Showing 15001 words to 18000 words out of 35284 words

Chapter 6 - MANYAN MATA BOOK 2 BY HADIZA BARAU GIDAN IKO.docx

bar ba shi koko idan ma madarar ta qare a sanar da ni.

Ta karva a sheqe, ni fa bana son kilbibi kin ji ko? Zan wanke qafata in je gidan ki karvar kuxin madara? Ai ba kiyi wannan isar ba tukuna

. In je gidanki kiji daxin qala min sata.”

Ni dai ban tanka mata ba, na fito inda naji Yusuf ya fasa kuka tamkar ya san na bar shi. Haka na dawo gida raina babu daxi, musamman idan na hango Amaka da Meri a cikin kayan Innata.

Na tashi na shiga kicin na haxa tuwon shinkafa da miyar xanyar kuvewa saboda Zainal na ce min yana so. Na gama girkin na shiga banxaki nayi wanka na fito nayi sallar Magariba na jira Isha’i kafin na soma shafe jikina da mayukan da Zainal Abidin ya tara min.

Ina cikin shafar na jiyo qarar mashin xin (

Vespa

) xin shi

ya shigo in da na taso da sauri na tarbe shi. Ya miqo min ledar hannunshi na karva, ya biyo ni har falon inda na soma kwance mishi takalmin qafarshi da safa.

Ya zuba min ido na xago naga yana kallona, nayi murmushi, “Na sauya maka ko?”

Ya lumshe idonshi kafin ya ce, “Ai nasan sauyin ko na meye.” “Na meye to?” Na tambaye shi.

Ya rungume ni yana shaqar qamshin jikina, ya soma shafa cikina. “Sauyin ai ba zai wuce na

Baby

ba, ko ba haka ba ne?” Sai a lokacin na tuna na daxe ban ga baqon watana ba. na kawar da maganar.

“Ruwa fa na jiranka idan ka fito kuma ka kintsa zamu je gidan Hajiya mu gaisheta (mahaifiyarshi).”

Ya ce, “To babu damuwa.” Ya fito wanka yana tsane sumarshi da tawul, inda na taya shi shiryawa ya ci abincin yana zuba santi. Ni dai ina ta kallonshi ina godewa Allah da ya azurta ni da kyakkyawan miji, domin ko Zainal Abidin kyakkyawa ne na qarshe.

Fari ne tas me gi

rare da sumar kai me tsari, idanuwanshi ma su sanyin kallo, sai dogon hancinshi me tsini da faffaxan qirji da qwanji da kuma suffar mazantaka.

Na lumshe idona ina qara godewa Allah a fili da baxini, sai ji nayi ya riqo hannuna ya matsa. Na buxe idona. “Ya ya dai?” Ya ce da ni “Babu komai, kai na jira ka gama.” Ya ce, “To ai na gama, na zaci bacci ki ke ji in ce me ki ke nufi da yin bacci?”

Duk da na gane manufarshi sai na ce, “Kamar ka san na gaji yau da mun dawo zan vingire.” Ya harare ni “To sai in ga in da za ki baccin.” Muka fita ya tada mashin xinsa na haye muka nufi gidansu.

Hajiyarshi tayi murna sosai da tuwon da na kai mata, ta yi ta saka min albarka. A kullum naje gare ta nasiha ce da nuni ga rayuwa, sai naji ko zan rasa kowa to Mahaifiyar Zainal Abidin ta maye min gurbin Innata

da na rasa.

Sai goma muka yi mata sallama muka nufo gida. A daidai qofar gidanmu muka iske wata qatuwar motar Maigidan da muke maqwabtaka da shi yana sauke

wasu kwalaye, inda maigadin ke jida yana shigarwa cikin gidan.

Da sauri Zainal ya

kafe mashin xin shi ya qarasa gare shi fuskarshi da murmushi. Alhaji ya juyo shima fuskar tashi da murmushi.

“Wa zan gani kamar Zainal Abidin?”

“Alhaji ni ne da kaina.” In ji Zainal. Ya miqo mishi hannu amma shi Zainal xin sai ya rusuna yana gaishe shi. suka gaisa inda na gane da akwai tsohuwar sanayya a tsakaninsu, don haka nima da ke gefe na gaishe shi da “Ina yini?”

Ya juyo yana damqe da hannun Zainal Abidin ya amsa yana me zuba min ido.

“A’a, Zainal kar dai ka ce min kayi iyali?”

“Qwarai kuwa Alhaji, ga Habiba nan matata ce, ko in ce Amarya.” Ya sake zuba min ido har na soma tsarguwa da irin kallon da yake min.

“Wai tsaya ma, ko kai ne ka kama gidannan ne haya?” Ya faxa yana nuna gidan namu. “Eh, nan ne qwarai ko?”

“Toh! Haba kwana ki fa Yusra ta nuna min qunshi ta ce Anti Amarya tayi mata (yarinyar da ta yi wa qunshi).”

“Haka ne.” In ji Zainal Abidin.

“To madallah, nima kaga gidana nan bayan na baro Dutsen Safe

Lowcost,

da fatan zamu yi zumunci.”

Da haka suka yi sallama inda Alhaji ya dumbuzo kuxi ya miqo min. “To Amarya ga wannan ko?” Zan yi

gardama Zainal ya qifta min ido na karva ina godiya, suka yi wa juna sai da safe muka shiga gida, inda Zainal ya ke faxa min tsohon ubangidanshi ne inda ya yi aikin tuqin mota a gidanshi, wato

Driving

kafin ya samu aiki.

Ya san shi ne a Dutsen Safe

Low cost

sai gashi yanzu sun zamo maqwabta. Allah Sarki, abin da na ce kenan don ni dai Allah ya sani bai kwanta min ba musamman idan aka cika kallona sai in ji na tsani mutum.

Na zube mishi kuxin da ya bani waxanda sun haura dubu goma. Ya dubi kuxin ya ce, “A’a, xauki abinki.”

“To ni me zan yi da su? Ka riqe kawai ga alama ba ka jin tsakiyar watan nan.” Na soke kuxin a cikin aljihunshi.

Washegari na tashi da yin kitso, kusan mutum biyar sai ga Yusra ‘yar gidan maqwabcinmu wanda Zainal ya faxa min sunanshi Alhaji Bashir Bangis.

Na dubeta “Ya ya aka yi ne Yusra?” Ta ce, “Dadynmu ne ya ce mu zo kiyi mana kitso da qunshi.” Na ce, “To kira su Zainab xin da Humaira (‘yan uwanta).” Ta tafi ta kira su nayi musu.

Sai washegari sai ga Yusra da ambulan

ta ce in ji Dadynsu

. Na buxe inda nayi arba da kuxi ‘yan xari biyar-biyar rafa guda babu hamsin kenan.

Tsoro ya kama ni, nayi saurin maidawa Yusra kuxin “Ki ce na ce a bar su kin ji Yusra?” Ta karva ta ce

“To.” Na bita da kallo sai ga ta sun dawo da ita da Humaira, wai Dadynsu ya



ce su maido min.

Na karva da nufin idan Zainal Abidin ya dawo in shiga in maida musu kuxinsu saboda su duka yara ne da ba su wuce shekaru biyar-biyar ba.

Zainal ya dawo na faxa mishi ya yi murmushi ya ce, “Haka yake da kyauta. Amma kije ki

ji.” Na shiga gidan bayan nayi sallama.

Matar gidan fara ce me matsakaicin jiki ta amsa sallamar tana murmushi. “Shigo mana.” Ta ce da ni, in da Yusra ta fito tana faxin. “Yauwa Momi ga Anti Beeba me qunshi.” Matar ta faxaxa murmushinta.

“A’a’ah, maraba da Anti Beeba.” Nayi dariya muka gaisa ta xora da yi min godiyar qunshin da na yi wa Yusra. Na miqa mata embulan xin inda na ce a bar kuxin.

Ta ce, “Yo don me Habiba?”

“Sun yi yawa ne Hajiya.”

“A’a basu yi yawa ba, ki riqe abinki ke dai kiyi ta gyara mana ‘yan

kids

xinmu abin da yafi haka ma za ki samu.”

Duk yadda na so ta karvi kuxin ta qi, dole na dawo na faxawa Zainal yadda muka yi. Zainal Abidin ya kalle ni yana dariya.

“Ai dama na faxa miki haka yake da kyauta, kaxan kenan da aikin shi.” Haka na aje wa Zainal kuxin a gabanshi “To ni meye zan yi da su…bare kuma ni ka manta da alqawarin da kayi min?”

“Na me fa?” Ya tambaya yana kallona.

“Na kai xin za ka zame min uwa da uba? Ban manta ba…ka riqe su a matsayinka na uba a gare ni har sai ka san yadda za ka yi da su. Dama akwai kuxin da ni ke tarawa na kitso da qunshi bari in kwaso maka su.”

Na miqe da shirin xauko kuxin, ya riqo ni “Bar su Beeba, waxannan ma aje su zan

amshe su.” Na dube shi… “Kar ki ce komai.” Nayi shiru. Ya riqo hannuna yana zaunar da ni a kan cinyarshi.

Ya soma shafa cikina “Kina jin motsi kuwa?” Na xaga kaina alamar eh, ya ce “To ni ban ga cikin yana girma ba.”

“To duka yaushe ya samu da har zai girma? Wata fa huxu ne duka-duka.” Ya kai bakinshi a nawa yana

kissing

.

Lokaci ya ja sosai inda aka jera wata uku ba a biya Zainal albashi ba, ga Maigidan da muke haya ya matsa da son a ba shi kuxin haya kasancewar wata shida-shida yake amsar kuxin maimakon sai shekara.

Na miqo mishi kuxin nan da ya ce in aje. Ya dube ni “Me za’ayi da su?” Na ce, “Ka biya ma su gidannan kuxinsu su daina yi mana zarya.”

“A’a ba haka za’ayi ba, kayan haihuwar ki zan siya in yaso shi Maigidan sai in haxa mishi na shekara idan na karvi albashina. Sauran kuxi muyi hidimar haihuwa.”

Ni kaina sai na yarda da tunaninshi. Bisa dole muka ture Maigida a gefe xaya, ashe ba shi da mutunci. Da

dai ya yi zuwa biyu Zainal ya ba shi haquri a kan ya bari a yi albashi bai sake zuwa ba har mun yi zaton ya haqura ashe ba haqura ya yi ba tsiya yake son qulla mana.

Shiru ba a biya Zainal albashi ba har ta kai yana son aje mashin xin shi saboda babu kuxin da za a zuba mai. Na ce masa, “A’a kar ka aje mashin xin ka, kuxin da za ka riqa biyan acava ai ba za su yi maka sauqi ba, kaga kuxin da na ce maka na tara na qunshi kwashe su kawai kayi hidimarka.”

Ya zuba min ido kafin ya ce

, “Me zan ce miki Beeba?” Na saqalo wuyanshi ina yi mishi raxa “Ce min

I love you



kawai ya ishe ni.” Ya rungume ni yana min

kiss

tare da furta min daddaxar kalmar da na buqata daga gare shi.



I love you! I love you forever

, na gode sosai My Beeba.” Da kyar muka rabu ganin hadari na shirin zubar da ruwa. Fitar Zainal Abidin babu jimawa naji mutum a saman rufin xakina.

Da sauri na sako hijabi na fito, inda na iske Maigidanmu a tsaye yana bada umarnin a cire rufin xakin. Na soma ba shi haquri.

“Kayi haquri Alhaji, wallahi da an yi albashi zamu biya, yanzu ma

ba a biya shi ba ne shi yasa bai baka ba, don Allah ka qara haquri…”

“Ke kar ki cika min kunne da zancen banza, ba ku san babu yadda ba a yi da ni in siyar da gidannan naqi ba? sai in ba da haya har tsayin wata takwas a kasa

biyana? To idan nasa aka cire kwanon ai kwa nemi wani matsugunnin.”

Ina cikin ba shi haquri inda mai cire kwano ke jiran umarni sai ga Alhaji Bashir Bangis maqwabcinmu. Ya fito daga motarshi me qololuwar daraja ta Kamfanin Marsandi.

“A’a, Xan Garba ya aka yi ne?”

“Yadda aka yi kenan. Na gaji da gafara Sa ban ga qaho ba, kullum sai a fake da ba ayi albashi ba, to ni in za a mutu ba ayi albashi ba babu abin da zai dame ni.”

“A’a ba haka za a yi ba, yanzu nawa ne? zan biya.” In ji Alhaji Bashir Bangis.

“To Alhamdulillahi, kai Dauda sauko Allah ya kure su!” Ina gefe ina kallon yadda ake qera rashin mutunci,

“Ni

in haka haya take ma anya zan kuma

ba da haya? Kai ni zan siyar da gidan in huta.” In ji shi Maigida wato Xan Garba kamar yadda naji Alhaji Bashir Bangis ya kira shi.

Alhaji Bashir Bangis ya ce, “Ai sai da na ce ka siyar min ka qi, yanzu in za ka siyar ai sai in siya…” “In ka siya miliyan biyar na saida maka, idan kuma ba ka siya ba bar min abuna.” In ji Xan Garba.

Alhaji Bashir Bangis ya dube shi jin yadda ya tsuga kuxi, gidan da bai wuce milyan biyu ba amma sai ya ce “Na siya.” Suka shiga mota idon Alhaji Bashir Bangis a kaina, inda ya yi min alamar in koma gida, na juya da sauri na koma gida.

Da dare

sai ga Alhaji Bashir da kanshi ya shigo inda na gaishe shi na koma xaki na bar shi tare da Zainal, inda yake mishi bayanin ya siyi gidan da muke wurin Xan Garba, don haka ya bar mu muyi ta zama har Allah ya hore mana namu.

Godiya sosai Zainal xin ya yi mishi, inda naji yana mishi tayin abincin da na jera mishi. A tare suka ci abincin har dai suka yi sallama. Ya faxa min yadda suka yi na taya shi godiyar alherin da aka yi mana.

Har gida naje na yi wa Maman Yusra godiyar abin da Maigidanta ya yi mana, muka soma abin arziki inda Zainal Abidin ke matuqar girmama Alh. Bashir Bangis, nima ina girmama shi da matarshi Hajiya Tamadina.

Sai ya zamo yana saka Zainal wasu ayyuka da dai sauransu, suka koma dai yaro da ubangida, inda har gida Alh. Bashir ke shigowa su tauna wasu al’amura shi da Zainal Abidin.

Ana haka Allah ya sauke ni lafiya na haifo xana me kama da Zainal tar-tar tamkar ya yi kaki. Mun yi murna ba kaxan ba, bare Zainal da ya yi hawayen murna.

Hidima sosai Alhaji Bashir ya yi mana shi da matarshi Hajiya Tamadina, har aka yi suna yaro ya amsa sunan Umar Faruq

.

A nan fa n

a soma fuskantar qalubale inda Alhaji Bashir

ya soma yi mana sintiri a gida da sunan ya zo ganin Umar

, a cewarshi wai Umar xin ya shiga ranshi.

Daxi ya kama Zainal, jin ana taya shi son xanshi, inda ni kuma har ga Allah hakan bai yi min daxi ba. Ba

don komai ba sai don matuqar Alhajin zai shigo gidanmu to har ya bar gidan idonshi a kaina, abinda na tsana kenan a rayuwa.

Sai dai ba ni da bakin faxar wani abu bare in yi tsegumi saboda nasan Zainal na matuqar girmama Alhaji Bashir xin, don haka na zuba ido idan Allah yasa shi Zainal xin ya ankara to shi kenan, idan kuma bai ankara ba sai in riqa shiga xaki ina ba su wuri.

Haka ko aka yi, in dai ya shigo to da mun gaisa zan voye kaina a xaki, amma duk da haka ba na tsira sai ya san yadda ya yi ya qirqiri abinda Zainal zai kira ni in fito in ba su wani abun.

A kan haka na miqe ina son yi wa tufkar hanci amma ina tsoron Zainal ya ce na cika zargi. Kayan sawa da na wasa kuwa ya cika wa Umar gida da su, abin da ba ya burge ni inda Zainal ke matuqar jin daxin hakan.

Abin ya yi ta cin raina amma babu hanyar da zan fallasar. Ana cikin haka aka yi wa Zainal Abidin canjin wurin aiki zuwa (

Headquarter

) ta qaramar Hukumar Dutsin-ma, inda ya zamo baya da lokacin zama gida sosai matuqar ba

morning

(aikin safe) yake ba.

Idan kuma yana

night

(aikin dare) to wani lokacin ma sai da safe zan gan shi. Da safe na shirya don zuwa gida in dubo Yusuf. Na isa gida inda na iske

Yusuf a kan fo yana zaune, a inda yake rana ta iske shi sai gyangyaxi yake babu ko riga a jikinshi, ga sanyi yana

kaxa shi yana kyarma, inda na hango Amaka kwance tana barcin safenta.

Tausayinshi ya kama ni, na duqa ina shafa fuskarshi da ke da layi-layin

hawaye alamar ya yi kukanshi ya gaji har barcin ya xauke shi a kan fo.

Na xauke shi na wanke mishi kashin na sava shi a kafaxa na fice daga gidan ba tare da Amaka ta farka ba. Na koma gida na xora ruwan zafi nayi mishi wanka, inda na gane ba ya samun kulawar da ta dace.

Na shafe shi da mai yana ta min gwalonton yarinta, na shi

Tea

me kauri sai ya vingire a qafata yana barci. Bayan ya gama sha na zuba mishi ido a raina ina cewa

“Ni ba marainiya ba ce Yusuf shi ne maraya, me yiwuwa Allah ya sauqaqa mishi maraicin ne ta hanyar kawo mishi na bayan ya xauke mishi gatanshi (uwa)

.”

Sai naji duk da nasihar Innata ta cewa in bar Yusuf Allah shi ke da rai da rayuwa, to amma idan na bar shi a hannun Amaka ban zalunce shi ba a matsayina na gatan da ya rage mishi a duniya? Zan jira zuwan Zainal, idan ya yarda da zaman Yusuf gare ni to zan riqe shi hannuna, idan kuma bai yarda ba to dole zan mayar da shi wurin Amaka, in kuma yarda da rai da rayuwa duka na Allah ne.

Haka Yusuf ya wuni cikin walwala da jin daxi kasancewar mun yi sabo me yawa, sai hawa jikina yake yi na wasanshi. Da dare Zainal ya dawo ya iske Yusuf ya haxe su duka shi da Umar ya xauke su yana musu

wasa.

“Yaushe Yusuf ya zo ne Beeba?” Ya tambaye ni, na kwashe komai na faxa mishi a kan yadda naje gida na same shi.

“To me zai hana ki tambayo Baba idan ya yarda sai mu riqe shi kawai ko?” Hawaye ya ciko idona. Ya dube ni kafin ya dire Umar da Yusuf ya rungume ni. A kunne yake raxa min “Me yasa ki kuka

my heart

?”

Na kwantar da kaina a qirjinshi. “Ina kuka ne a kan yadda ka ke girmama duk wani abu da ya share ni. Nayi kuka a lokacin da na rasa babban bangon jinginata (uwa), ashe kai ne za ka zamo matallafi a gare ni. To me zan yi maka in biya ka a rayuwa?”

“Kiyi ta sona kina min wannan abin…”

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login