Showing 30001 words to 33000 words out of 33160 words

Chapter 11 - MIJIN TACE 4 COMPLETE HAUSA NOVEL BY SODANGI.txt

na co mata ni wanne yafi ne cikin
biyun nan Inna? Tunda ke su duka biyun kin san
yanda suke kin zo kin samu an kuma zo an same ki?
Tayi murmushyi ta ce, ni kam a wurina ai dace ne
kawai.
Tunda ita rayuwar gaba dayanta sa'a ne, na tuna
mata da kalaman Mama a da cewar da take yi
'ya'yanta ba za suje gidan kowa ba zuwa za'ayi á
same su, tayi dariya ta ce ba gashi ba, kuma da aka zo
aka same sun sai aka kore su
Saboia sun kasa yin hakuri? Na ce haka ne, ta ce
ai babu mai cin ribar rayuwa sai yayi hakuri, na sake
cewa haka ne.
Mama tayi ta zuba ido tana kasa kunne ko zata ji
wate rigima ta tashi tsakanina da Ado, shiru babu
wata matsala, saboda yona matukar jin kunyata da
ganin girmana a dalilin na yarda da shawarar da ya
bani na in dan yi mishi kawaici da kuma kara.
Sai kuma hankalinta yayi matukar tashi ta rinka
fadin maganganu wannan aure da aka yi ai ba aure ba
ne an kawo 'yar mutane an ajiye a gida ana cutar ta.
Rannan ina daga falona na ganta ta fito kan
keken guragunta, tana tura tayoyinshi da hannunta
kofar dakin amarya taie ta tsaya saboda ba za ta iya
tura shi yı shiga ba. Ni yarinyar nan ana baki abinci
kuwa?
Ban ji abinda BilkisD ta ce mata ba na dai ga

145

kawai ta gyada kai ta ce au to, ta juya ta tafi. Ban san
yanda aka yi ba, daga tsayuwar bakin kofa tayi
magana sai kuma abu ya dawo in ta zo bakin kofar ta
tsaya sia ta kira Balkin ta tura ta su shiga ciki.
Ni kam ko a jikina saboda da na gaya wa Inna
ma abin da Maman take yi dariya tayi ta ce ai babu
abu mai dadi a rayuwa irin ka rayu kana addini kana
kuma yarda da kaddara na ce haka ne Inna.
Rannan sai kawai aka yi kacibis tsakanin Mama
da Ado a dakin amarya, shi zai shiga ita kuma z ata
fito ina jin shi yana fadin a'a-a'a Mama, ai kin ji
sauki tunda ki ka iya fitowa daga dakin ki ki ka zo
har nan ai shi kenan magana ta kare.
Mama tayi maza ta ce, a'a wane sauki? In ban da
karfin hali don in zo in duba wannan yarinyar abincin
da ake bata ne nake ganin kamar ba ya isanta, ya ce
eh wannan duk ai alamar samun lafiyarki nce tunda
gashi har kina iya shiga harkar da ba taki ba ce.
Don haka sai ki shirya za ki koma dakinki,
Mama ta soma kuka tana bashi hakuri, ya ce a'a aiu
ba za ki kasa zaman lafiya a naki gidan ki zo nima ki
bata min nawa ba.
Dama kwanaki an kira ni a gidan su aka yi min
wasu maganganun da nayi zaton da hannunkii a ciki,
tun a lokacin na gaya wa Mallam Haruna cewar ni
ban saba da irin wadannan maganganun ba.
Ban iya yin irin wannan surutun ba na kuma

146
gayawa ita Balkin cewar in aka sake kirana a gidan
Su kan wasu maganganun da ban san da su ba zata
koma gidansu. To ashe kece Mama, don haka zan
kira Baba an jima in gaya mishi yasa ayi miki fentin
dakinki ga ki nan zuwa, ai ba rabuwa ku ka yi ba.
Na dai kyale ki a nan din ne kawai don na gane
ba kya son zaman can din amma ba zai zama dalilin
da kuma za ki nemi kulla min fitina a cikin iyalina
ba.
Mama tayi kuka har ta gaji ta bai wa Ado hakuri,
har taji babu dadi ya ce a'a Mama ki koma dakinki
kawai ita mace ai bata da wani wurin da ya fiye mata
dakin mijinta daraja in kina da matsala kawai ga
sabuwar waya nan na saya miki ki kira ni ki gaya
min, nima kullum zan rinka kiranki muna gaisawa.
A haka Ado ya kammala mata shiri ya kuma sani
wai ni da yara muyi mata rakiya na ce mishi to, muka
je muka kwana muka dawo. Sai bayan dawowan
nawa ne naji labarin wa duk wanda yazo sai ta gaya
mishi cewar ni nasa Ado ya kore ta.
Bayan kuma ita din ita ce tayi sanadin aurena da
shi, amma a yau na shiga tsakaninta da dan uwanta
na raba su.
Ni kam tunda nayi sa'a Mama ta yi wa dan
uwanta abinda ya tattara ta ya maida ita inda dama
mazauninta yake, sai naji sakat na samu sa' ida, na
gane ashe ba kishiya ce ma babbar matsalata ba, ta

147

rayuwa Mamace to na rabu da ita shi kenan zance ya
kare.

**. * *.
Shekaru biyar ne yau tunda Dr. Ado Sulaiman ya
yi min amaryarshi ta farko Hajiya Bilkisu bayan ita
ya kara bayan wannan ma ya sake karawa.
Don saukin ma su din basu zauna ba can ta bare
musu suka watse, kenan in ana sabawa to na saba a
yanzu ma naji yana cewa da wata akan hanya.
Duk da har yanzu na kasa daina kishin mijin
nawa, ban cika jin zafin shi sosai ba, saboda ya riga
ya samu daukaka mafi yawancin aurenshi na baya-
bayan ba shi yake nema ba, yana zaman zaman shi ne
kawai za ki ji an ce Dr. ga wata tsuleliya an baka.
Shi kuwa sai ya ce wai mutumin kirki baya
maida hannun kyauta baya, don haka nake yi mishi
sassauci mai yawa.
Amma wai duk da hakan da nake yi in sun fitan
sai ka ji su da iyayensu dama Mama suna ta yada
zance cewar wai din ni nake hana shi zama da
amaren nashi saboda fin karfin da nayi mishi.
Iyakar sa'ar da nayi ita ce ni dashi da akwai
fahimtar juna mai yawa a tsakaninmu, a duk lokacin
da ya ji ana yada irin wadannan maganganun zaunar
dani yake yi ya rarrashe ni.
Rabu da su Humairah, toshe kunnuwanki kawai

148

kiyi kamar ba ki ji su ba, ni kam ai nasan kaina na
kuma san ki nasan kishi mai tsananin zafi da na
fuskanta a wurinki, ai wanda ki ka nuna ne akan
auren Bilkisu.
To ba gashi kin yi mata adalcin da ku ke zaune
lafiya tana kuma ganin girmanki ba? Surukuta ce irin
ta iyayensu ban saba da ita ba surukuta irin ta zamani
wace babu kawaici ko kara a cikinta.
Kuma babu kunya balle nuna sanin ya kamata, na
riga na saba da surukuta irin ta Inna wacce komai
suruki yayi wa 'yarta ba za ta daga ido ta kala ba, sai
dai in shi da kanshi ya yi tunani.
Kunyar kanshi ya kama shi kullum tsakaninta da
yarta nuni ne na alheri bi mijinki, kyautata mishi,
kiyi mishi biyayya, saboda girman hakkinshi da yake
kanki yawa ne da shi.
Bisa wannan dalilin ne yasa har yanzu dai ni da
Bilkisun mu biyun ne dai a gidan na Dr. 'ya'yanta
biyu dukan su maza, Sulaimañ da Adam. Nima na
kara daya da kyar bayan nasha kafirar wahalar da na
kubuta da kyar saboda matsalar da na samu da
mahaifar tawa.
A dalilin kaka ba ihata robar nasara da nàyi don
haka ina da mai sunan Babana Sirajo wanda
Sulaiman ya girma da shekara daya shima ya girmi
Adam da shekara daya. To har yanzu dai itama uwar
tasu shuru ban sani ba ko itama ta yarda da hikimar ta

149
maigidan ne na bin tsarin iyali don a samu
wadataccen lokacin kulawa da juna.
A wannan lokacin gaba daya 'yanmatan gidan
nawa su Umahmah, Nusaiba, Hindatu da Aisha suna
dakunan mazajensu har da rabo a tsakani saboda Ado
yayi musu auren ne da sha bakwai-bakwaj.
Sai dai har yanzu suna can suna ci gaba da
karatunsu a Jami'o'i daban-daban, shima kuma mai
daukan nauyin, shima Baba Yahya yana kasar
Malesia ya tafi karatun digirin shi na farko kan aikin
zane.
Sai su Zainab, Khadija da Fatima sune suke
Makarantar secondary ta Marigayiya Hajiya Maryam
Babangida, don haka a gidan a yanzu Sulaiman ne
kawai sai Sirajo da Adam.
Wadanda guda biyun farkon Sulaiman da Sirajo
a wurina suke duk inda zani kuma tare dasu nake
zuwa, Adam ne a wurin uwarshi.
Gonata tayi matukar bunkasa, don' haka a yanzu
a shekarun da nake da su guda arba'in mafi yawañcin
al'amurana da lokutana da farin cikina kan tafi ne
kan abin da ya shafi 'ya'yana, 'yan uwana, iyayèna,
gonata, hidimomina, .kwalliyata, karatuna da har
yanzu ban daina ba, da wasu abubuwan da suka
danginci hakan.
Aure-auren da Ado ya tsunduma yi a shekarun
bayan nan sun kara fahimtar dani cewar a shekarun

150

mace na girmanta tana bukatar farin cikin abubuwa
da yawa da nasarorinsu kafin tata nasarar ta tabbata.
Babba daga ciki kuwa shi ne nasarar 'ya'yana ta
kintsuwarsu, su kama hanya ta zama mutanen kirki,
wannan shi ne gaba da komai a wurinta, sabanin
lokacin kuruciyarta da zaman lafiyarta da mijinta
kawai ke gamsar da ita har kullum rayuwar Mama
kan zame min darasi saboda masu hikima.
Sai suka ce wanda duk bai hankalta ya lura da
abinda ya samu wani ya zamo mishi darasi ba, to
wani zai lura da abinda shi zai same shi ya hankalta
dashi ya koyi darasin rayuwa.
Rugujewar rayuwar Mama ta rasa farin ciki,
kwata-kwata mijinta ya subuce mata, gidan da take
gadara dashi ayfi karfinta ya faru nhe a dalilin
rugujewar al'amarin ya'yanta har a yau kuma a haka
take a zaman hakuri a zaman babu, yanda za' ayi
tunda har yanzu ita da Babana dai gasu nan ne kàwai
har yanzu babu wanda yasan inda babu yake.
Har yanzun su Anti Sha'awa basu wuce zawarci
ba, tunda tayi aure yáfi a kirga, Suwaiba sai kwanan
nan ta sau wani Dattijo ya aure ta bayan 'bukin su
Umahmah daga Giyade matanshi uku ita ce ta hudu.
Tana can Giyade a gidan kauye ga iyali wannan
dalili yasa ban taba yarda na sa kaina cikin 'damuwar
aure-auren Ado ba, balle in rinka daga ido ina ganin
abinda yake yi da 'yan kananan matanshi, har in je

151
ina neman in takurawa wani ko Wata.
Da na daga ido ni'imomin da aka yi min nake
kalla in tuna rayuwata da ta mahaifiyata a lokacin
kuruciyata, rayuwar rashin yanci, Kaskanci,
wulakanci, rayuwar da uwarmu zaune kawai take
tanfar ba matar gida ba ce.
Mu ma 'ya'yanta ba a dauke mu wasu 'ya'ya ba,
sai gashi a yau duk ya wuce, ina tuna wannan sai in
yi ta yiwa Ubangiji godiya, in na ga ma kamar Ado
zai yi wani 6are-6aren da zai 6ata min ko ya.daga
min hankali a kan wata.
Tattara shi nake yi in sa shi a.gefe bana kallon
abin da yake sai shi da kanshi yaga kamar abin nashi
zai wuce makadi da rawa sai ka ganshi yayi maza ya
dawo yana fadin ni me nayi wa yarinyar nan ne nake
ganin kamar sha min kamshi take yi tana wani
shasshare ni?
Ya rinka lallami kenan da kalamai masu dadi, na
fa je wajen Inna tana gaishe ki ko Umahmah ta ce
kaza, don yanemo dalilin da hira zai yi nisa, sannan
a hakan sai in ji itama matar gidan da ake ganin
zaman lafiyar tamu tana korafin ai ba shi da wani
zance sai nata in ma labari ya zauna zai, baki to ba ki
sanin yanda ake yi sai kiji labarin ya koma nata da
iyayenta ko da 'ya'yanta.
A haka sai na kara fahimtar cewar shi dai namiji
mai mata biyu ko uku a tsakani kawai yake, bai cika

152
samun gwaninta mai dorewa wurin guda daya ba, in
dai har akan adalcin ya tsaya ba karkata yayi ba.
Don haka yana da kyau wata tafi wata hakuri, da
kuma dan saurara mishi don a samu saukin al'amura
kan haka na sake yankewa kaina hukuncin kara
hakuri da mijin nawa a kowane lokaci a kuma
kowane hali.
Rannan mun ziyarci kasar Malesia ni da shi don
kaiwa Baba Yahya ziyara, mun ziyarce shi, a
makaranta ya kuma biyo mu masaukinmu don yi
mana hira suna zaune shi Babanshi kan kujera guda
daya irin zaman da suka saba yi tun yana dan yaro
dan karami.
Ado yana rungume da kafadar shi yayin da shi
kuma ya kwanto da nashi kan kafadar Baban a haka
sukc hirarsu, ni kam ina can a gefe kan wata kujerar
ni kadai kallonsu kawai nake ina tunani gaba daya
Baba Yahya ya sauya ya zama tanfar ba shi ba.
Ga wanda yayi shekaru bai ganshi ba, zai yi
wuya a yau ya ganshi ya gane shi. Gaba daya ya zube
kibar tashi babu ita, tebar shi ta zama kamar ba a
taba yin ta ya zama wani -dan dogon saurayi dan sirirn
wankan tarwada, kamanannin nashi na yanzu sun fi
kama da kamannin Kawu Ado a farkon zuwanshi
gidanmu.
Hira sosai suka yi da Babanshi tattaunawa suka
yi tayi kan karatun nashi da kuma bambancin

153

nomanmu na kasashen Africa da kuma na kasashen
da suka samu ci gaban zamani, tunda shima Baba
Yahya aikin gonar yazo karantawa.
Sai da yaga dare ya fara nisa sannan yayi mana
sallama da nufin komawa cikin makaranta in da yake
zaune.
Ado ya mike ya tsaya yana kallona bari in raka
shi cikin makarantar in dawo na ce mishi to a dawo
lafiya.
Ba mu baro kasar Malesia ba sai da muka kai
ziyara wasu manyan gonaki da Baba Yahya ya ba shi
shawarar ziyara saboda itama Malesia tana cikin
kasashe da Gwamnatocinsu ke bayar da muhimmanci
kan aikin gona.
Mun dawo gida babu dadewa muka nufi Bakori
saboda saukan ruwan saman da aka samu da ya
gamsar da noma na soma shukan wannan shekara.
Wata sabuwar gonar Ado ya bude a can ta
noman masara zalla wacce ba zai yiwu in tsaya in
dewatanta girmanta ba, a bisa tsarin da aka shirya
kuma za a rinka noma masarar ne sau biyu
maimakon sau daya.
Ina tsaye tarc da 'ya'yana Sulaiman da Sirajo
muna kallon aikin da ake yi Sirajo ya wage baki da
karfi yana hamma. Na kalli Sulaiman da ke rike da
hannun Bala na ce mishi dubi irin hammar da
Kaninka ke yi saboda baka koya mishi ladabin

154
hamma ba.
Yayi maza ya kalli Sirajo ya ce mishi, kai ba
haka ake yi ba in zaka yi hamma rufe baki ake yi don
kar shedan la'ananne ya shiga bakin in da hannun
dama zaka rufe sai kasa tafin hannu in kuma da
hannun hagu ne sai kasa bayan hannu.
Ado ya Zubaida yaron ido yana kallonshi cikin
murmushi yayin da Bala ke kallon shi yana fadin
ashe Babangidan Malami ne, da kuwa har naji
Umahumah tana fadin wai zata zo ta kwashe ku a
gaban Goggo don ta lura shagwabarku tayi yawa
saboda wai ba irin tarbiyar da aka yi mata ake yi
muku ba.
Ado ya kyalkyale da dariya ni kam cikin
zuciyata tunani nake yi na ranar da Ado ya kawo min
Bala da Hamza a matsayin 'yan almajiraina gaskiyar
da Bala ya riki Ado da ita, tayi dalilin da ya so shi ya
sanya shi karatun boko.
Bayan yayi haddar Alkur'ani har daga baya ma
ya bashi diyarshi Umahmah bayan ga mutane da
yawa 'ya'yan manya shi kam Ado ya ce ai babu wani
babban da ya fiye mishi Bala tunda makarancin
Alkur'ani ne kuma mai gaskiya ne.
A zuciyata na sakefadin babu abin da tafi yawa
babba a lokacin da yake zaune da na kasa dashi illa
adalci don bai san abin da gòbe zata haifar ba.
Kallon Baban na sakeyi cikin natsuwa na ce

155

mishi Bala, yayi maza ya amsa cikin natsuwa da nuna
ladabi ya ce min na'am, na ce mishi yanzu a irin
wannan aikin da kuke yi a gonakinku kuna da wani-
shiri da kuke yi na taimakon kananan manomna?
Cikin ladabi Bala ya ce min ba wannan ne asalin
taimakon da kananan manoma ke bukata ba Goggo
saboda injinan da muke amfani da su wajen yin kaftu
kunya da shuka injina ne da suke karawa manomi
kashe kudade masu yawa a gonarshi saboda suna
tono kasa tun daga can cikinta.
Ita kumna kasar wannan da muke takawa tafi
kowacce kasa danko da kuma sinadarin da amfani ke
bukata, shi karamin manomi yafi bukatar shanun
garma, muna kuma bada su bisa farashi mai
rangwame har ma mu daga kafa muyi lamuni
matukar mun san za'a biya mu muna bada taki bisa
farashin da Gwamnati take bayarwa.
Haka nan da akwai kungiya da gonarmu ke
jagoranta da take karbanwa kananan manoma rancen
da babu ruwa a ciki.
Ado ya galla min harara alamar muna takaicin
shi a zahiri ya ce kai ke ka surukutarki ba irin ta Inna
ba ce jeka wurin aikinka kaga abinda suke yi ka ji
Engineer Bala yayi min sallama ya tafi.
Yana barin wurin na kallo Ado na ce mishi
tausayin kananan manoma nake ji Dr. jaruman
manoma irin su, Baba Taniu wadanda jaruntakar

156

rayuwarsu ke farewą kan gona guda daya babu wani
ci gaban da suke samu.
Ado ya ce ch, Humairah ai kin san duk wani
abinda ilimi zai yi aiki a cikinshi to kuwa za ki tarar
da banbanci mai yawa tsakaninshi da abin da karfi ne
kawai jagoranshi.
Na cc to in kuwa haka ne Kawu ai yana da kyau
kuyi ta janyo hankalin masu ilimin mu na arewacin
kasar nan da su dawo su tsunduma sosai cikin harkar
noma tunda nikam a wurina banga sana'ar da ta fita
riba ba, musamman a wannan lokacin damnu Jama'ar
arewa uke cikin halin da muke ciki.
Muke fuskantar abinda muke duskanta muke
kuma ganin abinda muke gani, gaba daya arewarmu
ta zama tanfar ba ita ce arewar da iyayenmu ke bamu
labarinta ba ita da shugabanninta.
A yau mun zama komai na koma baya namu ne
rashin kishin kai namu ne, rashin aikin yi ma namu,
talauci ma nau, rashin ilimima namu rashin mafadi
ma namu rashin hadin kai namu, rashin tsaro ma
namu, rashin zaman lafiya...
Ado ya katse ni ta hanyar fadin komai a
Humairak, sannan da za'a kama aikin gonan gadan-
gadan fa da kin ga anyi magana mafi yawancin
matsalolin namu kamar talauci da rashin aikin yi
wadannan guda biyun kuma in da za ayi maganinsu.
To da sun isa su zama sanadin da za'a sau saukin

157

fitintinu da tashin-tashina, musamman ma da yake ita
arewa ai ta taba yi an gani, an taba yin lokacin da
kasar nan gaba dayanta ta dogara kacokan kan
tattalin arzikin da ake samu a arewa wanda Noma ne.
Cikin natsuwa na ce haka fa aka ce kawai Kawu
ya dan yi tsaki nuna alamar tsananin damuwarshi da
6acin ranshi kan sakacin damu da kanmu ne muka yi
wa kanmu da kuma saki na dafen da muka yarda aka
yi mana kafin ya sake sakin ajiyar zuciya mai karfi.
Sannan ya ce Ubangiji dai yana kallon komai
yana kuma sane da komai ya kuma san dalilin da
komai yake faruwa, mu kuma yasan gare shi muka
dogara gare shin kuma muke neman taimako muna
rokonshi ya taimake mu ya sanya mana sauki cikin
wadannan al'amura da suka addabe mu suka addabi
yankinmu na arewa.
Ya dawo mana da zaman lafiya da duk wani abin
da muka rasa albarkar Alkur'anin da muka yi Imani
da shi muke kuma karanta shi kullum.
Nayi maza na ce amin Kawu.

**
A gida a zaune nake ni kadai cikin falona saboda
yara suna makaranta, Bilkisu tana nata wurin yayin
da maigidan ya nufi Abuja tare da sabuwar
amaryarshi mai shekaru sha bakwai, tunani nake yi
kan shekaru ashirin da daya na rayuwar aure na da

158
Ado, auren da ya sha gwagwarmaya da kwaramniya
iri-iri.
Ya fuskanci matsaloli tun daga na iyaye har
kawo kan dangi da abokan zama kafin ya tsunduma,
cikin matsalar kishi ko in ce kishiyoyi.
Wadannan matsalolin da kwaramniyar duka basa
iya sani in rufe in mance alheri, jarumtaka da
tsayuwar mijin nawa a kaina balle ina daukarshi ina
jefa shi cikin mazan da ake cewa wai su din ba 'yan
goyo ba ne.
A'a, ni kam nawa mijin da na goya shi ban ga
komai ba sai alheri har ma nake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login