Showing 6001 words to 9000 words out of 35284 words

Chapter 3 - MANYAN MATA BOOK 2 BY HADIZA BARAU GIDAN IKO.docx

ma ‘Yansanda mummunar fahimta

, ba duka suke haka ba.”

Na sake qunduma musu ashar. “Wallahi haka suke Malam, kai dai Allah yasa kar ka haxu da sharrin ‘Yansanda.” Yayi saurin amsawa da “Amin, na gode.”

Ya tsaida Mashin ya haye ya yi tafiyarshi. Da haka na saida abinci na taho gida babu kuxin

kirki saboda nima idan naso gwadawa Amaka qeta sai in yi ta tuza abincin arha.

Idan ka ce na hamsin sai in zuba maka na xari a matsayin hamsin xin. Ta qirga kuxin taga ba su da yawa

, ta dube ni tana huci.

“Uban me ya ci sauran?” Na wurgo mata hararar da ta bani aro “To ni dai ko ruwa ban siya na sha

a kuxin ki ba bare ka ce ko na kashe miki kuxi ni fa na gaji da tallar nan wallahi ban da Inna ta ce in riqa yi Allah da bana zuwa.” Na faxa ina shirin zucewa.

Tayi saurin finciko ni. To ko ita uwar taki na azawa talla dole taje bare ke kayan banzan da bai kai ga na wofi ba saboda gidana ta iske ni ta kuma aurar min miji bare tayi bugun gaban zaman aure

.

Ban ankara ba ta tausa min fuska a cikin qatuwar robar me xauke da ruwa me yawa, na ko shaqi ruwan ta hancina na kuma kasa maida numfashi.

Wata irin azaba ta ziyarci qirjina. Na kasa xaga fuskata daga cikin ruwan saboda da qarfi Amaka ta danna kaina sai da ta saki don kanta inda na zube ina maida numfashi

da kyar na iya rarrafawa xaki ban ko faxawa

Innata cikin ciwo wanda na tabbatar naquda take, sai haxa gumi take tana cije baki.

Da gudu na fito ina haki na faxa xakin Amaka. Ta dube ni ta ce, “Ke lafiya za ki faxo min xaki kamar xakin uwarki?” Na ce, “Inna ce ba ta da lafiya Amaka.”

Ta ce, “To uban me zan yi mata? lokacin da na hana ta mijin saboda irin haka ai kewayewa tayi taje

ya quga mata ciki ita uwar son miji ko?”

Idona ya kawo hawaye, na juya na fito inda Amaka ta kunna Rediyonta ta saka kaset xin Gambu mai waqar Varayi, ta kuma qure qara. Na durqushe a gaban Innata ina hawaye, ganin yadda ta ke shan wuya. “Me zan yi miki Inna?” Na tambaye ta.

“Kirawo min Amaka.” Ta ce da ni. Na faxa mata yadda muka yi. Ta ce, “To je ki gidan Kawu ki kira min Tasallah.” Da sauri na fice kiran Tasallah na isar da saqon Innata. Sai dai me

? Tasallah cewa tayi ta xora sanwar alalarta don haka ko zata zo sai ta siyar.

Da sauri na rattaba mata Innar fa haihuwa zata yi. Ta dube ni bayan ta xaure fuska.

“To me zan yi mata? na isa in sa ta haihuwar ne ba sai Allah ya yi ba? idan zata jira in siyar da sana’ata to, idan kuma sauri take sai ta nemi wata.”

Da dai na gane ba zata zo xin ba sai na juyo inda na rasa abin da Innata yi musu. Ina tafe ina sharar hawaye har na iso gida da fatan Allah ya yanke mata wahala.

Na shiga xakin inda na iske Amaka bisa cikin Innata tayi zaune xare-xare! Wai da sunan taimako. Na bita da kallo in da ta dako min tsawar in fita. Da sauri na fito ina kuka.

Tausayin Innata ya kama ni, wai me ta yi wa mutane da suke nuna mata mugun hali? Innata me kirki ce, me kuma alheri, amma me yasa mutane basa yi mata alherin da take yi musu?

Ana haka naga Amaka ta fito daga xakin. Ta dube ni ta ce, “Je ta haihu sai ki kwashe qazantar da ta zubar don ni ba zan tava komai ba tunda ta ji ta gani.” Na shiga xakin da sauri. Ban bi ta kan Amaka ba.

Innata ta sha wuya a raina, na ce

ko zaman Amaka akan cikin ya isa ta sha wuta. Na kamo ta

ina hawaye na zaunar da ita a gefen katifa, duk da ina qyamar abinda ke qasa.

Haka na kwashe shi na zubar inda na dawo kan xiyar da Inna ta haifa, sai dai bata motsi ko kaxan. Innata ta buxe baki da kyar ta ce min ta rasu Beeba bata zo da rai ba!”

Naji dam! Gabana ya sara saboda Allah ya sani na qwallafa raina a kan cikin Innata saboda ina son

samun

‘yar uwa ko xan uwa. A take na ayyana wa raina zaman da Amaka tayi a kan cikin Inna ne ya kashe min ‘yar uwa.

Na dubi Innata “Ruwan zafi zan sa?” Ta kaxa kanta “A’a ai mabiya bata biyo ba.” Ban fahimci meye mabiya ba, don haka sai naja gefe ina sharar hawaye.

Amaka ta leqo “Ya ya ne?” Innata ta ce, mabiyar ce bata biya ba.” Taja tsaki “Ai Allah dai ya qara miki, gashi nan namiji ya quga miki ciki ya barki da jidali.”

Ta xebo garwashi ta watsa barkono ta lulluve Innata da abin rufa wai ta shaqi yajin barkonon, ai ko Innata tayi ta tari amma saboda rashin imani Amaka taqi buxeta sai da taji Innata ta daina motsi kafin ta buxe ta ta iske ta suma.

Ta sheqa mata ruwa ta farfaxo inda ta yi ta tari ba tsayawa, abin tausayi. Da dai Amaka ta tabbatar ta farko sai ta fice ta barta tana tari wanda na tabbatar Innata ta kamu da wani ciwon.

Kwana biyu mabiya bata biya ba, inda Allah ya jeho Baba muka nufi asibiti bayan an rufe jaririyar ‘yar uwata inda maqwabcinmu Malam Jigo ya kira wayar Babana ya sanar da shi, don haka a asibiti aka yi duk abinda ya dace har mabiyar ta faxi, inda kuma aka tabbatar da Innata ta kamu da cutar sarqewar numfashi sakamakon barkonon da ta shaqa.

Gaba xaya Innata ta rame ta fita hayyacinta, a wannan karon Babana bai wani tsaya ba ya koma

bakin aikinshi.

Na shiga da kulawa da Innata, saboda bata da qarfin jiki, ina yi mata iyakar abinda zan iya wanda tasan ba zan iya ba tana lallavawa tayi. Sai da ta kwana bakwai sannan Tasallah ta zo ta dubata.

Na dubi Tasallar da ciwon abin da tayi min wai sai yanzu ta zo ko ta ce wa Innar me? Da yake Innata me tsananin haquri ce sai bata nuna mata komai ba ta karve ta da girmamawa ta jajanta mata tare da fatan Allah ya bada na aikawa.

Da haka ta fice ina kwaxa mata harara. Innata ta dube ni “Kar ki sake harararta, uwata ce ban da kamar su duk abin da mutum zai yi kanshi ya yi wa.”

Na share hawayena na rasa abinda ki ka yi wa mutane Inna ke dai me kirki ce amma mutane basa yi miki kirki.” Ta share min hawaye “Bari kuka Mamana, duniyar nan fa ba zama ake din-din-din ba, naji daxi da ki ka gane ina yi wa mutane kirki matsalarsu ce idan ba su yi min kirki ba.

Ni dai Allah ya sani na sauke nauyinsu ke ma kiyi komi domin Allah kar ki dubi kirkinsu ko rashin kirkinsu. Ki dubi Allah kawai kin ji ko?” Na ce, “Eh naji.” Haka Inna ta yi ta jinyarta har Allah ya bata sauqi ta koma bakin sana’arta.

Ta soma samun ‘yan kuxinta, ni kuma

naci gaba da yi wa Amaka bauta tana gana min azaba.

Satin Baba biyu da tafiya ya zo gida, inda yazo da son Innata ta bashi haxin kai. Ta dube shi ta tuna mishi har yanzu bata ida warkewa ba, ya soma sababi wai ta

raina shi. ya yi faxanshi ya gama bata ce mishi komai ba.

Don haka ya fita yana masifa, bai ko qara kwana ba ya koma inda ya fito hakan yasa Amaka ta fito da qetarta ga Innata, inda ta ce Babana bai bar kuxi ba, Innata ba ta damu ba saboda tana kitso da qunshi, ni kuma idan na tafi tallah sai in ci

abin da ni ke so.

Wata huxu ya wuce, Babana bai zo ba, wai ya yi fushi abin da Innata tayi mishi sai da ya yi wata biyar cur kafin ya zo gida. Inda ya iske Innata cikin baqonta na wata.

Da ya nemi ta bashi haxin kai ta sanar da shi bata da tsarki, kawai sai ya hauta da bugu tamkar ya samu Jaka, sai da ya kumbura mata fuska inda Amaka ke ta qyalqyala dariya.

Cikin tsananin wahala ya bar Innata, na dawo na isko ta fuskarta a kumbure, da na nemi ba’asi bata faxa min ba inda na gano komai a bakin Amaka saboda habaicin da take sakarwa Innata.

Tunda Baba ya tafi mun daxe ba mu sake ganin shi ba, sai dai a zo a ce mana an gan shi a xakin karuwa a can kudu Tafa ko Ogyaro. Na xauki tallar abinci ba cikin daxin rai ba saboda ciwon cikin Innata.

Nayi zugum ina tunani inda aka fara siyen abinci abin da Bilkisu da Maijidda suka tsana kenan, in riga su siyarwa. Abin tsautsayi wurin in miqa abinci na tungule wa Bilkisu miya, ta wulwulo min ashar.

Na dubeta na dubi miyar da na zubar mata, “Wallahi tallahi sai kin biya ni miyata dubu da xari biyar na kashe mata.” Ta faxa tana son cin kwalar rigata. Na dubeta miyar da bata wuce xari bakwai ba ta ce wai dubu da xari biyar.

Na buge hannunta da ke son cin kwalata. “Da Allah sake ni da gangan zan zubar miki da miya? In ma da gangan ki ka yi wallahi ba zan yarda ba, sai kin biya ni.”

Rikici me tsanani ni da Bilkisu, inda Maijidda ta bata shawarar ta xauko min Xansanda. Ai ko Bilkisu ta xauko min Xansanda, inda jikina ya soma kyarma.

Ban tsinke da lamarin ba sai da naga wanda ya zo a matsayin Xansandar. Mutumin nan ne da na yi ta xurawa Xansanda ashar a gabanshi, wanda ya ce min ba duka ‘Yansanda ne ke yin abin da ni ke zato ba.

Idona ya kawo ruwa, ya dube ni yana murmushi wanda nasan na muguntar na zo hannunshi a kan ashar xin da na yi ta xura masu a gabanshi a she shima Xansanda ne.

Ya dube ni ya ce, “Ya ya aka yi ki ka zubar mata da miya?” Ya tambaye ni fuskarsa da murmushi. Sai naji kunya ta kama ni.

“Uhum?” Ya sake tambayata. Na ce, “Wallahi ba da gangan na zubar mata ba.” Na faxa kamar zan fasa kuka. Ya dubi Bilkisu “Kin ji ba da gangan ta yi miki varna ba, me zai hana kiyi mata haquri tunda tare ku ke zaune?”

“A’a wallahi ‘Yallavai sai ta biya ni, ta biya ni kawai.” Maijidda ta ce, “A kai ta bayan kanta har sai ta biya.” Ya ce, “A’a ba sai mun je

station

ba.” Inda naji fitsari na shirin kuvuce min saboda jin wai a kai ni bayan kanta.

Nayi maza na ce, “A’a don Allah kar a kai ni bayan kanta, tayi haquri zan biya ta da kaxan-kaxan…”

“A’a wallahi ban yarda ba, duka kuxina za a biya ni.” In ji Bilkisu

. Hawaye ya zubo min. Ya kaxa min kai alamar in bar kuka. Nayi saurin share hawayena.

Ya dubi Bilkisu “Ku sasanta kanku ta yadda ba sai mun je can ba, idan ba haka ba to…”

“Ni fa a biya ni kawai.” Cewar Bilkisu. Na dubi kuxin hannuna wanda ba su wuce xari huxu ba na miqa mishi.

“Ka ba ta waxannan zan cika mata idan na saida abincina.” Ya karvi kuxin ya miqawa Bilkisu amma ta ce ita fa ba za ta amsa ba in ba duka ba ne.

Ya dubi Bilkisu ya ce, “Na lura ko ba ki son ayi muku sulhu, ba tare ku ke ba?” Nayi saurin cewa “Tare muke.” Bilkisu dai ta kafe sai na biyata. Kawai sai saka hannu ya yi a aljihu ya xebo kuxi ya miqa wa Bilkisu kuxinta, ni kuma ya maido min xari huxuta.

“To gashi na biya mata shi kenan ko?” Bilkisu ta amsa. Na bishi da kallo ya yi tafiyarshi ba tare da ya saurari godiyar da nike mishi ba.

Na zabga tagumi ina tunanin karamcin wannan Xansanda, ko a mafarki ba zan tava yarda akwai

Xansanda me karamcinshi ba. Kunya ta lulluve ni da na tuno

zagin tsamar naman da nayi wa ‘Yansanda, ashe sara nayi da mutum a sama.

Anya ko zan iya haxa ido da wannan farin Xansanda? Kai ba zan iya ba. A nan na gane yadda wannan matashi yake fari tas kuma kyakkyawa haka zuciyarshi take da haske da kyawu, tunda ni dai ban tava ganin farin Xansanda ba.

Haka nayi ta saqar zuci

, in da na tabbatar da lallai ba duka aka taru aka zama xaya ba, shi wake xaya shi ke vata gari. Haka na tattara komai na watsar na kuma yi alqawarin ba zan sake haxa ‘Yansanda in antaka musu ashar ba, ko da zan yi xin to zan cire farin Xansanda, sunan da na qala mishi kenan.

Tsawon lokaci har ma na manta da shi kawai na fito da niyyar qetara titi kaxan ya rage Mashin xin (

Vespa)

ta banke ni, don har qafata ta taka kaxan.

Mai Mashin xin ya sauko yana duba qafar tawa, “Sannu ba ki ji ciwo ba?” Nayi murmushi na ce, “A’a ban ji ciwo ba.” Ya duba qafar tawa da ta xan koje ya ce, “Zo mu je asibiti a duba miki ita.”

“A’a kar ka damu babu komai na yafe maka.” Ya dube ni “To na gode, amma muje a duba ta saboda kar gaba tayi miki tsami.”

Bisa tilas na hau (

Vespa

) xin tashi muka je asibiti aka duba muka dawo, har gida ya aje ni. Tun daga wannan rana yake kulawa da ni kulawar da ta rikixe zuwa soyayya

ta gaskiya

Sai ga ni da so da qaunar Xansanda, abin da ban tava zato ba ko a mafarki. Soyayya me tsafta da nuna tsantsar tausayawa, na manta ban faxa muku sunan farin Xansanda ba, Zainal Abidin kamar yadda sunanshi yake me wuyar samuwa a cikin al’umma.

Haka kyawawan xabi’unshi suke wuyar samu a cikin al’umma. Bayan na dawo daga tallar abinci na iske Baba ya zo, nayi mishi sannu da zuwa ya amsa yana tambayata ina zuwa Makaranta? Na amsa mishi da “Eh, ina zuwa.”

Ya xebo kuxi ya bani a kan in sayi wani abu saboda bai zo da komai ba. A wannan karon sai da ya yi sati xaya saboda samun kan Innata da ya yi. Bayan ya koma ne da sati biyu watan Azumin Ramadan me albarka ya tsaya.

Washegari muka tashi da Azumi, inda na huta da fita siyar da abinci, a kullum ina gida ina taya Innata aiki, in da a kullum take mana nau’o’in girke-girke saboda ta iya girke-girke wanda nima na koya daga gareta.

Azumi na da kwana huxu na samu saqon Zainal Abidin, qwai ne kirat biyar da madara da

Bourn

vita

, kus-kus, da taliya da kayan kamun Azumi.

Na dubi Innata da ke ta murmushi kunya ta kama ni

.

Inna ta ce, “Oh ni Fatima Bintu! Yau ni ce da suruki?



Da sauri na baro xakin. Wannan kaya sun tsone idon Amaka, tana ta faxar maganganu ita da

Aminiyarta Meri, ba mu dai kula su ba muka yi ta sha’anin gabanmu ni da Inna.

Azumi na da

kwana

ashirin da biyar wani saqon na Zainal Abidin ya sake

r

iskata, atamfa ce me shegen kyau ‘yar yayi da tartsetsan les

,

da Jaka da takalmi masu kyau a zuwan kayan sallah.

Nayi farin ciki ba xan kaxan ba, Inna ma taji daxin karamcin Zainal Abidin, inda ni kuma Inna ta bani kuxi na siyo kayan haxin cak da samosa na yi wa Zainal Abidin barka da salla

h. Sai ga shi ya zo gaishe da I

nnata har ya yi mata alheri na kuxi har dubu biyar.

Taji daxi sosai

, ta kuma yaba da natsuwar Zainal Abidin, inda tayi mana fatan alheri. Baba da ya zo Inna ta faxa mishi abinda Zainal Abidin ya yi min na hidima a sallah, Baba ya yi fatan alheri.

A wannan karon ma ba su rabu lafiya da Innata ba, sai da ya bata kashi har ta riqa zubar jini a hanci. A xan taqi kaxan na fahimci Innata ciki gare ta, inda nayi ta murnar samun ‘yar’uwa ko xan uwa, inda kuma Amaka tamkar zata yi hauka ganin Innata da ciki.

Inda kuma a gefe xaya Zainal Abidin ya roqi alfarmar in daina fita siyar da abinci, na kuma amsa mishi da angama, duk da ina tsoron yadda

zamu kwashe da Amaka.

Sai dai Innata ta ce tunda Zainal Abidin ba ya so ya zama dole in bari, saboda ita ma tunda na kai munzalin mace ta sosai take son a bar tallar. Sai dai me? Amaka ta ce bata san zancen ba, talla yanzu na soma.

Na dubi Amaka na ce, “Kiyi haquri Amaka in dai talla ta fita waje ce ba zan yi ba tunda Inna bata so, ko dama can ita ce ta tilasta ni yanzu kuma tunda bata so ba zan yi ba.

Sanin da Amaka tayi yanzu ba da ba ce da zata hau ni da duka yasa bisa tilas ta haqura ta soma sana’o’in cikin gida, ni kuma na samu ‘yanci.

BABI NA GOMA SHA XAYA

Z

ainal Abidin ya fito da son a tsaida ranar aurenmu, aka yi sa’a Baba ya zo. Ya kira ‘yan’uwanshi aka tsaida ranar aurenmu wata huxu masu zuwa.

Tuni Innata ta soma shirin aurena, inda cikinta ya turo sosai. Innata jaruma ce me tattali, nayi mamakin inda take samun kuxin da ta ke yi min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login