na ganni da wasu maqotanmu mata kusan su biyar in da nayi musu kyautar Alkaki, sai dai ba su karva ba inda nayi ta shaqe su xaya-bayan-xaya har suka ce ga garinku nan.

Ai ko ina farkawa ya yi daidai da hargowar da na riqa jiyowa a waje, kan ka ce me? Sai ga wuta an

cillo a gidan wadda ta yi ta’adi ba kaxan ba, sai dai sa’ar da aka yi ba a yi asarar rai ba.

Ganin haka yasa ban tsaya sauraren Hajiya da shawarar zan bar su ba, sai da komai ya natsa na batun wuta har an maida komai a mahallinshi, na kwanta ina jiran dare ya raba can na lura da goma tayi. Na miqe ba tare da na xauki wani abu ba na sulale ba tare da kowa ya ganni ba.

Tafiya kawai ni ke ba tare da na san in da zan nufa ba. Kallo xaya za ka yi min ka tabbatar da ni xin mahaukaciya ce saboda na farko dai yunwa ta busar da ni, kayan jikina babu tsafta, haka kuma babu mayafi a tare da ni.

Wani lokacin in share hawaye, wani lokacin in zabga tagumi ban san ko ina ne inda na tsaya ba, don haka kawai sai na kwanta ina ta tunanin rayuwa har bacci ya xauke ni, inda nayi mafarki da wata maqwabciyarmu

a Saulawa kawai sai gani nayi na soka mata wuqa a ciki har ‘yan hanjinta sun zubo.

Abin mamakin shi ne da na farka sai naga wuqar da na soka wa Jamila a kusa da ni har da jini a jikinta. Na bi wuqar da kallon yadda abin yake. Ina cikin kallonta ne na jiyo hayaniya a kaina. Na xaga kaina in ga abin da ke faruwa kawai sai naga zugar matasa xauke da makamai a hannunsu.

Kan ka ce meye? Na soma jiyo saukar duka a hannuna da duka sassan jikina a ka rufe ni da duka ta ko’ina, in da naji an zubo min wani abu me kamar ruwa na samu na buxe idona da ya soma kumbura saboda bugun da aka yi min, in da naga wani daga cikin matasan yana zuba min ruwan daga cikin wani galan inda a take na gane ba ruwa ba ne fetur ne ko kalanzir.

Ina ji wani ya ce “Kyasta wa shegiya ashana ta qone, meye amfaninta tunda dai ta kashe muku iyaye?” Na runtse idona sakamakon raxaxin fetur xin ya shiga ciki.

Raunin da suka yi min ina kuma hango yadda zan qone qurmus! Sai dai wata murya da na ji tayi magana inda na tabbatar da na san muryar tayi magana da cewa, “Kar ku xauki doka a hannunku, ku miqa ta ga hukuma, nima dama nemanta ni ke saboda ta kashe min mata.”

Na buxe idona da kyar saboda fetur xin da ya shigar min idon, na dubi me maganar Alh. Bashir Bangis na hango, ina daga kwance na kasa motsawa saboda raunikan da ke jikina, naji mota ta tsaya a kaina.

Ina ji aka tallabo ni aka saka ba a zame da ni ko ina ba sai asibiti, inda da na dawo hayyacina na gane motar ‘Yansanda ce ta kawo ni asibiti, inda daga

qarshe aka sanar dani wasu matasa sun kai qarata akan kashe musu iyaye da na yi, da kuma Alh. Bashir Bangis da ya ce na kashe mishi matarshi don haka ana sallamata za a miqa ni kotu don yanke min hukunci, saboda an yi bincike an gano na kashe mutane da yawa.

Satina biyu a asibiti aka sallame ni kamar kuma yadda aka shaida min haka aka yi, aka miqa ni kotu

, inda kuma Alh. Bashir Bangis ya fito ya ba da shaida har da qarin gishiri, gaskiya da ma qarya duk ya faxa. Daga qarshe dai aka yanke min hukuncin zama na din-din-din a gidan yari, idan kuma nayi sanadin kashe wani a inda zan yi zaman hukunci (gidan kaso) to hukuncin kisa zai tabbata a gare ni.

Ina ji ina gani aka tafi da ni gidan kaso, inda naga dariyar da Alh. Bashir Bangis ya ke min, inda ya keve da wani mutum wanda ban san ko waye shi ba daga qarshe aka ce ba a Katsina za a aje ni ba sai dai Kano ko Kaduna, in da aka wurgo ni Legas duk a cikin makircin Bashir Bangis don kar in ji labarin wani ko wani ya ji labarina.

Ranar da aka kawo ni Legos na kwanta barci

inda nayi mafarki da Hajiyar Zainil Abidin tana watso min ruwa a fuska tana tofa min addu’a, kawai sai naga wuta na cin jikina, sai naji Hajiya na faxin “Shaixaniya, da ikon Allah mun karya alqadarinki.”

Na farka da son in ga jikina da qunar wuta amma babu komai, sai dai tabban dukan da aka yi min. Tun daga wannan ranar kuma ban sake yin mafarki da kowa ba bare a mutu, abinda ni ke son sani shi ne ya ya aka yi ake mutuwa a kan idona kuma a ce ni aka gani?

Shin wacece me yin kisan a zuwan ni ce? Na san amsar tana wurin Hajiya, sai dai ba yanzu zan iske Hajiya ba sai na biyo ta kan Bashir Bangis na xauki fansar abin da ya yi min kafin in gurfana ga Hajiya da son jin yadda aka yi ta haihuwa a ragaya.

Wannan shi ne labarina da silar haxuwarmu a gidan yarin qiri-qiri

, da kuma irin izayar xa namiji a kaina. Shin wace irin fansa ku ke son in xauka a kan Bashir Bangis? Anya ko duk fansar da zan xauka zata biya ni abinda ya yi min..?”

To bari mu saurari manyan mata a kan shawarar da za su ba wa Beeba, koda yake kuma masu karatu ku taya Beeba laluben irin fansar da zata xauka a kan Bashir Bangis, kun dai ji irin uqubar da ta xanxana kuma wai nan ita ce wadda namijin ya yi wa abu me sauqi.

To mu bi manyan mata kashi na uku don jin Deena da labarinta, wanda ya fi na Beeba jumurxa da takaicin xa namiji, wanda ta ce ya yi mata sanadin uwa da uba.

Lallai nima ‘Yar Gidan Iko na matsu in ji labarin Deena da kuma Rose me abin mamaki. Shin za su yi nasarar qarar da mazan da suke faxa ko ko dai ya ya abin ya ke?

Ku biyo ni a cikin littafin ‘MANYAN MATA’ kashi na uku don jin yadda badaqalar zata kaya, amma kafin nan kuma masu karatu kuna da gudummawar da za ku bada ta hanyar taya Beeba xaukar fansa.

Kun dai ji irin abin da Bashir Bangis ya yi mata, to idan ku ne me za ku yi ku huce haushinku? Turo da saqon kar ta kwana a kan lambar: 08035191669, sai na ji daga gare ku kafin mu ji Deena da nata namijin wanda ya ce wa Bashir Bangis bai iya yaudara ba, to ko ita Rose me zata ce? Mu dai haxe a littafin ‘MANYAN MATA’ kashi na uku don jin yadda Manyan Mata suke yin rayuwarsu da sharafinsu.

Taku a kodayaushe, HADIZA BARAU GIDAN IKO, ‘Yar Gidan Iko ke cewa mu zamo lafiya, Qadarallahu Li qa’ana. Alherin Allah Ya tabbata a gare mu.

Ma’assalam!

Kaxan Daga Littafin

DA SAURAN KUKA…



W

ai ke Nazifa wace irin yarinya ce da ba ta da kishi? A ce kina aure a gidan Likita Jalal a ce ba kiyi tunanin in mallaki mota ba?



Ta dube ta “Haba Mama, motar da ke gida fa? Kuma duka yaushe ku ka dawo daga umara? Kuxin nan fa Jalal ba haqo su yake yi ba…”

“Ke da Allah dakata Nazifa! Kin manta da ni nayi ruwa nayi tsaki har ki ka auri Jalal? To ki bini sau-da-qafa, matuqar kina son zaman aure a gidan Jalal. Don haka ki faxa mishi ya siya min mota

Final

ko

Prado

ko

Anaconder

a cikin su ni ke so ya siya min…”

“Wallahi Mama in dai niz an ce ya siya miki mota to ba zan ce ba, saboda naga abin ba na qare ba ne. Ko shi Jalal xin bai hau irin waxannan motocin da ki ke so ya siya miki xaya daga ciki ba.” Ta gyaxa kanta “Da kyau! Ni ki ke faxa wa wannan maganar don ubanki? To albishirinki ce min goro, ko a nan aka tsaya ni ce da riba tunda ga ki da cikin Jalal, abin da za ki haifa shi zai gaje dukiyar

Jalal.

Don haka a yau ba gobe ba zan miqa sunan Jalal a inda za a zuqe jinin jikinshi sai ki shirya tarar gawarshi…”

“Ni kuma na rantse da Allah Mama tunda a kan cikina ki ka xora mugun qudirinki to nima a yau zan je asibiti a kwakware cikin a zubar! Idan ni na rasa Jalal

ke ma za ki rasa dukiyar da zai bari kafin in fito in fallasa ke ce ki ka kashe Jalal ga mahaifiyar Jalal da ma duniya gaba xaya.”

Mama ta miqe “To mu zuba ni da ke shege ka fasa. Na kula Nazifa ba zamu tava wanyewa da ke lafiya ba sai na biyo miki ta bayan gida, ina me tabbatar miki da yau xin nan Jalal ba zai qara kwana guda xaya

tal a duniya ba, idan hakan bata tabbata ba ki ce ni xin shegiya ce ga uwata da ubana.”

Ta fice a fusace, Nazifa ta durqushe a gun tana kuka saboda sanin da tayi wa Mama ba ta da imani, kuma a faxace a cika ce…

‘DA SAURAN KUKA’ littafi ne da ya samu ingancin rubutu wanda marubuciyar ta kawo sabon salon haxa xiya da uwa qasaitacciyar rigima. Ku dai biyo ‘Yar gidan Iko a cikin littafin ‘DA SAURAN KUKA’. Lallai da jin sunan ma ka san da akwai jumurxa me wahalar warwarewa.

Taku a koda yaushe, Hadiza Barau Gidan Iko ke ce wa mu tabbata a cikin alkhairi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login