Showing 1 words to 3000 words out of 33160 words
Chapter 1 - MIJIN TACE 4 COMPLETE HAUSA NOVEL BY SODANGI.txt
MIJIN TACE
4
NA
HAJ. HAFSAT C. SODANGI
(Mrs. Yunus Abdullahi Dabai)
1
GODIYA
Godiyar ga Allah take, Subhanahu wata'ala,
Masanin yau da gobe, Gwani Mai Hikima, wanda
yayi halitta tasa duka bibiyu, mace da namiji, ya
kuma halicci mutum da aljan don su bauta mishi.
Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga
cikamakin Annabawa Shugaban Manzanni, Annabin
tsira, Annabin karshe Muhammad (S.A.W), da
Alayensaa da Sahabbansa, da wadanda suka bi ma
tafarkinsa na gaskiya har zuwa ranar karshe
AIkiyama.
Bayan haka, ina mika godiyata ga Makaranta
littattafaina, wadanda kullum sakonninsu basu
yankewa a gare ni, suke ma kara min hima wajen
ganin na fiddo musu da sabbin takardu.
Na gode da hakurinku a kaina, na kuma gode da
kulawarku kan rubutuna. Ubangiji ya saka muku da
mafificin sakamako.
Na gode.
Hafsat Chindo Sodangi
17/1/2013
2
SADAUKARWA
Sadaukarwar kullum ta Iyayena ne saboda kulawarsu
da tarbiyarsu a gare ni.
Alhaji Chindo Muhammad Sodangi, da Hajiya
Fatima C. Sodangi, Allah ya saka muku da mafificin
sakamakonsą, amin.
TUKUICI
Tukuicin littafin na dangin miji ne, Jama'ar Dabai.
Na gode.
JINJINA
Jinjinar taka ce
Muhammad Kabir Sodangi
(A.T.B.U Bauchi)
FATAN ALHERI GA
Sha'awa Kabiru Mamman Namani Tsafe
Da
Halima Ibrahim Dogarai
(Dauravwa S.P.S Primary School)
Da
Asiya Sani Yashe (Mrs Mustafa Marafa, Gusauu
Zamfa State)
Da
Hajara A.S Mai Salati Niger
Badi'atu Dr. Yusuf Dan Sadau
3
Amina Ibrahi Farouk
(Mrs Magaji Abdussalami Majia)
Dukkan ku na gode da kulawarku.
KUNA RAINA
Ubaidah Ladan Sokoto
Wasila Mahmud Kano
Mariya Aliyu
Halima Adam Kwayakusur
Karimatu Gamawa
Aisha Muhammad Jikamshi
Amina Ahmad Baballe
Umahmah Abdullahi Gusau, Zamfara
Abidah Kabir Usman Bauchi
Maryam Abdussalai Kabara
Dukkanku ina yi muku fatan alheri tare da iyalanku
baki daya, na gode.
GAISUWAR SADA ZUMUNCI GA
Ga Sister Baturiya Yar'adua
Psychiatric Hospital Katsina.
Na gode
YABO
Yabon naki ne
Hajiya Iyatu Abba (B.R.C) Bauchi
4
GODIYA
Ga Dr. Zayyanatu Ahmad
GAISUWAR BAN GIRMA
Ga dan uwana
, Mallam Jibrin Adam Sodangi
Da iyalanshi, Ubangiji ya saka maka da alherinsa kan
zumuncika, amin.
FADAKARWA
Litattafan Sodangi basa mufin habaici ko yi da
wani, an rubuta su ne kawai don fadakarwa,
nishadanmtarwa da taya hira, ana neman afuwa ga duk
wanda yaga wani abu. a ciki yayi daidai ko shigen
kama da abin da ya, shafe shi, bs da shi din ake ba
dace ne kawai. Na gode.
Fatan alheri gare ku dukkamku
Hajiya Hafsat C. Sodangi
2/4/2013
22/5/1433 Hijrah
Littattafan SODANGH
1- Uwar Miji
-Naga Ta Kaina
- Wayyo Duniya
- Rabon Kwado...
ikar Alkawari 1
-Tabbataccen Alamari
-Yi wa Wani.."
-Abu Naka.
Nufin Allah
-Garin Banza..
-Gani Gare Ka
- Me Za Mu Ce Da Maza?
- Biyan Bukatar Rai
- Kif Na Ganinka..
-Da Kamar Wuya...
- Daga Kin Gasciya...
- Shamaki
- Mai Uwa..
- Hattara
Mata Da Kicin Dinsu
- Mata Masu Duniya
- Duk Daya
Kyautata
- Ayi Dai Mu Gani,..
Wacece Ni?
-Wata Fuskar...
- Mijin-Tace
6
MIJIN-TACE 4
Gari ya gama wayewa ne kawai a cikin gida ni
da Ado muka ga gaba daya cewar jiya da
daddare Ado da Goggo Ayalle sunyi kaca-kaca akan
kawai ta gaya wa Humairah gaskiya.
In ban da ma ita Goggó ta nuna halin girma, bata
tanka wa maganganun nashi ba watakila da dukan
tsiya ya nada mata.
Baba Tanimu da kanshi a wannan lokacin salati
yake yi, yana karawa, tare da kanbama al'amarin, sai
fadi yake yi "Lalle al'amarin Adamu akar wannan
yarinyar ya wuce yanda duk ake zato."
Sai yada wannan maganar ake yi, Goggo Ayalle
tana ji ta ki yarda ta dubi girman sheckarunta ta gyara
al'amarin, ni na yarda ta fadi gaskiyar abinda ya faru
kar ta rufe komai, yafi min sauki kan ace wai Ado ya
zage ta a kaina, wai har mą in ban da tayi shira da
dukd ya nada mata.
Cikin zuciyata ha ce, watakila ma dai dama
itama Goggon dan kiris take jira da ni.
Tuni matan gida suka mike tsaye suna ta aikéwa
'ya' yan gidän mata da suke aure a wastu gidaje da
labarin abin da suka ce wai ya faru.
Ita kuwa Goggo tayi kwanciyarta a daki ko
kosan ranar bata fito tayi ba, wai ba za ta iya ba sai
Ruwaila ce tazo ta dauki kullin ta soya, wai don kar
7
abar shi ya lalace.
Ni kam ina kwance 1amo akan gado, in ban da
kuka babu abinda nake yi, ana cikin haka naga Ado
ya shigo dakin, ko kallon inda Goggon take bai yi ba,
ya ce min tashi Humairah tashi ki koma dakinki"
Ban motsa daga yanayin kwanciyar tawa ba, ban
ma so ya shigo in da nake ba, balle yazo yana yi min
wata magana ba tare da ya kula da Goggo Ayalle me
dakin ba, tashi mana. Hanmu biyu ya saka ya đauko
ni ya saukar dani, alamar zai iya daukana ya fidda ni .
in ma ban yi hakan ba.
Na kalli in da Goggo ke kwance, na gaishcta
idonta a rufe bata amsa ba, wai ita a dole bacci take
yi.
Tasa ni a gaba yayi ya kai ni wurinmu, sa bamu
ki share hawayenki, kerin sake-ganin zubarsu, in ba
so ki ke gaba daya ratimu ya baci ba, ka sani da baka
yi mata magana ba. '
Shhhhhhh! Ya dora dan yatshinšhi a lebenshi ya
fitar da sautin alanar kashedi na' kar in sake furta
mishi wannan maganar.
Sa kai yayi ya ita ya bar ni bayan yasan nayi
wanka ya tasa ni a gaba sai da yaga nayi shafa na
gyara jikina na sanya atamfata mai kyau na kuma
shiga dakin dahuwarmu wanda na same shi a gyare
tas, na kama aikin girka mana abincin da zamu ci.
Amma dai ni kam yi kawai nake yi, amma ni
8
kadai nasan yanda zuciyata take ciki gace da tsoron
abin da zai faru, duk da dai Adon yayi tayi min
kashedin wai kar in tsorata, yana kallon duk abin da
ake yi babu kuma abin da zai same ni.
Kan ka ce meye wannan? Matan gida suka hadu
akan sai an kama ni an dana min duka ne zai sa in
natsu in shiga hankalina, in daina kwasar maganar
mutane ina gayawa mijina, ina bata tsakaninshi da
'yan uwanshi.
Na shiga tsakaninshi da Hajiya Majadan ta
hakura dashi ta bar min shi, to su ba zan shiga
tsakaninsu da shi su hakura dashi su bar min shi ba,
maganina kawai zasu yi.
A wannan lokacin na kai matuka wajen tsorata,
ba wai dukan da zasu yi min din ne yafi tsorata ni ba,
a'a! abin da zai faru tsakanin Ado da masu zuwa
dukan nawa ne yafi zamo min abin tsoro, gashi kuma
ya tattara komai ya dora laifinshi akan Ruwailah, duk
da har zuwa yanzunnan babu wanda ya ji bakinta a
ciki.
Baba Tanimu ne ya hana yunkurin dukan nawa
da aka yi bisa dalilin da ya basu na ccwar shia
matsayinshi na babba, yana gida bai kamata ya bari
ayi abu na rashin hankali irin wannan ba.
Adau dai dan shi ne da dan uwanshi ya baifa ya
bar mishi, don haka ba zai yarda a raba shi da shi ba,
tunda kuwa abin yazo kan iyalinsti, to ai gab yake da
9
isowa kan shi, ko ma ya ce ya iso.
Don haka abar mishi lamarin kawai a hannunshi
a ga abin da zai yi, gaba daya suka amsa haka ne
Baba, haka ne.
Adamu ka ai bai taba sabawa da kowa ba, gaba
daya dangi da 'yan uwa kowa nashi ne, sai a wannan
lokacin a sanadin matarshi yanzu tsakaninshi da
Jafaru basa wata mu'amallah.
Shi da matar Jafaru kuwa Ruwaila basa ko ga
maciji, da ya ba, 'ya'yan Jafaru wani abu su anfana
dashi gara ya baiwa na waje da bai hada komai da su
ba, ai kuwa da magana suka ce kwarai Baba.
Duk wannan karin bayanin da na ji na Baban
yana yi musu ne, a zuciyata na ce uh'uh hun! Baba
ashe kaima "MIJIN-TACE' ne, wannan lokacin ne na
kara yarda da maganar Ado.
Tun kafin yamma tayi kuwa sai naji Babà yana yi
wa Ado magana, kan yaje ya duba wasu yanmata da
suke wasu gidaje da ya gaya mishi su.
Ina jin Adon yana ce mishi ni da ba ni da daki
Baba in naje naga yarinya aka ce an bani ita ina zaan
sa ta? A dai yi min hakuri kadan in samu in gina 'yan
dakuna koda biyu ne.
Da daddare muna tare da shi nayi wanka nayi
kwalliya da sabbin rigunan baccin da na tarar ya tara
a dakin don in sa shi ya ji dadi, duk da nasan cikin
6acin rai na wuni, amma nasan bai kai nashi ba,
10
tunda sau biyu ina jin shi yana tarmbayata.
Anya ca namiji yana da ranar da yake fita daga
maraicin wa kuwa Humaira? Na kalle shi cikin
natsuwa aa ce mishi, "Yana fita niana." Ya sake
kallona ya ce anya?
Sanin yana cikin wani hali da kua jin maganar
Baba Tanimu da na yi ya kara sa ni fahimtar Goggo
Ayalle ta niyyar taimakon surukarta a kaina ne,
yasa tusawa mijinta wasu maganganu.
Musamnan da yake rashir shirin Ado da
Ruwailah ya haifar da koma bayan mu'mamallah
tsakaninshi da Yaya Jafaru, tunda shi ma wata kila
tana gaya mishi wani abuu yana dauka.
Gyara yarinyar nayi tsaf, hayan nayi mata wanka
na gasa mata jiki don taji dumi tayi bacci mai nauyi
tun akan 'ya'yan da Innata take haifa na koyi
wannan.
Na kaita can gefen katifa ta karshe na kwantar da
ita, na lullube ta na daw0 na samu Ado a inda yake
zaune, ya mike kafarshi guda daya ya kuma tsayar da
guda daya ya tsaida gwiwan hannunshi akai don ya ji
dadin dafe goshinshi da tafin hannun nashi.
Na matsa jikinshi na jingina kaina da kirjinshi
nasa hannu ina cire mishi botin din da ke jikin T-shirt
din shi. Zubo idanuwanshi akan fuskata cikin murya
mai sanyi ya ce min a bacin ran abin da 'van wauna
suka yi mi a gidan nan yau Humaira har za ki iya
11
kulawa dani ki bani lokacinki?
Na kalle shi cikin natsuwa, sannu a hankali na
sakar mishi lallausan murmushi, don in samu damar
isar da sakon da nake son isarwa zuciyarshi, don
kuwa na nga na yi niyyar rike mijina a hannuna.
Na sani babu abin da zai farantawa Mama rai irin
ta ganni a gida babu auren Ado a kaina, ace mata
yan uwanshi ma'ana dangin ubanshi nc suka yi
nasarar raba ni da shi.
Yan uwanmu ne dukanmu kawu, ba 'yan
uwanka ba ne kai kadai, don sunyi mana wani abin
da bai yi daidai ba ba zai hana ka samun lokacina ba,
kai mijina ne.
Kai ne kuma mafi darajar mutancn yanzu a
wurina, ina kuma sonka. Ban taba furtawa Ado irin
wadannan kalaman ba, ban taba kallon idonshi na
furta mishi wata kala ta nuna kauna ko mihimmancin
a wurina haka ba.
Don haka maganar ta shige shi da kyau, abin da
kuma dama nake son gani kenan.
Humaira! ya fadi sunan cikin wani yanayi, yaja
bakinshi yayi shiru, wata kila saboda ya rasa kalmar
da zai gaya min, ina sonka kawu, na sake furta mishi
kalmar.
Jikin Ado ya dauki rawa, tanfar dai wani irin
tsimi aka bashi, nayi amfani da damar da na samu
wajen yi mishi abinda ya dace in yi saboda in kara
12
mallake abinda yake dama nawa ne.
Lokaci mai tsawo muka dauka ni dashi cikin
wani irin yanayin da ba zai yiwu in kwatanta shi ba,
sannu a hankali ya yi gyaran murya bayan ya samu
natsuwar da ta dace da shi, a hankali ya soma yi min
magana.
Zan sallame ki gobe in muna raye kije gida kiyi
bakuntarki, duk da ba a haka naso kiyi tafiyar ba, ba
kuma a goben na shirya ki tafin ba.
To amma kuma ba zan iya barinki a gidan a
yanzu ba don ina bukatar kwanciyar hankali da zan
yi wasu abubuwa kan abubuwan da suke 2aruwa.
Wani irin sanyi ya sauka cikin raina, ina fata za
ki je ki dawo ba tare da kin gayawa inna wannan
damuwar ba? Nayi maza na ce mishi ko, kadan, to
gaya min in ji ke da kanki don in ji irin adalcin da za
ki yi min, kwana nawa zaki yi?
Cikin zuciyata naji tanfar in ce mmshi to in yi
wata biyu? Sai naji tsoro kar ya ce ya tasa, na ce
mishi da dai kai da kanka ne ka gaya nin da yai.
Yana makale dani a jikinshi yayin da kurma nake
bai wa yarinya nono, ya ce a'a ai ni nace ki fada sai
dai a duk wani hukunci da za ki zartar a tsakanina da
ke, na roke ki kar ki so kanki a kaina, komai za ki yi
kiyi adalci a tsakaninmu.
Ki sani ba a yau ki ka fara ji na ina furta kaimar
ina sonki ba, nayi hakan yafi a kirga. A yau kua ina
13
so in kara jaddada miki ina sonki fiye da duk yanda
ki ke tunani, gaba daya fatana da burina kuma bai
wuce in samu wata dama da zan nuna miki halaccina
ba, in dai nuna miki cewar ni din namiji ne.
Na ce to in yi...ban san yanda aka yi ba, sai naji
bakina ya ce mishi, kwana goma? Yayi murmushi
alamar ya ji dadin hakan da na fada, za ki iya yin har
sati biyu babu damuwa. Na ce mishi to na gode.
Gari na wayewa na soma shirye-shiryen yin
tafiyar da Adon ya ce zan yi a ranar yayin da shi
kuma ya ce min zai je wani wuri ya dawo, na ce
mishi to.
Yana fita kuma ya toro min Bala, wai yazo in ba
shi ayyukan da zai taimake ni da su, na kuma san har
da tsaro yasa ya turo shi.
Yana taya ni aikin yana ta murna, Mallam ya ce
zai yi min rakiya zuwa gidanmu, kai Innarku da kirki
take Anti Humaira, na ce ko? Yayi ta rantsuwa, na ce
ai na yarda Bala huta da rantsuwar taka haka.
Tunda Ado ya bar gida wajen shidan safe bai
dawo ba, sai wajen sha biyun rana. Kan nan kuwa
babu abinda ban yi ba har miyar da na saba yi mishi
wacce yake tafiya da ita Danja tun bayan rikicin da
muka yi kan zamanshi a can na soma yi ishi.
Ki gama dai ko? Na ce mishi eh, ya ce ina
Umahmah? Na ce tana wurin Goggo Ayalle. Ya zuba
min ido, nayi mishi bayani na gyarata naje na kai
14
mata ita.
Ba zai yiwu ace zan dauki mataki akanta ba,
suma mutanen gidan duk naje na gaishe su, amma
ban yi musu maganar tafiyar ba, tunda baka gaya min
ba.
To kin kyauta, bari in je in gaya musu, na ce to.
Ya fita bai dade ba ya dawo, kai Bala jeka kayi shiri
kazo ka fitar da kayan nan ga motar da zaku yi tafiyar
da ita can a waje, yayi maza ya fita sai washe baki
yake yi.
Na zubo abinci naje na kai mishi na zauna yana
ci shi kuma yana yi min bayani, na dan yi miki
sayayyar tsaraba, sai dai bata da yawa tana bayan
mota nayi godiya tare da yi mishi addu'a bayan naa
tabbatar mishi da cewar ta ishen.
Ya turo min wani dan kunshi wanda ya nadc
cikin leda, ya kuma yi rafin din soletep ya nadu
sosai, nasa hannu na dauki kunshin ina dan jinjina
shi a hannuna, bai kalle ni ba ya ce min kudi ne a
ciki, ki kaiwa Baba ki ce mishi na roke shi ya biyawa
Inna kujera taje ta sauke faralinta.
Ban san san'da nayi jifa da sunkin kudin nan ba
na kankame Ado don farin ciki, in kin je gida ki ce
ina gaishe su na ce mishi to.
Sallama nayi da kowa a gidan cikin wani yanayi
da bazan iya kwatanta farin cikina ba, ina fitowa daga
wurin Ruwailah ina jin ta tana cewa yar hirarta ai
15
una nan da ita sai ya nuna mata cewar shi din da
namiji ne.
Na shiga wurin Goggo Ayalle nayi mata sallama
nasa hannu na dauki Umahmah na rungume a kafada
maimakon in bari a biyo ni da ita saboda gaskiyar
magana ita ce girma da kunyarta da nake ji sun yi
matukar raguwa don ta riga ta bar ni na gane in da ta
dosa.
A cikin motar ni da Ado ne a baya saboda wai
zai sauka ne a mararrabar Danja ya tafi Danjan mnu
kuma sai mu nufi Kudan zuwa Makarfi, daga nan mu
isa Kano mu dauki hanayr Bauchi, shi kuma Bala da
direba suna gaba.
Kwalliya sosai Ado yayi yana rungume da
yarinyar a cinyarshi, na kalle shi naji dadi mijina ai
cikar halitta ne mai kuma tsabta ga kwarjini ga zati
kalaman Baba Tanimu suka fado cikin raina na yaje
ya duba wasu 'yanmata.
A hankali cikin natsuwa na tambaye shi, amma ai
ba za ka fara zuwa tadi a bayana ba ko? Bai juyo ya
kaile ni ba murmushi yayi ba tare da ya daga shi daga
kallon 'yan yatsun hannun Umahnah ba a hankali ya
ce min kina tsoro ne?
Na dan matsa kusa dashi na kwantar da kaina a
gefen kafadarshi nayi mishi magana a hankali ba
tsoro nake ji ba ina dai son mijina ne kawai, shiru
yayi bai ce min komai ba.
16
A mararrabar Danja ya miko min yarinya na
karbe ta ina shirin sallama dashi yasa hannu a kui6in
wandonshi ya ciro kudin da ban san adadinşu ba, ya
jawo jakata ya sanya a ciki ya zuge zib din ya fita,
bayan yasa bannu ya dauki food flaks din miyarshi
Suka yi sallama da direba da kuma Bala ya
tsallaka in da zai hau mota mu ma muka mika muka
kama tafiya.
Tafiyace ta fara mikawa sosai kewar mijina taci
gaba da karuwa a gare ni ina kara nesa dashi kewa da
kaunarshi suna karuwa cikin zuciyata.
Ban san yanda aka yi ba sai kawai naji zuciyar
tawa ta kama yin nazari da tunani cikin al'amarin
aurena da Ado wanda aka faro shi watanni ashirin da
daya da suka wUce, watanni ukun farko muka yi su a
gidan Babana, kusa da yan uwana da iyayena da
dangina watanni goma sha takwas din bayan nan
kuma tare da na shi dangin.
Tunani na sosai nayi har kafin zuciyar tawa ta
kawo ga tunanin bali da kuma irin sallamar da nayi
da kowane bangare, na rabu da Ado ne bayan ya
tabbatar min da cewar fatan shi da burinshi bai wuce
nuna min halaccinshi ba, ta hanyar tabbatar min da
cewar shi din da namiji ne.
Yayin da ita kuma Ruwaila da nata mukarraban
suma suke yi min fata da barin muna nan tare daşu
shi Adon ya nuna min cewar shi din da namijin ne.
17
To wai wancne da namiji? Ko kuma me kalar da
na miji ke nufi? Wannan ita ce tambayar da ta zo min
cikin zuciyata.
Namiji ni a sanina shi ne suna mafi daraja da
Ado ke yi wa kanshi lakabi ko kuma in ce kirari
dashi.
Sannan duk da ban taba yi mishi tambaya yayi
min bayanin abinda yake nufi da kiran kanshi da
wannan sunan ba, ni, a fahitata kalmar Namiji' a
wurin Ado yana nufin suna na cikakken mutum
jarumi mai iya fuskantar kowane irin al'amari da
zärfin zuciyarshi.
Mai tsayawa kan abinda ya sanya a gabanshi,
mai iya tsayawa ya fuskanci kowane irin wahala da
jaruntakar shi don ya zamo kariya ga na kasa dashi,
mai sanin ya kamata wanda yake iya saka alheri da
alheri.
To amma a wurin mutane kamar su Ruwailah da
masu fahita irin nata, ina ganin shi 'namiji' ba kowa
ba ne a tasu fahimtar face jarumin da ke iya danne na
ƙasa dashi.
Jarumin da bai kamata mace ta bashí amana ba
saboda bai da alkibla guda daya, yana iya canzawa a
kowane lokaci, ya manta da farko ya saka aheri da
mummuna tunda shi din kanshi kadai ya sani.
Bai kuma damu da rayuwar kowa ba sai tashi,
tunda a bakunansu dai kusan kullum sai ka ji su suna
18
fadin in dai 'Namiji' ne ai gashi nan ga ta nan
yanzu-yanzun nan ne kuma zaka ji su suna cewa wa
shi 'namijin ba dan goyo ba ne.
Da dai na tsunduma sosai cikin wannan tunanin
musamman da na tuna tun kafin in ji irin wannan
kalmar a bakin su Ruwaila, na taba jin ta a bakin
Babana, shima ya taba ce min in dai Ado namiji ne to
gani nan gashi nan.
A bakin Mama kuwa ta gaya min yafi sau shurin
masaki,