Showing 12001 words to 15000 words out of 33160 words

Chapter 5 - MIJIN TACE 4 COMPLETE HAUSA NOVEL BY SODANGI.txt

na kore shi don takamar na gyara
wurina ba, wai kar su lalata min.
Sai dai ma in nei abinda na mika mishi don ya

60
kara mike kafa yayi zamanshi.
Sannu a hankali 'sai wurin nawa ya zama wurin
wasansu, kasancewata ba mai jurar magana ba ce in
dai ba da mijina zan yi tayin maganar ba.
Sai na soma ce musu ku kawo littattafanku muyi
karatu, kan kace meye wapnan? Kowa ya dawo
Makaranta da matsalar shi zai zo wurina Maman
Umahmah.
Rannan na ce musu kai kar wanda ya sake kiranaa
da wannan sunan.
Ado yana jin mu da su ya ce dawane suna ki ke
so su kira ki? Na ce oho, ya ce to ku rinka kirantada
sunan tsofafi Goggo na ce oho ya i min, tun daga
ranar gaba daya yara Oggo suke ce min in amsa.
Cikin hikima na baiwa Ado shawarar mu tashi
mu koma wai Wurin, da sauri ya tambaye ni muje
ina?
In bar dangina in je ina? Naja bakina nayi shiru
cikin zuciyata dai na san ina da aiki tunda ba zai
yarda ya tashi ba, don haka na dauki ataki na gyara
mu'amalla tsákanina da manya kamar yanda na samu
da yara.
Kullurm Juma'a in zan je gaida Goggo zan kai
mata goro murza-murza ko kuma abin sayen goron,
bini-bini kuma zan lallu6e abin dadi cikin hijabina in
kai mata.
Itama Ruwailah haka, danma kuma ina jin ta gaji

61

da zaman namua haka, don haka tunda taga na dan
yi sassauci sai tayi maza ta saki. Bini-bini zata leko
wurina.
Goggon yara nace ko da abù kaza ne a wurinki?
In ce mata eh, ko inf ce a'a ajea sayo mana in mika
mata kudin tayi godiyá ta tafi.
Gari yana wayewa kumă žata turo a daukan mata
Umahmah ta hada da Nusaiba tayi musu wanka ta
bar su a wurinta.
Rannan ba karamin tashin hankali Ado yayi min
ba, akan ya gane na koma yin mu'amallah da
Ruwaila nayi tayi mishi kuka, ita ta riga kowa
karbanmu a gidan nan abin da ya faru bayan häkan in
aka bar shi zai wuce ka bar ni in yi mu'amalla da
kowa don kaima ka sanmu natsuwa.
In yaso taji dadin koya miki iya shege ba? Na ce
to in ta koya min nan dauka mana ai jiki magayi, da
nayi maka ka kyale ni ne? wacce irin azaba ce ba ka
gana min ba? Ado ya kalle ni yayi murmushi ya ce ni
kar ki kulla min sharri.
A haka na lallaba Ado ya bar ni na soma shiga
harkar cikin gida, ina zuwa wurinsu muna hira, iyaka
dai ina kula da bakina bana kuma yarda da zaman
dakin wata.
A haka sai na soma shiga ayyukansu zan yi musu
tankade na tuwo ko na abin kadi zan zuba garin tuwo
suyi tuki zan zuba abin kadi suyi kadin zan yi sharar

62

wurin girki.
A haka rannan sai na karbi girkina daga hannun
Furerah ban kuma yarda mun 6ata ba, don haka sai
muka samu saukin zaman mu'amalla kuma ta gyaru
duk da dai nasan gyaruwar mu'amallar bata kawar da
Su daga dokin ganin Ado yayi aure ba.
Sai dai kuma an daina yin maganar a kan idona,
nima kuma nayi sassauci mai yawa a kan hakan,
saboda na riga na yarda da cewar a yau don Ado yayi
auren shi bai zalunce ni ba.
Shi yakai min Inna Makkah, ta sauke farali ko
wannan kadai yayi min ni ya biya ni, balle kullum a
cikin hidimarta yake ita da kaņnena.
A wannan lokacin ne Ado ya soa gini a cikin
gida ciki da falo ne guda biyu manya, daya da kicin
da bayan gida a cikin shi, daya kuma babu ga kuma
wani daki guda daya suma biyu a jere.
Yana soma ginin gidan gaba daya ya dauka aure
zai yi ya gano wata kenan, ai kin ga namiji ba?
Tuntuni tana zaune a tsukakken daki bai yi mata gini
ba sai yanzu da ya gano wata kuma ki duba ki gani
tun ba aje ko ina ba yana yiwa amaryar gini irin na
zamani mai hade da kicin da bayan gida a ciki.
Ita kuma nata babu bayan gidan bare kicin din,
ban ce komai ba ban kuma taba daga hankalina har
wani ya gane ba, na bar wa zuciyata komai.
Rannan dai muna tare da Adon a daki, laptop din

63
shi yake dubawa a dalilin ba wani kula juna sosai
muke yi ba, saboda wai na bata mishi rai nima naja
nayi shiru ban Bada, hakuri ba don fushin ya dan yi
tsawo saboda wasu dalilai nawa.
Ina jin dai aure ka ke shirin yi ko? Shi yasa ka ke
yi min abubuwan da ka ke yi barin abinda yake yin
yayi ya dago ya kalle ni me na yi miki?
Na daure fuska na ce, gashi nan wułakanci iri-iri,
wanne da wanne? Nayi shiru, ya ce ai kin lissäfo su
tunda ki ka ambaci wulakanci saï kin gaya min.
Shim nayi ban tanka mishi ba, ya gaji ya ce in
kuma kece ki ke yi min wulakancin saböda kin ga na
kasa yin auren"to zan yi wa kaina maganin abin
saboda na lura raini ya sbiga tsakanina da ke ba kya
ganin mutuncina.
Kullum kawu ya soma yi minirin wadannan
kalaman kuka nake yi doń ba sa yi min dadi na kuma
kasa sabawa da su
In yi mata biyu mana nima in ji dadi in wannan
bata tattake ni ba a yau to gobe wata zata yi.
A lokacin da Ado ya gama gininshi wanda ya y
matukar yin kyau ya kuma kawata wannan ciki da
talon mai kicin da bayan gida da kayataccen tails da
rufin silin irin na zamani.
Sauran kuma ya yi musu suminti jiranshi kawai
nake yi ya ce min ga ranar aurenshi ga kuma ni dakin
da ya bani.

64
Ana cikin haka, rannan sai gashi rannan yazo da
kujeru ana zubawa a falon nan ya sanya darduma ya
kawata wurin sosai. Mamaki ya kama ni na ce.
To wannan sai ya gama sanya musu komai ne za
su bashi 'yar ko yaya? Ni dai ban ce komai ba, tunda
dai na tseguntawa Inna maganar, ta ce in zuba mishi
ido na ce mata to na zuba.
Da daddare ranar muna hira ya ce min ni fa gado
bai damen ba, nafi jin dadin kwanciyar katifa shi
yasa bai sayi gadon ba, amma in kina so a sai miki.
Na ce a'a a sai min gado kawu ai mutuncin daki
ne ya ce to shi kenan.
Kwana biyu daga nan na tare a sabon dakina ciki
daya guda daya ya mayar min da shi aji don
karatunmu da yara har bencina da black boad yayi
mana daya dakin kuwa ya gyara shi don baki ya bar
daya ciki da falon.
Sai suka koma cewa sai ya gama gyara wannan
din tukuna zai yi auren gashi ya killace min wurin da
yar katanga amma duk da haka ban daina shiga can
cikin gida nayi abubuwan da muka saba ba.
Kaka tana zuwa ciki da falon Ado ya bayyanawa
mutanen gida cewar don buhunan hatsinshi ya tanade
shi tun da rumbunan da yake amfani da su basa isan
shi.
A wannan lokacin ne kuma ya sanya ni na fara
karatuna na (N.C.C) a makaranta nan a Zariya kullum

65

nake zuwa ina dawowa.
A wannan lokacin harka sosai yake yi don tun a
shekara ta biyu da soma aikin shi ya zama
mataimakin (Princepal) a makarantaryanmata ta
kafur a yanzu kuwa shi ne (Princepal) na makarantar
gozaki.
Ban shekara cur ina zuwa Zaria ba ya sai min
motar hawa ya kuma koya min duk da shi din har
yanzu babur din shi yake burgawa yaje duk in da za
shi, ko kuma ya hau motar haya in kuma ina gida ya
ce min in kai shi.
Umahmah, Nusaiba: da Hindu tare da Usman
makaranta daya ya sanya su, don haka kullum in zan
fita da safe nike kai. su in wuce Zaria in lokacin
tashinsu ya yi kuma 'sai. Bala yaje ya dauko su a
motar haya.
Rannan na dawo daga Zaria da yamma a gajiye
nake sosai saboda muna cikin karatu mai zafi, ina
zaune ina dama furar da zan sha don ragewa kaina
yunwar da nake ji sai ga Ruwailah ta shigo min da
dan waken da ta ce wai don ni tayi na karba cikin
farin ciki ina mata godiya.
Na soma ci, lomar farko da ta biyu da nayi abin
gwanin dadi, sai kawai naji ta ce min ni fa wata
magana naji na ce to ba za ka ji za a cuci naka ko ana
cutar shi ba kayi shiru.
Dole ka gaya mishi ko da kuwa ba jin dadin

66

maganar zai yi ba, sai da naji cikina ya ba da sautin
kulululu don tsoron abin da take shirin gaya min din.
Sai kawai naji ta ce min wai ashe Baban yaran
nan cikina ya sake ba da wani sautin na kulululu,
tunda nasan sunan da take kiran Ado kenan, wai ashe
matar nan da ake cewa ya ajiye yana karyatawa wai
har ta haihu.
Karfin hali nayi na iya karasa tauna dan waken
da ke bakina, na hadiye ban tofo shi waje ba, cikin
natsuwa na daga ido na kalle ta. Na ce mata shi.
Baban yaran nan wani irin mutum ne Yaya Ruwaila
da ban isa in tuhume shi kan abinda yake yi ba?
Kin san kowane mutum da yanda yake, da irin
lagon da matarshi take samu akan shi, to shi wannan
wanda nake da shi a kan shi bana in tuhume shi ba ne
in akan wannan ne ban isa ba.
Don haka ko kawo min dan ya yi ya ce in rike ba
zan tambaye shi inda ya samo shi ba, musamman ma
da yake nasan ba kan shi farau ba, don haka ko kin ji
irin wadannan maganganun daina gaya min su kawai.
Wai dama kai da naka ne kar kaji ana cutarshi
kayi shiru, na ce eh ai dama, to bani da iko akan shi
ai kin ga gaya min din bai yi min amfani ba kenan.
Sai dai ma kawai ya yi dalilin tashin hankalina ke
kuma nasan ba za ki so ganina cikin tashin hankali ba
tayi maza ta ce yo to ina fa?
Da haka sai na kashe bakin Ruwailah akan dauko

67

min wani labari ta kawo min.
Na kara haihuwa da namiji muka samu na roki
Ado ya sanya min sunan Babana ya ce min to sai
kawai ranar suna naji yana fadin sunan yaro Yahya
ban ce mishi komai ba tunda shi ma uban nawa ne
Baba Yahya kuma yayi matukar jin dadin takwaran
da Ado ya yi mishi don tasowa ya yi yazo har Dabai
wai yazo ganin takwaran nashi.
Rannan ina tare da yara a aji karatu muke yi
saboda wunin na ranar Lahadi ne tun safe kuma Ado
yana gida sai da yayi azahar ya fita, don haka nima
da muka yi azahar din sai na ce mu shiga ajin zuwa
lokacin La'asar sai mu fito muyi sallah su taya ni
aikin abinci.
Muna cikin karatun sai ga wani yaro dan
makwabta da nake kina Baba saboda sunanshi
Surajo, ya shigo da sauri sai da ya gaishe ni sannan
ya ce min Goggo wai kinyi bako wai a gaya miki wai
yayanki ne daga Bauchi.
Yana yi min maganar cikin wani yana kamar
tsoro ko kunya.
Jin da nayi ya kira Bauchi ya sani nuna mishi
kofar baya na ce mishi jeka ka shigo min da shi ta
wancan kofar, ya ce min to.
Ya tafi ya dawo ya zuba min ido, kafin ya ce
"Goggo kila ma fa karya ne, nayi murmushi na ce je
ka dai ka shigo min da shi."

68
Na ci gaba da toayuwa a wurin don ganin wanda
zai kawo min din, ai kawai gashi ya shigo min da
Yaya Ibrahim. Ysna ganina ya zube a kasa wai ni
yake gaisarwa, gaisuwar girmamawa, sannu Yaya
sannu dai, ina wumi yaya aka ji damu?
Zuba mishi ido nayi ina kalion shi, gaba daya
yayi baki, baki ya gama rubewa ko'ina a jikinshi
tabo ga wani katon yanka ya raba goshinshi biyu.
Yau kuma ni ka ke kira yaya? Nayi mishi
tambayar don in hutar dashi girman da yake ta
kokarin bani sai kawai naji yayi maza ya ce, au
Baba-Baba kiyi bhakuri ai mancewa nayi nake kiranki
Yaya.
Sallamar yara naji na bar Hasiya na ce ta kula
min da girkina naje na budewa Yaya Ibrahim dakin
baki na sauke shi a ciki na kai mishi abinci da na sha
na kuma zauna don mu gaisa dashi gaisuwa irinta
yan uwantaka.
Yana kai lomar abincin bakinshi ya sake canza
min suna Anti ai baki san abinda ya faru da ni ba, ai
hatsari nayi na rantse miki, Anti ai in ban da rabon
za'a sake shan ruwa a gaba ba ai da yanzubabu ni.
Ai mota da ta fadi damu ai ni kadai na tsira shi
ne naji wadannan raunukan gama wani ko warkewa
bai yi ba, ya kwace min wani shafcecen ciwo a
kwaurinshi babu ko kyan gani tausayinshi yayi
matukar kamani sannu Yaya lbrahim na soma gaishe

69

shi.
Kan ka ce meye wannan ya lamushe abincin da
na kawo mishin na fita don in karo mishi sai kawai
nazo na samu wai har ya fara bacci, don haka na
koma naci gaba da aikin abincina cikin zuciyata dai
tausayin Yaya Ibrahim yafi konai damuna.
Ko ina Baba yake ko suna tare bari ya tashi daga
bacci sai in tambaye shi.
Wajen karfe biyar da rabi Ado ya dawo gida da
sauri naje na same shi na gaya mishi albishirinka, ya
ce goro na ce mishi su Yaya Ibrahim da tunda suka
tafi ake cewa ba a taba jin ga wanda ya ce ya gansu
ba.
Ya ce, eh na ce to gashi nan yau yazo, yana ina?
Na ce gashi can yana bacci a dakin baki, ba ka ga
ciwanwukan da ke jikinshi ba, hatsarin mota suka yi.
Ya ce, ayya! Ya wuce ya shiga can cikin daki,
nima amsawar tashi ta ban haushi, na juya na nufi
kicin din tsakar gida wanda nake aiki a ciki.
Ban yi aune ba, ban san yanda aka yi ba sai
kawai na jiwo ihu mai tsananin firgitarwa, na zare
ido tare da kasa kunne don kokarin tantance daga ina
ihun yake fitowa, ban gane ba.
Daga ina ne Hasiya? Cikin natsuwa naji ta ce
min watakila Baba ne yake dukan bakon nan don
naga ya shiga dakin da dorina a hannunshi.
Da gudu na nufi dakin ban san yanda aka yi ba

70
ganina kawai nayi a kwance kan Yaya Ibrahimn na
rufe shi da jikina, gigitaccen ihun da na kurtna shi ne
ya fahimtar da Ado har dani a dukan da yayi Ado
yana haki yana tambayarshi me ya kawo ka gidana?
Nima kazo ne kayi min abinda kuka yiwa
ubanku? Hannu biyu na saka Da rufe baki na zaro ido
jikina sai rawa yake yi saboda tsoratar da nayi da irin
zagin da Ado yake yi mishi, amma ko a jikinshi
muna da gai daku ne uwarku ce 'yar uwata itama bata
takowa in da nake ba balle ku.
Fita ka bani dan iska... nayi maza nace ni dan
uwana ne wurina yazo na soma kuka don ban taba
ganin duka da wulakanci irin wanda Ado yayi mishi
ba.
To nemi inda za ki kai shi ki kai shi amma in ki
ka bar min shi a gidannan kin sanni da kyau lokacin
da zan turo N.D.L.A su kama shi ba za ki sani ba,
sai dai kawai ki neme shi ki rasa.
Kuka sosai na soma yi na ce mu tafi Yaya
Ibrahim tunda dan uwana ba zai iya zuwa wurina ba
ai nima bani da wurin zama ya ce eh baku dashi kuje.
Tbrahim yaja ya tsaya a'a Anti ba zan zo in same
ki a gidan mijinki in kashe miki aure ba, kiyi zaman
ki kawai bar ni ni in tafi aini kadai ya kora na çe a'a
tare ya kore mu.
Na tasa Yaya Ibrahim a gaba muka fita muka bar
gidan, Ado ko Baba Yahya ban dauka ba saboda

71
Zuciyata takai natuka wa en zafi wulakancin da Ado
ya yi wa Ibrahim ba shi ya yi wa ba ni ya yi wa tunda
dan uwana ne wana ne uban mu daya mu kuma da yä
zauna a namu gidan rayiwar yanci yayi babu wani
wanda ya wulakanta shi. "
Har mun shiga mota mun zauna muna jiran
direba yazo mu tafi, sai gá Baba Tanirnu da saurinshi
yana bin motocin da ke todi yana leka cikin su har
yazo kan tamu yana ganina ya ce, fito k fito nan.
Muka fita muka bi bayanshi, ba ki kyauta min ba,
ko kadan ba ki kyauta min ba. Ban taba sanin ba ki
dauke mu iyaye ba sai yau.
Čabana ya fadijin maganar tashi, in kin dauke ni
matsayin uba ba za kiyiumin haka ba, na soma yiwa
Baba Tanimu kuka saboda jin abin da yake fada.
Yaya za ki. fita ki bar dakinki da sunan 6acin rai
ba ki sanar dani ba'? Wato nayi kadan ko? Har muka
isa gida bai bar maganar ba.
Cikin zuciyata nayi nadama da na tuna mai
babban allo ya gaya min cewar Hajiya Kubrah bata
taba tsallake shi taje ta kai kara gun nata iyayyen ba.
Saboda ta yarda shi din ubanta ne.
Muna shiga gida Ado muka fara gani zai fita da
Baba Yahya a hannun shi, mutumin banza mutumin
wofi, wato ban isa a zo wurina ba sai kayi hukunci da
kanka? Wato ni ban isa ba?
Wato in ban da yarinyar nan Hasiya tayi hankali

72

tazo ta gaya min da sai kawai 1yaycn yarinyar nan su
ganta a gida ni ban san komai ba, to. ina amfanin
girman nawa kenan?
Kayi hakuri Baba, Ado ya ba shi hakuri ya hada
mu yayi mana fada, ya kuma hana Ado korar Yaya
Ibrahim ya ce mishi wurina yazo ba wurinshi ba, ya
bar shi tunda dan uwana ne, muka dawo muka zauna,
amma ni da Ado ta ciki-na-ciki.
Rannan da daddare muka yi mummunan tashin
hankali ni da Ado yayi min wulakanci irin wanda bai'
taba yi ba.
Ai ke ba ki san kowa ba sai kanki, shi yasa ba ki
san girma da darajar kowa ba in ba naki ba ne, ba a
bakin ki naji labarin irin lalacewar da Mama ta yi ba?
Har kina gaya min wai wadaman mazaunan na
Mama da take juijuyawa tana tafiyar takama duk sun
zagwanye sunz ama kamar fata ko tsunma?
Sannan ina zaune ni Adamu ina zaune a inda kii
ka amsa wayar da Atika tayi miki tana baki labarin
Mama ta fadi har ta samu stroke tana asibiti, ba ki ji
kunyata bare tsorona ki ka bude baki ki ka cewa
Atika ke duk abinda zai samu Mama ba zai dame ki
ba.
In da abin zai tsaya ne a kanta ita kadai. ba zai
shafi 'ya'yanta ba. Yaya Habiba ta koma dakinta aka
ce miki eh, ki ka ce to madallah.
Kina nufin don naki rabuwa da ke kamar yanda

73
Mama tayi min umarni shi kenan hakan yana nufin
bana sonta ko bana ganin girma da darajarta?
Idanuwanshi suka baiyanar da bacin rai mai
tsanani wanda yayi dalilin da náyi magana naja bakina
nayi shiru saboda a yanzu tsoroni abinda zai taba
lafiyar jikina nake yi.
Na kuma san na saki baki na fadi maganganu iri-
iri akan Maman a gabanshi ban taba sanin basa yi
mishi dadi ba sai yau.
Rainà ni ki ka yi yasa kike iya fadin mugum'abu
a kanta a gabana ko kuwa ke din kin manta ne cewa
ita din madadın uwa take a wurina? Shiru nayi ban
iya ce mishi komai ba.
Ibrahim ba zai zauna mih a gida ba na gaya miki,
don ba za su pakāsa min yar uwa suyi sanadin
shigarta cikin musibar rayuwa ba, sahman su zo min
gida su zauna don sùna gadarar ga ki a gidan, in da
ba su lalace ba in da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login