Showing 9001 words to 12000 words out of 35284 words

Chapter 4 - MANYAN MATA BOOK 2 BY HADIZA BARAU GIDAN IKO.docx

siyayya, a ganina kamar sana’ar kitso da qunshi kawai ba za ta tara mata abinda ta tara ba.

Ina jin tausayinta qwara

i

a raina, ganin bata da buri sai ni da abinda take shirin haifa, wanda ta ce mu kaxai gareta.

Ina mamakin dangin Innata a kan rashin riqo da zumunci da yin watsi da zumunci in ba jari hujja ba. Koda yake ita Innata cinye mata gadon aka yi, ba a son ta ce tana son wani abu a cikin dukiyar da ta gada.

Da sun fahimce ta

,

ita bata da buri a kan gadon nata irin ayi mata riqo irin na zumunci, a kuma nuna mata qauna har ta manta da maraicin da ya same ta.

Da ta samu hakan to babu ko shakka ba za ta tava waiwayar wani abu wai shi gado ba. koda yake ko a yanzun ba ta jin zata buxe baki ta ce tana son wani abu a cikin abin da ta gada, tunda Allah yayi mata rufin asiri a xakin miji.

Sati xaya da saka ranar aurena da Zainal Abidin, Innata ta tashi da ciwon naquda. A yadda na so kar

Amaka ta sani don kar tayi min sanadin xan uwan da zan samu, amma ban san yadda

aka yi Amaka ta san Inna na naquda ba.

Ta faxa xakin da sauri inda kan yaro ya soma fitowa, inda kuma Amaka taso gwadawa Innata mugunta wadda zata yi mata baqin sanadi. Ai ko Amaka ta fizgo yaron da qarfin tsiya, inda kuma tayi nasarar nakasa Innata har ta kamu da ciwon yoyon fitsari.

Lokacin da Amaka ta fizgo yaron Innata sumewa tayi saboda azaba da tashin hankali. Ta farko cikin wani irin raxaxi da zugi kafin jini ya valle mata tamkar an yanka Saniya, inda kuma Amaka ta barta ta koma bakin aikinta.

Na samu Innata cikin tsananin wahala ga kuma jini na malala, ga xan jariri yana ta tsala kuka. Na rasa abu xaya da zan yi tsakanin mahaifiyata da kuma xan uwan da na samu.

Mahaifiyata bata iya ko xaga yatsanta saboda jigata, shi kuma jaririn ban san yadda zan yi da shi ba. Ina cikin wannan hali can sai dabara ta faxo min, na fita da sauri na kira Unguwar-zoma, a take ta gyara yaron, Innata kuma ta ce min a kaita asibiti.

Da sauri na taro Adaidaita na kamota muka nufi asibiti, ina goye da jaririn. Allah ya taimake ni da kuxi a tare da ni, nayi komai sai dai abinda ya saka ni zubar hawaye shi ne Innata ta kamu da ciwon yoyon fitsari.

Nayi ta rusa kuka ina jin baqin cikin abin a raina, inda ita Innata ke bani haquri a kan in bar kuka ciwo ba mutuwa ba ne. Da haka muka dawo gida ban da ina qoqari a kan Innata da xakinmu ba zai shigu ba. Amma duk da haka sai ka ji tashin zarni.

Aka kira Babana ya zo ya samu baqin labarin, bai wani nuna damuwa ba in ban da cewa Allah Ya sauwaqe, daga haka bai sake cewa komai ba.

Bai qara ko kwana xaya ba ya koma, inda ya tafi bai bar mana komai ba bare haqiqar da za’a yanka.

Kwana bakwai daidai yaro ya amsa sunan Yusuf, bisa zavin Innata. Zainal Abidin ya yi hidima sosai ga Innata har ta soma manta baqin cikin da Babana ya qunsa mata.

Yusuf bai samu haqiqan suna ba saboda rashin gatan da Baba ya nuna mishi

. Hidima tayi min yawa, ga ta Innata ga ta Yusuf, kullum ina goye da shi.

Wani abu da ke faxar min da gaba shi ne, yadda Innata ke yawan yi min nasiha me kama da wasiyya, wani lokacin in yi ta kuka wani lokacin kuma in yi shiru.

Watan Yusuf biyu sannan Babana ya zo, ya shiga xakin Innata na fito don in ba su wuri. Ina goye da Yusuf nayi saurin kwanto shi a zatona Baba zai buqaci ganinshi

, sai cewa ya yi in je da shi.

Nayi shiru ina son in gano abin da yasa Baba ya ke nuna mana rashin kulawa mu da Innata, abin da na kawo wa raina shi ne don Innata

ta kamu da ciwon

yoyon fitsari wanda mafi akasari ake nuna qyamarsu muraran

,

kamar yadda Amaka take ce mana wai mun cika gida da zarnin fitsari ko kuma ta toshe hancinta tana tsartar da yawu, wai zamu saka mata qwayoyin cuta.

Ina cikin halin tufka da warwara na soma jiyo kukan Innata tana roqon Babana abin da ban san me take roqon shi ba, kawai sai ji nayi yana dukanta da iyakar qarfinshi.

A cikin maganganun da ya ke ne na fahimci abin da ke faruwa wato wai duk wannan halin da take ciki bai tausaya mata ba har yake son haxin kanta, ita kuma ta qi saboda ta soma yi mishi qorafin abinda ya yi mata na rashin yi mata komai ita da Yusuf, shi ne kawai ya hau jibgarta.

Wai ta raina shi kuma ba zai yi mata komai ba sai tayi abinda zata yi, ya yi ta dukanta tamkar an aiko shi, inda ina jin Amaka na ta qyalqyala dariya.

Ganin zai yi min sanadin Innata yasa na leqa xakin ina kuka, na soma ba shi haquri.

“Baba don Allah ka qyaleta bata da lafiya fa!” Cak ya tsaya

da dukanta sai ma ya fice ya bar xakin. Na shiga ina kuka don in bata haquri, sai gani nayi hancinta da bakinta na zubar da jini.

Na sake fashewa da kuka ina kallonta. Da taga hankalina a tashe sai tayi maza ta ja zani ta soma goge jinin tana gogewa wani na zubowa.

Na tashi na xebo ruwa na soma wanke mata har na samu ya tsaya, sai kuma ta shiga kokawa

da numfashinta, abinda ya tashi hankalina kenan. Na xebo magungunanta na bata tasha har barci ya xebe ta, inda na zuba mata ido ina kallonta.

Gaba xaya ta fyexe, tayi wani irin fari fat! Kayan jikinta sun jiqe jagab da fitsari sakamakon robar da ke jikinta Baba ya fincike ta wurin dukanta.

Nan take naji duniyar tayi min zafi, sauqina xaya Yusuf ba shi da rigima, yana bayana yana ta sharar barci abin shi.

Qaddarar farko kenan a rayuwata wadda ta soma girgiza ni, wanda har naso in koma ga Allah Mai duka, da dai in riqa buxe ido ina ganin yadda Babana ke son kashe min uwata.

Ashe qaddarar da ke jirana a gaba ta zarta wannan, wadda da a ce xan Adam yana da masaniya a kan qaddararshi to da ko Innata bata biye Amaka wurin zubar da cikina ba to ni da kaina ma zan sulale ba tare da Innata ta sani ba in koma in da na fito.

Sai dai kash! Sai na tsige kazar wahalar da aka yanka min, sai kuma na jira qaddarata ta isa gare ni har ma ta miqo min abin da ta tanadar min wanda dole ne in saka hannu biyu in karva.

A cikin dare ciwo ya yi wa Innata sallama, numfashinta ya yi ta kaiwa da komowa, na kwana kanta ina tofa mata addu’o’i.

Abin mamaki Babana ko ya leqo ya ce mata ya jiki? Na tsabtace ta na bata koko, sai dai bata sha ba na ce “Inna me ki ke so in yi miki?”

Ta ce, “Kira min Kawu!” Ta bani amsa da qyar. “Kawu ba zai zo ba

Inna.” Na bata amsa cikin yanayin tausayinta da ke shiga cikin raina.

Inna ta ce, “Ke dai kira min shi zai zo.” Na miqe da goyon Yusuf a bayana na doshi gidan Kawu, yana ganina ya haxe rai.

Na gaishe shi ya amsa kamar ana mishi dole. “Me aka yi kuma?” Ya faxa yana zaro min ido.

“Inna ce ta ce ka zo.” Na faxa a ruxe.

“Me zan yi mata kuma?”

“Nima ban sani ba…”

“To in ma wani abu take so ki koma ki ce mata bani da ko sisi, kuxina na siyo Takin zamani da su, ita da bata gajiya da son ganin mutane da a bata dai kamar Aluf ja!”

Na miqe ina jin takaicin yadda Innata ke biye da mutumin nan marar mutunci ko shi kaxai gareta ta rabu da shi kawai tayi rayuwarta saboda babu abinda za su iya taimaka mata

.

Na baro gidan Kawun ina tsine ma shi a zuciyata. Ina isowa gida na iske Innata a cikin wani hali na fita hayyaci. Ban tsaya sauraren komai ba na kwasheta zuwa asibiti, in da aka buqaci kuxi ba kaxan ba.

A take na yanke shawarar siyar da kujerun Innata in biya mata kuxin asibiti, haka ko aka yi. Na siyar na dawo asibiti aka yi mata magani.

Sai dai ciwo kullum da salon da zai fito. Sai da muka yi sati biyu a asibiti babu wanda ke leqo mu bare ya ce mana ya me jiki? Ko ya ta qara ji?

Aka sallame mu ba don Innata taji sauqi ba, sai don an lura ba mu da kuxin yin hidimar asibitin da ake buqata kullum.

Tuni Babana yayi tafiyarshi bai ko bi ba’asin inda muka je tsawon sati biyu ba bare Amaka da haka ta fi fata da buri.

Washegari jikin Innata ya yi sauqi sosai ta dube ni. “Kawun ya zo ko?” Na kaxa kaina “A’a bai zo ba.” Na faxa da hawaye a idona.

“Kiyi haquri Beeba, ba komai nake so ga Kawu ba illa yafiya, zan bar miki wasiyya zuwa ga Kawu, ki nemar min gafara ki kuma faxa mishi na yafe mishi komai nawa, ke ma kiyi haquri da maraicin da zai same ki

, wata rana sai labari.

Ke nema min gafara wurin Babanku kar ki tsane shi, shi ne mahaifinki duk abin da ki ka

ga ya yi min bisa tafarkin aure ya yi min.

Don haka ina kyautata zato a kaina da kuma ke da Yusuf, ki riqe shi xan uwanki ne ba shi da kowa sai ke, kema ba ki da kowa sai shi. Kuyi zumunci, ku so juna kin ji Beeba?”

Kukana ya tsananta don ji ni ke Innata mutuwa zata yi. “Share hawayenki tashi ki kira min Amaka.” Na miqe ina son riqe kukana na kira Amaka. Ta wurgo min harara

. “Ba dai wancan xakin naku me zarnin fitsari ki ke nufin in je ba? Allah ya sauwaqe, in dai wani abu ne to ta fito waje amma ni ba zan kai kaina cikin wannan zarnin ba.”

Na dawo na faxa wa Innata Amaka ba za ta zo ba. Tayi murmushi “Ba wani abu ba ne itama neman gafararta zan yi, ki nema min yafiyarta bayan raina.”

Na qanqameta “Don Allah Inna ki bar faxar mutuwa, wa gare mu bayan ke?” “Allah!” Ta faxa. Na ci gaba da kukana har Allah ya gajiyar da ni nayi shiru na koma kukan zuciya.

Inna ta yini lafiya har ta ci abinci, daxi ya kama ni a raina na ce dama can zafin ciwo ne yasa ta sabbatun wasiyya. Sai dai me? Dare nayi ciwo yayo sallama, inda kuma Yusuf ya soma kuka tamkar an tsinkule shi.

Jikin Inna ya rikice, numfashinta ya yi ta fita da sauri-da sauri. Na xauko magani zan bata ta xaga min hannu alamar in bar shi.

Na zuba mata ido ina kallonta, inda wani annuri ya shiga fuskarta ta ce in bata ruwa, na xebo ruwan na kawo mata ta shanye. Nayi jugum ina zuba tagumi.

Ina kallonta can naga bakinta na motsi, fuskarta da murmushi tamkar bacci ya xauketa. Shi kenan tafiyar da

babu waiwaye sai dai a mafarki.

Kukan da Yusuf ya tsanyara shi ya gigita ni, na sauko shi nayi rarrashin duniya yaron ya qi yin shiru, gashi ba zan iya tashin Inna ta bashi mama ba, ashe shi da Mama sai a qiyama.

Na lallava shi ya yi shiru da kyar, na goya shi har La’asar Inna bata farka ba, abinda ya tashi hankalina na soma tashinta amma ina sai dai bata motsa ba.

Na kamo hannunta ya biyo ni lauu, abin da ya sani fasa kuka na soma jijjigata amma ina! Sai dai fatan mu iske su muna masu Imani.

Kukan da ni ke yi ne me amon sauti yasa Amaka leqowa tana toshe da hanci. Ta ce, “Ke lafiya?” Ta tambaye ni fuskarta a yamutse. Ni kuma sai kukana ni ke ban tanka mata ba.

Ta shigo xakin inda tayi arba da Innata da ta komawa Maiduka Allah. “Ayya ai ta mutu.” In ji Amaka. Sai naji tamkar yanzu ne naji mutuwar Innar tawa, na sake fasa sabon kuka.

Amaka ta fice tana toshe da hanci, nayi kuka nayi kuka wanda ban san ranar gama shi ba, da dai na gane bani da kowa da zai suturta Innata sai na tashi na shiga gidan Malam Jigo na sanar da shi kafin in aikawa Zainal Abidin, su kaxai ni ke da tabbas a kaina waxanda za su suturta min Innata, suka kuma tausaya min suka zo aka yi wa Innata sutura a ka kira ni muyi sallamar bankwana.

Nazo na zubawa makarar ido bakina ya rufe na kasa cewa komi. Hawaye ya turaro min na samu da kyar na

ce “Allah Yasa can tafiye miki nan Inna, Ubangiji ya dubi farar zuciyarki da farar aniyarki ya sada ki da Manzon Allah, Allah yasa rahama ta baibaye ki, Allah ya jaddada rahama a gare ki kin tafi! Kin tafi!! Kin bar mu da maraicinki da kewarki, Ma’aiki ya san da zuwanki ya baki masauki.”

Na miqe ina sharar hawaye, yayin da Babana ya iso saboda kiran Malam Jigo, shima ya yi mata

fatan samun masauki me kyau.

Da haka aka fice da gawar Innata, inda Yusuf ya tsala kuka tamkar yasan ya yi adabo da Innarshi. Ina qanqame da shi a qirjina inda Zainal Abidin ya saka Innata a kushewa shi da Baba a ka rufe ta, inda gida ya cika da masu zuwa gaisuwa, inda Amaka ta soma jan carbi tana sharar hawayen qarya ita da Aminiyarta Meri.

Matan Kawu dukansu suka zo min gaisuwa, inda shima Kawun ya shigo ya min gaisuwa. Sai naji haushin su ya qule ni, wai sai da Innata ta mutu suke zuwar min gaisuwa.

Mahaifiyar Zainal Abidin ta zo min gaisuwa, mace ce me kirki da karamci, wadda na tabbatar wurinta Zainal ya samo karamci. Abinci da abin sha tamkar ana fati, wai ‘ya’yan Kawu ne masu hali suka kawo.

A take zuciya ta tuqo ni, naso in sauke kwandon rashin mutunci a kan su Tasalla matan Kawu da suka maida zaman zaman kitsa gulma da kallon zannuwan da matan da ke zuwa gaisuwa.

Haka na kwana ina jin haushin Amaka da Babana waxanda sune sahun gaba wurin kashe min Innata. Amaka ita ce sanadin kamuwar ta da ciwon yoyon fitsari, inda shi kuma Babana ya yi mata dukan da ya zama ajalinta, to wa ya kashe ta? Shi…!

Kuka

ya rikito min duk yadda naso in ba kaina haquri abin ya ci tura, musamman idan na dubi Yusuf sai tausayinshi ya kama ni in qarawa kukana sauti.

Haka na kwana ba tare da bacci yayi nasarar xaukata ba. Washegari gida ya sake cika da ‘yan gaisuwa, inda kuma Yusuf yake ta tsala kuka wanda bana ko shakka kukan alhinin rashin mahaifiya ne.

Na dubi idonshi da ke fidda qwalla sai naji idona ya kawo ruwa, amma babu wanda ya bi ba’asin kukan Yusuf bare ya ce kawo shi. Na xauko madara

r nan na soma bashi, yana gama sha bacci ya xauke shi

, n

a rungume shi ina jin shi ne

x

aya qwal

da ya rage min.

Kawu ya shigo wai zai yi mini gaisuwa, inda yara ke xauke da manyan kuloli wai abincin sadaka ne ya kawo. Ya soma matsar ido yana son nuna min shi ma wai ya yi rashin Innata.

Wani haushi me kamar zai tarwatsa zuciyata ya taso min, ya soma yin gaisuwa ga matan da ya iske inda nayi banza da shi sai Amaka ce ta amsa mishi, inda ya shiga faxar cewa “Innata mace ce me kirki, mutuniyar arziki, me halaye na gari.” Amaka taamshe itama tana xora nata ta’aliqin a kan kirkin Innata.

Su Tasallah

ma sai suka soma faxar kirkinta, sai kowa ya kama faxar alherinta. Ban san sadda

zuciya ta tuqo ni ba na miqe tsaye ina zare ido.

Inna fa ai kowa zai faxi kirkinta da tayi mishi. Alhamdulillahi wanda ta tsarwa wani abu sai ya sakata ya wala ta bar mishi filin duniyar, sai ya share wuri ya zauna.

Duk kirkin Innata ba ku san tana da shi ba sai da ta koma ga Allah, to meye amfanin kirkinta tunda ku ka kasa yi mata kirki a lokacin da take buqatar kirkinku?

Allah ya tsinewa wanda bai yi riqo da zumunci ba, domin Allah ni ban san abinda Innata tayi muku ba, ban san abin da ta tare maku ba

ku ka kasa riqo da zumunci ku ka kasa agazar baiwar Allah, ku ka tsaneta, ku ka kasa taimakonta, to ta mutu ta bar muku filin duniyar.

Amma ku sani ba zan tava yafewa wanda duk ke da hannu a mutuwarta ba, musamman irin ka kai Kawu da Amaka da Babana.”

Amaka ta qurma ihu wai na qala mata sharrin kashe Inna, shi ko Kawu sai ya soma sallallami inda su Tasallah ma suka xauki salati. Wata mata da ban san ko wacece ba ta dafa kafaxata cikin rarrashi ta soma faxar.

“Haba Habiba, kada raxaxin rashi yasa ki xora zargi a kan bayin Allah kin ji? Ita mutuwa da ki ke gani xaya ce, duk wanda ya mutu kwananshi ne ya qare

.”

Na dube ta na ce, “Ba zarginsu ni ke ba, in ke kina ganin zargi ne Allah shi yasan ba zargi ba ne. Amaka

ita ce silar fizgo Yusuf da son yi wa Inna sanadi, ta kuma yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login