Showing 3001 words to 6000 words out of 35284 words
Chapter 2 - MANYAN MATA BOOK 2 BY HADIZA BARAU GIDAN IKO.docx
ya gani yasa ya nemi aure a wurare da yawa ana hana shi, amma da ya zo kan mahaifiyata sai ba a hana shi ba saboda ita dai mahaifiyata marainiya ce wadda bata yi dace da uban riqo na kirki ba.
Ba kuma komai yasa yake gwada mata rashin Imani ba sai don kar ta nemi gadon da mahaifinta ya bar mata wanda ya daxe da cinyewa.
Koda yake ba cinyewa ya yi ba, sai dai yana jin baya iya bata saboda baqin ciki da rashin riqo da zumunci.
Mahaifiyata ta taso cikin wahala da tsantsar maraici, wanda hakan yasa koda mahaifina ya nuna son aurenta ba a ja ba, aka miqa mishi ita. Duk da qaurin sunan da ya yi saboda ko shi da Amaka xamara take suyi dambe ya jibgeta kamar kurar roqo.
Mahaifiyata ta shigo gidan mahaifina da rashin sa’a, domin ko ta gudu ne bata tsira ba, har gara ma ace gara zamanta gidan Kawunta a kan zama da Amaka, saboda ko ba komai jarabar gidan Kawun bata kai xaya bisa goman ta Amaka ba.
Hauka ne kawai Amaka bata yi ba lokacin da Malmo ya auro Binta. Sai dai ta lashi takobin babu Malmo babu shiga xakin Binta, wato don yaga ita bata haihuwa shi yasa ya saka mata da haka.
Cikin sa’a kuwa ta hana Malmo shiga xakin Binta, hakan sai ya yiwa Binta daxi, ko babu komai
zata huta ta kuma sakata ta wala.
Sai dai kuma a gefe xaya bata huta da hidimar gida ba, komai ita take yi. Ranar girkinta tayi komai amma fa bata da miji. Haka ma ranar girkin Amaka ita ke yin komai Amaka ta shige xakin miji.
Mahaifiyata mace ce me tsananin haquri, ban yi zaton da akwai mutum me irin haqurinta ba, in ma akwai shi to sai dai ya zamo na biyunta ba dai na xayanta ba.
Duk irin izayar Amaka bata dame ta ba, kuma komai Amaka ta ce mata ba ta tava musawa, zata ce mata to. Irin wannan zaman bai dame ta ba sai ma ta shiga yin ‘yan sana’o’inta.
Ai ko Allah da ikonShi ya zuba mata nasibi a kan Alkakin da ta soma yi, kan ka ce meye sana’a ta karvu, ta kuma soma siyen kayan xakin da ba a kawo ta da su ba, sai ga xakinta ya yi fes komai ta zuba, ga ‘yan kuxi tana adashe.
Ganin haka kuma sai Amaka ta ce ina wuta ta saka Binta. Wai ai ta rigata zuwa don me zata zo gidanta ta fi ta iyawa? Don haka ta ce ita zata riqa yin Alkakin.
Binta ba ta ja ba ta sakar mata, sai dai in da Gizo ke saqar Amaka bata iya haxin ba, mahaifiyata babu qyashi bare hassada ta koya mata yadda ake yi. Sai dai da yake Amaka irin mutanen ne masu kan dosa ta kasa
riqe yadda ake haxin, sai ya zamo Mahaifiyata ke mata komai, ta kuma siyar mata ta bata kuxinta.
Ganin haka yasa Amaka ta ce zata riqa biyan Mahaifiyata ladar wahalarta, sai dai sai ta jera yi mata aikin wata guda sai da kyar zata bata na kwana uku. Ganin haka yasa ta koma yin qunshi da kitso kasancewarta me son ta dogara da kanta, ko ko rashin gatan da ta taso ne yasa ta koyon sana’o’i? oho!
Sai ya zamo tana samun nasibi fiye da a kan sana’ar Alkakin, kuma ganin haka yasa Amaka cewa wai ana vata mata Alkaki da gashi, don haka sai dai a dakata da
yin kitso har sai ta gama cinikin Alkaki. Kun ji fa! Abinda aikin ma yi mata ake ba tare da tana biya ba. Mahaifiyata ta amsa da to, zata bari.
Ana haka Mahaifina yazo gida da tarin tsaraba, inda idonshi a kan Binta idon Amaka a kanshi. “Meye haka ne Malmo?”
Ya dubeta “Me aka yi?” Ta ce, “Naga kana kallonta?”
“To ba matata ba ce?”
Ta bugi qirji “Iye! Matarka ba? ni ka ke faxawa matarka? Lallai ka cika namiji.” Ta soma zuba ruwan rashin mutunci amma bai tanka mata ba sai ma ficewa da yayi.
Kwananshi shida amma bai koma bakin aiki ba kasancewar ba ya daxewa kwana uku huxu ya koma. Ashe fakaitar idon Amaka yake, ai ko ya yi nasara ya shigo xakin Binta ya isketa tayi wanka tana shafa.
Ta dube shi a ruxe saboda bata tava ganin ya shigo ba. ya shiga duba kayan da ta zuba irinsu ledar qasa da labule, da kujeru.
“A’a, Binta gyara ki ka yi ba ki kira ni na zo na gani ba?” Ya faxa yana zama kan katifarta. Tayi shiru
bata tanka mishi ba saboda tsoron kar Amaka ta same shi a xakinta tayi mata jaraba.
Mata da miji aka ce sai Allah, haka ya shiga lulluveta yana tarairaya har ya yi nasarar samun haxin kanta.
Bayan kwana biyu ya koma bakin aikinshi, inda ya bar kuxin hidimar gida a hannun Amaka, sai dai ran da ba ta so ayi girkin ba sai ta ce kuxin sun qare. Sai ya zamo duk yadda taso taga Binta ta tagayyara sai hakan bai samu ba saboda tana sana’a. Hakan yasa bata rasa abinda zata kai bakin salati ba.
Baba bai waiwayo gida ba sai bayan wata biyu, inda ya iske Binta ba lafiya. Ta tashi zaune da kyar tana yi mishi sannu da zuwa.
“Me ya same ki ne Binta?”
“Zazzavi da ciwon kai.”
Ya dafa goshinta inda ya jiyo zafi rau.
“Bari in samo miki magani a Kyamis.” Ya fita ya dawo da maganin ya bata inda tana sha ta amayo shi. Amai
tamkar zata amaye kayan cikinta.
Amaka ta xago labulen xakin tana duban Malmo da Binta. “Uhum! Dama nasan za’ayi haka, ashe cin amanata ake wato sai da ka saxaxo xakin nan saboda
jarabarka, sannu xan Akuya! Wato sai da ka fakaici idona ta bayan fage ka zo ka tava ta, to zamu haxu ne za ka san cewa iskancina na nan babu inda yaje.”
Ta saki labulen ta koma bakin aikinta. Malmo
bai bi ta kan Amaka ba, ya kwashi Binta zuwa asibiti, inda aka tabbatar da ciki ne gare ta wata biyu.
Yayi farin ciki ba xan kaxan ba, suka juyo gida ya shiga kulawa da ita. Sai ya zamo ko ya tafi ba ya wuce sati yake dawowa.
Amaka bata ankara da cikin ba sai da ya turo riga ta ganshi, ta qura ihu ihun ta shiga uku ta lalace me zata gani? Ciki?
A take rashin haihuwarta ya zamo qaton qalubale a gare ta. Ta ya ya za a zo bayanta a fi ta iyawa? A take Amaka ta tada bori wanda tayi ta watsi da kayan Alkakinta.
Malmo ya fito da nifin sauke mata Aljanun da ke kanta, ya soma sauke mata Aljanun ta hanyar jibgarta.
“Don ubanki baqin ciki ki ke min zan samu magaji saboda ke ba ki yi shegiya duk kin bayar da kanki ga qartin banza sun gama sukurkuta ki. Don kin samu na rufa miki asiri na aure ki shi ne za ki zo ki gallabe ni?
To bari in faxa miki ita xin sabuwarta gal na same ta ke ko fa? Shi ne za ki tada min bori saboda tsabar baqin ciki?”
Ashe borin qarya Amaka take, sai gashi ta sauke Aljanun da ke kanta ta miqe tana aunawa Malmo ashar. Tana faxin.
“Ni ka ke kira da shegiya? Ni ka ke yiwa gorin iskanci? To na rantse sai ka kashe ni yau tunda ka ke faxa min sabuwa gal ka samu waccan shegiyar, na kuma rantse sai na zubar da cikin nan matuqar
nima ba ka yi min ciki ba, na rantse sai dai ka mutu babu magaji don sai na zubar da cikin Binta.”
Suka soma dambe tamkar an buxe musu filin damben. Malmo ya fusata ya ce, “Ashe ko zan kashe ki in kashe banza, don ni ma na rantse sai na kashe ki matuqar wani abu ya samu Binta bare cikinta.”
Sai da suka daku kafin su raba kansu, inda Amaka tasha alwashin ganin bayan cikin Binta. Ai ko tafiyar Malmo ya bata damar shiga xakin Binta da tafkeken
belt
ta soma tsulawa Binta da nufin zubar da cikin.
Binta ta dubeta a tsorace saboda Amaka qatuwa ce irin matan nan maras
fasali.
“Kiyi haquri don Allah.” Ta faxa idonta da ruwan hawaye. “Kina cin amanata kina yin ciki zan yi haquri? Ai sai na rama dukan da Malmo yayi min a kanki.” Haka tayi ta dukan Binta har sai da maqota suka shigo suka qwace ta.
Haka Amaka ta jera kwana uku tana dukan Binta, duk ta fasa mata jiki da duka. Aminiyar Amaka ta shigo wato Meri tana tambayar Amaka.
“Wai ya aka yi ne Amaka?”
“Yo ba ki san abinda tayi min ba? ke wai waccan ‘yar iskar da bata wuce
a qulle a leda ba wai har tasan tayi ciki.”
Meri ta zaro ido “Ciki?” Amaka tayi kwafa ta ce, “Uhum, ai sai naga bayanshi wallahi sai in ni ba jikar Olu ba ce, kuma wallahi nima sai Malmo yayi min ciki ko yana samun zaman lafiya a gidan nan.”
Meri ta qyalqyale da dariya “Yo aka faxa miki shi ke yin cikin?”
Amaka ta ce, “To uban wa ke yi in ba shi ba? ita da yaso tayi cikin ba gashi ya yi mata ba?kowa yana da xanshi ni ban dani…” sai ta fasa kuka. “Wallahi nima sai yayi min cikin nan in ko ba haka ba sai na zubar da cikin Binta.”
Meri ta dubeta ta ce, “To kina aikin me har yayi mata cikin?”
“Yo ina na sani? Sai dai fa ganinta nayi da cikin amma ki bar ni da su.”
BABI NA GOMA
S
ati xaya daidai Malmo ya nufo gida da tarin siyayyar da ya yo wa Binta, haxa kayan shayi, kayan buqata dai rakwacakwam duk cikin tarairayarta.
Ya dubeta ya ce, “Me ya same ki ne a jiki naga shacin duka?”
“Babu komai.” Ta ba shi amsa.
“A’a kar ki voye min Binta, faxa min gaskiya fa. Nasan dukanki Amaka tayi.”
Binta ta ce, “Ka rabu da ita da Allah kar ka ce mata komai…”
“Kar ma Allah yasa ya qyale ni.” Cewar Amaka da ta xaga labulen ta ga abinda ya aje mata a matsayin tsaraba.
“Baqin munafiki, ina nawa kayan shayin?” Maimakon ya bata amsar tambayarta sai cewa ya yi da ita a fusace.
“Me Binta tayi miki ki ka doketa?” shima ya tambayeta.
“Ka manta da nace sai na zubar da tsinannen cikinta? To haka ni ke niyar yi, na kuma rantse ba za ka bar gidannan ba sai kayi min ciki.”
Yayi murmushi ya ce, “Kar fa ki manta Binta sabuwarta gal na sameta, ke ai kin gama zubar da ‘ya’yanki a rariya. Don haka bari in faxa miki, na rantse idan wani abu ya samu Binta da cikinta wallahi sai na qyasta miki ashana in banka miki wuta, kin san
kuma zan iya! Shegiyar mace da bata san rufa mata asiri ake ba.
Duk ranar da ki ka cika ni wallahi zan xauke Binta ne mu tafi mu bar miki gidan matuqar ba ki kauda kanki daga matata ba, ba ki san auren sunna muka yi ba ba na bariki irinki ba?”
Jikin Amaka yayi sanyi don ta tabbatar da zai iya yin abin da ya ce har ma fiye, bisa dole ta ragewa Binta wuri sai dai da burin yi mata kisan mummuqe.
Haka aka yi ta rarrafawa har Allah ya sauki Binta lafiya. Bayan naquda me sauqi ta haifo ni, na shigo duniyar me tarin abubuwa masu yawa. Duniyar da tayi ta dakon isowata
don ta miqo min qaddarorina da ke jirana da na sani na baiwa uwata haquri tun ina ciki
a kan cewa tayi haquri ta kuma taimake ni ta bar Amaka ta zubar da cikina don ta huta nima kuma in kaucewa qaddarar da ke jirana.
Ashe hakan ba me yiwuwa ba ne. Lamarin tun ran gini tun ran zane. Mahaifina ya yi murna ba qarama ba da yazo ya iske ni naxe a cikin zanen goyo.
Kyawu kam tamkar ‘yar tsana, in da kuma Amaka ta fasa kukan baqin ciki, musamman da taga Babana ya yankawa Binta xan Akuya.
Haka ya yi ta hidima har kwana bakwai, inda yaba Innata zavin sunan da take so ta ce mishi ya sa min sunan Mahaifiyarta wato Habiba. Haka kuma aka yi.
Na taso cikin qalubale me yawa, wanda har na shekara goma sha biyu inda kuma Innata bata kuma
haihuwa ba sai da na kai shekara sha biyar kafin ta sake samun wani ciki, inda halinta na haquri bai sauya ba.
Jajircewarta a kan neman na kai bai sauya ba, sai ma wasu abubuwan da ta qara a kai. Ita ta saka ni makaranta take kuma hidimtawa karatun nawa saboda a yanzu Babana har wata uku yake bai zo gida ba, sai dai a ce an ganshi gari kaza, irin su Marabar Jos
, da Tafa, da su Ogyaro
, kai har su Mai Mujiya, Maraxi, da dai duk inda Direbobi ke sheqe ayarsu.
Rayuwa ta juya sosai a gare mu, inda kuma na zamo baiwar Amaka, domin ko
talla ni ke mata tamkar zan tara mata kuxin garin Katsina, inda Mahaifiyata take tata sana’ar
a cikin gida amma ni ina kan titi ina nemawa Amaka kuxi, amma bata cewa komi.
Haka kuma Amaka bata iya kashe min sisinta koda ko ciwo zai kashe ni, bare kuma a ce nayi mata asara! Na dawo Makaranta kenan na iske Amaka ta sauke shinkafa da Doya da miya wan
da zan xauka
talla.
Ko sallah ban idar ba ta soma kwaxa min kira tamkar makauniya, nayi banza da ita ta qaraci kiraye-kirayenta. Na fito ina zuto baki “Ga ni.” Ta dube ni “Don ubanki ba ki san tun xazu ni ke jiranki
ki dawo ki fidda min abinci ba?”
Na xauki abincin wanda ta koma yi min zube akasin da da take kasa min na nufi Qofar Soro inda ni ke saida abincin.
A kullum
idan zan tafi talla sai Innata ta ja kunnena a kan in kama kaina kar in yarda ko maganar banza ayi
min. Tun ina jin nasihar tata a bayan kunnena har na riqeta ram a raina.
Don haka bana wasa da kowa, idan za ka siyi abinci ka siya, idan ba za ka siya ba to kama gabanka kawai.
Na isa Qofar Soro in da muke haxuwa da Bilkisu, da Maijidda, suma duk abincin suke siyarwa, sai dai wani ikon Allah ko sun riga ni zuwa to sai na saida ko za su saida, har ta kai suna cewa wai saboda kyawuna wasu ke siyen abincin.
To ko hakanne ko ba haka ba? Allah Shi ya barwa kanShi sani. Na gama
siyar da abincin tas nayi nufin wucewa gida inda wani me Mashin ya banke wani Matashi har ya ji ciwo a qafa aka taru ana kallo, in da har ta kai an xauko Xansanda.
Abin da na tsana kenan Xansanda. Shi wanda aka banken ya ce babu komai ya yafe amma wai sai Xansandar nan ya ce su basu yafe ba sai anje chaji ofis xinsu, Mai mashin xin ya haxa kuxin da ke aljihunshi ya miqa wa Xansandan nan amma ya ce ba zai amsa ba sai in sun kai dubu xaya.
Aka yi ta ba shi haquri har da haxa shi da girman Annabi amma ya kafe bisa dole wani mutum ya zaro dubu xaya ya bashi kafin a kashe kyas xin.
Tun daga wannan rana na tsani Xansanda, dama can ba wani kwarjini gare su wurina ba. Wai ashe ni ina can wurin kallo har an zuge min Jaka an zare ‘yan kuxin sai da nazo gida na zuge Jaka kuxi suka ce xauke mu inda ki ka aje
.
Amaka ta dube ni a sheqe ta ce, “Ke ‘yar duniya! Ni uwarki ma kar ni ke kallonta bare ke da ta haifo bayan ta saci kwanana!
F
ito
min da kuxina in dai kina son zamanki lafiya.”
Na soma rantse mata a kan zubewa suka yi, kawai sai ji nayi ta falla min mari, kafin ta soma jibgata, ta kuma haye kaina wai in ji nauyinta. Sai da ta tabbatar na daku kafin ta qyale ni da sharaxin idan Baba ya zo sai ya biya ta.
Kwana biyu ban je talla ba, sai a cikon na uku inda nayi tsalle na dire na ce ba zan je ba. Inna ta dube ni ta ce, “Me yasa Beeba?” Na ce “To Inna kina kallo fa sai walaha ni ke yi amma ba a bani komai, kuma idan nayi kuskure a dake ni…”
“To uwarki ma bata isa in ce eh ta ce a’a ba, talla kuma sai kin je ta ba asara ba, kuma ko da kuxina na duba naga ba su cika ba sai jikinki ya baki labari.”
Inna ta rarrashe ni a kan cewa Amaka uwata ce in je duk abinda ta sani. Na ce mata to, na xauki abinci na nufi Qofar Soro, inda muka yi ta maida batun Xansandan nan inda naji tsanar Xansanda ba kaxan ba.
Na farko dai dama ba sonsu ni ke ba, na biyu kuma Xansanda ya yi rashin mutunci a kan idona sai ga asarar kuxin da nayi sanadin faxan Xansanda.
Naja tsaki na dubi Maijidda na ce, “Wallahi babu abin da na tsana a duniya irin Xansanda, dama can ba sonsa ni ke ba.” Na haxa da wulwulo ashariya na antaka musu.
Wani matashin saurayi da ban kula yana kusa da mu ba ya ce “Ke ko ‘yanmata me Xansanda ya yi miki haka, ba ki ji ana faxar Xansanda abokin kowa ba…”
“Allah Ya sauwaqe, ai Xansanda ko abokinshi sai ya cuta, shi yasa aka xinka musu baqaqen kaya saboda baqin halinsu.” Yayi murmushi “Lallai kin yi