Showing 24001 words to 27000 words out of 35284 words

Chapter 9 - MANYAN MATA BOOK 2 BY HADIZA BARAU GIDAN IKO.docx

na tabbata idan wani namijin ne ba zai tsaya wani abu ba

zai rattaba min saki uku. Amma shi bai tava fuskantata da wata magana ba, bayan ta Bashir Bangis shima na san wani qullin ne ya zarga mishi.

Hawaye ya biyo idona…ya kai hannu ya share min “Meye abin kuka? Idan dai haka ne ai anyi aikin banza,

sai dai kar ki tava yarda da duk abin da za a faxa a kaina, da wanda aka ce miki gani can ina yi.

Nayi mamakin yadda mutumin can ya furta min cewa wai in sake ki saki uku shi zai aura min mata huxu. To me ya kawo wannan maganar? Ko a nan zan iya xora zargin da hannunshi a cikin lamarin masu turo saqonnin, don haka mu rufe duk wata jita-jita da ake son shigo mana da ita kin ji

my darling

?”

Na kaxa kaina, ya sumbaci bakina ya fice inda na xora aikin kuka. Matuqar mutumin can ya yi nasarar xora Zainal Abidin har ya xoru a kaina wa ke gare ni da zan kama a matsayin bangon jinginata?

Kwanaki da yawa sun wuce ba tare da tashin wata qura ba, inda na yardarwa kaina cewar an gano ba a yi nasara a kanmu ba shi yasa aka qyale mu, ashe ba a qyale mu ba wasa ma farin girki.

Ranar Laraba da wuri Zainal ya fice wurin aiki, bai dawo ba sai bakwai na dare, inda ya ke shaida min dalilin dawowarshi cewar wata mota ce suka kama xauke da kayan maye dangin su

cordin

da

Beneline

har ma da qwaya da kuma tabar wiwi. Kaya masu yawa na milyoyin kuxi, shi ne suka tsaya binciko me kayan, amma ba su samu ganinshi ba.

Washegari tun kafin ya tashi bacci wayarshi ta ishe shi da kwarmato, ya tashi cikin magagin barci ya xauki wayar inda aka sanar da shi wai yaron me kayan da suka kama ne ke son ganinshi.

Ya bashi lokacin da zai same shi a

office

.

Bayan ya dawo ne ya ke faxa min ashe kayan da suka kama na Alh. Bashir Bangis ne, inda yaron nashi yaso su kashe magana ba tare da shi oga ya ji ba, amma hakan bai samu ba saboda

case

ya je ga manya.

Na riqe baki dama sana’ar kayan maye yake, eh to ba zance eh kai tsaye ba, amma in ba siyarwa yake ba me yake da su? na tabbatar dai ba sha yake ba koda

yana sha xin to ya fi qarfin shan shi shi kaxai.

“To Allah Ya kyauta, amma gaskiya ban so wannan

case

xin ya zamo a hannunka ba, bana son wani abu da ya wuce gaisuwa ya shiga tsakaninka da mutumin can, domin ko sharrinshi ya zarta na Gamsheqa.”

“Allah Ya fi shi.”

“Haka ne, Allah Ya shiga tsakanin Nagari da mugu.”

Da dare sai ga Alh. Bashir Bangis ya shigo har cikin gida, abin da ya daxe bai yi ba. Na miqe da shirin shiga xaki, har zan share shi sai kuma na ce mishi “Ina yini?” Ban bari ya gama amsawa ba na shige xaki, ina jiyo su shi da Zainal Abidin.

“Ashe hannunku muka faxo Zainal Abidin? To meye abin yi

?” Zainal Abidin ya yi murmushi. “Nayi mamaki Alhaji ace kayanka ne ni na musa cewa kayanka ne, sai dai shi wanda ka turo xin ya tabbatar da naka ne, sai na yarda.”

Ya ce, “Ai na daxe ina wannan harkar Zainal, saboda duk kuxin da na samu ta hanyar ne babu irin

kuxin da wannan sana’ar bata tara min ba. Don haka kar ka ji komai me ka ke so a yi?”

Zainal Abidin ya muskuta “Gaskiya Alhaji ba daga gare ni ba ne, matsalar daga can sama ne. Abinda ya fi kaje ku tattauna su faxa maka sharaxinsu da dokarsu, tara ce kawai zasu yi maka ka biya amma ni babu abinda zan iya…”

“Kai ko za ka iya da ka so

case

xin ya mutu duk za ka iya don haka ga wannan.” Ya aje mishi zallar kuxi ta rafar dubu-dubu. “Idan ma ba su isa ba to zan qaro maka da mafiyansu.”

Zainal ya ce, “A’a Alhaji, ai ka fi qarfin wannan a wurina. Koda a ce zan iya yin wani abu a kai to ba fa zan ci amanar qasa ba. Amma babu komai na xauke ka a matsayin xan uwana, kuma Yayana, don haka zan yi wani abu a kai

, amma fa sai mun je da kai can sama don ka amsa laifin shigo da kayan maye da kuma biyan tara da sharaxin ba za ka sake shigo da kayan maye ba.

Sannan kar kayi gangancin nuna kuxi a matsayin toshiyar baki, ka bari ka ji irin tarar da aka yi maka sai ka biya.”

Haka kuma aka yi, Zainal Abidin ya shigo gaba har

case

ya mutu ya kawo kuxi masu yawa ya ba Zainal amma bai amsa ba. Godiya sosai ya yi mishi. Na jinjinawa Zainal Abidin a kan farar zuciyarshi da ba wa duniya da abin duniya baya duk da yasan yankan bayan da Bangis ya yi mishi.

Hakan bai hana shi taimakon shi ba, sai ya zama yana siyen kayan abinci da kayan masarudi yana aiko mana a zuwan shima ya rama alherin da aka yi mishi.

Wata biyar da yin haka tarihi ya maimaita kanshi aka kuma kama kayan Bangis na kayan maye. A wannan karon mota uku me xauke da kayan maye na manyan kuxi, kwanan Zainal Abidin huxu a gida yana zazzavi shi yasa bai san da

case

xin ba.

Yana kwance a kan cinyata ina dafa goshinsa “Ya ya zazzavin ai ya sauka ko Abba?” Ya riqo hannuna ya sauka sai dai kaina da ke harbawa kaxan-kaxan.”

Na kama kan na matse da yatsuna, ina kama mishi da tofa mishi addu’ar ciwon kai, ya qara damqe hannuna “Kin ga ko ya soma sauka.” Na rungume shi a qirjina, “Ina ma zan iya cire maka ciwon nan? Ba na son ganin abin da zai takura ka!”

Ya ce, “Na gode sosai

Darling

, Allah yasa miki albarka, ya ba ki Aljanna.”

“Qafarka kawai za ka xaga min in shiga.” Ya xaga qafar “Taho ki shiga na yarje miki, Allah Ya yarje mana zama tare a cikin Aljannar.” Na amsa da “Allah

umma Amin.”

Muna haka Bangis ya shigo da sauri na tashi ina gaishe shi, nayi cikin xaki don har yanzu bai bar zuba min ido ba, ina jin su daga cikin xakin bayan sun gaisa inda Zainal Abidin ya faxa mishi ba shi da lafiya kwana huxu bai je aiki ba.”

“Haba, shi yasa ba ka san abin da ke faruwa ba.” Nan ya kwashe komai ya faxa mishi a kan kama kayanshi da aka yi. Zainal ya yi shiru yana nazari kafin ya ce, “Maganar gaskiya Alhaji sai dai kayi haquri da kayan nan, domin ko wannan karon ba za su qyale ka ba, tunda ka saka hannu kun yi yarjejeniyar ba za ka sake shigo da kaya irin waxannan ba…”

Da sauri ya tari numfashinsa da cewa, “Kar ka damu Abidin, ba ni zan je a matsayin me kaya ba, zan tura wani a zuwan shi ne me su, kai dai qoqarin da za ka yi mana irin wancan ne har

case

xin ya mutu…”

Da sauri ya tare shi “Ba zan yarda in sake shiga cikin

case

irin wannan ba, domin ko za a gano ko ina daga cikin bara-gurbin jami’an tsaron da ke da hannu a safarar miyagun qwayoyi.

Kayi dabara sosai da za ka tura wani a zuwan me su, to ka samu wani da zai tsaya a kan maganar har

case

xin ya mutu!” Ya soma yi mishi roman bakan ba shi duk abin da yake so, kuxi milyoyi, kai alqawura dai tamkar zai ba shi duk abin da ya mallaka.

Amma ina, Zainal ya nuna mishi matuqar ya sake komawa a karo na biyu to sunanshi ne kawai zai vaci. Sai dai ya ba shi shawarar da yake ganin zata zamo maslaha.”

Suka rabu a haka, sai dai duk yadda Bangis yaso amsar kayanshi abu ya faskara. Kwana biyu da yin haka inda zazzavi ke tafiya yana dawowa, wanda ya yi daidai da kwananshi shida bai je aiki ba.

Kawai sai ga abokan aikin Zainal Abidin sun zo ba don su duba jikinshi ba sai don tafiya da shi, wai ana nemanshi cikin gaggawa.

Hankali a tashe suka fice tare da Abidin, inda hankalina ya kasa kwantawa. Bai dawo ba sai marice liqis. Na fito da sauri don in tambaye shi neman me ake mishi?

Takardar hannunshi na bi da kallo. Ya zauna tare da dafe kanshi alamar yana sara mishi. Na cire hannunshi daga kan shi na dubi idonshi wanda bai voye tashin hankalin da yake ciki ba.

“Me ke faruwa Abba?” Ya miqo min takardar yana min bayanin an sallame ni daga aiki sakamakon wani xungumemen sharrin cewa kayan Bangis da aka kama namu ne mu biyu, na kuma zama Xansanda me fuska biyu wanda ni ke fakewa a rigar ‘Yansanda ina qetarar da kayan maye.

Don haka an sallame ni aiki za a kuma xora da bincike a kaina.” Gabana ya bada wani dammm! Na zuba mishi ido. Zuwa can na ce, “Allah Yasa hakan shi ne alheri, amma ba zargi ni ke ba me muka yi wa mutumin can? Bana ko shakka da hannunshi a faruwar hakan.

Duk ma wanda ya yi hakan yaje shi da Allah

, bayan aikin Xansanda ina da damar neman wani aikin nan gaba. A gaskiya mu tashi daga unguwar nan Zainal wallahi ta ishe ni.”

Ya ce, “Kiyi haquri, in mun tashi ai tamkar gudun qaddara muka yi wadda ake cewa guzurin taddata komai ki ka ga ya samu bawa to da sanin Allah, ke xin ce dai ba za a yi nasarar raba mu ba, qwalelen duk me kallo.”

Haka muka jajantawa juna abinda ya same mu, muka shiga addu’ar Allah ya yi zavi mafi alheri. A ranar da abin ya faru sai ga Bangis wai ya samu labarin an kore shi aiki. Nayi mamakin wannan mutum me Musa a baki Fir’auna a zuci.

Ya yi mana jaje inda ya ce wa Zainal Abidin idan babu damuwa ya zo ya riqa yi mishi aikin tuqi kamar da can da ya fara yi mishi. Na dubi Zainal xin da son in ji abin da zai ce, kawai sai na ji ya amsa da babu damuwa. Suka aje magana a haka.

Bayan ya tafi na dube shi na ce, “Me yasa ka amsa da za ka yi Abba? Ba ka san mutumin can so yake yaga babu kai a doron duniya ba? to ka sani bani da sauran wani rai sai naka.

Ba ni da sauran wani buri sai kai, ban da sauran fata in ba kai ba, don haka wallahi ban yarda ka karvi aikin Bangis ba, idan ka gaji da rayuwarka ni ina da buqatarka, ban da bangon jingina idan babu kai.”

Ya damqi hannuna “Babu me kashewa da rayawa face Allah, wani ba ya kashe wani sai kwana ya qare. Kiyi min addu’a ba mu da tsimi bare dabara a kan abin da Allah ya zano a kanmu.

Na karvi aikin ne ba don komai ba sai don in nuna mishi ina mishi biyayya a kan matsayin da na ba shi. Aikin tuqi ba ya nufin zan dauwama a tuqin ba, a’a ina samun wani aikinz an aje mishi tuqinshi kamar yadda nayi a baya.

Don haka kar ki tashi hankalinki, babu abin da zai biyo baya sai alheri, in ma ya kashe ni xin nauyin da ke kaina ai kin ga ya koma kanshi ko?”

Faxar hakan ya sani fashewa da kuka, Allah ya sani raina da hankalina ba su xauke ba to amma na yarda da abinda ka faxa komai Allah ya zanewa bawa to babu wand aya isa ya goge. Ina yi maka fatan alheri.”

Kwana biyar da yin haka Zainal Abidin ya soma tuqi a gidan Bangis, a kullum zai tuqa shi ya kai shi in da ya ke muradin zuwa wata rana kuma a ba shi umarnin kai Hajiya Tamadina unguwa.

Abin da nafi tsana a rayuwata kai Tamadina unguwa, amma babu yadda zan yi dole

in haxiye. Kai sai ya zamo shi ke yo cefane ya kai yara makaranta. Sai dai idan wata ya yi albashi yake ba shi me tsoka wanda ya zarta albashin shi na aikin Xansanda.

Tafiya ta miqa a haka, inda Hajiya Tamadina ta wanko qafarta har gida ta wanke ni soso da sabulu ba tare da nasan abin da nayi mata ba. Amma a cikin kalamanta na gano bakin zaren.

To in ma maita ki ke sai in ce kurwata kur wallahi, wannan jaraba da me tayi kama? Bashir ba shi da abinda ke ranshi sai Habiba.

To in ma kin bashi wani abu ya ci sai in ce kin makara, domin ni ba irin macen da zan raba soyayyar miji da wata ba ce, bare ke matar korarren Xansanda.

Tuni ba tun yau ba na gano idonki a kan mijina. To na zo kashedi sau xaya kar ki bari in sake zuwa a karo na biyu, in ma ke Karya ce sai in ce ki bi Karen mijinki wanda ya zamo bawa a gare mu.”

Haka ta qare cin mutuncinta ta fice ba tare da na tanka mata ba, saboda ba ta zo gavar da zan tanka mata ba, gavar ko ba ta wuce tavo mahaifiyata da ke kwance a kushewa ba, ko zan qyale komai to ba zan yarda da hakan ba.

Sai kuma aka yi sa’a ba tazo gavar ba. ban yarda Zainil Abidin ya ji abin da Hajiya Tamadina tayi min ba, in ma ya ji xin to ba a bakina ba.

Sati xaya da yin haka, Hajiya Tamadina tayi shirin zuwa gida Kaduna, kasancewarta ‘yar Kaduna inda Zainil Abidin ne ya tafi kaita. Misalin takwas na dare ina zaune ina karatun littafin ‘KETA HADDI’ ina jinjinawa Marubuciyar littafin wato (ASMA’U LAMIXO), kawai sai ga Bashir Bangis.

Na aje littafin ina bin shi da kallo, na miqe tsaye ina faxin “Nan fa ba gidan karuwai ba ne, aure ni ke bare ka nemi taka alfarmata.” Ya soma matsowa kusa dani na soma ja da baya har ya yi nasarar cimmani.

Ya cire hular shi ya soma valle mavallin

links

xin gaban rigarshi. Na rasa abin da zan yi domin qwatar

kaina saboda na gane in ban yi da gaske ba to babu ko shakka zai keta min haddi…

“Kar ki damu Habiba, babu abin da zan yi miki saboda ni bana yi wa mace dole, ina dai so ne muyi magana na kuma fi son muyi maganar ina rungume da ke a qirjina.”

Ya kawo hannu zai tava ni nayi saurin xaga mishi hannu. “Kar ka tava ni. Wallahi tallahi ka tava ni komai zai iya faruwa, don na gama fahimtar ba ka tsoron Allah

.”

Ya ce, “Kar ki damu Habiba, komai za ki faxa min ina jin daxi, koda zagina ki ke daxi nake ji. Abu xaya zan faxa miki shi ne tarkon da na xana miki ya kasa kama ki a wuya ma ai kin lura da abubuwan da ke faruwa ko? To na kusa mallakarki ta kowace fuska, don zan gaje ki kamar yadda ake gadon kayan matacce! Kin kusa zama matar Gado.

Matuqar ruxewata tasa na kasa cewa komai, matar gado? Na tambayi kaina tsananin kiximewar da nayi yasa har ban san lokacin da ya fice ba. sai naga lallai ne tarkonshi ya kama ni a wuya in dai abin da ya faxa haka yake.

To ai dama ina son xora zargi a kanshi sai gashi ya hutar da zuciyata ya faxa da bakinshi, sai naga me ya dace in yi don in kuvutar da Zainil Abidin daga sharrin Bangis, wanda ni ce a tsakiya da har ake shirya mishi makirci? In rabu da shi kawai! To in na rabu da shi in kama wa?

Kaina ya shiga tsananin duhu, nayi sa’ar dawowa bisa saiti inda tunanina ya bani in kira wayar Zainil Abidin in ji halin da yake ciki. nayi sa’ar samun shi.

“Fatan kun isa lafiya?”

“Lafiya lau

my darling

, har ma mun juyo gamu a Malumfashi, insha Allahu nan da awa

biyu ina gida.”

“To Allah ya kawo ka lafiya.”

Ina zaune ina kuka ya iso, ya aje ledodin da ya iso da su wanda na gane dankalin Turawa ne da kifi xanye da su karas da kabeji, da wata ledar da ban fahimci ko meye a ciki ba!

Ya qaraso da sauri. “Me ya faru Beeba?” Na share hawayena “Zainil na gaji da mugun qudirin mutumin can a gare mu, don Allah ka aje mishi tuqinshi mu tashi daga gidanshi mu koma wani wurin

.”

Ya rungume ni yana faxin “Kar matsalar mutumin can ta qara sa ki zubar da hawaye Beeba, duk isar farin Kare ba zai tava zama Rago ba, insha Allahu ba za a tava yin nasara a kanmu ba, wanda duk zai yi wa sama tofi to fuskarshi kawai zai vata da yawu!

Ina sane da komai nayi shiru saboda ganewa nayi Allah Shi ke yi, karambani ke kai Xan Adam shiga hurumin Ubangiji, duk yadda aka so idan Allah bai so ba aikin banza ake yi.

Don haka bari vata ranki a banza, duk abin da qaddara ta miqo wa bawa amsa kawai yake yi. Gode hakan shi ne cikar Imani. Ki yarda Allah xaya ne! To

Allah Ya zamo gatanmu.” Ya amsa da “Allahumma Amin.”

Rayuwa ta miqe mana cikin abubuwa masu yawa masu daxi, saboda sana’ata ta kitso da qunshi ta qara bunqasa, inda na xora da Alkaki wanda ake zuwa har gida a sara a bani kuxina chas!

Ba ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login