Showing 21001 words to 24000 words out of 35284 words
Chapter 8 - MANYAN MATA BOOK 2 BY HADIZA BARAU GIDAN IKO.docx
a yanzu tunda ya makance ina ga rabuwa ita tafi maslaha! Ina mamakin yadda ki ke rayuwa cikin wannan gidan, irinki bai kamata ta rayu cikin rashi da talauci ba. Don haka nayi miki tanadi na kyakkyawar rayuwa a gidana matuqar na aure ki za ki san kin shigo duniyar nan da qafar dama.
Ki dubi Tamadina matata, motocinta uku, zinari kuwa ita kanta ba ta san iyakar waxanda ke gare ta ba. ke xin kuma ina sonki fiye da Tamadina, don in har ba ki son zama da ita to wallahi zan saketa duk da ba gida xaya zan haxa ku ba.
Don haka bari in bar ki kiyi shawara, abinda ki ka yanke ki sanar da ni.” Ya miqe ya bar gidan inda kuka ya rikito min, nayi saurin toshe bakina don kar in tashi Zainal ya kuma nemi ba’asin kukan.
Sai dai ashe tuni na makara sai ganin shi nayi ya fito yana dafa bango. Da sauri na tare shi ina tambayar. “Me ka ke so Abidin?” Na faxa da dasasshiyar murya.
Ya riqo hannuna “Me yake faruwa Beeba?” Hawaye ya sake ciko idona. To me zan ce mishi? Qarya zan shara mishi ko ko faxar gaskiya? Na rasa abu xaya cikin biyun da zan faxa mishi.
Ya soma rarrashina yana faxin “Komai ki ka ga ya samu bawa to dama can rubutacce ne ba zai kuskure ba, in don matsalata ce ke sa ki kuka to taho in faxa miki
nayi mafarkin a yanzu an faxa min surar da za ki karanta min da yardar Allah ganina
zai dawo.”
Na zuba mishi ido ina fatan hakan. “Faxa min ita in yi maka Abidin.” Ya ce, “Kiyi Basmala sai ki karanta Marhabib bi zikirillahi Ta Allah Qurratu a’ayununa bika Ya Rasulillah (S.A.W)’ sai ki tofa a ruwa sai ki wanke min idona, haka za ki yi min har tsawon kwana talatin insha Allahu idona zai koma gani.”
Na ce, “Allah Ya sa hakan don Annabi.” Haka na hardace wannan addu’a da aka sanar da shi a mafarki, kullum sau uku a gefe xaya kuma ina cikin tsaka me wuyar fita a kan garnaqaqin Alhaji Bangis.
Ya zama dole in sanar da Zainal Abidin amma kuma ta ina? Kuma ta ya ya? Kwana biyar da faruwar hakan Kabir qanin Zainal Abidin ya zo ya xauke shi don zuwa wata gaisuwa ta wani xan uwar Hajiyarsu.
Fitarsu kenan ya shigo inda na lashi takobin qare mishi rashin mutunci matuqar ya sake faxa min wata magana da ta danganci wadda ya faxa min kwanaki, sai kuma na gano ya fi kwalba sharri, zai iya mayar da allura garma a gare ni, in lallava shi kawai mu rabu lafiya.
“Me ki ka yanke a kai Habiba? Idan kuma kina son mijinki to babu damuwa zan fidda shi waje ayi mishi magani ya dawo ganinshi, in yaso sai ki san yadda za ki yi da ni. Idan za ki rabu da shi ki aure ni correct!
Idan kuma za ki raba mana kwana ne sai in aminta amma dai ni nafi buqatar aurenki.” Na dube shi kamar
ya ya in raba muku kwana?” “Eh ina nufin idan ya tafi aikin kwana ni sai in maye gurbinshi.”
“To ita kuma matarka ka faxa mata me a kan rashin kwana gida?”
“Ba zai zamo matsala ba, don nayi hakan. Ina iya sakinta don ni a yanzu komai zata yi min a matsayinke ni ke kallonta. Har xaki
na da take zuwa a matsayin ke ni ke kallonta.”
Gabana ya yi bala’in faxuwa jin abin da ya faxa. Ashe ni ban sani ba yana can ya gama baddala ni a zuciyarshi har yana kallon matarshi a matsayin ni.
Na dube shi na ce, “Don Allah kai ko musulmi ne?” Yayi murmushi “Qwarai kuwa, duk asalinmu ba mu tava maguzawa ba, bare arnan Tsumburbura na kan dutse.”
Na ce, “To amma gaskiya ba ka san abin da musuluncin ya sharxanta ga mabiyansa ba.” Ya zuba min ido yana kallo. “To ko ma dai meye na roqe ka ka fita harkata kar ka sake kallona da wata manufa fa ce ta matar yaronka
.
A da me ka ke zato idan mijina ya ji wannan kafircin da dabbancin? To ina so Zainal Abidin ya yi ta ganin mutuncinka har Ubangiji ya tashi qiyamarshi, domin ko ni girmanka ya zube a idanuna.
Kayi min faxuwar baqar tasa, har abada ba zan tava mantawa ba. haqiqa nayi zaton alheri a kanka a kan irin xawainiyar da kayi mana ashe da manufa kayi hakan, to mun gode ni dai ba s
ake amsar wani abu naka ba, ba
kuma zan hana Zainal Abidin ya karva ba, don ba zan iya faxar abin da ka faxa min ba.
Zan rufe wannan sirrin sai fa in kai ne ka so in buxe, don haka tashi ka fita in kuma ba haka ba wallahi zan taka har gida in faxawa matarka komai.”
Ya miqe yana murmushi har da kai hannu a kan fuskata yana shirin shafawa, nayi saurin ja baya inda ya sako min
kiss
ta hannunshi ya jeho min “Sai na cika burina a kanki Habiba, daga yau zan xana miki tarko!” Ya fice ya bar ni ina kokawa da numfashi.
Anya ko zan iya rufewa Zainal Abidin wannan maganar
? To in na faxa xin in ce me? Allah don arzikin Annabi kar ka bar mutumin can ya yi nasara a gare mu.” Na rufe bakina a kan in sanar da mijina, ashe kuskuren farko kenan da na soma tafkawa.
Muka ci gaba da rayuwa ni dai cikin zullumin tarkon da mutumin can zai xana min ni ke, don ban san kowane iri ba ne. Babban farin cikina shi ne cikar kwana talatin da fara addu’a ga idon Zainal Abidin ya wayi gari ganinshi ya dawo.
Murnata bata voyu ba, na rungume shi ina kuka me zan ce wa Ubangiji a kan xaukinShi gare mu? Muyi salati ga fiyayyen halitta ina jin shima godiya ce.
Haka muka kasance cikin murna da godewa Mai duka Allah, Hajiya Tamadina ta shigo yiwa Zainal barka da arziki
, inda muka gaisa ba yabo
ba fallasa, ba kamar da ba inda na shinshina matsalar.
Sai dai ni da aka yi
wa laifi ban sha qamshi ba sai ita da ya ci in xaukewa kai? muka gama gaisawa tayi mana barka ta fice tana min kallon uku saura kwata.
Na bita da kallon nafi qarfin ki
taka ni ke da shegen mijinki me halin xan akuya. Nayi zaton mijin nata zai shigo ya yi mana barka amma shiru wai ashe ba ya gari. Sai da ya dawo inda ya zo ya yi wa Zainal Abidin barka.
A ranar ne kuma na jiyo hayaniya a gidan wadda ban san ko me ya haxa ba har sai da Tamadina tayi yajin kwana biyu kafin ta dawo, wai ashe duk a kaina suke ta tafka rigima.
Tuni Zainal ya koma bakin aikinshi inda na yaye Umar wanda Hajiya ta ce mu bata shi yaye, muka kuma bata sai dai shaquwar da ke tsakaninsu da Yusuf kasancewar sun zamo tamkar ‘yan biyu yasa Yusuf xin kukan rashin Umar xin.
Hajiya ta ce, a kawo Yusuf xin don haka ta riqe Yusuf da Umar xin, har a yanzu xin nan suna hannunta duk da ban san ko a yaya suke ba.
Rayuwa ta buxe mana wani shafi me daxi kasancewar hankalinmu a kwance sai zuba soyayyarmu
muke ni da Zainal Abidin, inda a gefe xaya ina ta sana’ar qunshi da kitso har ma ni kan karvi aikin Alkaki musamman na biki ko suna, sai ya zamo dai bani da wata matsala.
BABI NA SHA HUXU
“K
a ce min ya warke makanta Bangis?” Mits! Ya ja tsaki “Ina dawowa fa Yusra take faxa min mijin Aunty Beeba ya warke! Ban tabbatar ba sai da naje gidan, abin da ya bani haushi da takaici bai wuce iske shi maqale da Beeba a qirji ba, gaba xaya naji duniyar ta ishe ni.”
“A’a bata ishe ka ba abokina, ai sai da na ce kawar da shi kawai ya kamata ayi ka ce wai ba ka son kisa a cikin lamarin, to ina me tabbatar maka shi ya kusa kashe ka.
Ya zuba wa Barden ido, “Yanzu ka san abin da za’a yi?” Ya ce, “Sai ka faxa.” Barde ya ce, “Kawo kunnenka ka ji.” Ya yi mishi raxa inda suka qyalqyale da dariya.
“Shegen sama kenan, lallai Barde ka san takan cuta da mugunta.” “To duniyar ce sai da haka.” da haka suka rabu.
Ina kwance kan kujera (Three seater) na jiyo wayata na qara, na miqe na xauko inda nayi arba da baquwar lamba, kamar ba zan xauka ba sai kuma na tuna ban san me kiran ba.
Ina xauka naji muryar mace tana sanar da ni in zo (Liyafa Palace) in ga abin mamaki. Wai Zainal ne ya kama wa karuwarshi xaki a Hotel! Tana gama faxar haka ta datse kiran.
To wace ce wannan xin da ta kira ni? Gabana ya amsa da jin cewa wai Zainal ne ya kama wa karuwa xaki a hotel! Haka na yini cikin sanyin jiki inda sai dare ya dawo akasin qarfe huxu ko biyar.
A take zuciyata ta yarda da abinda aka sanar da ni, sai dai duk yadda na so in share shi abin ya faskara. Ya shafi fuskata ya ce, “Me
ye Beebata?” “Babu komi.” Na bashi amsa. “Ban yarda ba, ko kewar yara ki ke?” “A’a.” Na faxa. Ya ce, “To faxa min abin da ke damunki.” Kai tsaye na ce, “Bana son kana daxewa waje.”
“Ayya, ban so haka ba nima wani cas muka tsaya amma ba zan sake ba.” Ya faxa yana haxa tsinin hancinshi da nawa. Na bar komai ya wuce saboda har ga Allah ina qaunar Zainil Abidin, shi yasa ko ya yi min laifi ba ni damuwa sosai.
Tsawon sati biyu da yin haka yana zaune wurin aiki saqo ya shigo wayarshi, inda saqon ke cewa
‘Ka zo gida kaga irin varnar da matarka ke aikatawa yanzu.’
Ya kira lambar da ta turo mishi saqon amma a kashe. Don haka sai ya miqe ya nufo gida inda yana zuwa motar na barin qofar gidanshi, ya bi motar da kallo kasancewarta me baqin gilas.
Ya dubi lambar motar a take ya hardace. Ya shiga gida gabanshi na sarawa saboda shi bai kawo ganin wani ba abinda ya yi zato ko faxa ake da ni. Ya shigo ina kwance kan gado ina barci ya dube ni ya dubi
Gadon wanda ya yamutse ga kaina da babu dankwali, gashina ya hargitse.
A take ya gano varnar da ake cewa ina yi. Ya zuba min ido zuciyarshi a ruxe sai dai da yake mutum ne me yin uzuri idan yana son gano gaskiya koda ranshi ya vaci ba zai nuna ba.
Ya tashe ni na buxe ido ina kallonshi “Yaushe ka shigo ban ji ba?” Na faxa ina kallonshi. “Yanzu na shigo kina barci, me yasa ba ki rufe gidan ba da za ki kwanta?” Ya yi hakan don ya tabbatar da abinda aka faxa mishi
.
Abu ga qwararren Xansanda mai basira. Na dubi littafin da ke hannuna wanda ya suvuce min ya faxi, saboda ina cikin karatu baccin ya xauke ni. Na ce mishi “Wallahi karatu ni ke bacci ya sace ni, dubi littafin ban san ya faxi ba.”
Ya xauko littafin ya miqo min “Ki riqa rufewa idan za ki yi barci, don kar a shigo
a satar miki wani abu.” Na amsa ina tambayar shi mantuwa ya yi? Ya ce, “A’a wanka zai yi.” Na haxa mishi ruwa ya yi wanka ya koma aiki, ya bar hakan a matsayin idan halina ne zai kama ni da hannunshi.
Sati biyu da yin haka ya dawo aiki, Bangis ya tare shi da wani zancen. “Yauwa Zainal, dama ina son ganinka shigo
sit room
xina muyi magana.”
Ya dube shi ya ce, “Gaskiya ba zan voye maka ba, matarka ba mutuniyar kirki ba ce, ban so na faxa maka halin da take ciki ba, sai don nuna min da tayi ita xin
bata tsoron Allah, in ba rashin tsoron Allah ba ta ya ya zata dube ni ta ce min wai ba ka gamsar da ita?
Ni fa a matsayin Yayanka ni ke, amma ta iya duban idona ta faxa min wannan maganar. Ba ma wannan ne abinda yafi vata min rai ba irin yadda ta nuna son yi min fyaxe, wai in taimake ta in biya mata buqatar da kai ka kasa biya mata.
Wallahi da ina da iko da tuni na raba aurenku, don gudun ta kawo maka ‘ya’yan wani a zuwan naka, kuma tunda ta fara haka to rabuwa da ita tafi alheri.
Don haka shawarar da zan ba ka ita ce, ban ce ka binciketa ba, ka bar ta da halinta illa ka rubuta takardar saki uku ka bata, ni kuma nayi maka alqawarin aura maka mata huxu tunda ta nuna bata muradin zama da kai da son tona asirinka, kaga kenan
ba matar rufin asiri ba ce.”
Zainal Abidin ya yi shiru yana nazartar maganganun Alh. Bashir Bangis. Ya dube shi ya ce, “Amma Alhaji yaushe ne hakan ta faru donni kaina naga wasu abubuwan da nike zargin me suke nufi?
Ba zai wuce sati biyu ba.
Nayi zaton sharrin shaixan ne shi yasa ban faxa maka ba, amma sai ya zamo na lura da irin yadda maza suka maida gidanka wani dandali na taruwar maza tamkar gidan karuwai, kana fita aiki maza za su fara sintiri, wannan mota ta aje ta, wancan ta xauka, wasu ma a cikin gidanka za su sheqe ayarsu da matarka.
Ganin ba ka san abin da ke faruwa ba yasa naga gara in sanar da kai, duk da na ji maka haushi a kan rashin sa’ar da kayi, amma dai yanzu ba wani tone-tone za ka tsaya ba, ka rabu da ita kawai ni zan yi maka aure.”
“Na gode sosai Alhaji da ka ankarar da ni abin da ka iya cutar da ni.” Suka yi sallama, Bangis na qyalqyala mishi dariya.
Kwana uku a jere ina lura da Zainal Abidin kamar wani abu na damunshi. Na riqo hannunshi “Kamar wani abu na damunka
Abban Faruq.”
Ya zuba min ido yana kallona, na hure idon. Yayi wani busasshen murmushi “Yaushe rabon da ki ga Alhaji Bashir Bangis?” Ya jeho min tambaya, gabana ya bada dum! Na dube shi na ce, “Wani abu ya ce maka?”
Ganin irin firgitar da nayi yasa ya xora ayar tambaya a kaina. Ya sake maimaita min tambayar, na amsa mishi da “Gaskiya tun lokacin da ya zo maka barkar idonka.” Ya kaxa kanshi.
“Kun tava yin wata magana da shi?” Na ida rikicewa har na kasa riqe kaina.
“Me ya faxawa Zainal xin? Kar fa ya soma xana min tarkon da ya
faxa min?”
Na kaxa kaina alamar “Eh, mun yi magana.” Sai yau na tabbatar da ba qaramin kuskure nayi ba a kan rashin faxawa Zainal Abidin abin da ya faru tsakanina da Bangis ba.
Ya zuba min ido yana kallona kafin ya ce, “Me ya faru ne Beeba?” Na dube shi na ce, “Haqiqa nayi kuskure da ban sanar da kai tun farko ba. Abin da ya faru ko a kan ciwon idonka ne, inda ya ce min ba za ka tava warkewa ba, ni kuma bai dace in qare rayuwata a yi maka jagora ba, abin da yafi mu rabu in auri me ido kai ma ka auri makauniya!”
A take ya gano wani abu a kan Alh. Bashir Bangis, tuno ya so xora ayar tambaya a kan shi saboda yawan kama shi da kallon Beeba da yake, sai ga shi maganganun masu kama xaya sun fito daga bakin matarshi, ta ce mata da ya yi su rabu kamar yadda ya ce mishi ya sake ta har ma yana mishi alqawarin aura mishi mata huxu.
To me hakan ya ke nufi? Ba ma wannan ba, meye alaqar hakan da turo mishi saqon matarshi na aikata varna? Da yake Xansanda ne me hikimar aikinshi da ya haxa zaruruwan labarin sai suka ba shi zare xaya.
Hawaye ya biyo fuskata. “Kayi haquri da rashin faxa maka da ban yi ba, nayi hakan ne don rufe asirinshi saboda naga kana girmama shi bana son kuma girmanshi ya zube ko don alherin da ya yi mana, na kuma tabbatar mishi da za ka shiga halin da ya fi haka ina tare da kai.”
Ya share min hawaye yana faxin “Daina kuka Beeba, na san abin da hakan yake nufi, sonki yake yi shi yasa yake ganin zai yi nasarar raba mu bai san haxin Allah ne ba. Sai dai ina so idan irin haka ta faru
ki bar voye min, ki riqa faxa min don in san da abin.” Na amsa da “To.”
Duk da Zainal Abidin bai faxa min abinda Bangis ya faxa mishi a kaina ba, na san tarkon da ya faxa ne ya soma qulla min mugun qulli, sai nayi addu’a Allah ya kare mu daga sharrin shi.
Sati uku da yin haka aka turo min saqon ga mijina a hotel zai yi wa karuwarshi
birthday
, na kira layin da ya turo min saqon amma a kashe.
Misalin uku da rabi sai ga Zainil Abidin ya dawo, akasin lokacin da yake dawowa huxu da rabi ko biyar. Na dube shi ina murmushi “Har an gama
birthday
xin?”
Ya dube ni yana murmushi “Wa ake yi wa
Birthday
?’ Na nuna mishi saqon da aka turo min, ya karanta yana murmushi ya dubi lambar, ya zaro wayarshi ya duba saqonnin da ake turo mishi a kaina, inda ya gane mutum xaya ne me aikin.
Ya miqo min wayarshi “Duba ki ga abin da nima ake turo min a kanki.” Na duba inda na jinjina wa haqurin Zainal Abidin, don