Showing 3001 words to 6000 words out of 33160 words

Chapter 2 - MIJIN TACE 4 COMPLETE HAUSA NOVEL BY SODANGI.txt

sai na kasa ganewa na kasa gane wanne zai
dauka cikin biyun?
Namiji zan dauka a fahimtar da na yi wa Ado ko
1amiji zan dauka a fahitar su Ruwailah? Mama har
da Babana?
Da na kara nazari cikin tunanin hankali sai naga
to ai ba zai yiwu in karyata fahintar su Ruwailah ba
tunda har da Babana a cikinta. Haka nan ba zan
Karyata mijina kai tsaye ba, saboda girma da darajar
shi a wurina.
Don haka sai naga to me zai hana in bar komai na
bar wa zamani lokaci mu kara tafiya cikin al'amaring
rayuwa a sannu don in kara yin ilimi da fahitar da
zan gane wane ne cikin biyun'?
Zan gamsuda nasu ra'ayin? Tunda ai kwata
kwatana ma yanzu ne nake cika shekaru ashirin da
daya a duniya, don haka bai kamata in fara yankewa
al 'amura hukunci ba kallo kawai ya kamata in yi tayi

19
ana kara ilimi da fahinta, musamman ma da yake
masu ra'ayoyin nan duka biyu ba sa'o'ina ba ne.
Watakila kowane bangare a cikinsu yana da
madogarar da ya dogara da ita, wacce shi din ganau
ne a kanta ba jiyau ba.


**

Mun isa gidanmu lafiya, Inna tsaya cewa an
karbe ni? To na tsaya bata bakina ne, sai dai abinda
yafi komai bani mamaki shi ne wanda yafi kowa
karban nawa da nuna farin cikin ganina wai Babana
ne.
Duk da cikin dare uka isa, daren ma har ya fara
nisa dakin Mama na fara shiga saboda umarnin da
Adon ya bani kenan amma wai a wannan tsohon
daren ina gaida Mama, 1donta yana kan zanina tana
kokarin tantancewa super ta asali ce ko ta
kwaikwayo?
Ni kuwa na gyara mata sosai don taga abin da
take son, cikin zuciyata kuwa cewa nake yi uh uhun,
ba a dai bar hali ba.
Na fito daga dakin Mama jikina a sanyaye
kwarai saboda tsananin ranmar da na gani a tare da ita,
gashi tayi duhu ga wasu wunduna guda biyu a
tsakanin hakoran gabanta guda biyu.
Nayi tunanin abinda ya baddasa mata hakan, sai
da kyar na iya tunawa da cewar jajayen hakoran da ta

20
sanya ne sanda ta tafi aikin Hajji suka tafi suka bar
mata bakin nata, a zuciyata nayi dariya na ce kai
wadannan hakora sunyi tsiya.
Maimakon su tafi su bar mata natan sai ga hadfa
har dasu? Na ce to ko da yake dai ai tayi ado dasu, na
sake tunawa da irin adon da Mama tayi da hakoranta
na ce to sun mori juna.
Na shiga dakin Innata wacce ko lekowa mu hada
ido bata yi ba tun zuwana gidan, jikina a sanyaye kar
dai duk mutanen gidan haka suka zama tunda Baban
nawa ma ya zube ba kamar da ba, amma kam nashi
wasa ne akan na Mama
Inna tana nan kalau dinta, sai ma kara murjewa
da tayi, ta yi shar gwanin sha'awa da ita, kuruciyarta
sai karuwa take yi, tayi kwalliyarta daidai da ita,
gashi komai da kuma ko'ina dinta sai kamshi yake yi
a cikin kuma tsabtar da ta dace da shi.
Zama a gaban kujerar da take zaune nayi a kasa
na kwantar da kaina a jikinta ina shakar kamshinta,
waiyyo Inna! Na fadi hakan cikin murya mai rauni
kwarai.
Ashe kuna tafe? Ai bai fadi kuna hanya ba, sai
dazu dazun nan da ya tabbatar kun kusa shigowa gari
wai don kar in yi ta damuwa.
Na kara makalewa na kara kwantar da kaina a
cinyar Inna sosai, cikin shagwaba na soma ce mata
naji mararinki Inna, naji marmarinki na ii mararinki

21

har na rasa yanda zan yi ke kuma ki ka ki zuwa."
Ta ce, to ba muna gaisawa a waya ba? AAi
abubuwan rayuwa ma sunyi sauki, ko baka ga mutun
ba zaka ji muryarshi ku debewa juna kewa, mu da
iyayen mu suka bada mu ai gamu gasu amma basu
ganmu ba basu kuma ji muryoyin namu ba sai da aka
dauki lokaci mai tsawo.
Sa'adatu tazota wuce tana goye da Umahmah a
bayanta, Babana ne yake kwala nata kira, a zuciyata
na ce kai lalle wani sabon abu yana faruwa a
gidanmu, ko ma in ce ya faru. Babana yana
mu'amallah da kowa daidai da cewar mu'amallar a
gaban Mama tana kallo lalle an samu yancin
rayuwa.
Sa'a ta sake dawowa tana kallona cikin
murmushi, "Kai Anti, wane irin tsarata kika yi haka?
Na kalle ta cikin natsuwa na ce mata, ban ma ganta
ba Sa'a, sayayyar yayanki ne.
Tayi murmushi, to wai in ji Baba a ina za a sa
miki kayan gasu nan ana shigowa da su, na kalli Inna
naga sha'aninta take yi.
Na maida kallona wajen Sa'adatu na ce mata kin
ga ni Sa'a akwatin kayana kawai za ki dauko, tsaraba
asa a dakin Baba ko falonshi, ta ce haka ne ta juya ta
fita.
Rannan ni da Inna muna kan gadonta yayin da
Umahmah take wurin Sa'a a dakinsu, na kalli Inna

22

bayan mun gama magana da Ado a wayar Inna nayi
murmushi na ce, inna ina ta tunanin yanda zan gan ki
gabana yana ta faduwa sai kuma na gan ki fa da ke.
Komai din ki kalau, sai ma abinda ya faru ga su
Baba karani da...ban san yanda aka yi ba kasa fadin
sunan Adam nayi kamar yanda na saba, ban taba
sanin sunan yana yi min nauyi haka ba sai yau.
Don haka na bar fadin sunan na ce duk sun girmna
Inna, komai na ki a cikin rufin asiri yake.
Inna ta saki wani irin lallausan mnurmushi ta ce,
ai haka al'amarin Ubangiji yake, wani lokaci sai ya yi
maka wani abu, kayi ta bakin ciki saboda wauta da
ajizanci na rashin sanin abinda yake boye.
Sai daga baya a hankali sai ka gane ai wanan
abin da ya baka shi ne alherin da kullum da kullum
ka ke rokon shi ya ban, ba tare na fahimci in da
zancen Innan ya dosa ba na ce mata haka ne Inna sai
naga ta zuba min ido cikin tsananin natsuwa ta ce
min ki kadai nasan irin bakin cikin da nayi akan
aurenki.
Ni kadai nasan irin kukan da nayi a bayan ido
kowa, ni kadai nasan tunda aka furta auren ban sake
rufe ido cikin dare nayi bacci ba, gayawa Ubangiji
ina rokonshi ya kawo wani dalili da auren zai fasu.
Ba tare da wata fitina ta auku ba, in kuma
kaddara ce sai an yi, to ya hana su cutar min da ke ya
kuma tsare min ke daga duk wata fitina, ya kuma

23
nuna mnana alheri mai yawa bayan hakan.
To gashi nan a yau ba a je ko'ina ba auren naki
ya zama shine aure mafi 'yanci da duk yaran
gidannan suke yi, gabana ya fadi jin abinda Innan ta
fada, na kuma san da iyakacin gaskiyarta take yi.
Don haka nayi shiru kawai ina sauraronta, ta ci
gaba da cewa, auren naki shi ne aure mafi zaman
lafiya da kwanciyar hankali, cikin raina na sake cewa
uhun, Inna kenan, ko dai don ban tona miki abinda
nake ciki bą?
Shi nekuma auren da yafi kowanne zamo min
sanadi na rufin asiri mai yawa, shagon nan da yaron
nan ya bar min ai ba karamin alheri ya bar min ba
Ga wannan yaron da aka sanyawa suna kina ta
kuka ina baki hakuri don bai kamata komai in biye
miki muyi tayin abu ba, ashe shima alherin ne, na
samu A.C saboda shi.
Na samu albashin wata sabo da shi, nayi maza na
kalli Inna na ce, albashi? Ta ce, eh, bai gaya miki ba
ne? nayi maza na ce, a'a Inna.
Ta ce, ai tunda mijinki ya soma aiki bai taba
fashin aiko mishi da kudin madararshi ba, a zuciyata
na ce uh uhun, Inna tana ta famann murna kan
wadannan abubuwan don ma bata san wani alherin
da Adon ya sake aiko mata ba.
Sai na ji ta ce min, shi yasa dukanku a yanzu
nake gaya muku dama duk wani wanda zan gayawa

24
ya ji, kullum ka tsaya akan yin addu'a, kar kuma ka
cuci kowa, a kan saninka.
Abinda duk ya same ka kuma ka dogara ga
Ubangiji kar ka yarda zuciyarka ta raya maka cewar
wani ne yayi maka ko da kuwa a zahiri shi ne sanadin
abin.
In ka nemi abu baka samu ba kuma ko wanda ba
ka zato yazo maka to ka roki Ubangiji ya zama shi ne
mafi alheri a gare ka, tunda duk al'amarin nashi ne.
Cikin natsuwa na ce mata haka ne Inna.
Rannan haka muka kwana muna hira ni da Inna
akan gadonta muna kwance yayin da itama Sa'a ta
kwana hidima da Umahmah, wacce ta ki yin bacci
tana 'yan koke-kokenta a nasu dakin.
Ko kawota kuma bata yi sai in Inna ta ce to tunda
ba ki da nonon da za ki baiwa yar taki ai gara ki
kawo ta a bata ko ta kara jin dadin rikicin nata, a duk
lokacin da na karbi Umahmah ina bata nono Inna ta
rinka kallonta kenan tana bin gabobinta tana dubawa.
A duk sanda ta gama dubawan kuma sai ta ce to
yaushe wa ya taba sanin wannan shi ne abin da zai
faru?
Ni kam ban mike na gyara kwanciya da nufin yin
bacci ba, sai da aka yi kiran sallar farko, Inna tayi
maza ta kallen ta ce, wannan ai shi ne karya, ki
kwana kina magana Asuba tayi ki ce za ki yi bacci
Ai mikewa za ki yi kivi alwala kivi nafila kafin

25
lokacin sallar tayi.
Ina idar da sallah su Atika da sauran yan uwa
suka soa kiran wayar Inna suna yi min sannu da zuwa
tare da fadin ga sunan zuwa, don haka na mike naje
nayi wanka da ruwa mai dui na watsake, nazo na
zauna ina shafa. Sa'adatu ma tana sanyawa
Umahmah kayanta, suma wankan suka yi.
Kai Anti, kin iya sayen rigunan yara, na ce bani
ba ce Sa'a kai ji wannan ma, wanne zan sa mata? Ji
wata ma, kai ga wata. Inna ta ce, da dai kin hakura
kin sa mata guda daya yau da gobe sai ki ga kin
sanya mata sauran ma, kin gansu a jikinta.
Kwalliya sosai nayi, wata super na sake daukowa
gara ta jiya da nazo da ita ma na taba daurata,
wannan sabuwa ce dal, Sa'a ta kalle ni tayi dariya ta
ce "Anti ai ke har kin fi ma matan masu kudin daura
zannuwa.
Nayi murmushi na ce, "Wannan shi ne iya shege
matar me kudi bata daura zani ta daura gwal ta hau
mota me numfashi ba me tayi?
Inna tayi murmushi ta kalli Sa'adatu ta ce mata,
kawo yarinyar ki kawo mata ajiyarta, ta kawo mata
ita ta wuce cikin dakin Inma, wata 'yar leda ta kawo
min wacce da gani na sani daga Saudi take, ga kuma
alamarta, ga yan akwatina a ciki har guda uku.
Daga ina wannan Inna? Ina bude su ina tambaya,
sarkokinki ne da ki ka tafi ki ka bari na baiwa Mama

26
sanda za su tafi aikin hajji da Aliya, na ce ayi ciko a
canzo miki sarkoki ne guda biyu babba da karama,
ga kuma warawarai guda hudu da zobuna biyu,
wanda ni su suka fi daukan hankalina ma.
Don nan take na zuba su a hannayena ta kuma sa
zobunan, in ban da Inna ta ce in sanya karamar
sarkar ma ni ka da hakan ma ya ishe ni. Godiya mai
yawa nayi mata.
Na tashi na fito tsakar gida saboda jin da nayi
Babana yana tambayar wai ni Aisha bata tashi ba ne?
nayi maza na ce ai ban ma kwanta ba Baba, wanka
nayi.
Akan katuwar shifidaddiyar tabarma na same shi
a tsakar gida yana zaune wanda wannan-ba wani abin
mamaki ba ne, dabi'ar gidan ne yin hakan, abin
maakin dai shi ne, yau shi kadai na ganshi zaune
akai, ban ga Miama ba, ban ma ji motsin fitowarta
wajen ba tunda gari ya waye ban ma ji wo muryarta
ba ko da daga cikin dakin ne, shiru.
Sai Zubaida da ke ta faman kai-kawo tsakanin
kicin da tabarmar Babanmu.
Kai Antin Sa'adatu kin yi kwalliya kin kuma yi
kyau ba an ce min garin naku kauye ne ba? Na kalli
Zubaida nayi murmushi na ce, Anti kenan. Karo na
farko da bakina ya yarda ya kirata Anti, ba akan an
tilasta mishi ba.
Babana yayi tsaki ya ce, ka ji wani zance wurin

27

yarinyar nan, to harkar yau aljihunka ba shi ne
birninka ba? Kana zaune a birni ba ka da ko kwabo ai
ka zama dan Rauye, sai dan kauye ya ci duniya in
yana da kudinshi kai baka ci ba.
Tayi maza ta ce, haka ne kam, itama bin atanfar
tawa take yi da ido, a zuciyata na ce itama ta koya
wurin Mama, zuwa can kuma sai naji ta ce mu ma fa
atamfofin da ya aiko mnana super ne, ban tanka mata
ba
Na kalli Babana wanda shia dadin ganina ya
kama shi, ga kwalliya mai kyau mai kuma tsada, na
ce mishi Baba bari in je in gaida Mama, ya ce to kar
ki dade, don yanzu zamu karya. Me ki ke so ki karya
da shi?
Na ce duk abin da Anti Zubaida tayi dashi zan
karya. Yana murmushin jin dadin ganin mu'amallata
da Amaryar tashi, Sa'adatu ta kawo mishi Umaimah
daidai zan shiga dakin Mama.
Sau biyu nayi sallama katin ta amsa, bayan tana
ganina ina ganinta, na ce mata sannu Mama, ta ce
yauwa sannu kadai, muka sake gaisawa ba tare da ta
tambayeni Ado ba, balle 'yarshi.
Ni kuwa na bararraje na zauna mata a daki sosai,
cikin zuciyata ina fadin abinda ka shuka shi ka ke
girba, komai na dakin yayi dikin-dikin alamar datti
ya kama shi saboda ba ta shi ake ba, ba a da lokacin
shi balle a samu zarafin gyara shi.

28

Wai Mama da Babana suna hade a gida amma
babu mai kula wani, kowa harkar gabanshi kawai
yake yi, in da wani abin da ban taba zaton zai faru
ina raye ba ai shi ne wannan.
Ni 'yanjakar ubannan sun ma zo sun gaishe ki
kuwa? Daga waje Babana ya daga murya yayi min
wannan tambayar, nayi kamar ban gane su waye ba,
tunda ina jin motsin mutane a dakın Mama, na kuma
san su Suwaiba ne sun ki fitowa ne kawai don kar
muyi ido hudu da su.
Watakila suna tunanin kwana daya ko biyu zan
yi, su waye kenan Baba? Cikin natsuwa da murmushi
mai yawa don dai ma Mama ta kara sanin mun shirya
da Baban nawa, nayi mishi tambayar.
"Wadannan 'yanjakar uban mana." Ya sake yin
zagin, mamaki ya kama ni ban san Babana da yawan
zagi ba, watakila itama Mama abin ya dame ta, don
wani mummunan tsaki naji taja kafin naji ta ce.
"Kai Allah kenan, rayuwa dai bata yi ba tunda an
kare da zage-zage. Da sauri na kalli Mama saboda
jin maganar tata dan kirin ya rage in kyalkyale da
dariya, saboda yanda ta tsuke fuska ga ta kuma dama
ta zama 'yar karama.
Wadannan yan jakar uban Mama su Habiba
masu gadon mugun abu ai suna nan a ciki."
Gabana ya yanke ya fadi, cikin tsoro da kunyar
masu gadon mugun abin da yake fada nayi maza na

29
ce, a'a Baba, ai ma ba laifinsu ba ne nawa ne, da na
yi wa gidan shigowar dare.
Da sauri na mike na nufi can cikin dakin na
Mama na barta tana tsaki tare da fadin wannan yaron
ai wahala ta same shi, tunda ya gamu da mutane
marasa Imani, balle tausayi." Ko a jikina.
Ashe kuna ciki? Nayi tambayar daidai na daga
labulen kofar wanda ya zama tanfar ba na Mama ba
don datti. Abinda na ganin yayi matukar kadani,
tukunyar alala akan risho a bayan kofar Mama yana
tafasa, ga Anti Sha'awa da Habiba suna kwance kan
katifar da ke yashe a kasa sun tasa 'ya'yansu a gaba
suna basu non.
Suwaiba ce a gaban tukunyar tana rantsuwar ita
da kanta zata raba don ba za ta yarda ta bar musu ba
su kwashe su baiwa 'ya'yansu, su bar mutane da
yunwa.
Na kalli 'ya'yan sun kai biyar ban da masu shan
nonon, sun takura waje daya gaba dayansu ya'yan
Anti Sha'awa ne. na ce, kai su Buhari ne haka? Suka
zubo min ido alamar a cikin doka suke.
Muka gaisa da Sha'awa da Habiba har na karasa
shiga na yi wa 'ya'yan da suke shayarwa wasa,
Suwaiba ta sunkuyar da kai kasa tayi kamar bata
ganni ba, nima na wuce na fito ban tanka mata ba.
Na kama hanya zan fita saboda jin muryar
Salisusu da nayi, na kalli Mama nayi murmushi na ce

30
Kawu fa ya ce a gaishe kir da kyau-da-kyau, ta ce
madailah.
A tsakar gida Salisusu yana tsugune suna
gaisawa da Babana, ga katuwar kula a gefenshi
alamar shi yazo da ita, sannu da zuwa Yaya, ya dago
ya kalle ni cikin murmushi, Anti ashe kun iso? Na ce
eh.
Ina Baban ba ka zo min da shi ba? Yayi
murmushi, suna nan zuwa. Muka gaisa sosai, cikin
yanayin suruka kafin ya mike ya shiga wurin Inna.
Babana ya kalle ni ya ce min, ga abin karyawa nan
daga wajen Atika.
Nayi murmushi na ce, an gaishe su, amma sai
naci na gida na Anti kafin in ci na wani, dadi ya sake
kama Babana.
Muna cikin haka sai ga su Buhari a guje Suwaiba
ta biyo su tana duka, wai ta ce kar suyi warwaso sun
yi, Baba ya daka musu tsawa kai ku min shiru ku
koma dakinku ku zauna kar kuzo nan ku cika min
kunne da ihu, 'yan jakar uba kawai marasa da'a masuu
abin tsiya. To an koya musu.
Cikin zuciyata na ce, oh oh, Baba kuma sarar da
ya samu kenan? Ko da yake dai ba laifin shi ba ne,
Maman ce ta koya ishi komai yaro yayi, ta ce mishi
wai uwarshi ta koya mishi.
To gashi abin yazo kanta, a wancan lokacin da
take sha'aninta kuwa bata taba tsammanin abin zai

31
koma mata ba.
Salisusu ya yi wa Babana sallama ya tafi, sai
kuma ga dan aika daga gidan Hajiya Aliya, da
manyan kuloli itama abin karyawan ta aiko dashi, ga
kuma na Zubaida shima ya kammala.
Na kalli Babana a hankali cikin natsuwa na ce
mishi, bari in kira su Habiba mu karya tare Baba. Ya
yi maza ya yautsa fuska, kar. ki kira in wadannan
yan jakar uban yaran.
Na sake bashi hakuri kafin na dauko wata
katuwar tabarmar na shifida na leka falon Mama na
ce "Habibah ku fito nan mu karya. Buhai ku ma
kuzo dukkanku.
Na koma sabuwar tabarmar don mu zauna dasu,
tunda sun kasa zuwa kusa da Baba, na ce 'rai dai' wai
in ji kuda, Mowowin Baba wadanda suke komai suka
yi daidai ne, sune yau suka zama babu wata
mu'amalla a tsakani sai na zare ido da mmuzurai.
Na kira Zubaida na nuna mata abin da Atika da
Aliya suka aiko dashi, na ce mata samo wuri ki diban
wa Baba nashi da na Mama da Inna da naki ta ce to,
nayi zaton Mama zata ce ba ta so sai naga tasa hannu ta karba.
Mu ma na Zuzzuba mana har yaran nasa musu
nasa kuci a natse in baku koshi ba sai a kara muku,
suka ce to ita ma Suwaiba na aike mata na kira Sa'a
na ce mata ta kawo mana kunun gyadan da inna tayi.

32
Gaba daya mun suke muna hira har Habiba tana
tambayata mace fa kema ki ka haifa ko? Nayi
murmushi ban yi magana ba, sai kawai naji Babana
yana cewa uh'uh hun, rabin da suka iya kenan, su sami
abin dadi su rufan mishi su rinka ci suna zare ido
suna gwalo.
Amma su su zauna ana su' dakunan auren sun
kasa mugun halin da aka koya musu ya hana su, gaba
daya zaman aure ya gagaresu, sun dawo min gida
sun z0 Sun zama min da:wasu munanan ya'yansu
masu kama da "ya'yan tanda.
Duk ku watse a nan ku bani wuri, yan jakar uba.
Gaba daya su da ya'yan nasu suka watse da gudu,
yuu suka shige dakin Mamna.
Ni kam duk da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login