Showing 12001 words to 15000 words out of 35284 words

Chapter 5 - MANYAN MATA BOOK 2 BY HADIZA BARAU GIDAN IKO.docx

nasara har ta kamu da yoyon fitsari, inda shi kuma Baba ya yi mata dukan da ya zamo asalinta.

Shi kuma Kawu ya ba da gudunmawa sosai ta yin watsi da lamarinta bare ya bibiyi halin da take ciki. To duk sai su huta ta kuma ce a nemar mata gafararku, ita kuma ta yafe muku.

Kiranku da tayi dama don kuyi sallama ne, don haka ni ban ga amfanin zamanku a makokinta ba, in donni ku ke yi to na yafe ku tashi ku bani wuri bana so.

Zumunci kuma tunda kun yanke shi to kuje babu shegen da zai ga qafata a gidanshi kowa ya tsaya inda Allah ya aje shi, ku kwashe abincinku bana buqata. Na jiya ma da aka kawo zan biya ku abinku, ku tashi gabana.” Na faxa da amon murya.

Kawu ya miqe yana kallona. “Dama idan ba kiyi haka ba yaushe zan san ke jinin Binta ce? To mun gode da cin zarafinki, kuma zumunci na yanke shi da ke…”

“Ko ba ka yanke shi ba Kawu ni zan yanke shi, don ku xin baqaqen ‘yan uwa ne da ba ku da rana, ga ku ga duniyar nan itama da tayi alheri ta kuma yi kirki yau ta mutu bare ku da ku ka yi mata sharri? Za ku mutu ku iske baqin halinku a can.”

Kawu ya fice yana sharar hawaye inda su Tasallah suka soma miqewa suna savar mayafinsu. Kan ka ce me? Gida ya rage daga ni sai Amaka da ke ta sharar qwallar na qala mata sharri.

Baba ya shigo ya iso gare ni “Me ki ka yi wa su Kawu, Beeba?” Na dube shi cikin jin haushin ya kashe min uwa, “Na faxa masu ku uku ku ka yi tarayya wurin kashe min Inna!” Ya zaro ido! “Mu uku muka kashe ta Habiba?” Nayi banza da shi.

Ya soma magana “Ban kashe Binta ba kwananta ne ya qare, duk wanda ya mutu to kwanan shi ya qare, babu wanda ya isa ya kashe wani face Allah. Don haka kar ki bar zuciyarki ta saka miki cewa wasu ne suka kashe Binta.”

Kalmar kashe Binta tayi ta yawo a kaina, shi kenan ni ce me damuwa ni nayi rashi daga ni sai xan tahalikin Allah Yusuf, wanda ba a bar shi ya rayu da uwarshi ba bare ya gane alherinta da kowa ya gane tana da shi.

Kuka ya ci qarfina, nayi ta abuna ina jin tsanar Babana a raina da bai tausayawa Innata ba sai ma kashe min ita da ya yi.

Ya soma rarrashina da kalaman da yake tunanin za su yi min daxi alhalin bai san qona zuciyata suke ba. Na dube shi cikin hawaye.

“Don Allah Baba ka qyale ni in ji da abin da ya same ni, Inna dai ta mutu, to shi kenan wanda ta tsarewa wani abu sai ya wala.”

Na xauki Yusuf nayi shigewata xakin Innata ina ci gaba da kukana. Yusuf ya yi kashi na fito in wanke mishi inda na iske Baba a inda na bar shi ya kasa motsawa.

Ina cikin wankin kashin Yusuf, mahaifiyar Zainal Abidin ta iso don ta qara yi min ta’aziyya, na karveta da mutuntawa muka gaisa kaina a qasa ta qara yi min gaisuwa tana ta bani haquri.

Ta karvi Yusuf tana shafa kanshi tayi mishi addu’o’i masu yawa. A raina naji da ace mutanen duniya irin su Mamar Zainal Abidin ne to da ba a yi watsi da zumunci irin yadda su Kawu suka yi ba.

Ta yi wa Babana gaisuwa kafin ta fito daga gidan. Sai ya zamo babu ruwana da harkar kowa a gidanmu, in ban da gaisuwa babu abinda ke haxa ni da Amaka da Baba, in ban da gaisuwa daga haka ba na xorawa da komai.

Rayuwata daga ni sai Yusuf, shi ko Zainal Abidin wanda ke matuqar qoqari a

kaina da kuma Yusuf wurin siyen madarar (NAN) da kuma ciwuka irin na jinjiri duk baya gazawa. Haka ma mahaifiyarshi tana matuqar qoqari a kanmu, in da ni ke jin sun maye min gurbin ‘yan uwan da na rasa ba don sun mutu ba sai don rashin riqo da zumunci.

Kwanci tashi asarar mai rai, yau an wayi gari Innata tayi wata biyu da rasuwa, wanda ya yi daidai da tsayawar watan bikina.

Haqiqa Zainal Abidin shima wani bango ne a gare ni ban da haka da babu abin da zai sa ina cikin alhinin mahaifiyata. A tashin hankalina da batun wani biki amma Zainal ba irin Babana ba ne.

Don haka sai na ba da kai ko don in fita daga gidan da ni ke ganin shi da baqi. A cikin satin aka shiga bikin aurena da Zainal Abidin.

Ban gayyaci kowa ba daga dangin Innata don da gaske na yanke zumunci dasu. Maijidda da Bilkisu qawayena na talla sun yi min karamci na yin hidima da su da kuma matan Malam Jigo makwabcinmu.

A duk inda zan je Yusuf yana goye a bayana, inda ni ke son ganin Zainal don in roqe shi alfarmar tafiya da Yusuf, sai dai Baba ya ce babu in da zan je mishi da xan shi Amaka ya ba wa shi.

Wani baqin ciki ya damqi zuciyata, ta ya ya Amaka zata iya riqe Yusuf? Ta dai kashe shi kawai. Don haka sai na nunawa Baba ban yarda da hakan ba.

Ya dube ni a fusace “Saboda ke ce uwar shi ko ko ubanshi?” Duk yadda Baba yaso in miqawa Amaka Yusuf naqi, don haka ya rufe ni da duka ai tunda kin zama ‘yar iska to bari nima in nuna miki kalar nawa iskancin, ke da iyakarki Katsina a Saulawa layin shaixan, ni ko babu inda ba a sanni ba

.

Duk wani wuri da ake zuwa ayo iskanci babu inda ban je ba, Tafa da Ogyaro

da Mai Mujiya babu in da ban je ba, bare Marabar Jos da ko ni ke ganinta gida.

Kuma da ki ke cewa na kashe Binta to na kasheta xin in ga abin da za ki yi.” Duk waxannan maganganun yana yin su ne lokacin da yake jibgata. Ina kallo ya karve Yusuf ya miqawa Amaka wai har yana faxin ya

bata shi kyauta, inda ita kuma ta ce wai ta samu xan talla.

Haka abokan arziki suka fice da ni ina kuka zuwa gidan da Zainal Abidin ya kama haya cikin unguwar ta masu jin sauqin garin wato Qofar Marusa

Lowcost

.

Haqiqa gidan yana da kyau sai dai ba har can ba, don ba irin na masu ido da kwalli ba ne. Qaramin gida ne me shafe da brekin tile, sai xakuna uku masu xauke da ciki da falo, sai madafi (kitchen) da makewayi (banxaki)

guda xaya.

Gidan yana tsakiyar wasu tankama-tankaman gidaje masu xauke da shukoki da furanni. Abin da na kawo wa raina ma Maigidan irin ma su qi-faxin nan ne wanda basa iya siyarwa me kuxi qaddararsu don ban fidda zargin wani ya ce yana son gidan ya siya ya haxe da nashi ba saboda irin waxannan gidajen za ka iske ba a barin me shi ya zauna cikin masu kuxi, sai dai a siya a haxe shi kuma ya koma cikin talakawa ya siyi daidai da shi.

Washegari bayan an yi walima na dubi xakina babu komai sai katifa, itama ta Innata ce Baba ya rako ni da ita bayan ita babu abin da Baba ya siya min.

Xakin ya sha ledar qasa wadda Safare matar Malam Jigo ta siya min, kishiyarta Lamunde kuma ta bani zanen Gado. Bayan su babu abin da wani ya bani da sunan tallafi ko taimako.

Hawaye ya kasa barin zarya a idona. Takaicin abin da Baba ya yi min da kuma raba ni da

Yusuf da ya yi

ya miqawa Amaka. Ina cikin haka Zainal Abidin da abokanshi biyu Naziru da Adamu suka shigo.

Ina zaune qasan ledar nayi maza naja hijabina na rufe kaina da fuskata na gaishe su naja bakina nayi shiru ina jin su suna ta zolayata da yau ga Beeba matar Xansanda, ko ya ya za a qare?

Na dai yi shiru ban tanka ba nasan Zainal ne zai faxa musu abinda na faxa kan Xansanda, duk da ina lulluve da mayafi hakan bai hana ni jin kunya ba. Ina ji Zainal ya ce “Adam bana son iskanci kai fa xan iska ne, kai da na faxa maka magana ai sirri ne tsakanina da matata.”

Haka suka yi barkwancinsu suka gama inda aka karanto salatin Annabi (S.A.W) aka shafa kowannensu ya aje min kuxi suka yi mana fatan alheri ya raka su suka fice.

Zainal Abidin ya dawo ya iske ni a lulluve, ya

kama mayafina ya buxe in da ya iske hawaye a idona. “Bana son ganin hawayen nan Beeba, an ce fa kukan Amarya ba na qin Ango ba ne, haka ne?” Na xaga kaina alamar “Eh.”

Ya soma share min hawayen. “Na san dalilin kukan ba zai wuce na rabuwa da Yusuf ba, da kuma tunowa da Inna.” Na dube shi tamkar ya duba zuciyata yaga abin da ni ke tunowa.

“Haka ne aiko! Haka ne.” Na ba shi amsa. “To kiyi haquri, Yusuf Allah zai raya shi a duk inda ya ke, ita

kuma Inna da kin tuno ta to yi mata addu’a kin ji Amaryata?” Na amsa da “To.”

Ya zubo min abin da ya shigo da shi na sha madarar kawai shima ya sha ya kuma ci naman kaxan inda ya bani umarnin kwanciya saboda yaga cikin alhini ni ke.

Washegari na riga shi farkawa saboda mafarkin asubahi da nayi inda nayi mafarki da Innata. Na ganta cikin kyakkyawar shiga inda kuma tayi min nasihar zaman aure wadda babu wanda ya yi min ita.

“…kiyi haquri Beeba da duk yadda rayuwa tazo mik

i, kiyi biyayya ga mijinki domin ko shi ne bangon jinginarki. Ki riqe shi uwa kuma uba duk umarnin da ya ba ki kar kiyi mishi gardama.

Ki taimaka mishi ta ko ina kar kiyi qyashi ko baqin ciki, ki mu’amalanci mutane da zuciya xaya, ki riqe mutuncinki, ki kuma kiyaye mutuncin mijinki. Maganar Yusuf kuma kar ki tashi hankalinki namiji ne shi ba zai tava dawwama a wahalar Amaka ba.

Rai da rayuwa duka a wurin Allah suke, idan yaso ya raya to zai raya ba tare da tallafinki ba, haka kuma idan bai yi me nisan kwana ba ne duk gatan da za ki nuna mishi sai ya mutu.

Kiyi haquri da rayuwa, kiyi haquri da halin mutane, albarka ta bibiye ku ku da yaran al’ummar musulmi…”

Ta soma tafiya inda nayi nufin bin ta amma sai naga bata son in biyo ta. Da naga haka sai na xaga qafa (gudu) amma abin mamaki tamkar walqiya ta fice fit! Sai ma na daina ganinta.

Ina zuwa nan a mafarkina sai na farka inda na

ji hawaye a idona. Da sauri na tashi Zainal Abidin ni kuma na xaura alwala nayi addu’o’i ma su yawa ga mahaifiyata tare da musulman da suka riga mu gidan gaskiya.

Ina kan sallaya Zainal ya dawo daga Masallaci. Na zube a gabanshi ina gaishe shi, ya yi murmushi ya ce “Ya baqunta?” Nayi murmushi na ce, “Ai na zama ‘yar gida.”

“Anya ko kin zama ‘yar gidan?” Ya faxa yana kallon idona. Kunya ta kama ni saboda sanin abin da yake nufi. Nayi nufin shiga kicin don haxa abin kari, sai dai bana da komai na yin girki, hatta flate xin da zan ci abincin bani da shi.

Zainal ya hana ni girkin inda ya ce mahaifiyarshi zata kawo mana abin kari. Muna tsaka da maganar sai ga qaninshi Kabir ya shigo da kulolin abinci. Har qasa ya zube yana gaishe ni, muka gaisa

a mutunce na gane mahaifiyar su jarumar uwa ce me iya tarbiya

da nuna karamci.

Tsayin sati mahaifiyar Zainal Abidin na hidimta mana da girki, inda na ce wa Zainal ko za a hutar da Mama wahalar girki mu soma yin namu kar fa abin ya zamo ya wuce gona da iri.

Ya ce, “Hakan ya yi, bari idan naje za a sanar da ita.” Kunya ta hana in faxa mishi bani da kayan girkin, amma ga mamakina lokacin da zai dawo sai ga shi da kaya masu yawa. Babu abin da bai siyo ba.

Hawaye ya biyo idona, anya ko akwai maza da yawa irin Zainal Abidin a duniya? Koda akwai su dai ba su da yawa.

Ya rungume ni “Me ki ke wa kuka? In dai Inna da Yusuf ne ai na ce kiyi musu addu’a ko?” Na kwantar da kaina a kafaxarshi ina kukana don farin cikin turowa rayuwata da Ubangiji ya yi ba ni da bangon da zan jingina Zainal, sai ga shi ka zamo bangon jinginata.

Ina da uba amma gara a ce maraicinshi ya same ni. Na rungume shi ina kuka, ka zama uwata kuma ubana. Me zan ce maka? Ya yi murmushi yana share min hawaye ya ce, “Ce min

I love you

Beeba, shi kaxai ya ishe ni.” Ya faxa yana haxa tsinin hancinshi da nawa.

“Ke kaxai ni ke so a duniya, kiyi min addu’ar Allah Ya buxa min in wadata ki kiji daxi har ki manta komai, nayi miki alqawarin ba zan tava bari kiyi kuka ba. Ba zan tava bari ki ce ya zan yi ba, Allah ya cika min burina in zamo madadin Inna a gare ki ke da Yusuf.”

“Allahumma Amin.” Na amsa. Sai ya zamo a duk sadda zanyi girki sai na ware na mahaifiyar Zainal an kai mata. Zamana da Zainal zama ne na nuna tsantsar soyayya da kulawa, har na gane so xaya tal Zainal yake min ba wai sha’awa ba da ta fi tasiri a zukatan wasu masoyan.

K

asancewar

Innata mace ce me yawan sana’o’i yasa na koyi sana’o’i masu yawa, a ciki na koyi qunshi da kitso, da Alkaki har ma na qara da wasu a kai.

Ina yawan jin tana cewa zaman banza ba shi da daxi, mace tayi sana’a a gidanta ko don ta agaji kanta ta kuma agazawa mijinta hakan yasa na miqe da son in agazawa Zainal Abidin. Na sanar da shi ina son zan xan riqa yin sana’a koda ta kitso da qunshi ce, bai hana ni ba sai ma qarfafa min gwiwa da ya yi.

Koda yake ban tava zuwar mishi da buqatata ya tankwave ba, sai dai yanayin unguwar ba irin unguwar da ke da yawan jama’a ba ce. Amma duk da haka ban kasa ba.

Cikin yaran da ke shigowa kasancewar al’adar Hausa gidan da ke da Amarya ba ka raba shi da ‘yan suntiri yara. Hakan yasa nayi wa wasu yara qunshin kyauta, ai ko sai ga iyayensu sun zo har gida wai godiya. Ai ko tun daga wannan lokacin sai ya zamo ni ke masu qunshin har da kitso suna biyana, kan ka ce me? Har sunana ya zaga a cikin unguwar ana faxin ‘Gidan Beeba Mai Qunshi.’

BABI NA SHA BIYU

W

atana uku a gidan Zainal Abidin, tuni na goge na yi wani irin kyau, fata ta goge shar dani saboda kulawar Zainal a kaina. A lokacin ne na nemi izinin zuwa gida in gano xan uwana, ya kuma bani dama.

Nayi wanka cikin leshi me kalar qwaiduwar qwai, nayi kyau sosai ga wanda ya sanni a baya ba lallai ne ya gane ni a yanzu ba. Na isa gida cikin xokin ganin Yusuf inda na iske shi yashe a kan Tabarma yana tsotsar yatsunshi, ga kashi yayi amma Amaka bata bi ta kanshi ba, tana can xaki ita da Meri suna ta batun duniya.

Nayi ta sallama ba su ji ba, don haka kai tsaye na nufi Yusuf na xauke shi na zuba mishi ido shima kallona yake har yana vangala min dariya. Na wanke mishi kashin na leqa xakin Amaka muka gaisa ita da Meri suka bini da kallo suna ganina tamkar an vare ni daga cikin qwai

.

Muna gama gaisawa

na fito na bar su da bina da ido, tsegumi fal bakinsu. Xakin Innata

na shiga, sai dai xakin babu komai, an kwashe kayanta babu komai sai filin xakin.

Na fito ina save da Yusuf na nufi xakin Amaka da nufin in tambayeta inda aka kai kayan Innata, kawai sai naga gadonta da ledar qasarta a xakin Amaka, kenan ita taci gadon Innata.

“Amaka ina aka kai kayan Innata?” Da na lura da kyau ma kayan Innata ne a jikinta. “A’a wannan ai kayan Innata ne, Amaka har da ke a cikin masu gadon Innata ne?”

“A’a siya nayi kar ki nemi tara min mutane ki ce na saci kayan uwarki. Dama kin qala min sharrin ni na kashe uwarki, to kayanta siya nayi wurin ubanki.”

Na dubi Meri da ita ma ta samu kayan gadon Innata da Amaka ta raba musu, don ita ma sanye take da wani leshin Innata, zuciya ta tuqe ni a kan yadda aka yi min wannan kama-karyar.

Ai sai dai ko a mutu har Liman in yaso a rasa me yi wa kowa sallah, sai kuma nasihar Innata ta dawo min tamkar a lokacin ta ke min ita.

Bisa tilas na haxiye fushin da ya taso min inda kuma Amaka ta xora yi min fashin baqin yadda Babana ya yi mata gwanjon kayan Innata, ban tsaya saurarenta ba saboda nasan komai zai iya faruwa.

Babana zai iya siyar da kayan Innata

, haka ita ma Amakar zata iya gaje kayan saboda ko dama can tana jin zafin Innata a kan kayan xakinta wanda Amaka ba ta da ko rabin na Innata.

Don haka nayi shiru ni da na rasa Innata nayi haquri sai kayan xakinta da za su lalace wata rana? Na yini ni da Yusuf wanda ya sauya ya rame. Inda na gane baya samun kulawa, inda Amaka take ba shi koko a matsayin madarar nan. Da zan ta

fi sai na siyo madarar

na bata na ce mata a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login