Showing 15001 words to 18000 words out of 33160 words

Chapter 6 - MIJIN TACE 4 COMPLETE HAUSA NOVEL BY SODANGI.txt

ba su maida kansu sika. zama
abin da suka zaa.ba, Babanku zai rinka yi mata abin
da yake yi mata a yanzu?
Wai har yana gayawa mutane ita din macuciya oe
shi da ita wa ya cuci wani? A ina aka ce wa namiji ya
bari mace ta... da sauri na kátse Ado.
Na ce, a'a ya ya haka? Me Babana ya yi maka?
in anyi wa Mama...kan in karasa ya wanke ni da
mari, ai ba za ki sake zaginta a gabana ina kallonki
ba, ai kun riga kun kure ni.

74
Yau ma Baba Tanimu ne ya raba ni da Ado.
Kwanaki kadan bayan nan ma aka sake masifar
Ado ta ishe ni naje na kai karar shi wurin Baba
Tanimu ya hada mu ni dashi duk gaba daya bayanin
akan Ibrahim ne.
Baba Tanimu ya ce to ke ki bar shi mana kawai
ya kore shi ba yarshi ce ta haife shi ba? Na ce a'a
Baba ba wurin shi yazo ba, wana ne sune ya'yan
Babana manya ba asan in da dayan yake ba, shi yazo
wurina a kore shi, in shima ya tafi bai sake dawowa
ba fa?
Na yarda tunda gidán shi ne yasa mishi ka'idar
zama' in bai bi ba shi kenan, amma ba kora ba, in an
bar shi ma in yaga zai tafi sai ya tafi don kan shi.
Baba Tanimu ya ce, gaskiya' ne, kasa musu
ka'ida ita dashi in basu bi ba ni ne zan kore shi ba kai
ba.
Ado ya ce, za'a rinka salloli biyar dashi a
Masallaci, Baba ya ce ko ba ka nan zan sa maka ido
kan wannan, ban yarda kuma asha ko da sigari ne ba
a cikin gidana, balle wani abinda yafi sigari.
Kina ji? Baba Tanimu ya tambaye ni na ce mishi
eh Baba. Sai me kuma ya sake juyawa wajen Ado,
Adon ya gyara zaa ya ce, zama kawai zai rinka yi a
gida ban da fita in kuma ya ki ya fita to kar ya dawo.
A baka maganar ta dan lafa ni kuma na tasa Yaya
Ibrahim a gaba kullum ina kaf-kaf-kaf dashi ina

75
tsoron kar yayi abinda za a ce yayi laifin kora tunda
maganar tana gaban Baba, ba zan iya jayayya da shi
ba.
Kwanaki kadan da ya yi yana tsare a gida sai da
jikinshi ya canza ya soma yin kyau.
Rannan ne nemi Yaya Ibrahim na rasa, ban gan
shi ba baya cikin gida ba kuma lokacin Sallah ba ne
balle in ce yana masallaci.
aNa kesa buda bakina in tambayi wani shi, don
kar ya yada maganar cewar ba a gan shi ba har Ado
ko. Baba suji, don haka naja bakina nayi shiru nayi ta
leke-leke ko zan hango shi har dai na hakura.
Ina zaune tsakar gida sai gashi ya shigo layi yake
yi nayi salati mai karfi ya waiwayo ya kalle ni "Anti
Humairahhh ki shouumn kawai kin gane? Ki rabu da
wannan mugun mutumin muuu dah yah zan...
Nayi maza na tura shi dakinshi na tura mishi
abincin shi wanda sakwara ne da miyar taushen da
aka yi da kayan ciki da busasshen kifi naja kofar na
rufe shi a ciki ina ta addu'ar kar Ado ya dawo ya ce
ina yake?
Washegari da Asuba Ado yana fita Masallaci da
yake yana fita da wuri tun kafin kiran Assalatu nayi
maza na tashi naje na shiga dakin Yaya Tbrahim.
A kwance shame-shame na same shi, yayi filo da
sakwarar da na mika mishi, ko loma daya bai yi ba, a
tsorace na tashe shi ya wastsake na nuna mishi

76
abinda yayi, shima ya tsorata.
Na sa shi yayi wanka kafin ya fita Masallaci aka
yi sallar Asuba dashi ya shigo gida ya gyara dakin
nashi.
A haka ina zaune da Yaya Ibrahim kullum ina
kab-kab-kab ina kuma addu'a har nayi sa'a zaman
nau ya mike ya soma wastsakewa daga abubuwa
masu yawa.
Natsuwa ta soma zuwa mishi, har dai daga baya
ya yarda ya koma makarantar addini da ta boko.
Ado ya yarda da zamanshi a gida, ya saki jiki
dashi ya soma jan shi zuwa gona da ma wuraren
harkokinshi, har ma daga baya yake iya tura shi ya
wakilce shi kan al'amura masu yawa.
Shekaru goma cif sun cika daga wannan ranar ta
daidaituwar al'amuran Yaya Ibrahim.
Shekaru goma sha biyar kuma kenan na aurena
da Ado, auren da kaddara da rabo na abubuwa masu
yawa suka tilastawa Mama yin sanadin shi.
A yau ni din mahaifiyar 'ya'ya biyar ne cif na
Kawu Ado, cikinsu akwai namiji guda daya Baba
Yahya, sai kyawawan 'yan mata guda hudu,
Umahmah ita ce ta farko, sai Baba Yahya bayanshi
ne kuma muka samu Zainab da Khadija da Fadima.
Wadanda mahaifinsu ya zaban musu Sunayen
nasu saboda kaunar da yake yi wa yayarsu
Umahmah, don haka ya ce to tunda a tarihin da ya

77
karanta na Umahmah Zainab yar Annabin Rahama
ce mahaifiyarta ita kurma Zainab kowa yasan 'yar
Nana Khadija ce.
Sannan ita Nana Fadima sonta da take yi wa
Umahmah ne ya sanya ta bar wa mijinta wasiyyar
auren Umahmah bayanta, to bari ya jera mana
Sunayen.
Haka don neman albarkar masu sunan na ce
mishi to Kawu don haka Ado bai taba yiwa kowa
takwara ba tun bayan wanda yayi wa Baba Yahya.
Duk kuma da wadannan 'ya'ya biyar din da ke
gare ni shekaru kusan biyar ne kuma yau rabona da
haihuwa a dalilin son miji da neman gindin zama a
wurinshi ya sanya ni shiga harka ta bin tsarin iyali.
Mahaifar tawa a daure take, watakila in ban dá
haka da yanzu an wuce biyar an kai shida ko bakwai
ko ma takwas ko da yake dai ina da sani da kuma
Imani na cewar babu wani wanda ya isa ya hana wani
zuwa duniya a lokacin da kaddarar zuwanshi tazo.
Don haka na yarda nayi hakan tunda abin da
maigidan yake so in yi kenan ni kuma kullum a kan
bin ra'ayinshi nake matukar dai bai zamo sabo ba
tunda nasan ni din ni kadai ke gare shi a gida ko a
waje ba mai leke-leke ba ne.
Yanda na zamo mahaifiyar ya'ya biyar a cikin
gida, to a waje shima mai gidan al'amura masu yawa
ya sanya a gaba farko dai a yau shi din shi ne 'Dr.

78

Ado Sulaiman', don kuwa digiri uku ne da shi.
A yanzu yana aiki ne tare da hukumar inganta
ilimin makarantun primary ta kasa. Shi ne kuma
mamallakin shahararriyar gonar nan ta "HUMAIRAH
FARM'.
Wacce ita ce kadai gonar da a nan kurkusa tayi
fice wajen bayar da kayayyakin amfani irin na lambu
rani da damina, irin su (Brocooli, Beetroot,
Asparagus, Aborigine, Cabbage, Kore ja, ko na
Chinese, carrot, ganyen celery, cucumber, lettuce, da
abubuwa masu yawa da suka danganci lambu, ga
kuma 'ya'yan bishiya irin su gwanda, abarba, lemo,
gwaiba, da makamantansu, wadanda duka ana' tafiyar
dasu ne bisa tsarin nomna irin na zamani.
Haka nan wannan babbar gona ko kusa harkarta
da dawainiyarta bai fitar da Ado daga cikin harka ta
noma damina ba, wanda da shi dama ya fara.
A yanzu shi din manya-manyan gonaki ya
mallaka na noman masara, dawa, wake, ga kuma
fadamun noman shinkafa da rake wadanda mutane da
yawa suke taimakon shi tafiyarwa.
Amintattun yaran da ya rike irinsu Bala wanda
bayan kammala hada haddar Alkur'aninshi, Ado ya
trua shi ya dan karanci Boko har ya zamo ya mallakii
ilimin digiri akan aikin gona da kuma wasu yaran da
anbatonsu zai y yawa...
Ina zaune cikin katafaren gidan da sanda na yi

79
wa Ado rakiya zuwa kasar Singapore ne na dauko
sanfurinshi bana komai na aikin hukuma bayan
kanmaluwar karatuna na N.C.C. nayi aikin
karantarwa a makaran tar primary ta Dabai na tsawon
shekaru bakwai.
Ado ya bani umarnin' ajiye aikin don in zauna a
gida in yi aikin da yati kowanne dacewa da ni, wanda
yafi kowanne zamo min dole don shi ne in ban bayar
dashi baza a tambaye ni.
Shi ne aikin tarbiya, tarbiyar 'ya'yan da ke gare
mu wadanda ba biyar din da na ambatan wa kaina ne
kawai tarbiyarsu ta hau kan nawa ba, manyan
yanmata kadai guda hudu ne da ni ga Umahmah ga
Hindatu ga Nusaiba ga 'yar gidan Furerah da ta haifa
bayan haihuwarsu da shekara daya har tayi min
takwara da ita.
Da zan taso duk na hada su muka dawo a maza
kuma ga Usman sai Baba Yahya sai kuma wasu
yaran da Adon ne ya kawo su gidan to ga kuma su
Nana.
Bisa wannan dalilin ne maigidan ya zaunar dani
yayi min gamsasshen bayanin da ya sanya ni
gamsuwa da barin aikin nawa na zauna a gida nake sa
mana ido kan al'amarin tarbiyar ya'yanmu.
Ganin da yayi na hakura da albashin nawa da
nake samu wanda yasan amfaninshi wurina yana da
yawa, tunda yasan ina da iyaye da 'yan uwa da dangi

80
wadanda nake tafiyar da al'amuran da ke tsakanina
da su na zumunci ba tare da shi1 yasan yanda aka yi
ba.
Sai yaga na hakura na bari na kuma ja bakina
nayi shiru, ban taba tanbayarshi yaya za ayi ba? Ya
sanya shi yi min tukuici da gonar HUMAIRAH
FARM.
Ina zaune a falona ina karatun littafin (Riyadus-
salihin) babin godiya kan ni'imomi nake karantawa,
Baba Yahya ya shigo da gudu, can bayana ya tsallaka
ya wuce ya buya.
Sai ga Umahmah ta biyo shi a fusace, ga dukkan
alamu tsokanarta yayi, ta bude baki da nufin yin
magana fushin nata yayi tsanani, na daga ido na
kalle ta cikin natsuwa na ce mata.
"Umahmah sau nawa zan gaya miki cewar
Ubangiji yana son masu hadiye fushinsu, nan da nan
ta 'sauka, ta kalle ni cikin ladabi ta ce na hadiye
Goggo, na ce to ai kin san kuma yana son masu
yafiya, ta ce na yafe mishi.
Na ce to kuma har ila yau yana son masu
kyautatawa na kasa da su, tayi murmushi ta ce to
Goggo ya biyo ni yazo ya karba.
Tana barin dakin na kamo Baba Yahya na jawo
shi gabana, kumnenshi na kama na rike da hannuna
ina ja yana bin hannun nawa yana fadin kiyi hakuri
Goggo, na zaro ido ina kallon shi sau nawa nake gaya

81

maka ba sa'o'inka ba ne?
Sau nawa nake gaya maka da Hindu da
Umahmah da Nusaiba shekaru uku-ukı suka baka?
Don haka ka daina tsokanarsu, ka daina yi musu
rashin kunya."
Jin da ya yi na ce da jan kunnen nashi ya sanya
shi tunanin da dokar da yasan an kafa min, cikin
natsuwa ya ce Goggo Babana ya hana ki kama min
kunne saboda yana min ciwo.
Na saki kunnen nashi cikin sauri na ce, to ama ba
zai hana in saka, in saka tsallen kwado ba ai, tunda
kai baka son a tsokane ka amma ka iya tsokana. Sun
ce maka superdi ka gaya mishi ya ce kar a sake.
Sannan sun ce maka Tanko ka sake gaya mishi
ya hana, to zan gaya mishi ni da kaina ba ka da aiki
in ka zauna a gida sai tsokanar yayunka kawai kake
yi, don haka ya zabi abinda za'a rinka yi maka cikin
biyu, ko dai ya bari in rinka sa Yaya Bala yana tafiya
da kai gona ko kuma a gida Yaya Usman ya rinka
horar da kai yana saka tsallen kwado.
Cikin natsuwa ya kalle ni ya ce, kiyi hakuri
wahala zan sha in an sani tsallen kwado, nayi nauyi
da yawa, na ce to bi bayan 'yar uwarka kaje ka bata
hakuri, ya ce min to. Ya tashi ya fita.
Yana fita ya bar dakin, na amsa wayar Yaya
Ibrahim daga Kaduna, Anti Humaira ina kwana?
Nayi murushi na ce lafiya Yaya Ibrahim, ya ya gida?

82

Ya ya yaran?
Ya ce, lafiyarsu kalau, na ce to Mamansu fa? Ya
ce ga ta nan tana jin ki, wai tana gaishe ki, na ce to na
gode ina amsawa.
Yaya Ibrahim ya ki ya. daina kirana Anti
Humaira, duk da a yau shi din wani irin kammalallen
mutum ne natsattse, mai addini, mai mutunci da
ganin girman na gaba dashi, don haka ba kirana Anti
Humaira akan yanayin shirme irin na baya ba ne yana
dai kiran nawa ne kawai saboda sunan da ya zabi
kirana da shi kenan.
Yayi aurenshi tun a lokacin da ya gama
karatunshi na (N.C.C) saboda sanin da nayi cewar shi
din ba yaro ba ne karami, yana bukatar aure ya sani
tsayawa wajen ganin yayi auren yana koyarwa yana
kuma taimakon Ado kan al'amuranshi.
Da haka ya soma rike iyalinshi daga baya na
bashi shawarar janyewa daga harkokin Adon don ya
tafi yayi nashi na karishi saboda lura da jaruntakar shi
da nayi.
Kan haka na tasa Ado a gaba sai da ya ware
dukiya mai dan nauyi ya bashi nima na tattara abinda
na iya tattarawa na hada na mika mishi ya soma
harkokinshi na kasuwanci.
A yanzu yana zaune a Kaduña a gidanshi na
kanshi da ya gina da matarshi Rumana da 'ya' yanshi
maza guda uku.

83
Dama na ce bari in tambaye ki yaya jikin na
Mama? Na ce da sauki sosai, ya ce to ki rinka hakuri
fa, ko kuma in ce kiyi ta karawa tunda nasan kina yi.
Nayi murmushi na kawar da zancen ta hanyar
tambayarshi an samu sakon nawa kuwa? Ya ce eh an
samu, na ce to in Rumana zata zo sai tazo min dashi,
zata zone? Nayi murmushi na ce ba za ta zo duba mu
ba ga Mama ta dawo?
Ya dan yi murmushin ya ce, to' to shi kenan sai
ta zo din na ajiye wayar can cikin zuciyata nasan
tsanar da Mama ke nunawa Rumana ke damunshi, ita
kuma Mama tana tsanar Rumaia dama Ibrahim din
baki daya ne har da ma 'ya'yan da suka haifan
saboda ni.
Saboda tayi juyin duniya Ibrahim ya dauke ni
kamar yanda ita da sauran ya'yanta suka dauke ni ya
ki, don haka taki shi ta hakura dashi akan idona akan
idonshi. Ado yayi dariya ya ce ai ta kwarc ki Mama
daina barin Humnairah tana kara kwararki.
Daina bar mata abin da ki ke so, ki rinka yarda
kawai ke da ita kuna haduwa kan abin da ki ke son
tunda kaddara ta riga ta hada ki ke da ita.
Gaskiyar Ado ne kaddara ce ta hada ni da Mama
kaddarar kuma ta kaddara min mallakar mutanen da
take matukar so a rayuwarta don haka kiyayyata da
ita maimakon raguwa kullum karuwa take yi ban
Kara sani da fahintar hakan ba.

84

Sai a shekarun baya-bayan nan shekarun da Ado
ya sake komawa cikin al'amuranta saboda yawan
rashin lafiyar ta da kuma wulakanci mai tsanani da ta
fuskanta a wurin Babana ga shigar ya'yanta cikin
matsalolin aure da ma rayuwa.
Ganin da yayi zata tozarta, ya sanya shi yin
tattaki zuwa har gidanmu tafiyarshi gidan na farko
kenan tun bayan barin gidan da yayi yaje ya daukota
ya kawo ta yayi jinyarta sai da ta warke tayi garau ta
samu lafiya ta murmure tayi kiba tayi kyan gani.
Sannan ya maida ita dakinta bayan' ya gyara mata
shi yasa mata duk wani abin da ta bukaci a sanya
mata, ya daurawa Anti Sha'awa aure ya kwashe
ya' yanta ya maida su gidan ubansu ya baiwa Habiba
jari mai karfi don yin sana'a, tunda a gidan su kullum
fada ake yi akan abinci sannan ya dawo.
Amma duk da haka bai sa Mama ta samu zaman
lafiya a dakinta ba gatan da ta ga ta samu wurin Ado
da kulawar da taga yana yi mata ta hanyar yi mata
aiken kudi akai-akai saboda maganinta da ma wasu
al'amuran rayuwarta.
Sai ya sa ta yunkurin sake tasa mutane a gaba da
fitina, shi kuwa Babana ya ce ina? Ai wannan
zamanin ya wuce, bai zai yiwu ba, ba zan lamunci
hayaniya da fitina ba, ba kuma zai yarda a tasa mishi
wata mata a gaba ba tunda a yanzu kam a zahiri ai
Zubaida ce. ta damu Mama.

85
Sai dai idan nayi nazari naga ta kasa hakura da
kiyayyar da-take yi min yanda take kina kuma haka
take kin Umahmah, sai in gane ta hakura da Innan ne
kawai saboda ta gane tafi karfinta bata kuma kallon
inda take.
A wannan lokacin kullum wurin Ado Mama ke
kawo karar Babana, kullum kuma karar ba ta wuce
ba ya shiga dakina ya dade kamar nasa, ba ya
saurarona ba ya bani hakkina.
Rannan ina jin kan Ado ya daure ne da
al'amuran, bai fahimce su da kyau ba, yasa shi
kallona cikin natsuwa ya ce min ni me Mama ke nufi
da wadannan kalmomin, na sauraro da hakki ne?
Ko tana nufin har yanzu itama bata daina ba ne?
nayi shiru nayi kamar ban ji shi ba, can cikin zuciyata
na ce ai da ita ka kira ka tambaya.
Ba ki ji ina magana da ke ba ne? tunda ba zai
yiwu in gaya mishi. abinda ke zuciyartawa ba tunda
nasan yin hakan bacin rai zai zama, sai kawai na
maida maganar wasa na ce mishi, towwwo! Wato in
mutum ya girma sai ya hakura?
Kenan nima in shirya, ya yi maza ya jawo ni
jikinshi yana dariya tare da fadin a'a-a'a ai ke ban da
ke a cikin Humairah tunda ke ai ke kece.
Zuwa can yaja tsaki an jima ya sake jan wani
tsakin ina dai jin shi ban tambayi dalili ba, can
anjima abinda ke damun nashi ya kasa zama yayi

86

Shiru a cikinshi. Sai naji ya ce kwata-kwata Mama
bata fahimci rayuwa ba.
Ba ta ma san yanda rayywar take ba, ai baka cin
zamaninka ka ce zaka ci na wani, ya sake jan wani
mummunan tsaki sannan ya ci gaba, ke kuma kin ci
naki kin hana wasu cin nasu.
Kin kama hakkokin mutane kin daddane kin yi
samadin da abubuwa da yawa suka caccabe, kin hana
'ya'ya jin dadin rayuwarsu saboda baki yi musu
tarbiyar da ta dace da su ba.
Ga alhakin Jama'a da ki ka yi ta diba amma wai
har yanzu ba ki fahinci komai ba? Wai lokacin
saduda ma bai zo miki ba? Haka ake rayuwa
Humaira? Nayi mishi murmushin yake naja bakina
nai shiru.
Ya zuba min ido yana kalloma amma kin san
bana so in yi magana ayi min shiru ko? Nayi
murmushi na ce kayi hakuri Kawu mu bar wannan
zancen kawai muyi wani tunda ni ai ba ni da bakin
magana kan wannan batun.
Saboda dai ka riga ka karantar da ni na gane wata
gaskiyama fadanta rashin kunya ne.
Yayi murmushi saboda yasan nasha fadar
gaskiya akan Mama in muna hira ya ce shi na zaga
dai haka na daina.
Ya ce, to naji kawo mana wani zancen muyi
funda na kawo nawa kin ce a'a, na matsa jikinshi

87

kawai na soma yi mishi abubuwan da na san sun fiye
mishi hirar dadi da kuma muhimmanci.
Tun sanda Mama ta sake dawowa cikin al'amarin
aurena ban samu wani cikakken zaman lafiya da
kwanciyar hankali ba saboda har a yau dinnan bata
hakura ba burinta bai wuce na taga, ta ga bayan auren
nawa ba saboda kullum tana gidana.
Nata gidan da tsawon rayuwar kuruciyarta take
kirarin nata ne, mijin ma nata ne wanda duk zai
zauna da su kuma sai dai yayi hakuri, to zaman
cikinshi ya gagare ta, a yanzu a shekarunta na girma,
shekarun da a su ne ya kamata ace gidan ya zama
nata dop tafi bukatarshi.
Shi kuma Ado a baki ne kawai yake fadan halin
Mama kaga kamar babu wanda ya kai shi sanin halin
nata bale ya fishi arnaidan ta zaunar dashi ta gaya
mishi abin da ta gaya mishi ta kulla abinda take son
kullawa.
Sai ka gan shi yana huci yana zare ido, yana
fadin maganganu da in ba ayi hankali ba ráyuka zasu
yi matukar baci.
Haba Humaira! Haba wannan abin tausayi har
ina? Zaman gidanku kuma ya gagareta da gimanta ta
baro dakinta ta dawo nan, nan din ma zai gagare ta
ne?
To in nan ya gagare ta taje ina? Rannan dai
danne ziciyata kawai amma kiris ya rage in ce mishi

88
to ta shiga daniya Mama.
Rannan ma da wata matsala ta sake samun Mama
ta sake yanke jiki ta fadi, stroke dinta ya dawo, da
sauri na yi wa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login